Showing 51001 words to 54000 words out of 177840 words

Chapter 18 - FITAR TSIRO COMPLETE HAUSA NOVEL BY RUFAIDA UMAR

11 Jul 2024

79132

madubi tana murmushi kafin ta maida dubanta ga Umma wacce ita ma ke kallonta tana murmushin.

"Umma, kayan sun min kyau ko?"

"Sun yi, hankalinki ya kwanta? Kafin ki tafi dai ki yi abin da na sanya ki."

Ta ɗan yi shiru tana nazari can ta tuna, ashe fa Umman ta ce ta kira Mu'az a waya ta mishi godiya.

"Toh, ina wayar taki?" Umma ta miƙa mata sannan ta miƙe daga saman darduma ta naɗe ta fice zuwa falo. Lambar Mu'az ta lalubo, ba ta ci wuyar ganinsa ba don ko da safe sun yi magana da Umma yake tambayarta ko lafiya bai samun wayar Haulatun, Umman ke labarta mishi cewa ai laifi ta yiwa Yayanta Sadauki shi ne ya hukunta ta ta hanyar karɓe wayar.

Sau uku ya yi ƙara kafin ya ɗaga da sallama, ta yi gyaran murya ta amsa.

"Ina wuni." Ta furta tana ɗan hararar iska kai ka ce shi ne a gabanta.

"Oh, ƴar ƙauyen Kano ce? Lafiya lau."

"Eh ita ce ɗan birni. Dama godiya na kira na yi maka. Allah ya saka da alheri. Na ga waya."

Ya yi murmushin da ta ji sautinsa a kunne.

"Kar ki damu, ai yiwa kai ne. Bai ba ki wayar ba?"

Taɓe baki ta yi.

"Wai wancan? Eh na bar masa ya ƙara da na hannunsa ya riƙe."

Ya yi ƴar dariya.

"Na kula dai dole taku ta ƙi zuwa ɗaya da Bestina, wato ba kya shiru. Ga tsiwa ga rashin kunya. Anyway, kar ki damu, zai ba ki. Ni na san halinsa."

"Uhum. Ni zan tafi islamiyya."

"Ok, bye." Ya ba ta amsa, daga haka ta katse wayar, har ƴar ƙarar da wayar ke yi dadi yake mata a kunne. Kai abu mai tsada kyau gare shi, ta shiga latsawa har sai da Safina ta shigo kiranta kan ta fito zasu yi latti sannan ta mike suka tafi da ƴar jakarta da Maama ta siyamata mai dauke da litattafan karatu.

Tun biyu sai karfe shida na yamma suka dawo gidan, ba ta kula kowa cikin yanmatan gidan kamar yanda ba su shiga harkarta ba sai Safina. Kai tsaye sama ta haye bayan sun gaisa da Baba Saude da wata yar budurwar jikarta dake taya ta aiki. Ganin Dr Khaleefah zaune suna magana da Umma ya sa suna hada idanu ta kauda kai tana cin magani.

'Ɗayan mugun.' Abin da ta furta a ƙasan ranta kenan, ta ƙarasa ta yiwa Umma sannu da zuwa, Hajja ba ta nan. Ta gaida Khaleefa kamar wacce aka yiwa dole, ya yi kamar bai ji ba ya ci gaba da maganarsa da Umma, ta kula wani sabo ke tsakaninsu don hirar wata marar lafiyarsa ta ji kamar yana yi da Umman. Ɗaki ta shige ba ta ƙara fitowa ba sai da ta ji ana kira Magriba, ta tabbata ya tafi.

Sai kusan bayan sallar isha'i ta tuna da kiran da Alhaji ke mata aikuwa ta mike.

"Ina za ki je?"

Ta dubi Umma.

"Na manta wallahi, jiya Baba Alhaji ya ce na je na same shi bayan Magriba. Ga Isha'i har ya yi."

"Sai ki yi sauri to don yana bacci da wuri." Fadin Hajja da ke gefe saman darduma. Haulatu ta dube ta kawai ba tare da ta amsa ba ta juya ta kama hanya. Hajja dai ta kula jikarta ta soma saukowa daga dokin fushin da ta hau da ita. Bayan fitar ta ta dubi Umma fuska a sake ta ce
"Kin kula ɗiyarki an fara sauyamin?"

Murmushi Umma ta yi.

"Dama ai sakarci ne irin nata. Allah dai ya shirye ta."

"Aa fa, ba sakara ba ce. Kar ki kuskura ki ƙara jinginata da wannan kalmar."

Umma ba ta ce komai ba, dama ai ta lura Haulatu ba ta laifi wurin Hajja.

A can kuwa, Baba Alhaji ta iske shi saman darduma yana jin rediyo, ganin ta ya sanya shi rage sautin rediyon har yana zolayarta akan saɓa lokaci shi zai bar ba da kudin cefane. Suka yi dariya. Nasiha ce sosai ya yi mata dangane da rayuwa da kuma yi mata nuni da girma na iyaye. Ya nuna rashin kyautatawar abin da mahaifinta ya yi a zamantakewarsu sai dai ya ce ko wace irin cutarwa ya yi mata ita ta yi hakuri ta bar munana kalamai a kansa. Wannan karo na farko ne da Haulatu ta ji ba za ta iya ja da abin da babba ya fadi ba. Sai ta ji maganganun Baba Alhaji na tasiri a wajenta. Ya kuma kara da cewa ta dage ta maida hankali ga karatunta na addini, boko kuma ya mata alƙawarin in sha Allahu za ta yi har sai ta ce ya isa tunda shi ne burinta. Bayan ya kammala tana ta jin dadi da murnar, ƙaunar tsohon na ratsa zuciyarta. Tana shirin tafiya ya dakatar da ita ta tsaya.

"Ga wannan inji ɗan uwanki."

Ta kalla, wayarta ce da Mu'az ya siya mata. Da mamaki ta ce.

"Au, ya aka yi ya bada?"

Murmushi Alhaji ya yi.

"Karɓi, nima ban san da batun waya ba. Dazu da ya zo zai tafi ya ce na ajiyemaki idan kin zo a ba ki."

Ta sa hannu ta karɓa ita har a sannan mamakin yanda aka yi ya bayar take, ai ta yi zaton ita da wayar sai a lahira tunda ance tun can baya ma kafin a ba ƴanmatan ƴancin riƙe waya suke riƙewa a ɓoye, muddin ya ji labari to fa kwacewa yake yi, kuma idan ya kwace ba su ko ganin wulkawarsu shikenan. Ballantana kuma ita da ya kama da laifi. Haka ta yiwa Alhaji sallama ta tafi. Koda ta koma ta iske Khaleefa zaune yana cin tuwo da miyar kuɓewa ɗanya a falon. Har da cire hularsa ya ajiye saman kujera. A gefe itama Hajja nata lomar take yi, sai Umma da alama ita kam ta kammala. Ganinta ya sa Khaleefa tamke fuska kai ka ce ba shi ke ƴar raha yanzu da Umma ba.

'Aikin kenan. Fuska kamar alkubus.' Ta furta a ƙasan rai. A fili kuwa sai ta yi hanyar daki.

"Haule, kin ci abinci kuwa?"

Sunan Haule da Hajja ta fadi ya sa ba shiri Haulatu dubanta kamar ta yi kuka, rai a bace ta ce.

"Ni sunana Haulatu kar ki kara cemin wani Haule."

Dariya Umma ta yi, Khaleefa ko kamar bai san wainar da suke toyawa ba.

"Oh to, ai ban san ma na fadi haka ba. Wata mai siyar da fura sunan ke tunamin a Malumfashi. Yi hakuri kin ji? Maza taho ki ci abinci."

"Sai anjima zan ci." Ta fadi a fusace sannan ta yi ɗaki da haushin Hajja ta kira ta da Haule gaban Khaleefa.

Shi kuwa bayan ya kammala ya wanke hannu sannan ya miƙe.

"Sai tafiya kenan? An dai ji kunya, mace har mace amma ba ta iya tuƙa tuwo ba?" Hajja ta fadi cike da zolaya. Khaleefa ya yamutse fuska.

"Ke Hajja kin fiye tada zaune tsaye, to ni ne ban nemi a tuƙa ba."

"Ba wani nan, kai dai ka je ka ɗauko matar da ba ta ko matsar da tsinke a gidanta. Kwanan nan zan samo maka mata a Malumfashi. Bari dai su zo bikin yaran nan."

Ɗan murmushi.

"Ba ni Khaleefan ba ko?"

"Gidanku, kai dai Khaleefa. Akwai wani Khaleefa da na sani ne bayan ka?"

"Sai da safenku. Umma, mu kwana lafiya."

Ya fadi yana kama hanyar barin falon lokaci guda yana gyara zaman hularsa. Umma ta amsa mishi tana dariyar diramarsu da Hajja. Har bayan ya tafi Hajja ba ta bar mita da jin takaicin yanda matan zamanin nan ba su maida hankali da gyara cikin mazajensu ta hanyar sarrafa girke-girke masu rai da lafiya. Ta dinga zayyanawa Umma matsalar gidan Khaleefan na cin girkin ƴan aiki da ma rashin tsaftar matar gidan. Komai sai dai yan aikin su yi.

"Ina ce dai Haule ta iya girki ko?"

Murmushi Umma ta yi, dom girki kam Haulatu ta iya wanda ta iya. Sai dai na zamanin da ta ga Baba Saude na sarrafawa. Jin ba wani sosai Haulatu ta iya girki ba ya sa Hajja ta ce ya kamata ta sa ta fara shiga kicin don ta koya. Umma ta amsa da toh. Don ta sani idan har Hajjar ce za ta saka, to fa babu abin da Haulatun za ta yi. Ita din ma da ya ya wasu lokutan take tursasa ta abin da ba ta so?

***
Babban falon da ya sha kayan ƙawa, ga haskem fitilu ta ko'ina. Cike yake da manyan ƙusoshi na ƙasar, da ma manyan jami'ai na tsaron al'umma da dukiyoyinsu sai kuwa Alhazai da suka jiƙu da daloli da kuma wadanda suka kasance abokan hulɗarsu amintattu da suke da tabbacin duk wuya kuma duk runtsi asiransu a rufe suke a bakunansu irin su Hajiya Adama, Ɗan Mutuwa da sauransu. Rayukansu duka babu daɗi ganin an fara kai wa ƙungiyartasu hari. Wani babban Comptroller General Haisam ya dube su gaba daya ba a nutse ba.

"Abin fa ya wuce yanda muke tsammani. Wato a yanzu yunƙurin da suke yi, ni ma da suka soma zargi da saka hannuna dumu-dumu a kan shige da ficen kayayyakin can na hannun NDLEA, so suke yi su dakatar da ni. A yanzu haka an yimin iyaka da barin ƙasar nan zuwa lokacin da bincike zai kammala. Ya kamata mu yunƙuro mu samarwa kanmu mafita tun lokaci bai ƙure ba. A yarda an faɗi zaɓe, mu rungumi wannan ƙaddarar, amma kuma mu tashi tsaye don kar mutunci da girmanmu ya zube. Ranku ya dade, idan girmanku ya zube to namu fa mu ma zai zube ne ƙasa warwas. Sai mu san abin da ya dace a yi. Ga Sanata Tukur can a hannunsu dai."

Wadannan zantukan na Comptroller Haisam ya ƙara ɗagamusu hankali. Nan kuma tsohon gwamnan ɗaya daa cikin manyan jihohin arewa shi ma ya yi nasa jawabin. ƊanMutuwa suna gefe, abin na manya ne, nasu kawai jinjina kai da kuma kambama manyan wurin. Tattaunawa ta yi zafi da har DanMutuwa bai samu damar shigar da ƙoƙon bararsa ba, babu wannan walwalar a fuskokin jama'a, kowa cike yake da fargabar tonuwar asirinsa.
Sai wuraren ukun dare sannan taro ya tashi ba tare da an samu kyakkyawar matsaya ba sai ma rarrabuwar kai, inda wasu ke ganin a yi duk yanda za'a yi kawai a ga bayan Sanatan da ke a hannun jami'ai yadda ba zai ji wuya ya tona asirinsu ba amma wasu kuma sun yiwa abin kallon cin amana a cewarsu ba ƙaramin hidimtawa ƙungiya Sanatan ya yi ba don haka bai kyautu a yi mishi wannan yankan bayan ba. A nan ne DanMutuwa ke jin labarin wani wai Uban Dodo, ya sha jin idan ana taro sukan kira wannan sunan sai dai bai kai ga fahimtar komai ba don haka koda ya biyo hanya a mota shi da Hajiya Adama ya watsa mata tambayar waye hakan. Ta yi dariya.

"Hanyarmu ce mai sauƙi ta yin kudi, Uban Dodo, shugaban ƙungiya ta musamman ce bayan wannan wanda ka sani. Ba kowane ƙaramin shege ke shiga ba, ƙungiya ce mai matakan sirri da yawa. Nima ban yi ko wata uku da shiga ba, kuma ka sani, duk wanda ya shige ta, ba zai fita ba har abada. Idan ma mutum ya yi wani yunƙuri na ficewa, toh na rantse maka mutuwa zai yi."

Cike da al'ajabi ya dube ta kaɗan kafin ya maida kai ga tuƙin da yake yi.

"Yanzu kina nufin kin shiga? To kuma idan abun bai yi aiki ba fa?"

Ta daure fuska tamau.

"Ya isa hakanan, mu bar zancen. Kai dai na fadamaka, muddin ka shiga, za ka samu duniya a tafin hannunka. Wannan tserewar da kake yi da wasan ɓuya kan abin da bai taka kara ya karya ba za ka fi ƙarfin kowa ya taka ka."

Ɗan Mutuwa ya yi shiru cike da tunani, tabbas yana so ya ga ya tara maƙudan kuɗaɗen da suka wuce hankali, yana so ya gan shi a matsayin da zai tara masu yi masa fadanci ciki kuwa har da jami'an tsaro da ma wasu da ke raina shi a baya. Ba shi da tsoro sam, amma fa nazarin da yake yi idan har abu ya kwaɓe, wane irin ƙarshe zai yi? Shi da bai da uwa a gindin murhu. Har suka isa gidan Hajiya Adama, ba ta bar kwaɗaita masa girman ƙungiyar da tace masa ba zai taɓa sanin sunanta ba muddin ba shiga ya yi ba. Tana kuma nunamasa babu wanda ya isa ya taka shi, zai je duk inda yake so a ƙasar nan da ma wajenta. Zai siya abin da yake so komai tsadarsa, mace kuwa ko balarabiya ce to fa zai same ta ya gama. Ba wannan ba ma, zai tashi daga manyan yara masu siye da siyarwar miyagun kwayoyi ya koma daya daga cikin masu yin dila. Sosai Ɗan Mutuwa abin ya fara tasiri a zuciyarsa, a wannan daren kasa bacci ya yi yana faman tufka da warwara. Bai shiga tsananin ruɗu ba sai da tashi guda Hajiya Adama ta yi mishi kyautar wani ƙaramin gida mai kyau, ɗaya a cikin gidajenta uku da ta mallaka a jihar Kaduna, ta ba shi takardun ta ce ya koma can ya tare, amma fa ya yi kokarin yanke shawarar da zai sa ya cigaba ya mallaki maƙudan kuɗaɗe a asusunsa.
Da wannan ya yi sammako ya koma Gwarzo gidan gona don haɗa shirginsa ya wuce Kaduna. Ya kuma ji a ransa zai karɓi tayin Hajiya Adama ya faɗa ƙungiyarsu, ya shirya sadaukar da ran ko ma wane ne muddin dai za'a dama a duniya.

***
A can Katsina kuwa, sati na zagayowa aka kawo lefen Batulu, dukkansu an saka ranar biki watanni biyu, ya yi daidai da bayan ƙaramar sallah da sati bai fi uku ba. Haulatu ta maida hankali fiye da tsammanin Umma wurin zuwa Islamiyya, ga kuma falon Alhaji wanda ta maida shi wajen hirarta, kusan kullum sai ta je babu ma kamar kwanakin nan da aka wayi gari mutumin dake hana ta sakewa da Alhajin ya yi doguwar tafiya na kasuwanci zuwa China. Ba karamin dadi hakan ya yi mata ba, ko ba komai ta huta da yin kiciɓus da shi a wurin Baba Alhaji don wasu lokutan ma sai ta kusan saka kai a falon nasa za ta hango Sadaukin zaune a dole take juyawa ta koma ɓangaren Baba Dakta ta sha hira da Inna (matar Baba Dakta) da su Maama da Safina.

Tsakaninta da Mu'az zumunci sosai ya ƙullu, suna gaisawa a yi barkwanci. Ko kusa ba ta shakkarsa irin yanda su Safina ke yi, ta ma soma sabo da jikokin gidan da dama musamman wadanda islamiyya ta haɗa su. Yara da manyan su an sake da ita ana gaisawar mutunci. Bayan Safina, sun ƙara ɗinkewa da Radiya ɗiya ga ƙanwar Alhaji Ridwan, Yusuf (Baban kowa). Yarinya marar ɗaukar musamman ganin babanta ba shi da arzikin sauran, sai dai kuma yan uwansa ba su bar shi haka ba, domin duk abinda suka dinkawa yaransu su na haɗawa da na shi iyalin. Sosai nutsuwarta ya sa suka saba da Haulatu don ajinsu ɗaya a makaranta.
Tana gaisawa da matan iyayen nasu a mutunce idan ka cire Mommy (Mahaifiya ga Mu'az) da ke jin haushinta sosai. Tun da labari ya riske ta na cewar Mu'az ya siya mata waya ita da Ummanta ta tada hankali da masifa wai jinin Hajja ba zai ci arziƙin yaranta ba. Sai da Injiniya ya tsawatar kafin a dole ta janye ƙudurin karɓe wayoyin amma fa ta rantse muddin Mu'az ya ƙara kashe musu sisin kobonsa ba tare da saninta ba Allah ya isa. Haulatu sau daya ta taɓa shiga wajensu, amma irin tarba da zagin da Mommy ta yi mata a ranar sai da ta fusata, a kan idanunta kuma sai da ta ce mata darajar ɗanta ta ci ba don haka ba sai ta rama kuma zumunci yanzu ta soma shi da ɗanta bai raba su sai Allah. Wannan ya sa Mommy ƙara jin tsanarta a rai, ita ma tun daga ranar ba ta ƙara taka ƙafarta gidan ba duk da ta samu tarba na mutunci a wajen Yaya abokiyar zaman Mommyn.

Tsakaninta da Hajja ma babu laifi ta ɗan sakar mata don ta bar guduwa ɗaki, za ta fito ta zauna amma ba ta saka baki a hirarsu, takan zauna ta yi ta latse-latsenta a waya. Idan ma ba ta komai za ta sauka ne wajen Baba Saude su sha hira.

Yau ma tana zaune a falon ƙasa ta manna earpiece a kunne, kallon comedy take yi a tiktok tana dariya. Sam ba ta ji sallamarsa ba sai gani ta yi ya shigo. Mikewa zaune ta yi gami da cire earpiece din da zummar gaishe shi sai dai kallo ɗaya da ya yi mata bai ƙara ba ya sa kai ya nufi bene. Guntun tsaki ta ja wanda sarai ya ji har ɗan juyowa ya yi ya kalle ta, da sauri ta kauda nata kan bai tanka ba ya haye. Taɓe baki ta yi, ta fahimci wannan likitan babu abin da ya sa a gaba sai girman kai da taƙama. A haka ƴan gidan ke cewa Anti Madina ke cutar da shi a zamantakewa alhalin iya zama da mutum mai girman kai irinsa sai wacce ta shirya. Hakan ta ayyana a ranta.

Baba Saude ce ta sauko daga sama hanninta riƙe da wayar Umma ta nufo Haulatu, ganin haka sai ta cire abin jin sauti na kunnenta.

"Ga shi nan, wai kawarki ke nemanki a waya.". Ganin sunan Hindatu ya sa ta miƙewa zaune ba shiri. Rabon da su yi magana an kwana biyu, koda aka bude mata whatsapp ta yi mata magana ba ta hau ba har zuwa yau din. Hatta a waya ba a samunta. Wannan yasa ta ɗaga da azama.

"Haba Big Mama, ke kuwa ina kika shiga haka? Kin yi shiru kamar ruwa ya ɗauke."

Da murya mai nuni da damuwa Hindatu ta amsa.

"Ina gidanmu fa. Mun rabu."

Sai da kirjin Haulatu ya buga da ƙarfi.

"Ban gane kun rabu ba? Da wa ku ka rabu? Malama yi min gwari-gwari yadda zan fahimta? Wace irin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login