Showing 42001 words to 45000 words out of 177840 words
gidan, ba musu kuwa ta biyemata. Ɗan fitar da ta yi da Maama ta ji dadinsa sosai, zuwa lokacin manta ji ba ta kaunar rayuwa a dakin don har falon takan fito. Hajja da Umma abin ya musu dadi. Umma dai dama ta san duk daren dadewa dama za'a zo gurin.
Koda ta gansu sun sauki ƙasa ita da Safina murmushi ta yi. Ta maida hankali ga taya Baba Saude girki don acewarta zaman shiru babu wani aiki takura ta yake yi.
"Umma zamu je mu dawo." Fadin Haulatun. Kai kawai ta gyaɗamata kafin su fice tana sanye da riga doguwa ta atamfa ɗaya daga cikin wacce aka karɓo daga wurin tela. Ta yane kanta da mayafi. Kusan hatta tsawonsu ya zo ɗaya da Safina bayan shekarun da dama ɗaya ne.
Su shiga can, su faɗa nan, kowa ya ga Haulatu mamakin yanda aka yi Safina ta shawo kanta yake har ta yarda ta fito. A ƙarshe suka ƙarasa ɓangaren Alhaji don gaishe shi. Tun daga ƙofar shiga Safina ta yi saurin dakatawa gami da riƙo hannun Haulatu. Ta dube ta cikin rashin sanin dalilinta. A ɗan tsorace ta ce.
"Ke mu wuce kawai, Yaya Sadauki na ciki. Yanzu kya ji ya balbale ni da faɗan rashin zuwa makaranta alhalin ciwon mara ce ta hana ni ɗazu amma yanzu na warke." Yamutsa fuska ta yi.
"Shi kuma waye hakan?"
Zaro idanu Safina ta yi.
"Ba ki san shi ba? Taɓ. Ai wallahi ya gan ni kashina ya bushe."
Haulatu ta ji wani irin haushin Safina yanda duk ta ruɗe akan wani ɗan adam. Ita a duniya ta tsani ta ga mace mai tsoron namiji kamar haka. Babu ma abin da take tunawa a kanta sai mijin Umma da kuma yanayin shakkarsa da Umman ke yi.
"Wallahi sai na shiga. Ke dallah taho muje. Ai dai ba zai kashe ki ba ko?"
"Yes, ba zai kashe ta ba. Amma kuma zai hukuntaki ke mai maganar."
Suka juya da sauri. Mu'az ne tsaye a bayansu yana ɗan murmushi. Ba yau ta fara ganinsa ba tunda yana leƙawa wajen Ummanta, kusan ma har sun ɗan fara sabo da Umman. Ita ce dai gaisuwa kawai ke haɗa su nan din ma sai sun hadu ba ta ƙule a ɗaki ba.
"Ina wuni Yaya Mu'az." Faɗin Safina, ita kuwa Haulatu dai huci take jin abinda ya ce, wai wani ƙato zai hukunta ta. Ita akwai ma namijin da ya isa ya yi mata ba ta rama ba? Ba ta tunanin akwai shi.
Mu'az na hankalce da yanayin yanda take cika da batsewa. Madadin ya amsa gaisuwar Safina sai ya ƙara fadin.
"Ku shiga mana kun tsaya. Ai ba dodonku ba ne Sadaukin."
Safina dai gaba daya jiki ya dauki rawa, ta zame hannunta daga na Haulatu ta ja baya.
"Aa, dama ni wajen Baba Dakta Daddy ya aike ni. Bari na je."
Kafin Haulatu ta dakatar da ita tuni ta fice da gudu-gudu. Ta ciji lebbanta na ƙasa don takaici ta maido kallonta ga Mu'az wanda shi din ma ita yake kallo da murmushi. Ya lura yarinyar dagaske ƴar diramar da ake faɗi ce. Sai ya ji ta burge shi. Shi yana so ya ga mutum mai kasada a rayuwa marar tsoro. Ko don hakan na daga cikin ɗabi'arsa? Bai dai sani ba. Ya rungume hannuwa a ƙirji ya ce.
"Kin san waye Sadauki kuwa?"
Ba ta san sadda ta ɗan harare shi ba, ya yi ƴar guntuwar dariya mai nuni d mamaki. Shi dai ƙanwar ƙanwarsa ke harara yau?
"Ko waye shi ai ba mala'ikan daukar rai ba ne. Kuma Allah ma bari ka gani sai na shiga."
Juyawar da za ta yi a fusace ta ci karo da mutum har wayar hannunsa na faɗuwa a ƙas. Ta waro idanu tana kallonsa, shi ɗin ma ita yake kallo ransa a tsananin ɓace.
"Ke wace irin mahaukaciya ce? Ba kya gani?"
Ya furta da kausasshen murya. Haulatu ta waro idanu sosai, wannan balaraben kuma waye shi? Fari mai ɗan faɗin fuska, da manyan idanuwa kalar nata. Yana da tawadar Allah ƙarami a gefen haɓarsa. Ga wani kwantaccen sajensa baƙi wuluk.
Abeed Ridwan Malumfashi kenan wanda ake kira da Sadauki, sunan da Alhaji ya raɗamasa. Ɗa ga Alhaji Ridwan da Haj Nuratu. Rainon Alhaji da Nene ne. A gabansu ya yi wayo har ya kammala karatunsa.
Yanzu kuma shi ke riƙe da babban kamfanin mahaifinsa Alhaji Ridwan na yin takalma designers da ma jakunkuna, abubuwan dai da suka shafi fata. Sosai Alhaji Ridwan ke alfahari da shi ba don komai ba sai irin ƙwazo da jajircewar Abeed din a fagen aiki, uwa uba zai wahala ka ƙure Abeed. Yana da kaifin basira da naƙaltar mutane. Wannan yasa Abeed ke da wuyar yarda da mutum, duk wanda ya yarda da shi kuwa, an san ko waye shi din mai amana ne na gaske. Idan kuwa aka yi rashin sa'a ka cutar da shi da saninka, to fa yana rabuwa da kai ne na har abada ba tare da ya ƙara waiwayarka ba. Jininsu da Mu'az ya haɗu kwarai, Mu'az ba shi da ɓoye-ɓoye shi ɗin kusan kai tsaye yake gudanar da lamuransa. Duk abin da ke ran Mu'az idan ka zauna da shi sai ka gane. Dalilin da yasa Mu'az ke shiga sabgar Hajiya Babba kenan duk da takun saƙar da ke tsakaninta da Mamarsa.
"To ai ban gan ka ba ne, karɓi wayarka."
Muryar Haulatu ta shiga kunnuwansa bayan ta durƙusa ta dauko wayar tana mai miƙa masa ba tare da ta ƙara kallon fuskarsa ba, kallon da yake mata ke tsorata ta amma ta daure.
'Taɓ, wannan dole Safinah ta gudu, mutum ga tsawo ga ƙira. Wannan ya murɗewa mutum wuya ai kashe shi zai yi murus.' Ta yi maganar a ƙasan ranta tana duban ƙafafunsa farare ƙal kai ka ce ba sa taka ƙasa. Ganin har lokacin bai karɓi wayar ba. Shi tsananin mamakinta ne ya kama shi. Ita kuwa wannan daga ina haka? Babu wani bada haƙuri babu komai.
"Miƙo nan." Muryar Mu'az ta ji, da sauri kuwa ta miƙa masa ba tare da ta jira komai ba ta juya ta nufi hanyar da za ta kai ta sashen Hajja. Da murmushi Mu'az ya bi ta, yau dai ya ga rashin ta idon Haulatu da ake faɗi ganin idanunsa.
"Who's this mad girl?"
Mu'az ya dube shi har a sannan murmushinsa bai gushe ba.
"Haulat."
Sadauki ya kalle shi dakyau kamar zai ce wani abu sai kuma ya ja guntun tsaki ya sa hannu ya karɓi wayarsa ya soma tafiya. Mu'az ya mara mishi baya da sauri yana ƙara labarta mishi cewa ai ita ce baƙuwar zuri'ar tasu, jika ga Hajja. Sarai ya gane kan zancen, hirar ce dai ta ishe shi. Ya kuma ci alwashin duk radda ta ƙara shiga gonarsa sai ya koyamata hankali.
"Ba ka da abin cewa ne muhimmi?"
Ya katse Mu'az ta hanyar wurga masa wannan tambayar. Mu'az ya shafi sumar kansa da bai jima da rage ta ba.
Ya fi kowa sanin waye ɗan uwannasa, hakan da ya yi na nuni da cewa ya gaji da zancen ne. Ya ma ƙosa ya kyale shi don haka ya ɗan yi wurgi da hannuwa cikin iska.
"Babu, zan je gidan gonar Daddy ne. Zan samu rakiya?"
"No, i am busy."
Daga haka ya yi gaba. Mu'az ya zura hannuwa cikin aljihu jeans dinsa gami da ɗan ɗaga kafaɗa. Shi fa ba ya son tafiya shi kaɗai, ya fi kaunar abokin taɗi duk da dai Sadauki bai fiye maida hankali a yi hira da shi ba amma saboda haɗuwar jini yana son zama tare da shi. Idan ma ka ga Sadaukin na dariyar da har haƙoransa suka bayyana to fa bayan su Alhaji da iyayensa, Mu'az ɗin ne a layi. Sadauki ya ba shi shekara ɗaya, amma hakana suke zamansu tamkar sa'annin juna. Wani tunani ya zo mishi ya yi murmushi.
"It will be fun." Ya furta a fili kafin ya juya ya fiddo waya ya yi kiran Safina ya ce ta shirya su yi mishi rakiya gidan gona ta kuma kira ƙawarta Haulatu.
***
Safina jiki na rawa ta miƙe bayan kammala waya da Mu'az, Maama dake ɗaga ankon iyaye na bikin su Raudha da Batulu ta dube ta.
"Ke kuma da wa kike waya? Saurin zuwa ina kike kuma?"
Ta ɗan ji kunya kaɗan ya kamata duk da cewar ta sani, Maama kaɗai ce a gidan ta san irin ƙaunar dake a ranta na Yaya Mu'az. Babu abin da take ɓoyemata dangane da rayuwarta. Maama mace ce ta mutane, ta riƙe girmanta, tana kuma jan yaran ƴan uwanta a jiki, dalilin da ya sa kenan ta zama abokiyar shawarar da yawa a cikin yaran. Sam ba su raina ta ba.
Safina kusan za'a ce haihuwarta ne kawai ba ta yi ba, amma tun ma kafin ƙaddara ya raba ta da uban ƴaƴanta, ake kai mata Safina tana wuni. Yanzun ma dai kusan rabin rayuwar Safina a babban gida take yin sa ba hannun mahaifinta Dakta Hashimu ba.
Murmushi Maama ta yi don ta gane mai kiran.
"Aiken ki ya yi?"
Kai Safina ta girgiza kafin ta murmusa ta ce.
"Cewa ya yi mu shirya ni da Haulatu zamu yi mishi rakiya gidan gona."
Maama ta jinjina kai.
"Sai ki je ki faɗamata ku tafi. Allah ya tsare."
Daga haka Safina ta amsa da amin ta dauki wayarta ta shige daki. Mayafi ta dauko wanda ya hau da atamfar jikinta ta yafa ta ƙara shafa hoda a fuskarta gami da fesa turare. Tsaye ta yi ta ɗan kalli kanta. Daidai gwargwado tana da kyawunta wanda ta gado a wurin mahaifiyarta da ta kasance ƴar ƙabilar shuwa. Ba ta da tsayi amma babu laifi masha Allah ta a da dirin jiki mai fisgar hankali. Ta sauke ajiyar zuciya ta sanya takalmi ta fito zuciyarta cike da tunanin dalilin da ya saka Yaya Mu'az bai taɓa yi mata kallon abar so da ƙauna ba face na zallar ƴan uwantaka da zumunta. Sanin dai kowa yana ɗan ɗasawa da ita sama da sauran, hakan ya ja wasu cikin yanmatan masu son sa ke kishi da ita. Ba su san ita ɗin ma bai ko taɓa furta kalmar so gareta ba.
***
Haulatu sadda ta shiga sashen Hajja kuwa, falon ƙasa ta yi zamanta tare da Baba Saude dake aikin yanka alayyahu.
"Ƴar Umma, lafiya na ga fuskarki ba walwala?" Faɗin Baba Saude tana dubanta. Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta yi ƴar dariya.
"Toh Baba Saude, aiki biyu dai kike yi kenan a yanzu. Na saka wa mutane ido da na girki ko?"
Baki sake Baba Saude ke kallonta. Can kuma ta girgiza kai.
"Ni kike faɗawa haka Ƴar Umma?"
Ganin sauyin fuskar Baba Saude sai Haulatu ta daina dariyar.
"Na ɓata maki rai ne? Ni fa ba wani abu nake nufi ba. Kawai dai na ga duk yanayin da mutum ke ciki kina ganewa kiyi magana. Ina nufin kin damu da damuwar mutane, kina kula da kowa toh."
Baba Saude ta kalle ta, tuni ta fahimci dama ba ta tauna magana, Umma ma ta sha faɗamusu yadda yanayinta ya ke amma komai na buƙatar tsawatarwa da kuma gyara. Don haka ta ce.
"Na fahimce ki yanzun, sai dai kalamanki na farko ba su dace ki yiwa duk wani ko wata da suka girmeki ba kin ji ko?"
Haulatu cike da jin ba dadi ta amsa da to kafin cikin damuwa ta ce.
"Wai ni Baba Saude don Allah ya zan yi ne na gyara yanayin maganata? Umma da mutane da dama sun sha faɗamin ban iya magana ba. Tab, ai Umma sosaima dukana kawai ne ba ta yi ita fa lallai ban iya magana ba. Na rasa ya zan yi na gyara. Kuma wai fa sai ki ji ana cewa ina yiwa babba rashin kunya ko ina faɗawa wanda ya girme ni baƙar magana. Hakane wai?"
Ɗan murmushi Baba Saude ta yi, sai yanzun ta saki fuskarta.
"Kar ki damu, ki dinga kiyaye duk abin da kika faɗi ki ka ji an ce ba daidai ba ne, sannan zama da mutane yau da gobe zai sa ki sauya. Na ji ma za ki fara zuwa islamiyyar da yaran gidan nan ke zuwa ko? Ki dage da zuwa, ilimi na sauya rayuwar ɗan adam."
Ta murmusa. Sosai maganganun Babar suka yi mata dadi, daga haka ta miƙe ta haye sama. Ba jimawa da shigarta falon wurin Umma da Hajja, Safina ta shigo da sallamarta. Duban Umma ta yi ta nemi iznin Haulatu ta zo su yiwa Yaya Mu'az rakiya gidan gona. Jin abin da ta ce nan da nan Haulatu ta tamke fuska gami da ɗan turo baki. Ta gane waye Mu'az din, shi ne dai suka gama dirama yana son nuna mata girman isa da ƙarfin ikon da Sadauki ke da shi akan yaran gidan. Ita kuwa ba ta jin za ta yarda ya juya ta kamar waina a tanda. Jin Umma ta nuna hakan babu laifi ya sa da sauri Haulatu ta katse godiyar Safina da fadin,
"Ni fa babu inda zan je."
Fadin haka yasa Safina ta shiga haɗa ta da Allah gami da kwaɗaita mata yanayin gidan gonar, faɗi take.
"Wallahi wurin zai burgeki sosai, har da su ɗawisu da jimina da barewa. Ya haɗu ƙarshe. Ga kayan marmari kala-kala."
Jin haka kuwa Haulatu ta waro idanu.
"Dagaske? Toh jira na dauko mayafi." Daga haka ta yi ɗaki da sauri ta bar Hajja da dariya. Tana son Haulatu sosai, Allah ya jarabci zuciyarta da ƙaunarta ga Haulatun ba ta nata.
Ta fito sanye da wani hijabinta mai kyau ruwan ƙasa wanda aka yiwa ado a hannu da kewayen fuska. Suka kama hanya don tuni har Mu'az ya ƙara doka wa Safina kira.
***
Da sauri Haulatu ta bude gidan baya ta shige tana ƴi wa Safina dariyar mugunta don tun a hanya Safina kan su ƙarasa take roƙonta akan ta shiga mazaunin gaba ita a baya za ta zauna don ba ta nutsuwa idan ba ta nutsuwa idan ta na kusa da Mu'az. Har Haulatu sai da ta tambaye ta meyasa? Kodai tana son sa ne, amma Safina ta harareta cikin wasa. Ta yi dariya kawai a sannan.
Mu'az ya kalle ta ta cikin madubin gaban motar.
"Dariyar ta mene ne? Matsoraciya."
Ta haɗe fuska daidai sadda Safina ta bude gidan gaba ta zauna.
"Ni wallahi ba wanda nake tsoro sai Mahaliccina."
Ya yi murmushi.
"Good."
Shi ne kawai amsar da ya ba ta daga haka bai ƙara uffan ba. Duban Safina ya yi.
"Madam, ƙara rufe ƙofarnan ba ta rufu ba."
Ai kafin ma ya ƙarasa tuni ta buɗe ta kuma rufewa. Haulatu ta ɗan taɓe baki, a ranta fadi take 'Ai ga matsoraciyar a gefenka.'
Sun yi tafiya mai ɗan tazara kafin su iso wani ƙaton wuri mai gate. Hon ya yi aka bude suka shiga ya yi parking. Gaba daya suka fito, Haulatu ta bude baki tana kallon wurin. Babban wuri mai fili, a can gefe an yi gini lafiyayye mai ɗan girma, gefe guda kuwa wuri ne na musamman da aka yi shuke-shuke masu kyau da burgewa. Ya dubi Safina.
"Ku na iya zagayawa kafin na kammala. Ki nunawa ƴar ƙauyen nan wurare."
Ya ƙarashe yana duban Haulatu, ita kuwa ta ɗan harareshi. Ya yi murmushi ya sanya baƙin gilashinsa.
"Ni kike harara?"
Ta kauda kai tana ɗan tsuke fuska ba ta tanka ba, daidai sadda wani ya zo wurinsa suka yi gaba suna maganganu. Haulatu ta dubi Safina yanda take bin Mu'az da kallo tana wani murmushi kamar me. Zagayowa ta yi ta dawo ta gabanta gami da jingina bayanta jikin motar. Safina ta kauda kai tana wayancewa da fadin.
"Muje na nunamaki wu.."
Hannunta Haulatu ta riƙo hakan ya hana ta yunƙurin tafiyar da ta yi niyya.
"Wai son shi kike yi? Wannan ɗan wulaƙancin? Ke kuwa me za ki yi da shi don Allah?"
Nan da nan Safina ta tamke fuska.
"Kar ki ƙara ce mishi ɗan wulaƙanci please. Ko babu komai idan an cire ma ƴan uwantaka ya girme mu. Kuma wallahi ma rashin fahimtarsa ne ba ki yi ba. Yana da kirki da fara'a, kawai watakila don ba ku taɓa zama wuri guda ba."
Haulatu ta jinjina kai cikin gamsuwa, ta karɓi gyaran. Suka soma tafiya sannan ta katse shirun.
"Ya san kina sonsa?"
Murmushi Safina ta yi tana mai shaƙar iskar wurin da ke kaɗo ƙamshin ganyen gwaiba da ma na sauran kayan marmarin wajen.
"Bai sani ba, ba kuma na jin yana sona ma. Muna hira da shi, a duk cikin kannensa ma ya fi kula ni mu yi hira kadan. Sauran kuwa yana nunamusu hali na seniority. Wallahi tun fa ina ƙarama ban san mene ne so ba nake kaunarsa."
"Taɓ! Iska na wahalar da me kayan kara. To kuma idan ya zo ya auri wata ba ke ba ya za ki ji? Ni fa shiyasa bana son lamari na soyayya, wannan ai wahala ce. Shi ake cewa son maso wani ko?"
Ta ƙarashe gami da yin dariya tana maida dubanta ga wasu kyawawan geese da ke wasa cikin ɗan tafkinsu.
"Uhm." Shi ne amsar da ta samu daga Safina, ba ta kara ce mata uffan ba har dai Haulatu ta fahimci ranta ya ɓaci ta lallaɓa ta ba ta haƙuri. Ga mamakin Haulatu har da hawaye Safina ta fitar, ta kuma jinjina girman son da Safinar ke yi ga Mu'az. A ranta tana ji kamar ta yi dariya ko don ba ta san me ake kira da son ba? Ba ta da masaniyar ya ake jin sa idan ya kama zuciya. A fili dai tausarta ta dinga yi har a ƙarshe ta ce.
"Ke daga yau ma zan dinga ce maki Mrs Mu'az. Sunan ya yi?"
Safina na dariya ta zaro idanu.
"Rufamin asiri don Allah. Ai bayar da kai ne na bari ya sani ma. Kira ni da sunana na yanka Safina. Ki kuma taya ni addu'a please."
Murmushi Haulatu ta yi dake ƙara mata kyau.
"Shikenan Mrs..au, Safina. Ai ke tawa ce, ba zan manta da kaunar da kika nunamin ba tun ma farkon ganinki da ni. Ba ki hantare ni ba."
Suka yiwa juna murmushi. Tun daga nan wata ƙauna ta domin Allah ta ɗarsu a zuƙatansu mai girma.
Suna tafe suna cin guava da suka tsinka suka wanke, Safina na