Showing 150001 words to 153000 words out of 177840 words
ta yi.
"Na'imatu kenan, ai koda ace ban yi zama dake a farkon rayuwa ba, yanzu tsawon lokacin da muka ɗauka tare ya ci ace na fahimceki. Damuwar dai tun ta farko ce da ki ka yi ƙorafi a kai ba ta sake ki ba."
Umma ta yi shiru tana maida murfin man ta rufe. Sadda ta samu Hajja da batun Haulatu da Sadaukin, ta yi ne don ta nunawa Hajjar abin bai kwanta mata a rai ba gudun abin da zai je ya zo, Hajjar kuma ta fahimce ta sosai amma ta nuna mata hakan duka ba hujja ce mai ƙarfi da zai sa ta dakatar da yaran ga samun farin cikinsu ba.
"Na'imatu, ki bar wa Allah komai ki taya ƴarki neman zaɓinsa. Sadaukin Alhaji a kaf matasan nan idan ka ɗauke Dakta (Khaleefa) ya fi su nutsuwa da sanin ya kamata. Ban taɓa jin inda aka koka da halayyarsa ba, don haka kar ki yarda ki sanya damuwar komai a ranki. Ballantana ma ina da tabbacin Nuratu da Ridwanun da ki ke tunanin ba za su amince da Haulatu ba, sai sun fi ki murna da wannan haɗin. Ki cire damuwar nan a ranki mu aurar da Haulatu, kema fatan samun miji nake ta maki don in sha Allahu ba zan zuba idanu da ƙuruciyarki ki tsofe a gida ba sai dai kawai idan Allah bai nufeki da auren ba."
Tsam Umma ta tashi, an zo darasin da ba ta so ta ji Hajja ta ɗauko shi, Hajja ta yi dariya tana bin bayanta da kallo.
"Ka ji min wani shirme? Au auren ne ba kya so a tayar da zancensa? Ai shikenan."
***
Ta yi zaune gaban Baba Alhaji shi kuwa sai da ya ja ta da hirar makaranta kamar koyaushe har ta ɗan saki ranta sannan ya yi gyaran murya.
"Haulatun Hajja, ɗan uwanki ne ya zo min da wata magana shi ne mai dadi sai dai ban yanke hukunci a kai ba na fi son jin ra'ayinki tukunna."
Ya ɗan yi shiru yana ɗan tari. Dama ita ta san inda zancen ya kwana, ya ɗora maganarsa da jefamata tambaya.
"Ke kika amince da Sadauki ya fito neman aurenki?"
Kunya ya sanya ta murmushi kawai kanta na ƙasa, ya kula da hakan, a matsayinsa na babba kuma ya fahimci amsarta sai dai zai fi ƙaunar ji daga bakinta ta amsa. Don haka ya ce.
"Haulen Hajja." Ya furta kamar yanda ya saba idan yana cikin raha.
"Na'am." Ta amsa.
"So nake ki ce min eh ko a'a. Ni yau suruki kika maida ni ne?"
Ta girgiza kai tana murmushi.
"To ki faɗamin, kin amince da Sadaukin Alhaji, kin ba shi damar ya fito neman aurenki ko kuwa shi ma irin wadancan ne na baya ne, ba da yawunki ya zo ba?"
Ta ƙara girgiza kai sannan ta yi magana murya a ƙasa.
"Na amince Baba Alhaji."
Tana faɗin haka ta yi saurin rufe fuska da tafukan hannuwanta. Ya yi dariya.
"Ja'ira, yau ni kike jin kunya kuma? Toh Alhamdulillah. Na ji dadin wannan amsa taki kwarai, dama can na maki sha'awar miji irin Sadaukina, ban bayyana ba ne don kar ya zama na so kaina da yawa, ba na son tursasawa kowa, na fi so ace ban yiwa kowannenku dole ba a jikokina don dukkanku tsatso guda ku ka fito. Allah ya zaɓa abinda ya fi alheri, tashi ki je, zan yi magana da iyayen naku."
Ba musu Haulatu ta miƙe ta fito, sai ta ji gaba daya zuciyarta ta yi wani sanyi, duka wannan fargabar ta kau, ta sani Umma kawai damuwa ce ta sanya a rai amma ba za ta ƙi aurenta da Sadauki ba. Kuma ta tabbata idan da Ummanta ce, nan ba da jimawa ba komai zai wuce a ranta. Kiciɓus suka yi da Anti Mabruka wacce shigowarta gidan kenan, yanzu ba ta zama kusan kullum sai ta fita, yau ɗin ma ta sha kwalliya kamar wacce ta dawo daga yawon gidan biki. Ta gaishe ta, ita kuwa ta bi ta da kallon sama da ƙasa kafin ta ja tsaki ta maida duba ga ƴar dattijuwar dake kuma da mahaifiyarsu.
"Inna ta yi bacci?" Ta amsa mata da eh , za ta wuce ta dakatar da ita.
"Baba Alhaji ya ce idan kin dawo yana nemanki."
Jin haka ran Mabruka ya ɓaci, Haulatu dai tuni ta ficewarta don ba ta ga dalilin da zai sa Anti Mabruka ta lalata mata farin cikinta na wannan rana ba.
Ita kuwa Mabruka tana shiga Baba Alhaji ya rufe ta da faɗa sosai ya kuma rantse muddin ba za ta bar yawace-yawacen gidan ƙawaye da bokaye ba shi zai yi maganinta. Nan da nan ta zaro ido ta dafa kirji.
"Ni? Baba ni ke bin bokaye?"
Ya kalle ta kawai, Safina ta ba shi labarin abin da ya faru kafin auren Maama, ya yi shiru ne kawai bai ce komai ba tare da addu'ar Allah ya shiryamasa ɗiyar, amma ya kula abin nata nema yake ya fi ƙarfinsa don har sanyawa ya yi ana bibiyarta a ga inda za ta je, a nan ya gano ba ta sauya zani ba, ya so yiwa yayyunta zancen amma ya sani matakin da zasu dauka zai fi na sa tsaru dalilin kenan da ya zaɓi fara gwada nasa ikon tunda dai ba ta fi ƙarfinsa ba.
"Na san da komai da kike aikatawa Mabruka, kin maida kanki kamar jahilar da babu arabi balle boko. Kon kasa yarda da kaddararki, a hakan ki ke tunanin za ki samu mijin aure? Maza nawa suka fito suna sonki amma tsabar raina arziƙinsu da ki ka yi, ki ka wulaƙanta su? Yanzu kuma madadin ki bar wa Allah komai ko rungumi kaddarar da ya rubuta mako har mijin aurenki ya fito amma kin gwammace ki yi shirka ko? To ba a gidan nan ba, wallahi kin ji na rantse maki muddin ki ka cigaba da bibiyar gidajen bokaye don yiwa ƴar uwarki mugun abu ko kuma don wata buƙata ta kanki, sai na yanke hukuncin da ba ki taɓa zaton zan ba a kanki."
Ita dai Mabruka ji ta yi kamar ta saki fitsari a wando. To waye yake faɗawa Baba Alhajin abin da take shukawa? Kuma tun yaushe ya sani ya yi shiru bai ce komai ba? Nan da nan ta shiga zufa duk kuwa da sanyin Ac da ya mamaye falon.
"Baba waye ya soma zuwa ya yimin sharri a wajenka? Ni kuwa Mabruka me ya yimin zafi da zan bibiyi boka ak.."
"Ya isa hakanan, tashi ki je, ni dai na gargaɗeki, ki kiyaye don idan babu wannan rayuwar, akwai wata. Idan ba ki koyi aikin da zai nisantaki da wuta ba, hakika za ki faɗa mawuyacin hali a gaba. Komai ki ka yi hakuri kika bar wa Allah idan rabonki ne sai ya taddo ki a inda ki ke."
Nan dai ya yi mata doguwar nasiha mai ratsa zuciyar duk mai imani, amma Mabruka jin sa kawai take, sai ta ga ma kamar ai raina mata hankali aka yi kawai, komai ace ita ke da laifi, an kasa a cikin manyan abokan yayyunta wani ya samar mata mijin aure ya haɗa su, kuma shi kansa Baban ai yana da yaran abokansa da har gobe suke zuwa gaishe shi, manyan mutane amma bai taɓa cewa zai haɗa ta da kowa ba, sai yanzu da aka ga ta tashi tana fafutukar yanda za ta samu miji ake nema a tauye ta. Har ya sallame ta ta miƙe ta fice a dakin ba ta ko ji ɗarr na tsoron lahirar da kwanciyar kabarin da yake ta kirari ba.
Baba Alhaji ya bi ta da kallo, shi ya haife ta, ya kuma fi kowa sanin wace ce ita, don haka ya girgiza kai zuciyarsa na ɗaci, sam bai ga alamun saduda ba a tattare da ita. Yanzu kuwa ya yanke zai tara yayyunta su taya shi nema mata mijin aure, idan har auren ne a gabanta gwara a yi shi da koma waye muddin ta amince za ta zauna.
***
Momi Nuratu ta yi shiru bayan gama sauraron bayanan da suka fito daga bakin Mijinta Alhaji Ridwan.
"Ya na ji kin yi shiru? Ko ba ki yi farin ciki da zaɓinsa ba ne?" Alh Ridwan ya tambaya.
Ta girgiza kai gami da yin murmushi.
"Ko kusa, akan me zan ƙi Haulatu? Na ji daɗi kuma ina fatan Allah ya sa su zamewa juna silar dukkanin alkhairai, Allah ya sa albarka a ciki. Sai dai na samu waya daga Hajiya Rahma (Mamin Khaleefa), wai don Allah na roƙi yaronka ya zo su yi hira da Jannat ko Allah zai sa su fahimci junansu. Har take cemin yarinyar ta tada hankalinta akan ita fa lallai shi take so. Toh ni dai nace mata ta yi hakuri dai har sai na mishi magana tunda yaran yanzu ba a gwada yi musu dole abin ba ya dadi. Akan hakan dai har saɓani muka samu don gani ta yi wai na goyi bayan ɗanka."
"Ikon Allah, ita Jannat din ke son Sadaukin Alhaji? Toh zan kira shi ɗin na ji ta bakinsa."
Daga haka ya ce a bar batun, dama Momi ta sani, idan har Sadauki ba ya so ba zai taɓa takura masa ba. Ita ɗin ma hankalinta sam bai kwanta da Jannat ba, ta san wace ce Hajiya Rahma tun ma zamanin ƴan matancinsu, kasancewar sun je makarantar kwana guda, ta san irin azabtarwar da ta yiwa juniors da kuma bin malamanta ita da mahaifiyarta duk a fadi tashin neman mijin aure mai hannu da shuni. Sam ba ta hanyarta ta haɗu da yayanta Barr Dawud ba, can suka hadu a wani biki har Allah ya kaddara aure. Ita dai ba ta ce komai a kanta ba har aka yi auren kuma ta samu karɓuwa a cikin dangi. Ba ta iya ta ɓata mutum ba, amma kuma daɗin daɗawar samun kwanciyar hankalinta, bai wuce cewar Yayan nata mutum mai yawan ibada da kuma kamewa ba. Ta sani har abada da yardar Allah, Mamin Khaleefa ba za ta taɓa nasara a kansa ba kuma hakan ce ta tabbata don har yau ta kasa mallakar shi yanda take so, Barr Dawud ya ƙi tanƙwaruwa. Sai dai kuma wasu lokutan rigimarsu ta fi tasiri ne akan tarbiyyar yaransa da take neman lalatawa, ba ta damu da suturun da zasu sanya su fita ba, ba kuma ta damu da zuwansu islamiyya kan kari ba. Wataran har cewa take yi su yi zamansu a gida kwakwalwarsu ta huta tunda an sha karatun bokon an dawo a gajiye. Duk tana da labarin komai, ita din ita ce babbar aminiya ta shawarar yayanta Barr Dawud, ta sani hakuri kawai yake yi da Mamin Khaleefa sai dai babu yanda ta iya mishi tunda ya ce shi sam babu ra'ayin kara aure a rayuwarsa ballantana kuma rabuwa da uwar yaransa Rahma.
"Nuratu!" Kiran sunanta da Daddy Ridwan ya yi har sai da ya sa ta ɗan yi firgigit.
"Na'am? Magana ka ke yi?"
Ya girgiza kai da mamaki ya ce.
"Tunanin me kike yi haka ne? Zancen da ku ka yi da Rahma ki ka sa a rai har ta kai haka ko ya ya? Ban gane ba."
Ta wayance da ɗaukar gorar ruwa ta hau kokarin buɗewa.
"Babu komai. Kawai dai wani abin ne ya ɗauki hankalina. Allah ya nunamana, ya sanya albarka a aurensu."
Ba don ya gamsu da maganarta ba ya share ya na mai amsa addu'ar da amin.
***
Barr Dawud, mutum mai cikar kamala da dattako. A kallo ɗaya tak idan ka gan shi za ka gane shi ya haifi Khaleefa saboda tsabar kamanninsu. Tsawon, farin, har ma da ƙirar jikin babu wanda ba iri ɗaya ba. Idan ka cire shekaru ba su sa bambancin a zo a gani.
Yana zaune a falonsa yana kallon labarai a tashar NTA. Shigowar Mami kamar wacce aka jefo ya sanya shi dubanta lokaci guda yana ɗaukar remote ya ɗan rage murya.
"Rahma, lafiya?"
Ta nemi wuri ta zauna fuskarta a turɓune ta ce.
"Ina fa lafiya Dawud? Yanzu fisabilillahi kana kallon ƴarka a cikin mugun yanayi akan abin da kake da iko da shi za ka iya magance mata amma ka gwammace ka yi shiru ka zuba idanu rayuwarta ta lalace?"
Kansa ya ɗaure, yau wace kalar rainin wayo Rahma ta zo da shi?
"Kin san me kike cewa? Ki shigo min falo ba sallama, ki zo ki hau yi min maganganun shirme da shiririta? Me na cewa ita Jannat ɗin? Ban ce ta haƙura ta fawwalawa Allah lamarinta ba? Ita ba ta san tawakkali ba? Yaron nan ba fa sonta yake ba, kuma ke kin fi kowa sanin ba zan kai ɗiyata hannun wanda ba ya kaunarta ba."
"Na ji na ji Dawud, fito kawai ka cemin Ridwan da Nuratu sun fi ƙarfinka. Ba za ka iya nemawa ɗiyarka auren ɗansu ba saboda ɗansu ba ya so. Shikenan, ni da kaina zan je na samu Alhaji Ridwan din na yi mishi batun Jannat ko..."
"Kar ki fara! Kar ki kusa ki fara."
Ta wurga masa wani kallo mai kama da harara sai kuma ta ja tsaki ta fice ta bar shi da jin ciwon wadannan ɗabi'u nata. Wai shi Rahma ta raina har haka, tsaki, harara, baƙar magana da ma nuna bai isa ba babu wanda ba ta gwada mishi. Idan wasu lokutan ya yi nasarar tanƙwara ta, wasu lokutan takan nuna masa fin ƙarfi. Ya sauke ajiyar zuciya gami da girgiza kai.
"Allah ya ganar da ke." Iyakar furucin da ya yi kenan daga haka ya cigaba da abin da yake. Ya yanke zai ƙara kiran Jannat ya bita da nasiha da kwantar da hankali, gwara ace ta haƙura gudun abin da zai je ya dawo.
***
Washegari kiran Baba Alhaji ya sanya duka yaransa maza suka isa gidan. Barr Dawud sai da ya fara shiga ɓangaren Baba Dakta suka gaisa sannan ya nufi na Hajja. Da sallamarsa ya shiga falon, Hajja na sama a lokacin ba ta kai ga saukowa ba. Haulatu ta fice makaranta, Baba Saude dake kicin ta fito tana amsa sallamar tare da Umma wacce ke tsakar falon, ba ta jima da idar da sallar walha ba hakan yasa ko hijabinta ba ta cire ba, ya ƙaraso ciki suna hada idanu ta sunkuyar da kai fuskarta a sake ta ce.
"Sannu da zuwa Abban Khaleefa."
Ya amsa mata da dan murmushi saman fuskarsa. Bayan ya zauna ta gaishe shi, nan ma bai kasa a gwuiwa ba ya amsa.
"Ina Hajja da ƴar gidanta?"
Umma ta murmusa.
"Haulatu ta wuce makaranta, Hajja ko tana sama, bari a kiramaka ita."
Ya dakatar da ita daga yunƙurin tashin da take.
"A'a Na'imatu, ki bari kawai zan ƙarasa wajen Baba Alhaji, idan na fito sai na shigo mu gaisa."
Sai a lokacin ta ƙara dubansa, shi ma har a sannan bai ɗauke nasa idanun a kanta ba, wani abu ya ji yana tsirga masa a zuciya, ta kauda kai karo na biyu.
"Toh. Sai ka fito."
Daga haka ya miƙe suka yi sallama, bayan fitarsa ta sauke ajiyar zuciya.
***
Kano...
A gigice Ɗan Mutuwa ya zube a gaban Dodo yana kuka da sheshsheƙa ga majina da ta wanke masa hanci.
"Tuba nake Uban Dodo, kai kada ne mai yimin da ba ni, ka taimake ni da wata damar bayan wannan! Na yi iyakar yi na amma cikin nan sai da ya fice a jikinta."
Tsawa mai firgitarwa ya daka masa.
"Ƙarya kake yi! Mu ba ma son mayaudari wanda ba ya cika alƙawari! Ka rasa dukkan wata dama ta arziki! Daga yanzu za ka fara ganin masifu da bala'i iri-iri a rayuwarka! Sai ka zama abin tausayi abin kyama!"
Wani irin mikewa tsaye Ɗan Mutuwa ya yi yana nuna inda Uban Dodo yake da yatsa. Murya a ɗage ya ce.
"Ba ka isa ba wallahi ka yi kadan! Kai waye da za ka cemin zan ga bala'i! Muddin ba ka yimin abin da nake buƙata ba sai na tonamaku asiri kai da dukkan wadanda ke cikin ƙungi..."
Bai kai ga ƙarasawa ba ya ji an ɗaga shi sama cak an narka a ƙasa. Hakan bai hana shi mikewa yana kurarin sai ya ga bayan Uban Dodo ba tunda ya ci mutuncinsa.
Wata wawuyar dariya Uban Dodo ya saka tare da mabiyansa baki ɗaya.
"Ka shiryawa masifu da bala'i a rayuwarka Ɗan Mutuwa! Sai na nunamaka ni Uban Dodo ba'a ja in ja da ni! Ku fice min da shi yanzu!"
Ai Uban Dodo bai kai ga rufe baki ba wasu kattai suka cicciɓi Ɗan Mutuwa suka yi waje da shi.
Hajiya Adama ta bi shi da kallo tana jin wani sanyi a zuciya, ba ta kai ga aiwatar da shirinta akansa ba, sai ga shi nan sakayya ta tabbata da gaggawa. Haka aka cigaba da hada-hadar shan jini da cin naman kare zuciyarta wasai.
A hanya tuƙi yake yi kawai yana ɗura-ɗuran ashariya. Koda ya koma gidansa ma kasa zama ya yi, komai ya samu jifa yake da shi yana zage-zage. Ƙarshe kuma ya ɗauki wayar ya dannawa Hindatu kira, bai ko damu da cewa dare ne ba. Tana ɗagawa ba tare da ya amsa sallama ba ya ce.
"Baƙar azzaluma mai mugun hali! Ni ki ka ci mutunci ki ka zubarmin da ciki! Ki je na sake ki saki uku don uwarki! Kuma ke da uwarki ku shirya kashin kuɗaɗena da ku ka ci!"
Daga haka kitt ya kashe wayar ya yi wurgi da shi. Ya mike ya shiga banɗaki don kama ruwa kenan ji kake tim! Ya faɗi ya zube a bakin ƙofar kamar matacce.
AWANNI BIYAR KAFIN NAN....
Misalin ƙarfe takwas na dare, Ɗan Mutuwa na haramar fita tare da Duna, sauri yake yi ya je su yi zama meeting akan kayayyakinsu da suke saka ran a saka nan da kwana uku, wayarsa ta dauki ƙara. Ganin Hindatu ce ya sanya shi ɗagawa da sauri don dama tun ɗazun yake gwada wayarta ba ta shiga.
"My Dear.."
"Yi hakuri Yallaɓai, ba ita ba ce. Suna na Mansur daga Dr K's Hospital."
Dakyar ya hadiyi miyau mai zafi. Kirjinsa ya hau bugu da ƙarfi.
"Ina jinka, meke faruwa?" Ya tambaya a can ƙasan makoshi.
Nan yake shaida masa hatsari ta yi amma jikinta da sauki, yana iya zuwa yanzu. Ai nan da nan hankalinsa ya