Showing 165001 words to 168000 words out of 177840 words

Chapter 56 - FITAR TSIRO COMPLETE HAUSA NOVEL BY RUFAIDA UMAR

11 Jul 2024

79149

Malumfashi da amaryarsa Haulatu Ibrahim Khalil. Daidai lokacin Haulatu na kan darduma, ta idar da sallar Azahar, guɗa ya karaɗe sashin Hajja, ga kuma su Safina da sauran ƴan matan dake ɗakin ciki har da waɗanda a baya kallo ma ba ta ishe su ba, yanzun kuwa ta samu mutuncin darajar Sadauki. Da yawansu tun ma ba ta san ya gidanta yake ba sai santi suke suna bada labari. Cikin waɗanda ke wurin har da su Zuhra ƙanwar Sadauki, sosai ta shigo ake damawa da ita kamar wasu sa'anninta. Dama can ba ta da wata hujja mai ƙarfi na ƙin Haulatu.

Mikewa ta yi tsam ta tada kabbara ta kawo nafila raka'a biyu, dole suka rage hayaniyarsu, ta jima cikin sujjada tana addu'o'in nemawa aurensu albarka da roƙarwa mahaifinta gafara da shiriya, har ma da ingantacciyar rayuwa da ma gamawa da duniya lafiya ga Ummanta sannan ta ɗago ta yi sallama. Tana miƙewa tsaye suka shiga guɗa da yin kanta da shewa da zolaya iri-iri. Ita rabonta ma da Angon nata tun safiyar juma'ar da ya kira suka gaisa, ba su ma samu yin wata magana mai tsayi ba suka yi sallama zai je hotel ɗin da suka sauke baƙinsa da suka zo daga Abuja. Wayar kuwa tun a lokacin ma ta kashe ta ba Hajja ajiya.

Manyan iyayen ne aka shigo aka ja ta zuwa falon ƙasa, babu hawaye ko ɗigo a fuskarta, sai dai sunne kai da ta ke faman yi. Jikinta duk ya yi sanyi, haka aka shiga hotuna bayan an zaunar da ita an yi guntuwar nasiha da addu'a. Ana cikin hotunan ita Haulatu ma sai neman inda za ta ga Ummanta ta ke yi, sai da ta gaji ta sa Radiya taya ta nema. Lokacin ne shi ma ango da abokansa suka shigo. Tsoffi aka shiga rangaɗa guɗa tun daga waje da kuma kirari. Sai da ta ji ƙirjinta ya buga jin da ta yi ana kira Angon Haulatu. Daidai sadda suka shigo a hankali ta ɗaga kanta ta kalle su. Khaleefa da wani abokin Sadaukin ne a gaba, sai shi da ke a bayansu. Ya shigo fuskarsa sai wani annuri ta ke yi yana zabga murmushinsa mai bayyana fararen haƙoransa a waje, mutumin da takan jima ba ta gan sa da hula a kai ba, yau kam ya sha hularsa Tangaran. Farar shaddarsa sai wani sheƙi ya ke yi. Shi ma idanunsa ya faɗa cikin nata, sai da ya ji tsigar jikinsa na tashi, kusan a tare suka janye ƙwayoyin idanunsu daga na juna.

"Mrs Abeed, me ku ke ci na baka na zuba? Da kai da kaya duk mallakar wuya ne fa."

Ta tsinci muryar Zaituna na mata raɗa, ai kuwa ta yi saurin sauke kanta tana wasa da zoben da Sadauki ya ba ta murmushi dauke a saman fuskarta. Zaituna ta mike daga kusa da ita ta ja baya tana dariya har tana karo da mutum, da saurinta ta juyo, suka hada idanu ya yi mata murmushi. Sai itama ta maida masa martani.

"Abu Affan, yi haƙuri."

Har wata ajiyar zuciya ya sauke.

"Ba komai, please ki dinga rufe jikinki. Na kula ba kya son yafa mayafi."

Yana faɗin haka ya yi gaba ya bar ta da binsa da kallo baki sake. A hankali ta kuma ɗan bin jikinta da kallo, sai kuma ta ɗan tura baki. Toh wai shi mene ne ma laifin shigarta? Atamfarta chiganvy ta sha aikin stones a ƙirjin, ya fiddo surarta ta kuma yi kyau ga kwalliyar da aka yi mata a fuska, ta ɗan kalli sauran dake wurin babu mai mayafi a ƴanmatan sosai sai ko kalilan a ciki. Toh don me zai matsa mata?

'Ko kuma kishinki ya ke ne?'

Wata zuciyar ta jefamata tambayar da har sai da ta murmusa kafin ta kuma ƙaryata tunaninta. Toh me Yaya Khaleefa zai yi da ita? Ita ma ai ta bar soyayya, ba ta kuma son ta yi auren zumunci yanzu.

'Har da Yaya Khaleefa?' Ta ƙara jin tambayar a cikin kwakwalwarta, a sace cikin cunkoson jama'a ta ƙara dubansa, hankalinsa yana can suna gaisawa da Amarya, kishiyar Momin Mu'az. Tabbas Khaleefa ba shi da makusa ko kaɗan. Miji ne da kowace mace za ta yi burin samunsa. Kafin ka ji mai zaginsa guda ɗaya, ka ji masu yabonsa fiye da goma a fannin halayya da ma sanyin hali. Matsalarsa dai bai wuce miskilanci ba wanda a yanayi na surutu irin nata ba ta jin za ta iya sabo da shi.

Can kuma ta ji haushin kanta da kunya, to mene ne ma abin wadannan tunanikan alhalin ba wani abu ya furta mata ba?


A ɓangaren Haulatu wacce kanta ke ƙasa, ba zato ta ji mutum a gefenta saman kujera har cinyoyinsu na gogar juna.

"Yauwa ko kai fa, bari a yi muku hotunan." Maganar Maama ta ji, ya ba ta tabbacin ita ta jawo shi daga wurin mutanen Malumfashi wadanda gaisuwar ta ƙi ƙarewa. Suka haɗa idanu karo na biyu, sai ta yi saurin kauda kai. Shi ma basarwa ya yi ya maida hankali ga mai hoton na musamman da aka ɗauko a wannan rana.


Mu haɗu gobe in sha Allah. Saura post guda.....
"Na fa gaji da hotunan nan, a bar ni na ji ɗumin matata."

A hankali ya yi furucin ba tare da ya ko kalleta ba, ita kaɗai ta iya jin me yace saboda tsabar kusancinsu, ta kuwa ƙara ji kamar ta nutse a wurin. Umma ma ta zo sun yi hotuna, ashe can ta maƙale a gefe tana hira da Maman Radiya. Har aka yi aka gama babu ƙeyar Zaid, an ce dai ya je ɗaurin auren, bayan an kammala ya taya Angon murna ya fice. Nan ma duka an fi zaton umarnin Mahaifiyarsa ne.

Haulatu na ji su Radiya na gulmar bayan sun koma falon sama, ba ta ce musu uffan ba. Ina ruwanta da wani Zaid a yanzu? Babu kamar ma tunda ta riga ta zama matar Abeed Sadauki. Wani murmushi ta yi da ba ta shirya ba.

Da misalin karfe biyar, gidan Maama suka wuce don ya fi kusa da ɗakin taron da za'a gudanar da bikin,  ita da su Safina da sauran ƙawayen makarantarsu su uku. Maama ba ta biyo su ba asalima ta yi gaba can wurin taron don kula da tsarin komai. Ta ƙara sabon wanka ta yi alwala, wata sabuwar kwalliya mai make up ta yi mata na tafiya gurin yini wanda za'a yi a eventcentre. Dinnerparty wanda Sadauki ya shirya kuwa sai a washegari za'a yi.
Wannan karon shigar kayan saƙi ta yi ruwan ƙasa. Ta fito tsaf da ita, sosai kwalliyar ta amshe ta. Duka wannan zaɓen na Maama ne.

"Masha Allah TubarakAllah. Kin yi kyau sosai sosai Mrs Abeed."

Faɗin Safina tana murmushi, ita ma ta sha nata adon cikin nasu kalar ankon na atamfa su ma ruwan ƙasa da surkin baƙi. Sai da suka yi sallar Magriba sannan suka yi haramar tafiya, motoci biyu ne suka zo don tafiya da su. Idan ka ɗauke Siena na gidan Maama wanda zai kwashi ƙawayenta, sai ko motar Sadauki. Yana zaune a kujerar baya, sai ko wani ɗan uwansu daga Malumfashi mai suna Bilal dake jan motar, Safina ta shiga gidan gaba bayan ta gaishe su, sauran kuwa gaba daya suka ɗuru a ɗaya motar. Shaddarsa ruwan ƙasa amma bai ciza kamar na Haulatu ba. Bayan sun soma tafiya ta ɗan dube shi. Dama idanunsa na kanta, murmushi suka sakarwa juna cike da yaba yanda kowannensu ya burge ɗan uwansa. Murya a sanyaye ta gaishe shi ya amsa mata a nutse. Bai yi kowane yunƙuri ba idan ka ɗauke yatsun hannunta na hagu da ya lalubo ya harɗe cikin nasa. Kusan lokaci guda suka sauke numfashi. Ya lumshe idanu yana ɗan matsa tafin hannun nata cikin nasa a hankali kuma yana ɗan saki, sai da ta shiga kokarin zame hannunta kafin ya haƙura ya bari, kansa ya jinginar jikin kujera ya zuba mata narkakkun idanunsa. Sautin waƙar  Salim smart na So kenan shi ne ke tashi a motar. Hankalin Bilal da Safina ma ba ya kansu, ita tana amsa wayar wasu abokan karatunsu masu neman kwatance, shi kuwa Bilal hankalinsa na ga tuƙi. Har suka ƙaraso Bilal ya nemi wuri ya yi parking, suka soma fita sannan Ango da Amaryarsa su ma suka fito abin su tsaf suka jera zuwa ciki. Kiɗa na musamman mai taushi aka sanya, ƙawayen Amarya su biyar, Safina ita ɗaya a gaba tana ɗan rangajinta sai sauran suka jeru bibbiyu. Kowa a gurin daga mai hoto daga zaune saboda an tsara babu shiga ɗaukar hotuna, sai masu murmushi da wangale haƙora tsabar burgesu da suka yi. Momin Mu'az sai wani murmushi take, ko babu komai ta raba ɗanta da mugun iri a cewarta yayinda Mamin Khaleefa ke kula da ita, sai ta tsargu, wato dai Momin Mu'az ba ta taya ta baƙin cikin rashin Sadauki da ƴarta ta yi kenan? Kodai dagasken ne kamar yadda ƴan uwanta ke yawan yi mata hasashen da biyu take zaune da ita? Ranta ya ɓaci amma sai ita ma ta zaɓi nuna wa duniya ba ta baƙin ciki da abin duk da dai can ƙasan ranta har a lokacin haushin Nuratu da Ridwan har ma da ɗan nasu Sadauki na cin zuciyarta.
  Jannat ko ƙeyarta babu a wurin, Fahima kuwa dalilin rashin ganinta bai wuce takunkumin fitar da Mahaifinta ya saka mata ba, tun sadda suka kai shi gaban Baba Alhaji akan ya yi haƙuri kar ya aura mata mai shaye shaye ya ji zafinsu, a ganinsa mugun raina hankalinsa a ka yi har a tsaya nuna masa iko akan gidansa. Dakyar ita ma Haj Hadiza ya bar ta zuwa bikin don sai da suka yi fada sosai, karshe yace ita dai ta je amma Fahima babu inda za ta taka. Idan kuwa Fahima ta fita to ƙarshen zaman Haj Hadiza a gidan ya zo kenan. Kuma aure dia ɗan ɗan uwansa babu fashi sai an ƙulla shi, idan an ɗaura ta mutu. Da wannan baƙin cikin ta halarci bikin Haulatu, kowa ya gan ta yasan akwai abin da ke damunta. Ita yaƙen ma ta kasa, tana zaune kawai ta zubawa Haulatu da Sadauki idanu tana ji inama Fahimarta ce da wannan matsayin. Ita dai auren ma ba yabo ba fallasa, ba ta san me take ji a kan aurensu ba. Babu ƙin babu kuma son. Anti Mabruka na gefe kujera guda da wasu hamshaƙan ƙawayenta, kallo ɗaya idan ka yi musu za ka fahimci masu gidan rana sun zauna a nan. Sai tau a cingam suke suna kallon kowa ɗaɗɗaya. Zaituna ce tare da Maimuna sai Zuhra  da Fa'iza suka dinga bi tebura suna rabon ƴar jaka mai kyau na souvenir. Ɗauke da notepad mai biro a gefe sai ko madaidaicin mug mai murfi da aka rubuta Best Wishes, Abeed & Haulatu a jiki sai ko kwanan wata.

Abin ya ba mutane da dama mamaki don ba a san da kayan rabon ba. Ta yi su ne kaya guda, da kudinta da wanda mahaifinta ya turo mata, kusan shi ne dalilin zuwanta da wuri ƙasar. A Abuja ta bayar da aikin komai, sai kuma ana gobe za'a fara bikin saƙon ya iso kaya guda. Kai tsaye gidan Maama ta sa aka kai, Maama ta ji dadi sosai ta kuma yaba da wannan kokarin na Zaituna, sai da suka ware na iyaye da waɗanda suka cancanta kafin su ƙaraso nan.

Komai ya tafi a tsari na wayayyu kuma ƴan boko. Koda ta ƙarasa ɓangaren inda su Khaleefa ke zaune, haka ta ajiyewa kowannensu a kusa da shi. Yana riƙe da ɗiyarsa Iman wacce a yau kam ƙamshin turare kawai ke tashi a jikin yarinyar, an mata kwalliya an naɗe ta a shawul. Hafsat kuwa na can zaune tare da su Ihsan yayar Fahima da wasu sa'anninsu. Da murmushi ta dube shi bayan ta ajiye kafin ta maida duba kan bebin, shi kuwa hankalinsa na kanta. Ta yi mishi kyau ainun cikin atamfarta ruwan hoda mai haske da kuma duhu wanda aka ƙawata ɗinkin riga da siket ya zauna ɗabas a jikin. Sai ko mayafinta madaidaici na chantily shi ma pink. Hannu ta kai ta ɗan shafi kumatun Iman tana wani murmushi sai kuma ta miƙa hannuwa.

"Abu Affan, please ba ni ita." Bai ko san sadda ya miƙa mata ba. Ta sumbaci goshin yarinyar har tana ɗan shafa mata jan baki sai ta yi saurin gogemata da yatsa tana ambaton kalmar sorry. Daga nan ta dubi gefenta inda ta hango Zuhra ta taho, umarni ta ba ta akan ta ɗauki sauran kayan rabon da ta bari a kusa da su Yaya Khaleefa su je. Suna tafe tana nuna mata inda za ta kai. Ita kuwa Zuhra na ajiye musu. Khaleefa ya kasa ɗauke idanu a kanta, duk inda ta je ta dawo sai ya bita da kallo yana ji dagaske har zuciyarsa yana ƙaunarta. Ya yi amanna akan abin da yake ji ba na wasa ba ne, ba kuma wai na kwanaki ne ba kawai a bar shi. A'a, yanayi ne na ƙauna da soyayya da kuma fatan ya mallake ta a matsayin matarsa.

Duka wannan abu dake faruwa a kan idanun Hafsat wacce tun lokacin da Zaituna ta isa ga mijin nata take kula da su, har ma murmushin da Khaleefan ke bugawa yana bin su da kallo sai da ta lura. Har wani jiri ta ji yana kwasarta daga zaune.

"Ke, je ki ki karɓomin ƴata a hannun waccan uwar ƴan iyayin."

Ta ba ƙanwarta Fadila umarni, ita ko da ta maida hankali ga cin abinci, sai a lokacin ne ta lura da abin da ke faruwa. Zaituna tuni ta koma mazauninta tana faman rainon Iman tana sauraron MC da ke ba da umarni akan ƙawayen Amarya da abokan Ango su fito fili.

"Meyasa za'a karɓo ta? Wani abun ya faru ne?" Tambayar da Fadila ta jefa mata kenan. Ita kuwa ta watsa mata harara.

"Babu ruwanki, kawai ki karɓo min ƴata."

Taɓe baki ta yi tana turo baki.

"Gaskiya ki bari na kammala cin abinci wallahi. Ni ba zan iya tashi ba."

Aikuwa tashin da ba ta yi ba kenan, Hafsat ta shaƙa iya wuya, ba kunya ko ta mike da kanta ta zagaya har inda Zaituna ke zaune tare da su Fa'iza waɗanda suka suka kammala rabo an nutsu ana kallon diramar da MC ya ce a yi, wato rawa tsakanin ƙawar Amarya da abokin Ango, duk wanda ya ƙi yi kuma zai yi liƙi ga abokin rawarsa. Lokacin riƙon Iman ɗin ya koma ga Fa'iza, ita a sannan ma ta fidda rai ga samun Khaleefa har ta tsaida mijin aure cikin manemanta. Kawai sai ganin Hafsat suka yi a kansu, ta ja ta tsaya tana mai sa hannu ta karɓi Iman ɗin a hannun Fa'iza har tana kokarin fisga da ya yi sanadin yarinyar ta firgita ta canyara kuka.

"Haba Anti Hafsat? Don Allah ki yi mata a hankali." Cewar Zaituna, duk da ba duka abin da ta ce ɗin ya shiga kunnuwan Hafsat ba sakamakon kiɗan da Dj ya saki, amma hakan bai hana Hafsat watsa mata kallon banza da harara ba sannan ta yi gaba. Zaituna da Fa'iza suka dubi juna kawai. Ita Fa'izar ma har da jan tsaki. Koda ta yi wani furucin, Zaituna sam ba ta ji ba don hankalin ya koma kacokam ga sowar da wuri ya ɗauka dalilin karin da wani abokin Sadauki, Jameel ke zubawa Rumanatu da ke rawa shi ko da ganinsa irin miskilan nan ne wadanda rawar bai dame su ba.

Ɓangaren Amarya da Angonta kuwa, shi gaba ɗaya ma ya gaji da abin. Sai raɗa yake mata akan ya dace a tashi haka. Tana murmushi ta ɗan dube shi. Ita ma cikin ɗan raɗan yanda zai ji ta ce.

"Wannan fa duk mu ake tayawa murnar aure, don Allah ka ƙara haƙuri, ai an kusa tashi."

Ya jingina kansa jikin kujerar a saitin kunnenta ya ce.

"Haƙuri ki ke ban? Wani abu na ce maki zan yi? Ko wani abun ki ke so?"

Ta kauda kai tana maida duba ga MC wanda ya yi umarni ga Dj ya tsaida kiɗa.

"Don Allah ka bari mana." Ta furta a hankali kamar mai shirin kuka da narkakkiyar muryar da ya ruɗa kan Sadauki. Daƙyar ya samu ya saita kansa sannan ya ce.

"Na rantse ki ka ƙara min magana da wannan yanayin daga nan babu inda za ki zarce sai gidana. Idan ya so a biyo ki da kayanki."

Maganar MC ce ta katse Haulatu daga cewa komai, umarnin su fito fili yake ba su. Sadauki ya ji kamar ya buge shi. Fadi yake.

"Shi kuma wannan kamar wani ubanmu sai mulki da mallaka ya ke nuna mana."

Ita dai ba ta tanka ba sai murmushi a ciki-ciki. Ba ta son ta yi abin da zai sa ya yi wani yunƙurin don haka ta ja baki ta tsuke.

Koda aka tashi kusan su ne ƙarshen tafiya don sai da Sadauki ya yi bankwana da wasu abokansa da suka zo tun daga Lagos, a gobe da Asuba zasu kama hanyar Kano daga can kuma su hau jirgin dare da zai maida su. Har gyangyaɗi ta fara, ba don ma Safina na motar su na ɗan taɓa hira ba da babu abin da zai hana baccin ya yi awon gaba da ita sosai.

Koda suka isa shi kansa Angon a gajiye yake amma fa hakan bai hana shi ɓata lokaci da Amaryarsa ba don Safina na ficewa shi ma Bilal ya bar motar ya fita don ba su wuri su yi sallama. Ta kai hannu za ta buɗe murfin ya sa hannunsa ya jawo ta gaba ɗaya ta dawo jikinsa har suna jin hucin fitar numfashin juna, da sauri ta sa tafin hannunta na dama a saman ƙirjinsa, a hankali kuma ta soma kokarin zamewa ya sa hannu ɗaya ya dafe yatsunta. Ta kasa motsi kwakkwara, zuciyarta na umartarta da ta janye daga jikinsa sai dai gangar jikin ta kasa mara mata baya. Ba ta san ya aka yi aka haihu a ragaya ba, sai dai kawai jin da ta yi sun faɗa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login