Showing 171001 words to 174000 words out of 177840 words

Chapter 58 - FITAR TSIRO COMPLETE HAUSA NOVEL BY RUFAIDA UMAR

11 Jul 2024

79140

ya jawo ta yana shaƙar kamshin turarenta na musamman sannan ya hadiye abin da ya yi niyyar yi ya sake ta bayan tsayuwarta ta daidaita. Ƙofar ya nufa ya rufe ruf. Ita kuwa ta nemi wuri ta zauna. Adon fari da ruwan toka aka yi a falon. Ba wani tarkacen a zo a gani, komai na ƴan boko da zamani ne.

"Muje na raka ki ɗakinki sai ki rage kayan nan ki yi alwala ko? Nasan ba a yi sallr isha'i ba."

Murmushi ta ɗan yi ba tare da ta dube shi ba. Shi kuwa ya maida ledojin saman dinning table, ɗakin suka nufa, bayan sun shiga tana tsaye tana kallo, ya riƙota ta baya, lumshe idanu ta yi. Ita har wani tsoro yake ba ta don ta kula gaba ɗaya ma a yau ya sauya tamkar ba wanda ta sani ba. A hankali ya sumbaci gefen wuyanta kamar mai raɗa ya ce.

"Bana son matsawa daga gareki ko na sakan ne."

Kirjinta na bugu ta ma kasa magana, tana ji yana safa da marwa da hannayensa tun daga kafaɗarta har zuwa tafukan hannayenta. Cikin sauri ta janye jikinta ta dube shi da manyan idanun nan da suka ƙanƙance.

"Bari na yi alwalar."

Shi ma duban ta ya ke ba a hayyaci ba, sai kuma ya shafi sumar kansa yana mata murmushi ya soma tafiya da baya-baya a hankali kamar zai faɗi. Babbar riga dama tun a mota ya cire ta wai zafi yake ji.

"Ok, ina jiranki."

Daga haka ya juya ya fice ya rufo mata ƙofar. Yana fita ta ɗan zauna gefen gado. Sai da ta ɗan samu nutsuwa kafin ta miƙe. Rage kayan jikinta ta yi, kai tsaye wanka ta soma yi karo na biyu don tana sane da karatun da Maama ta yi mata kafin su fita wajen dinner. Bayan ta fito ta buɗe dirowar gaban madubi inda Maama ta ce ta mata ajiyar wani abu, turare ne ta gani a kwalba mai ɗan karen ƙamshi. Duk inda Maama ta gwada mata ta shafa hakan ta yi. Tana buɗe wardrobe ta ga kayan da Zaituna ta ce ta fiddo mata na bacci. Wasu jajaye ne masu santsi. Ta cikin siririn hannu gareta kuma ko gwuiwarta ba ta kai ba, ta saman kuwa mai ɗan gajeran hannu. Ƙamshi kayan suke yi na musamman, bayan ta shirya ta ɗora farar laffaya don yin sallar isha'i. Kamar ta tayar ita ɗaya sai ta tuno ya ce yana jiranta. A kokarinta na bin umarni ta fice daga ɗakin zuwa falo. Yana zaune ya shimfiɗa dardumai har biyu, ta kula kaucewa kallonta yake yi, shi jallabiya ce fara a jikinsa. Ya ja su sallah, ƙira'arsa mai dadi ita ya yi, suna idarwa kowannensu ya yi shafa'i da wuturinsa sannan suka yi addu'a gaba daya aka shafa. Dafe kanta ya yi ya yi addu'o'i bisa koyarwar sunnah. Zama ya yi saman kujera yana kallonta tana aikin naɗe dardumai ga kuma faman da take yi da laffayar dake neman kuncewa. Kallonta yake yi daga sama har ƙasa yana wani murmushi, gaba ɗaya jin jikinsa yake babu ƙwari. Ta zo gifta shi kuwa ya kai hannu daidai saitin da ta ɗan maƙale na laffayar ya shiga ja, aikuwa a kokarin ta juyo jikinta don ta yi magiyar ya bari, gaba ɗaya laffayar ta warware ta yi ƙasa, rigar jikinta kuwa har gefen hannun dama na zamewa. Bai ba ta damar magana ba ya janyo ta jikinsa ya ce.

"Haba, kayan sun miki yawa, ji nake kamar ni ne na yi wannan shigar, ai takura kanki ki ka yi. Ko duk saboda tsaro ne?"

Ita sai ta kasa ma magana, ta yi lamo a kan kafaɗarsa tana kici-kicin ɗin kwacewa. Dakyar ta samu ta ce.

"Please ka bari."

Sadauki dake aikin zame top ɗin kayan da ta sa a hankali ya ce.

"Please me zan bari?"

Muryarsa na kashe mata jiki don haka ta lumshe idanu ta sa hannu a ɗaya kafaɗar tasa na hagu da zummar samun madafar da za ta miƙe tsaye. Amma kamar ta kawo kanta, sai da ya yi abin da ya ga dama kafin don kansa ya bari, gaba dayansu babu ƙwari a jikinsu. Da sauri ta miƙe ta soma kokarin daukar laffayarta da rigar baccinta na sama da ke yashe a gefensa ya dube ta.

"Tsaya mu ci abinci kin ji."

Girgiza kai ta yi.

"Ka yi hakuri, ni fa ba na jin yunwa."

Ya yi murmushi kawai, shi yanda ma duk ta zama wata matsoraciya lokaci guda yake ba shi dariya. Haka dai dole ta ci kazar kaɗan ta sha youghurt. Dama shi ba yunwar ke gabansa ba.

Ranar kam Haulatu ta san ta shiga ƙwaryar manya. Da kansa ya yi aika-aikar kuma ya zo yana rarrashi da jinya. Sabuwar ƙauna da shaƙuwa har ma da tausayin juna suka ƙara shiga tsakaninsu. Sadauki na godiya ga Allah da samun Haulatu matsayin mace kamilalla da ta kiyaye mutuncinta har gidan aure. Ita kuwa tana hamdala da samun miji mai ƙaunarta.

Wannan kenan.

Washegari kuwa dangi kowa ya je gidan Amarya da Ango sai ya dawo baki cike da yabon yanda Sadauki ke ririta Amaryarsa. Ɗaiɗaiku ne yake jin nauyinsu ba ya iya kataɓus a gabansu. Kowa sai sam barka da fatan alheri.

***
A gefen Zaituna kuwa, duk iyakar kokarinta na ganin ta kaucewa kaunar Khaleefa abin ya ci tura. A karshe bayan shawara da Umman Haulatu wacce ta ƙarfafa mata gwuiwa ɗari bisa ɗari don a cewarta Khaleefa miji ne da duk wacce ta same shi kuma ta iya takunta za ta yi alfahari da shi, ta amsawa Khaleefa da cewa ta amince da shi. Umma da kanta ta sanar da Maman Zaituna da Hajja bisa hakan da Zaitunar ta roƙa don ita wai kunya take ji, farko ta ji tsoron kar a maimaita ƴar gidan jiya. Ko kuma a samu matsala da Mami. Amma ganin Hajja ta goyi bayan lamarin ta karɓa da hannu bibbiyu tana ta yabo baki yaƙi rufuwa ya sanya ita ma ta bar wa Allah zaɓi.

Sati biyu da bikin Sadauki da Haulatu, Zaituna suka tattara suka koma Malaysia. Kafin sannan, tuni Khaleefa ya kasa hakuri ya tuntuɓi Baba Alhaji, hamdala Baba Alhaji ya dinga yi. Tabbas ko sadda Zaid ya ƙi auren Zaituna, sai da ya ji ya yiwa Sadauki ko Khaleefa sha'awar aurenta, sai dai ba ya son tursasawa wani a cikinsu hakan yasa ya haɗiye kwaɗayin. Shi kansa albarka ya sanya wa lamarin ya kuma ce ya cigaba da neman yardarta kafin sannan zai yi magana da iyayensa maza, kuma an ji abin da mahaifinta zai ce. Da haka aka bar maganar ba a kara yin ta da wasu ba gudun abin da zai je ya zo.

***
Bayan Shekaru Uku...
Babban falon saukar baƙi na ɓangaren Alhaji Ridwan, cike yake da matasan jikokin Marigayi Amadu, Baba Alhaji, Marigayi Baba Dakta, Marigayi Baba Mu'azzam da kuma autarsu Hajja.
  A sannan yaran Alh Bello S Malumfashi, Baba Alhaji da Hajja ne kaɗai suka rage a doron ƙasa. Hajja na fama da matsalar ƙafa wanda ko fita ba ta iya yi. Sai faɗanta ya fi na baya, abu kaɗan ka yiwa Hajja za ta hau sababi wani lokacin ma idan a cikin ƴaƴanta ne har hawaye take ta ce wai saboda girma ya kama ta sun bar yi mata biyayya. Shi kuwa Baba Alhaji rikicin tsufa sosai ya kama shi, yanzun sai ya yi sallah ko wani uzurin, anjima ya ruɗe kan lokacin sallah ya wuce bai yi ba, nan da nan zai ƙara sabuwar alwala ya hau ramuwa. Hakanan kowa ke haƙuri da su a na lallaɓa su.

Musabbabin haɗuwan jikokin maza bai wuce na ƴar walimar sunan ƴan biyun Zaituna da Khaleefa, sun samu yaransu biyu mace da namiji a lokaci guda bayan shekara ɗaya da aurensu. Namijin ya ci sunan Baba Alhaji, wato Usman sai macen da aka sanya mata suna Zakiyya (Maama), ana kiransu da Amir da Amira.

Fuskokin kowanne a matasan nan cike da fara'a, abin burgewar bai wuce yanda suka haɗe kai ba. Zaid da Sadauki na zaune kusa da juna inda suke buga musu dangane da hirar siyasa. Khaleefa da su Mu'az kowa na mara wa jam'iyyar da yake yi baya. Can kuma bayan hirar ta lafa ne Sadauki ya ɗan ja guntun tsaki.

"Kai nifa yunwa nake ji, wai matan nan ko sun mance da mu ne, su fa idan suka haɗu hirarsu ba ta ƙare ba ce."

Faɗin Sadauki yana ƙarashewa da ɗan yamutse fuska. Khaleefa ya yi ƴar dariya.

"Sorry ɗan uwa, mun yi waya da Jannat, yanzu za'a kawo."

"Ai da ka ce mishi sai anjima, kai fa ba don kana motsa jiki ba na tabbatar ko tashi ba za ka iya ba idan ka ci abinci tsabar ƙiba. Gaskiya Maman Suhail na ƙoƙari." Faɗin Zaid kenan yana duban Sadauki cike da zolaya. Aka yi dariya, Mu'az ya cafe.

"Toh kai da shi ɗin ai duk tafiyar ɗaya ce. Gwara bestyna ma a kanka, ji fa tumbin da ka ajiye."

Zaid ya ɗan shafi ƙaramin tumbinsa yana ɗan hararar Mu'az. Sadauki dai murmushi kawai yake don dagaske yunwa yake ji. Sallamar su Bebi ƙanwar Zaid da wasu ƴanmata ɗauke da kulolin abinci ya sa suka amsa da gyara zama. Haka aka dinga jera musu bayan an shimfiɗa ƙatuwar leda ta cin abinci. Sai da suka yi serving din kowa sannan suka fice.

***
A falon Hajja kuwa, Zaituna na tsaye tana hoto da ƴan uwa da abokan arziƙi, ta ci ado ta yi shar abinta, har a lokacin fuskarta bai gama komawa daidai ba duk da cewa a sannan satinta biyu da haihuwa. Ta kai duba ga Safina dake gefenta tana kokarin goya ɗanta Safwan a baya tana mita, shi kuwa yaron sai ihun kuka yake.

"Ya dai? Wai har yanzu yaron nan bai yi shiru ba? Don Allah ki watsa mishi ruwa ko zafi ne ya ishe shi."

Safina ta narkar da fuska kamar ta yi kuka ta ce.

"Anti ya zan yi? Ni na san ko wanka na masa da wahala ya bar ni na yi sakat. Allah kuwa wajen Babansa zan bayar a kai shi."

"Kunto shi, babu inda za'a kai shi suna cin abinci ya hana mijina ci yanda ya kamata, ba ya son kukan yara." Haulatu kenan mai maganar, ta sa hannu ta karɓe Safwan ta nufi sama da shi. Nan ta bar su daga mai dariya sai mai kiran wato ita mai miji.

Ita kuwa daƙyar take takawa ga haye saman sakamakon tsohon cikin da ke jikinta, kai tsaye ta nufi tsohon ɗakinsu ita da Umma, wanda a yanzun ya zama na zaman jegon Zaituna duk kuwa da irin dagiyar Khaleefa na cewa matarsa ba za ta gida wanka ba, amma Hajja suka kafe kan lallai ya bari ta je tunda haihuwar fari ce kuma har yara biyu. Kaya ta cirewa Safwan ta shiga banɗaki ta wanke shi tas ta fito da shi, aikuwa tun ma kafin ta gama goge masa jiki ya soma gyangyaɗawa, murmushi ta yi sadda ta jawo jakar kayansa da Safina ta zo da shi, ta bude ta zaɓo masa marar nauyi riga da wando sai famfas. Jikin ta shafemasa da hoda, kafin ta kai ga sanya masa kayan sai ga Safina ta faɗo ɗakin riƙe da hannun Suhail wanda ke faman rigima wai shi bai ga Maminsa ba.

"To ga ta can, maza jeka."

Jin haka yasa Haulatu saurin sanya yatsa a baki alamar ya yi shiru. Yaron bai fi watanni biyu ya rage ya cika shekaru uku ba a duniya, ɗan ɓulɓul da shi ga kumatu masha Allah. Fari tas har wani ja fatarsa ke yi, ya sha kwalliyar shadda light blue kansa cike da suma. Kana kallonsa ka ga Sadauki don Momi Nuratu ma cewa ta yi babu ta inda ya bar ɗanta da yana ƙarami.

Suhail ya kama leɓansa da yatsun hannunsa yana mai alamar shiru kamar yanda Maminsa ta umarce shi. Safina baki ta saki ma da ganin ɗan nata ma bacci. Wato dai ta yarda dagaske har yau ba ta iya raino yanda ya kamata ba. Sai da Haulatu ta kammala shirya shi sannan ta gyara masa kwanciyar, zasu fice kuwa ya motsa, a dole Safina ta goye shi, babu rigima ya koma baccinsa.

"Kai wallahi sai yanzu na samu nutsuwa, amma duk ya hana ni sakewa na yi sha'ani."

Harararta Haulatu ta yi, ita kuwa Safina ta danne dariyarta, ba na komai bane sai yanda hancin Haulatun suka kara buɗewa. Gaba ɗaya kamanninta sun sauya.

"Allah ya baki hakuri, ranki ya daɗe Mrs Abeed."

Murmushi ta yi, duk a yanayin da ta tsinci kanta matuƙar za ka jingina sunanta da na mijin nata ba za ta iya haɗiye daɗin da hakan ya ke mata ba. Sun shekara tare amma kullum soyayyar nan tamkar sabuwa fal a leda take jinsa. Eh, su ma ajizai ne tunda ƴaƴan Adam ne, amma kuma sukan yi kokarin mallakar kansu zuƙatansu a yayin fushi ta hanyar yin shiru ko kuma ita da take ƙasa da shi ta lallaɓa ta hanyar kwantar da kai komai ya wuce, ko kuwa shi idan ya san laifinsa ne, ya dinga abubuwan da zai burge ta kamar siyomata abin da yasan tana so da kuma nuna ƙauna a zahiri da sakin fuska.

"Wai ke ba kya gajiya da soyayyar nan? Shekarun fa sun soma tafiya."

Tambayar Safina ta sanya Haulatu yin murmushi karo na biyu.

"Naki wasa ne yarinya, da alama Abban Safwan bai gama kama ki ba har yanzu, na maki uzuri don ba lallai soyayyar ta kasance irin namu ba."

Safina dariya kawai ta yi, tabbas soyayyar Haulatun da Abeed Sadauki na burge kowa ma, abinsu tsaf gwanin ban sha'awa sai fatan kar Allah ya ba wani ko wata ikon shiga tsakaninsu.

"Allah ya bar ƙauna toh."

Ta maida mata martani, Haulatu ta amsa da amin. Suna karasawa farfajiyar gidan inda aka sa tamfol manya aka zuba kujeru, kai tsaye inda su Umma da Maman Zaituna da ma sauran iyaye ke zaune Haulatu ta nufa ita da Safina, hango Malama ne ya sanya su ƙarasawa don ba su gaisa da ita ba. Gaishe su suka yi, Haulatu na kokarin ɗan russunawa Malama ta riƙo hannunta.

"A'a, rufa mana asiri mana Haulatu, ki dinga bi a hankali." Cike da kunya ta ɗan gyaɗa kai tana murmushi.

"Ai fa, ni sai na ga ma kamar naƙudar kike yi." Faɗin Haj Hadiza wacce zuwa lokacin gaba daya tamkar ba ita ba, ta sauya ta kuma nutsu, musamman da aure ya ƙullu tsakanin Fahima da Hamza ɗan shaye-shayen da ba ta so, ƙarshe ma ashe zaman ba mai tsawo ba ne, ya rasu ya bar Fahima da ciki wanda zuwa lokacin ta haihu, ta kuma girgije abinta ta koma makaranta, gaba ɗaya ita ma ta yi sanyi ta cire komai a ranta ta yarda da ƙaddara.

"Ina alamun naƙuda a nan Hadiza, kawai dai koda ba ta soma ba, haihuwar dai na hanya, fatan Allah ya raba lafiya." Cewar Momin Mu'az kenan fuskarta cike da walwala. Haulatu ta ɗan kalle ta sai kuma ta musu sallama ta wuce tana tunani, idan aka ce mata akwai ranar da za ta buɗi idanu wai Momin Mu'az za ta nuna mata ƙauna za ta ce ba haka ba amma kuma ga shi nan a yanzun sun samu kusanci sosai. Babban dalilin sauyawar Momin Mu'az bai wuce ganin yanda duniya ta juyawa Mamin Khaleefa baya ba. Hajiya Rahma ta dauki wuƙa ta burmawa cikinta, ma'ana ta tonawa kanta asiri duk a kokarinta na hana auren Umma da Barr Dawud. Asirin da ta ƙullo da zummar ya faɗawa Umman, sai ya koma mata, nan ta hau ciwon fidda ruwa da ƙuraje daga gabanta, a lokacin ne kuma tana kuka ta faɗi duk abinda ta aikata tana neman gafara, amma Barr Dawud yace ta tafi gida. Saki ɗaya ya yi mata har yau da aka shekara biyu bai ƙara waiwayarta ba, a ƙarshe ta warke ta samu lafiya sai dai duk da haka da irin magiya da nacin da ta dinga yi bai sa shi maido ta ɗakinta ba. Ita kuma ta rantse nan duniya ba za ta ƙara wani auren ba idan ba shi ba. Haka take waya su gaisa da Umma, tun tana roƙonta akan ta sa baki ta dawo ɗakinta har ta haƙura don Barr Dawud ya ce ma Umma kar ta sake ta ƙara yi mishi zancenta. Wannan babban dalilin, da kuma tonuwar asirin cewa da Momin Mu'az suke yawon gidan bokaye ya sa gaba daya Momin Mu'az ta tsorata ta kuma tuba ta yi alƙawarin ba za ta ƙara ba. Ita ma dai sai da ta ɗanɗana kuɗarta don har girkinta daina ci Abban Mu'az ya yi a ƙarshe kuma komai ya wuce ya yafe mata da manyan sharuɗɗai.

A yanzu haka Jannat tana auren wani hamshaƙin ɗan siyasa suna zaune a Abuja, haihuwar Zaituna yasa ta zo takanas da yarinyar da take goyo Hidaya. Tsakaninta da Haulatu babu komai face zumunci. Fa'iza ma ta haƙura tun sadda Khaleefa ya auri Zaituna, itama ta samu mijinta ɗan Katsina, tana aure da zama a garin.

Haka Haulatu ke ta tunanin rayuwa har ta samu wuri ta zauna ta yi shiru ba tare da ta kula ma da wanda ke gefenta a zaune ba.

"Haulen Hajja, ko abin ya zo ne?" Ta ɗan waiga, ganin Anti Mabruka da Maama ya sa ta sakin fuska da murmushin yaƙe, shakka babu tana ɗan jin ciwo sai dai bai yi ƙarfi ba sosai.

"Lafiyata kalau Anti, Maama, ban ga Ashraf ba tun ɗazu."

Ta maida akalar zancen ga Maama.

"Ya bi Babansa, kinsan shi har yanzu ba son zama a taro yake ba. Gwara su yi gaba na samu na huta nima."

"Ke dai Maama kina ban mamaki, a duniya na kula bakya son raino. Kuma naki kike yiwa haka, amma ɗan kowa zai rayu hannunki lafiya kalau." Faɗin Anti Mabruka kenan tana kokarin buɗe murfin robar ruwa bayan kammala cin abinci.

"Nawa nake raina, Ashraf naku ne, ku ya kamata ku ji da shi."

Fadin Maama kenan. Murmushi Anti Mabruka ta yi. Haka suka hau hirarsu, Haulatu na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login