Showing 108001 words to 111000 words out of 177840 words
samun labarin abin da ka shuka a baya? A'a Zaidu, kar ka sake, kar kuma ka fara. Ni dai babu hannuna cikin wannan zancen. Ka rufa ma kanka asiri ka dauke idanunka a kanta. Ka bar gini tun ran zane."
Daga nan ta miƙe fuskarta babu ɗigon fara'a ta tsallake shi ta wuce zuwa ɗakinta. Zaid ya kasa ko motsi, idanunsa suka kaɗa. Dama ya sani, zai fuskanci sama da hakan, kamar kuma yanda ya yi wa kansa alƙawari, zai jure har ya cimma burinsa. Don haka ya miƙe cikin ƙarfin gwuiwa bisa shawarar da ya yanke na yin zancen da Maama.
***
A can babban gida kuwa, shirye-shiryen babbar sallah kawai ake yi, Haulatu sosai take farin ciki babu ma kamar idan ta juya ta ga walwala da annashuwar mahaifiyarta ya dawo har ya ninka na baya. Takan yi hamdala a zuciyarta. Zuwa lokacin ta ɗan samu sa'ida daga yawan kiran da Zaid ke yi mata har ma da turo saƙonni sai tunaninta ya ba ta cewa ya gajiya ne. Shi kuwa Mu'az ta kula ma yanzu babu abin da ke haɗa su face gaisuwa. Ba ya ko jan ta da hira kamar koyaushe. Hatta Umma sai da ta tambayi ba'asi, aikuwa ta sanar da ita komai. Umma ba ta ce uffan ba duk da a ƙasan ranta ta ji daɗin rashin ba sa fuskar da Haulatun ta yi, ko ba komai ta fi kaunar su tsira da mutuncinsu. Sam ba ta kaunar abin da zai ƙara haɗa su da Momin Mu'az.
Ranar Alhamis ana gobe za'a fara azumin goman farko na Zhul-Hajj. Kasancewar babu islamiyya, Radiya da Safina da kuma Haulatu suka shirya don ziyartar Maimuna jikar Hajja ɗiya ga Haj Hadiza don su duba ɗiyarta dake fama da malaria. A hanyar fita daga babban gate zuwa inda Gali Direba ke jiransu a waje suka ga Zaid ya fito a motarsa. Da sauri Haulatu ta kauda kai ta cigaba da tafiya yayinda Safina da Radiya suka gaishe shi ganin ya nufo su.
"Noor."
Jin sunan da ya ambaci Haulatu da shi har yake bin ta a baya duk da ta ƙi tsayawa ballantana ta gaida shi ya sa Safina da Radiya kallon juna baki sake kafin su maida kansu.
Haulatu kuwa ranta ya ɓaci, fuska ɗaure ta dube shi bayan ya shiga gaba ya hana ta nufar gate.
"Lafiya?" Abin da ta furta kenan. Zaid ya ɗan numfasa, rabon da ya gan ta ba zai ce ba. Ta ƙara kyau da haske.
"Idan na aikomaki saƙo ba kya reply, kin ji ni shiru, ba ki damu da sanin halin da nake ciki ba. Rashin kaunar ta kai a yanke alaƙa koda ta zumunci ne?"
Ta dube shi a fisge ta kauda kai, ya ɗan rame.
"Sauri muke yi, Malam Gali yana jiranmu."
Abin da ta furta kenan cikin bagarar da wancan zancen nasa ganin su Safina sun ma fice daga gate din zuwa waje. Duk sai ta ji ta tsargu, wato Yaya Zaid ya shirya yi mata tonon silili, abin da take ɓoyonsa yake son bayyanawa duniya a yanzu.
"Ba wannan zancen nake son ji ba Noor..."
"Please suna na Haulatu. Kar ka ƙara kira na da wata Noor."
Ta na kai wa nan ta ƙara yunƙurin tafiya sai dai ya kuma dakatar da ita ta hanyar riƙe gefen mayafinta. Ta fisge mayafinta.
"Kar ka ƙara taɓa ni Yaya Zaid. Na ce maka ka fita hanyata amma na ka ke yi ka shigemin hanci da ƙudundune. Da alama ka shirya daɓawa kanka wuƙa, shikenan mu zuba, ga fili ga mai doki."
Ta na kai wa nan ta banka masa harara ta fice. Sam ba ta ganinsa da wani girma ko kaɗan a yanzu. Kallon mutum mai mugun son kansa ta ke mishi. A motar duk yanda ta yi zaton jin wani abu daga Safina da Radiya ta ga ba haka ba, sun share batun kamar ba su kula da komai ba, sai ma hirar duniya da suke yi suna kallon tiktok su na gulma. Ganin babu mai yi mata zancen a cikinsu sai ita ma ta saki jiki ta watsar da zummar daga baya za ta fayyace musu komai idan sun dawo.
Sun samu tarba daga wajen Maimuna, dama ita ba ruwanta kamar ba Haj Hadiza ce ta haife ta ba. Ta bambanta da Ihsan da Fahima. Yarinyarta guda mai sunan Hajja da ake kira Husna. Ita ke fama da ƙyanda. Gidanta tsaf, mijinta ma'aikacin gwamnati ne. Daidai gwargwado asirinsu a rufe, sun sha hira da dariya. Ta yi musu girkinta mai dadi sun ci sun yi nak. Sai bayan la'asar suka yi shirin tafiya, tamkar kada a rabu, har bakin ƙofa ta yi musu rakiya Husna na ta kukan sai ta bi su ta je wurin Hajja. Sai da dabara sannan ta haƙura.
***
Zaid kuwa wannan karon ma Hajja ba ta wani sakar masa fuska ba, suna gaisawa ta kunna rediyonta ta na jin shiri. Umma ce dai ta sakar masa sosai amma duk jikinsa a sanyaye ya miƙe ya fita da zummar ƙarasawa ciki. Bayan tafiyarsa Umma ta dubi Hajja.
"Hajja don Allah ki yi hakuri haka ki yafewa yaron nan. Ni tausayinsa nake ji. Gaba daya ya kasa samun sukuni, ke kuma duk sadda ya shigo ko ya kira ba kya wani sakar masa. Tun da dai abu ya wuce mai afkuwa ta afku ba shikenan ba? Sannan mutum fa ba ya aurar matar wani."
Hajja da tun soma maganar Umma ta rage sautin rediyon dama hararar Umman take tana jira ta kai aya kafin ta tanka.
"Na'imatu kenan. Ke dai ki kalli mutum kawai. Amma ni tsakanina da Zaidu, hum. Na dai yi shiru. Wa ya fadamaki ya wuce kuma? Toh idan ba ki sani ba ki buɗe kunne ki ji ni dakyau, har gobe Zaituna tana mutuwar sonsa. Ni na rasa hasken fatar ke kwasarta ko kuwa wannan tsawonnasa marar ƙira kamar mace."
Umma dai ta girgiza kai ba tare da ta ce uffan ba amma haƙiƙa ta ji ya soma ba ta tausayi. Fatanta Allah ya daidaita lamura komai ya wuce.
"Ni gani nake ma wannan sunne kan da ya ke yi da biyayyar nan duk ta dole ce da sa kai, na fi tunanin ba banza ba. Watakila dai an yi dace uwarsa ta ci galaba wajen tanƙwara shi, wataƙila kuma mutuwa ce ta kusanto shiyasa ya gyara hali."
Maganar Hajja ya sa Umma dariya, ba tare da ta ce komai ba. Wayarta dake gefe ta yi ƙarar shigowar saƙo ba ta ko damu da buɗewa ba don ita dai idan har saƙo ya shigo wayarta bai wuce na kamfanin layukan dake kan wayar.
***
Cike da mugun kaɗuwa Maama ta saki baki tana kallon Zaid. Ta ma kasa fitar da harafi ko guda ɗaya. Daga yanayin duban da ta ke masa sai ya ƙara jin babu dadi. Kada dai a nan ma ba zai samu goyon baya ba. Sallamar Sadauki ce ta sa nan da nan Zaid haɗe girar sama da ta ƙasa, meyasa bai zaɓi lokacin shigowa ba sai da ya riga shi zuwa gidan? Sadauki shi ma ganin wanda ke zaune ya maida murmushin da ya shigo da shi ciki. Hakan kuma bai sa ya haƙura ya fasa sanyo kai falon ba. Maama ta amsa sallamarsa tana duban Zaid sannan ta maida kallonta ga Sadaukin. Sam ba za ta so su ɗora maganar a gabansa ba. Zai fi ta takawa abin burki tun wuri.
Zama ya yi ya gaida Maama ta amsa tana ɗan murmushin yaƙe. Ta maida duba ga Zaid.
"Ba ka gaida ɗan uwanka ba."
Ya ji kamar ta watsa masa ruwan zafi, sai dai Maama ce, dukkansu ba sa tsallake umarninta. Ba tare da ya kalli inda Sadaukin ke zaune ba ya ce.
"An wuni lafiya?"
Shi kuwa Sadauki ganin yanayin gaisuwar sai ya yi kamar bai ji ba. Sai da Maama ta yi magana kafin ya ce.
"Oh, lafiya."
Abin ya yiwa Zaid zafi ƙwarai don haka ya miƙe.
"Maama bari na je mu gaisa da Baba Alhaji, ma ƙarasa maganar idan na fito."
Hakan ya yi wa Maama dadi don haka ta amsa masa da toh shi kuma ya juya ya fice.
"Sadauki, ba a haka, girma ku ke yi, bai kamata ace kai a matsayinka na babba ba ku na yiwa zumuncinku riƙon sakainar kashi ba. Ni ban ga amfanin wannan rashin jituwar taku ba."
Ɗan murmushi Sadauki ya yi.
"Maama kin fi kowa sanin halayyata. Ba ni da riƙo, shi ne dai mai wannan banzar halin. Kuma ace abubuwa da suka faru tun ƙuruciya ba su wuce ba? Sannan ko yau ko gobe ya ƙara yin wani laifin bai fi ƙarfin na yi mishi faɗa ba."
Maama ta jinjina kai, babban abinda a baya ya sa Zaid ƙullatar Sadauki bai wuce don kama shi da ya yi yana shan sigari ba, lokacin ƙuruciya da tashen balaga ne suka kwashe shi ya buga wannan wautar kuma a bayan gida. Sau biyu Sadauki ya kama shi ya kuma gargaɗe shi, a na uku ne ya je ya sami Baba Alhaji ya sanar da shi. Ai kuwa Zaid ya fuskanci hukunci sosai, wannan shi ne babban dalilin da ya sa har gobe ya kasa ganin mutuncin Sadauki. Shi ma kuma a hali na rashin yarda irin ta Sadauki, ya sa sam Zaid ya sire mishi. Ya sha yi mishi rantsuwar ya bari amma sai ya tarar ya na yi. Yanzun ne ba shi da masaniya tunda ba wuri ɗaya suke rayuwa ba.
"Shikenan. Ina fatan ba wata matsala ce ba yanzu?"
Faɗin Maama kai tsaye. Ya shafi sumar kai yana murmushi.
"Ko ɗaya. Toh wai ma shi ke nan ba zan zo ganin uwata ba sai da matsala?"
Ta yi dariya ganin yanda ya yi maganar a shagwaɓe.
"Ai fa kam ban ga laifinka ba."
Daga haka kuma suka shiga hirar da ta shafe su har Zaid ya dawo, ganin Sadaukin ya ja guntun tsaki ƙasa-ƙasa, wannan ba zai bar shi ya yi abin da ya ci ɗamarar yi a yau ba kenan? Sadauki kuwa kamar ya san ganin bai mishi daɗi ba, ya ƙara kishingiɗa ya hau danna waya saboda Maama ta maida hankali ga tambayar Zaid har ya fito?
"Na fito Maama, sai mun yi waya kawai."
Ta gyaɗa kai.
"Shi ke nan toh, ka gaida mutan gidan."
"Ok, za su ji." Daga nan ya yi gaba, jin Maama ta sauke ajiyar zuciya ya sa Sadauki dubanta ba tare da ya ce komai ba.
"Abeed, ajiye wayarnan mu yi magana."
A duk lokacin da Maama ta kira sunansa na yanka ya sani ko mene ne zai fito daga bakinta to fa mai muhimmanci ne."
Wannan magana ta Maama ya faɗa kunnen Mabruka da ta soma saukowa daga matattakala sai dai ba ta riga da ta kawo inda za su hangi fuskarta ba. Wannan ya sa ta ja ta tsaya da zumuɗin so ta ji me zai fita a bakin Maama.
Maama kuwa duban Sadaukin ta yi a nutse ta fara magana.
"Ina tunanin lokaci ya yi da za ka fito a mutum ka nunawa yarinyarnan kana sonta. Tunda dai kana gani jami'a za su shiga, ba ka san mai gaba za ta haifar ba. Gudun samun kowace matsala."
Ya murmusa. Wato ya na ƙaunar Maama, irin ƙaunar da bayan mahaifiyarsa Momi Nuratu to fa babu wata sai ita. A farko abin da ke ransa kenan da ya shigo, ya na so ya nemi shawararta don ya kasa danne so, ba ya jin ma akwai yanda zai yi ya cigaba da ɓoyon abin da ke ransa game da Haulatu ba tare da ya cigaba da amayo shi ba. Sai dai ya ji nauyin ya yi wa Maama zancen, aka yi katari ita da kanta ta furzar.
"Nima na yi wannan hangen Maama."
"Yauwa, ka yi kokarin shawo kanta, ka kuma bari sai komai a tsakaninku ya daidaita sannan ka je mataki na gaba. Allah ya zaɓamaku abin da ya fi alheri."
Ya amsa da amin, Mabruka ta juya ta koma sama cike da tunanin wace ce wannan da Sadaukin ke so ake batun ya shawo kanta? Ta sani dai ba Jannat ba ce tunda ita yanzu ma tana shirin shiga aji biyu a jami'a. To wace ce?
'Ko a cikin ƴan matan nan ne masu shiga jami'a? Ko Haulatu?'
Wata zuciyar ta jefamata tambayar, sai ta ji wani irin zafi a ranta. Wai da ace yaran nan na ganin mutuncinta kamar yanda suke ganin na Maama, da tuni ta san wacce ake zance a kanta ba wai ta tsaya kame-kamen banza ba. Ta ja tsaki har ta koma dakinta zuciyarta sam babu dadi, balle ma idan ta tuna nan zuwa bayan sallah mai son auren Maama zai fito a yi komai, wasu hawaye suka zubomata. Kowa na aure har matasan yaran yan uwanta da take nan aka haifa amma ita duk wanda ya zo da zummar aure sai ya fasa kamar wanda ake kora. Tun ba ta biyewa bin malamai har ta soma, kullum yanzu cikin zargin mutane take da daukar alhaki don wani Malami ya ce mata na kusa da ita ne ya yi mata asiri. Sau da yawa ma tunaninta kan ba ta cewa Maama ce ta yi mata asirin. Shiyasa nan duniya ta ke jin tsanarta kai ka ce ba ciki guda suka fito ba. A yanzu ji take ina ma akwai yanda za'a yi wanda zai auri Maaman ya dawo da maganar kanta.
'Ke Mabruka, tsaf zai yiwu matukar kika koma wurin Malam Mai Carbi.'
Wani ɓangare na zuciyarta ta raya mata, ai kuwa ta yi zumbur ta dauki wayarta, kai tsaye Malamin ta kira ta zayyane mishi buƙatarta. Ya ce zancen ba na waya ba ne, ta zo ta same shi a gidansa gobe amma babu abin da ba zai gagara ba. Nan suka yi sallama ta ajiye wayar zuciyarta kamar ta yi tsalle ta fito don dadi. Ai ko ba ta aura ba, ta rantse Maama ta gama aure ita ma a duniya. Gwara su zauna su yi ta kallon juna.
***
Bayan Magriba ƴanmatan na zaune a dakin kwanan Safina dake faman haɗa kaya don gidansu za ta je yin babbar sallah. Haulatu da Radiya suna taimaka mata amma zuƙatansu duka ba dadi ji suke kamar su bita su tafi wurin Dakta Hashim da mahaifiyarta da ake kira Yaya. Tana da kirki ita ma kwarai. Ga kawaici da hakuri, ba ta taɓa nunawa duniya Safina ɗiyarta ce, ta maida riƙonta kacokam ga Maama. Ita ce ɗiyarta ta farko, ƙannenta biyar cif da ita cikon shida.
Haulatu ta fisge rigar da ke hannun Safina.
"Feenah." Ta furta, sunan da sukan kira ta kenan a wasu lokutan. Ganin sun tsaya su na dubanta ta ɗora.
"Wai ma ba za ku tambaye ni game da abin da ku ka ji Yaya Zaid na fadi ɗazu da safe ba?"
Suka dubi juna suka sa dariya ita kuwa ta hau harararsu.
"Ah, mene na tambaya? Kin san dai mun gane ko?"
Fadin Radiya. Safina na ƙarawa da "Ai shi ne."
"To na rantse ba ku ga daidai ba. Abin da ku ka gani ba haka ba ne."
Nan ta labarta musu duk abin da ya faru tun ma farkon saƙonnin da ake aikomata a waya har zuwa yau din."
Jikinsu ya yi sanyi.
"Amma Yaya Zaid shi ma dai ya na da mantuwa. Yanzu duk abin da ya faru a baya ya manta da har ya ke tunanin wani zai kalle shi ya goyamishi baya akan ki? Wane irin kuri da cika baki ne bai yi ba na nuna shi fa ba ya ra'ayin auren zumunci. Hum, wai ma, har ya manta da Anti Zaituna?"
Radiya ta taɓe baki.
"Ke ma dai Safina kin manta su maza ba kunya suka cika ba? Ai idan su na son abu idanunsu rufewa yake yi. Ni kam ba na maki fatan ma mutum irin Yaya Zaid, sam halinsa na riƙo na tsana, amma idan an cire wannan ba shi da matsala."
"Hum, ai ko mene ne Radiya, ni ba zan taɓa ba shi fuska ba har abada kuwa. Ashe ma kaunar da nake yiwa Anti Zaituna na ƙarya ne. Hum, wai ma dagaske yake shi aurena ya ke so yi, bai dubi da fuskar da zai kalli Hajja ba ma? To koda ina ra'ayin soyayyar nikam ban ga wanda zan iya so ba."
"Har Yaya Sadauki?"
Tambayar da Radiya ta jefomata ne ya sa ta jin wani irin faduwar gaba, sunansa kadai idan ta ji yana ma ta yawo a kwakwalwa ta ji ta wata daban. Ballantana kuma idan ta ji muryarsa ko ta yi tozali da shi. Ta kauda kai daga kallon tuhumar da suke bin ta da shi jin sun kashe mata baki, daƙyar ta tattaro jarumta ta ja guntun tsaki.
"Ni wai meyasa ku ke min wannan tunanin? Shi ya ce maku yana sona?"
"Ba fa batunsa ake ba, ke muke tambaya idan misali ya ce yana son naki, za ki amince?"
Ta yi murmushi ba tare da ta tanka ba ta dauki wayarta tana ƙoƙarin miƙewa suka yi saurin dakatar da ita daga mai warce wayar sai mai riƙo hannunta dole ta faɗa gadon suna dariya.
"Banzaye, ni wallahi duk kun takuramin. Ke ba za ki mana batun Yaya Mu'az ba."
Safina ta yamutsa fuska cike da jin wani iri a rai saboda fami da aka yi mata.
"Ni kinga na fa haƙura da shi. Na kula son maso wani nake yi. Don rannan na ji yana cewa Maama wai ta baza idanu yana dab da gabatar mata da wacce zai aura kuma a family dinnan take. Ban baku labari ba saboda ban ga amfaninsa ba tunda dai dama ni ke so ba wai ni ake son ba. Na soma rage sonsa, a hankali ma zan daina gaba ɗaya."
"A family? To wa yake so kenan?" Radiya ta cafe zancen, ita ko Haulatu sai ta ji duk ta tsargu, ko dai ta ba su labari ne? Kai ba za ta iya ba. Gwara idan zancen ya fito ta nuna ba ta ma san ita yake so ba sai da ya furta din. Mutumin ma da sun bar ko waya balle tura saƙo na waya?
"Ohon masa. Shi ya sani, in sha Allahu ma a wannan azumin na Zhul-Hajj zan dage da addu'ar