Showing 30001 words to 33000 words out of 177840 words
akan ya kai masa ni mu yi magana kada mutuwa ta ɗauke shi, amma firr ya ƙi. Sau biyu Ɗanmutuwa ya zo duba shi, kuma duk zuwan shi ne ke matsawa abokn Ɗanmutuwar kan lallai su ce ya zo yana buƙatar ganinsa. Daƙyar ya samu ya zo. Zuwan ƙarshe ne kuma har kuka ya yi masa kan ya taimaka ya kawo ni, shi ne muka je. Na ce meyasa bai je asibiti ba, ya yi ƴar dariya kawai ya ce min an je asibitin ya fi a ƙirga amma sun ce ba su gane mai ke damunsa ba. Haka na wuni zaune muna hira da Baba wanda ke magana daƙyar, ya ga Haulatu amma koda na miƙa masa ita don ya ɗauka girgiza min kai ya yi ya nuna aa. Ya cemin itama kamannin kakarta ta biyo. Sai da dare ya yi, Falmata tuni ta kwanta, Baba ya ciro wata baƙar leda ya damƙamin, ya ce wannan ko babu shi a raye, zai taimakamin na je ga mahaifiyata ko danginta, kuma yace duk radda na samu zuwa na nemar masa gafararta amma bai faɗamin dalili ba kawai sai na sa a rai watakila dai saboda halin rayuwa yau da gobe akan saɓawa mutum.
Allah ya ƙaddara ina garin Mahaifina zai rasu domin ba a wayi gari da shi ba, cikin dare ya rasu babu wanda ya sani daga ni har Falmata sai da gari ya waye. Kukan da na yi a lokacin ba zai misaltu ba, na shiga tashin hankali irin wanda ban taɓa zato ba. Anan ne Ɗanmutuwa ya zo domin mu tafi, jin Baba ya rasu shima na ga jikinsa a ɗan sanyaye. Ko ba komai na san, ya tuna da kaunar da Baba ya nunamasa ko dai wani abin da shi ya bar wa kansa sani. Sai da na ƙara sati guda cif a garin Kaduna kafin mu tattara mu koma Kano. Sai bayan komawarmu ne na bude ledar naga abin hannun azurfa da hoton Mahaifiyata, a bayansa an rubuta adireshi da kuma cikakken sunanta.
Shekarar Haulatu biyu a duniya, muka bar unguwar da muke dalilin makwaftan da Ɗanmutuwa ya ce suna shigar masa hanci da ƙudundune, sun saka wa rayuwar gidansa idanu kan kawai watarana yana dukana wani makwafcinmu ya buga masa ƙofa ya ce matuƙar bai bari ba zai haɗa shi da hukuma. Shi ne silar komawarmu inda muke a yanzu. Ya cemin dai kyautar gidan ma aka ba shi. Anan ne komai ya ƙara dagulewa na rayuwar Ɗanmutuwa, ba shi da aiki sai tara majalisar ƴan daba, mun taso a rayuwa da babu makwaftan da ke raɓar mu bisa tunanin mu ɗin tsoffin ƴan bariki ne. An sha Haulatu ta fita waje wasa ta dawomin tana kuka wai yara na ce mata shegiya. Yana daga cikin dalilan da yasa na hana ta fita wasan. Zama a lokacin ya ƙara tsananta, Ɗanmutuwa ya bar ba ni ko sisi, ni kuma duk sana'ar da nayi, daga na fara na soma samun abin rufawa kai asiri, sai daga baya a daina zuwa siya wai ba za su ci bin hannun karuwa ba.
A ƙarshe na yanke siye da siyarwar abinci a kasuwa, shi dama Ɗanmutuwa koda na ce masa ga abinda zan yi cemin ya yi shi fa ko wasu mazan ma zan bi ko a kwalar rigarsa. Haka muke rayuwa da Haulatu, tun tana ƙarama take ganin yadda mahaifinta ke dukana, wannan ne silar jefa tsanarsa a zuciyarta. Tun ba ta mallaki hankalin kanta ba take cemin ita dai mu gudu daga gidan nan, ita ta tsani mijina domin tun a bayan ma ba ta kiransa da suna Baba. Kai ko shigowa gidan ya yi suka yi kiciɓus a hanya zai ɓallamata harara ko kuma ya sa ƙafa ya shure ta yace wai ta kafe shi da mayun idanunta.
***
Daga haka Umma ta labartamusu duk abin da ya faru dab da za su bar Kano zuwa Katsina. Hajiya Babba ta girgiza da jin kalar rayuwar da ɗiyarta ta yi, koda dai dama a bariki ta bar ta, ta sani komai zai iya faruwa gareta. Jikinta ya yi mugun la'asar, anya kuwa haƙƙin Na'imatu zai bar ta? Lallai da gaskiyar Alhaji da yace ta godewa Allah ma da ya sa tana da rabon ganin Na'imatu har ta nemi gafararta. Umma kuwa kallon su Baba Dakta ta yi karo na barkatai ta ce.
"Na kawo mata jikarta, koda ace ni ba zan samu karɓuwa a wurinta ba. Ta taimake ni kar rayuwar ɗiyata ta wulaƙanta irin yadda nawa rayuwar ya tafi a wulaƙance. Zan iya sadaukar da komai akan samar da farin ciki da kwanciyar hankali a rayuwar ɗiyata."
"Um um, bari faɗin haka Na'imatu, ai nan da kike gani, kin zo kenan da yardar Allah. Shi kuma maigidan naki duk inda ya shiga a faɗin garin Kano ko wajenta, in sha Allahu zamu neme shi a raba auren sannan ya fuskanci hukuncin abin da ya shuka maku a rayuwa. Ai da kai da kaya duk mallakar wuya ne, yau ko Asma'u ba ta raye, mu ba zamu taɓa gudunki ba ballantana kuma ga ta nan a zaune da ranta da lafiya cikin iko na Allah. Abin da dai ya faru ya riga ya faru sai dai a kiyayi gaba. Ki kwantar da hankalinki, ina maki alƙawari kan cewa babu wata matsala da za ki ƙara fuskanta kwatankwacin ta baya."
Baba Dakta ke wannan kalamin cike da kwantar da murya. A ƙarshe ya ce Baba Saude ta ja su Umma ɓangaren Hajiya Babba su huta su ci abinci. Haulatu ta dube shi.
"Don Allah Baba kar a kai mu ɓangaren matarnan, kai ina ne ɓangarenka? Nan nake so."
Umma ta dubi Haulatu, ita kam a ko'ina sai ta kwaɓa magana. Hajiya Babba kuwa hawaye take yayinda ta kai hannu da zummar riƙo na Haulatun aikuwa ta yi wani irin fisgewa tana huci.
"Wallahi kar ki ƙara gangancin riƙe ni. Yanda kika tsani Ummata, nima na tsaneki kuma har ki mutu ba zan yi fatan Umma ta yafemaki ba."
"Ke Haulatu, yimin shiru." Umma ta furta cike da murya mai nuni da rauni duk a kokarinta na son tanƙwara Haulatun.
"Rabu da ita Na'imatu, ko mene ne ni na jazawa kaina. Don Allah ki yafemin Na'imatu. Na yi kuskuren da ba zan iya maida hannun agogo baya ba ballantana na gyara shi. Na bar maki tabon da zai yi wuyar goguwa a tarihin rayuwarki, haƙiƙa ban cancanci ki kira ni da sunan uwa kuma mahaifiya gareki ba. Ki yi hakuri ki yafemin kin ji?"
Tun soma maganar Hajiya Babba, Umma ta sunkuyar da kanta ba tare da ta ce uffan ba. Ta fi mintuna biyu ba ta ce komai ba, Haulatu kuwa sai hararar Hajiya Babba take tana ji ba don Umma ta kwaɓe ta ba, to fa babu abin da zai hana ta gasa mata maganganun da za su hana ta bacci. Wani tunani ne ya zo kanta, ai idan ma suka bar sashen Hajiya Babba, babu damar da za ta dinga ƙuntata mata a gidan tunda dai ta lura da tsarin gidajen nasu, za'a iya kwana da wuni ma ba'a sanya juna a ido ba. Wannan dalilin ne yasa Alhaji na ɗan saka baki da zummar tausar Haulatu akan ta zauna sashin kakarta, idan ma ba ta so duka ɓangarorin ta duba wanda ya yi mata, sai su zauna a ciki. Nan take ta ce ta amince da zama ɓangaren Hajiya Babbar. Ita dai Umma ba ta ce komai ba don da alama ta ɗan soma karaya. Wannan raunin nata shi Haulatu ba ta so, sai mutum ya gama cutar da ita a lokaci guda idan ya yi ƴar murya sai zuciyarta ta wanku. Suka miƙe har Baba Saude suka nufi ɓangaren Hajiya Babba inda suka bar ta tare da yayyunta suna ƙara yi mata faɗa da kuma nasiha.
A hanyarsu Haulatu sai cin alwashi take a ranta, ta rantse zaman da za ta yi a gidan nan sai Hajiya Babba ta raina kanta. Sai ta san cewa ita din jikar Saleh Maikalangu ce, ko ba komai ta haɗa iri da barikin tunda dai haka take kallonsu.
Baba Saude ta kai su wani ɗaki mai kyau da girma, babban gado ne a cikinsa sai kuwa bandaki. Ga na'urar Ac ga kuma fanka. Ce musu take yi.
"Anan Hajiya Nafisa ke sauka idan sun zo daga Malaysia. Ai ita can take aure amma nan kusa za su zo za'a yi bikin jikan Baba Dakta."
"Kenan idan ta zo kina so ki ce zamu bar ɗakin ko?" Fadin Haulatu tana kallonta. Umma ta harare ta, ta yi kamar ba ta gani ba.
Baba Saude kuwa ta yi ƴar dariya.
"A'a ƴar nan, ai akwai wasu ɗakunan har ma a can ƙasa. Ku huta ku yi sallah, bari a haɗo maku abinci."
Tana kai wa nan ta fita. Hajiya Rabi ta dubi Umma dake zaune gefen gado bayan shigar Haulatu bandaki ta ce.
"Kai Na'imatu a gaisheki, gaskiya kin ga rayuwa. Kin yi kokari ba kadan ba. Allah yasa ƙarshen wahalar kenan. Amma fa da alama wannan ɗiyar taki ba ta huce ba."
Umma ta ɗan yi murmushi ba tare da ta ce uffan ba. Ita kadai ta san me take ji a ƙirjinta, tun tahowarsu har wani jiri ke neman ɗibarta, sam ba ta jin dadi ta sani. Akwai abinda ke mata ciwo a jiki tabbas, ga ciwon kai dake damunta. Wannan ya sa ba ta son magana. Ita zancen ma gaba ɗayansa ya ishe ta. Fitowar Haulatu ya sa Hajiya Rabi ta bar surutan da ko kusa ba shiga jikin Umma suke yi ba, itama ta faɗa banɗakin don kama ruwa da yin alwala don lokacin ɗaya ma ta gota.
***
"Which kind of nonsense is this?"
"Haidar anya ba ka soma abar ba?"
"Please dagaske? Kar fa ku sa a gan ni a Babban gida yanzu?"
Ire-iren waɗannan tambayoyin har m da masu aiko ƴan aljanun sitikoki a cikin whatsapp group ɗin nasu na Zuri'ar Bello S. Malumfashi. Labarin zuwan Umma da Haulatu ne, Jabeer da Haidar suka fesa musu. Nan fa maza da mata aka fito aka yi caa ana tattaunawa. Rantsuwar da suka yi ce ta sanya aka yarda. Nan fa gulma kowa ya ɗauka, abin ma har ya ba wasu haushi musamman jikokin Hajiya Babba, suka fice daga gidan. Ya zame musu tamkar dai fitina. Masu cewa mugun bakin da Hajiya Babba ta yi musu saboda tana ganin suna aikata ba daidai ba a rayuwa shi ne ya koma kanta, manyan ciki kuwa na kokarin su ga an kashe zancen. Akwai wacce ma aka tashi aurenta da wani da uwa ta nuna ba ta so ita a barta da zaɓinta, nan Hajiya Babba wai ba irin zagi da cin mutuncin da ba ta yi gareta ba, har da cewa in sha Allahu sai ta haifi kangararriyar ƴa irinta. Aikuwa jin wannan labarin har da muryarta ta aiko tana guɗa, tana fadin gashinan ta haifi yaranta har biyu salihai, amma Allah ya nuna iko akan Hajiya Babba. Maganar ba ta mutu ba sai da labari ya je kunnen manyan jikokin gidan su hudu wadanda ko group din ba sa ciki. Nan da nan ɗaya a cikinsu ya danna kira ga ɗaya cikin wadanda aka ce su ne admins na gidan ya ci musu mutunci kafin a samu a bar zancen. Aka kuma rufe gidan ta yadda babu wani ko wata da zai iya magana a ciki bayan admins.
***
Ƙarfe uku da mintoci, tuni gidan ya soma ɗinkewa da manyan iyaye da ma wasu a jikoki.
Yara biyar na Alhaji Bello S Malumfashi, Allah ya albarkace su sun hayayyafa. Kafin rasuwa Amadu, ɗansa na farko, yana da yaransa bakwai cif waɗanda matan suka rinjayi mazan, maza biyu ne sai mata su biyar. Uku a cikin matan na tare da iyalinsu a nan birnin Katsina yayinda biyu ke aure a Malumfashi. Iyaye mazan kuwa, su biyun duka suna da nasu ɓangaren a Babban gida, Alhaji Ridwan wanda ya bi sahun mahaifinsa ya zama cikakken ɗan kasuwa da har yake fita ƙasashen waje sarin kaya, sai ko ƙaninsa Alhaji Yusuf da suke kira Baban kowa saboda son jama'a irin nasa. Shi kuwa yana harkar chanji na kuɗaɗe ne kafin ya samu karayar arziƙi sai dai hakan bai sa yan uwansa kasa yin tsayin daka wajen ganin sun yi iyakar yin su na kyautatawa iyalinsa ba. Sau wajen uku ana ba shi jarin amma abin ba kamar baya ba, dole ya rungumi ƙaddararsa.
Mu'azzam kuwa mai bi ma Amadu, shi Allah bai yi shi mai yawan yara ba a duniya. Yaransa uku. Namiji ɗaya ne, Barista Dawud sai mata biyu. Nuratu (mai sunan mahaifiyarsu ake kiranta Mami) an musu auren zumunci da Alhaji Ridwan, sai ko Aishatu mai auren wani babban Farfesa a garin Kano.
Usman wanda shi ne a yanzu suke kira da Alhaji, yana da yara biyar tare da Bilkisu wacce suke kira da Nene. Biyu sun rasu tun ma kafin su kai ga girma sai uku da suka rage. Hajiya Zaituna, mai auren wani babban soja a garin Kaduna, sai Engr Faisal dake zaune da iyalinsa a can gefe guda cikin Babban gida, sai ko Malama Safiyya. Ita mijinta ya rasu ya bar ta da marayun yaransu huɗu wadanda duk sun zama matasa, tana zaune a unguwar Tudun Matawalle. Sam ta ƙi yarda ta yi aure duk da cewa ba shekaru ne da ita na a zo a gani ba.
Suleiman, da suke kira Baba Dakta kuwa. Yaransa biyar a duniya da matarsa Maijidda. Ɗiyarsa ta farko ita ta ci sunan Hajiya Babba, wato Asma'u ake kiranta Husna, yara kuma su ce Umma, tana aure a garin Kaduna itama. Sai mai bi mata Dakta Hashim. Shi kadai ne a mazan da ke cikin garin Katsina, ke rayuwa a muhalli na daban bai yi gini a babban gida ba duk kuwa da cewa gidansa babu tazara sosai da nan din. Zakiyya tana zawarci sanadiyyar rabuwar aurenta da mijinta, yaranta uku duka su na hannunta. Maryam kuwa aure take a Daura. Sai autar Baba Dakta da har a sannan Allah bai kawo miji ba, shekarunta talatin da takwas a duniya, Mabruka suke kiranta da Anti. Ita da Zakiyya duka su na zaune a ɓangaren Baba Dakta sai dai wasu lokutan tamkar su na ganin hanjin juna, sam ba su jituwa duk kuwa da girme matan da Zakiyya ta yi da shekaru kusan uku ma.
Asma'u kuwa, wato Hajiya Babba. Idan ka cire Na'imatu, akwai Nafisatu dake ƙasar waje, sai Hadiza mai auren wani tsohon ɗan siyasa a cikin Katsina sannan Bello mai sunan Abba wanda ke aikin Custom, yana zama a Yobe tare da iyalinsa.
Waɗannan a taƙaice su ne suka haifar da zuri'a mai girma ga Marigayi Alhaji Bello S Malumfashi da Hajiya Nuratu.
Su biyar ɗin, su ma sun gina rayuwar yaransu cike da tsari na ilimin boko da arabi har suka girma suka ƙara bunƙasa zuri'ar ta hanyar haifar musu jikoki masu jini a jika.
Daidai gwargwado kowannensu yana taƙama da kuɗi, hakan ya sa idan wannan ya kawo tsarin wani gyara a gidan yau, sai idan an kwana biyu wani a ciki ya kawo nasa shi ma. Ga matasan jikokin kuwa, burin kowannensu su yi abin bajinta da burgewar da zai faranta ran iyayensu. Ga su nan Allah ya halicce su da baiwar kyau na fuska da ma na gangar jiki.
Manyan matasan gidan kuma jikoki masu ji da kai ga aji da kuma uwa uba kuɗi. Su huɗu ne cif, kowannensu harkar gabansa kawai yake yi, ba su fiye shiga harkar juna ba. Idan ma wani abin ya faru, aka ce wancan ya tsawatar toh wani a ciki ba zai sanya baki ba. Haɗuwarsu ma kan yi wuya a wuri don ba su da lokacin shiga sabgogin gidan. Idan kuwa iyayen ko kakannin na buƙatar ganinsu, sai ko sun sanar musu a waya kan su shigo don dukkansu suna da gidajensu ba kuma sa sha'awar rayuwa a cikin gidan. Ƙarshen boko dai su ne. Sauran jikokin gidan har sunaye na daban suka sanya musu. Ƴanmatan kuwa da aurensu bai haramta ba, nan duniya kowacce da wanda take hari a ciki duk kuwa da cewa biyu a cikinsu ma suna da aure amma ba su da babban burin da ya wuce su kasance cikin masu sa'ar auren ɗaya a ciki.
Wannan kenan.
***
Duk wanda ya shigo gidan babu inda yake fara zuwa sai ɓangaren Alhaji saboda anan ne Haidar da Jabeer suka ce an haɗa taron. Sai dai duk wanda ya shiga sai ya ga babu kowa face Alhajin, kuma kana shiga zai zaunar da kai. A haka har ya fahimci tabbas labari ya je ga jikokin gidan. Ya kuma yanke dama zuwa bayan Magriba za'a haɗa taro a sanar da kowa halin da ake ciki. Na nesa kuwa, sai a ba su labari. Ya dubi matasan mata da maza dake zaune a falon nasa.
"Ku tashi ku je, mun yi waya da iyayenku bayan Magriba kowa ya zo nan akwai muhimmiyar magana da za'a yi."
Wata budurwa baƙa mai kakkauran jiki, tana sanye da riga da wando na Pakistan, ta rufe kanta da hula, ta ɗan taɓe baki.
"Atoh, gwara dai a yi ta ta ƙare Kakus, don a bambance tsakanin aya da tsakuwa."
Ta ƙarashe tana ɗan yin dariya ta rainin hankali lokaci guda tana satar kallon gefen wata matashiyar budurwa dake fidda hawaye. Ranƙwashi ta ji a saman kanta, ta juya ta kalli mai wannan aikin. Yayanta ne wanda daga shi sai ita a gidan Engr Faisal. Shekara ɗaya ya ba ta wannan ya sa ta fusata kuwa ta miƙe ta kai masa duka, nan za su fara kokawar da suka saba Alhaji ya yi musu tsawa.
"Bana son shashanci, duk ku tashi ku fice daga ɗakin nan, ba kuma na son na ji koda wasa kun aikata wani abu da zai ja magana. Ku yi hakuri komai za ku ji zuwa bayan Magriba, kai