Showing 135001 words to 138000 words out of 177840 words
dube ta.
"Toh kenan kina nufin na zuba ido ya cutar da Maimunatu? Don ya ganta yarinya ba mai son hayaniya ba?"
"A'a, ba nufina kenan ba. Ki bar ni zan yi magana da Maimunatun, in sha Allahu za'a dace, zai bar ta ta fito. Amma abun duka ba na tashin hankali ba."
"Ai shikenan." Ita ce amsar da Hajja ta ba Umma sannan aka bar maganar.
***
Haulatu a can kuwa tun da Hajja ta ce mata Sadauki ne zai zo ɗaukar su ta ji wani irin sanyi a zuciyarta, sai ta nemi ciwon kan ma ta rasa.
"Wai ke murmushin me kike ta yiwa mutane ne? Ke ko jimamin daren da muka yi ba kya yi? Ni dai na san Mama yau zan sha faɗa." Radiy ke maganar duk ta rikice duk kuwa da sun yi waya da Mamar, ta sanar da ita Hajja ta saka a zo ɗaukarsu amma hankalinta bai kwanta ba.
"Rabu da ita Radiya, ni wallahi dama na ce maki son Yaya Sadauki take yi amma ki na ganin kamar wasa ko? Yanzu ke ba ki kula duk cikin murnar zai zo..."
Haulatu ta yi saurin toshe mata baki ganin wasu mata dake cire lalle su na kallonsu. Cikin ɗan raɗa ta ce.
"Banza, mene haka wai? Ba kya ganin a cikin mutane muke?"
Dariya Radiy da Safina suka yi duk kuwa da gajiyar da ke tattare da su, don ma Allah ya sa sun sauke nauyin sallolinsu.
Wayar Haulatun ce ta yi ƙara, ganin sunan Yaya Sadauki saman screen sai ta nutsu gami da ɗagawa da sallama. Ya amsa mata kafin ya ce.
"Ba wa Safina ta kwatanta min inda ku ke."
"Ai zan iya ma Yaya."
"Ko? Toh ina jin ki. Allah yasa kar ki ɓatar da ni."
Ta yi ƴar dariya wanda shi ɗin ma tana jin sautin nasa murmushin. Tiryan-tiryan kuwa ta yi masa kwatance tunda dama gidan bai da wani ɓata kusa yake da transfomer a gefen titi. Ai kuwa ba jimawa da katse wayar sai ga shi ya ƙara kira ya ce su fito. Dama sun kammala komai suka yi sallama da Hasiya mai ƙunshi da matan dake nan suka fito. Motarsa tana daga tsallaken gidan har ya yi U-turn.
"Kalli mutuniyar sai wani goge maiƙon fuska take da gefen mayafi."
Radiya ke yiwa Safina zancen ƙasa-ƙasa, tana jin su amma ba ta da sukunin ramawa don gani ta ke yi kamar kowane motsi da za su yi idanun Yaya Sadauki yana kansu.
Duk saurin da Radiya da Safina ke yi don su samu mazauni a gidan baya amma ina, Haulatu ta yi farat ta buɗe ta shige ta saitin bayan Yaya Sadauki. Nan da nan kuma Radiya ta riga Safina shiga ɗaya ɓarin, a dole Safina ta buɗe gidan gaba ta shiga. Sadauki ya kalle ta bai ce komai ba ya na amsa gaisuwarsu. Sai da ya kunna fitila haske ya mamaye motar, sannan ya dube su, Radiya ya iya gani bai samu damar kalle sanyin idaniyarsa ba don ta maƙale sosai a murfin ƙofar. Kamar ya ce wani abu sai kawai ya fasa ya kashe fitilar. Tafiya yake yi kawai sautin kiɗa na tashi kaɗan-kaɗan na muryar breaker cikin waƙarsa na Burina. Shi ɗin idan ya so nishaɗi yakan kunna waƙoƙi, ranar da ustazancin ke kansa kuwa sai dai ka ji tashin ƙira'a ko kuwa yabo. Sai yake jin waƙar Burina ɗin na shigarsa tamkar da shi ake, to ba shi kaɗai ba, ita kanta Haulatun sai ta lumshe idanu ta yi shiru tana shaƙar ƙamshin turarensa, kaunarsa na ƙara ratsa ta. Kafin su kai ga isa gida tuni an fara ruwa kuma waƙa ɗaya suke ta maimaici, daga Burina ya ƙare sai Sadauki ya ƙara ya ƙara maido ta. Sadda suka isa kuwa ruwan ya yi ƙarfi sosai, ya dube su.
"Ga ruwa kuma, ko na baku lema tunda dare ya yi."
Suka amsa da toh, ya ba Radiya umarnin saka hannu a baya ta dauko lemar sannan ta bude ƙofa ta fito da yake ita tana ta gefen wajen ƴar rumfar adana motoci sai ruwan bai taɓa ta ba har ta buɗe lemar. Haulatu ma ta fito ta ɓangaren hannun da Radiya ta ke, tuni Safina ita ma ta fice.
"Ba zan ga lallen ba?" Maganarsa ta ɗan dakatar da Haulatun daga fita, ta juyo suka haɗa idanu, tarr suke ganin juna cikin hasken fitilar motar da ya kunna. Kusan a tare suka numfasa, ji ya yi lamar ya shekara bai gan ta ba. Ita kuwa Haulatu ta kasa ba shi amsa, ta kuma kasa fita. Can kuma a hankali ta haɗe hannuwanta ta yo gaba da su kaɗan yanda zai gani, ji ya yi inama halal ɗinsa ce, da babu abin da zai hana shi sumbatar hannun saboda yanda lallen ya yi mata kyau ainun.
"Ya yi sosai, ku je kin bar ƴan uwanki cikin ruwa. Ki ajiye waya a kusa, zan kira."
Ta ji abin banbarakwai sai ma ta kasa amsawa da sauri ta fita, duk diramar da suke yi, Safina suna kallo don hasken dake cikin motar ya ba su wannan damar ganin abin da ke faruwa a ciki. Suna kama hanya da gudu gudu suna yiwa Haulatu tsiya, ita ta ma yi laƙwas kamar wacce ruwan saman ya doka. Duk yanda Haulatu ta so su yada zango a gidansu kafin ruwa ya tsagaita amma ina, su kansu sun fi so su gan su a nasu ɗakunan musamman Radiya da Mamarta duk ta damu. Suka yi sallama Haulatu ta shige su kuwa suka yi gaba.
Umma na ganinta ta harare ta.
"Wato ku ba ku san dare ya yi ba ko? Ku je ku zauna haka, idan da layi me ya hana ku haƙura?"
Haulatu wacce ta zube a kujera cikinta har wani kuka yake yi tsabar yunwa, ita sai sannan mata ji ashe ciwon kan ba wai ya tafi gaba ɗaya ba ne, tsabar ɗoki da kauna ne ya sa ta ji ya lafa a ɗazun, haƙuri kawai ta ba Umma. Hajja kuwa sannu take mata bayan ta sa jikar Baba Saude da ta dawo daga ƙauye ta kawowa Haulatun abinci. Ita kuwa hannu ta mike ta wanko a banɗakin falon, koda aka kawo abincin tana can nunawa Hajja ƙunshi da Umma, sun yaba sosai, ta dauki farantin abincin da wayarta ta nufi sama. Hajja na fadin ta zauna ta ci tukunna amma cewa take yi sai ta yi wanka tukunna. Nan kuwa tunanin kar Yaya Sadauki ya kira ne a gabansu ya hana ta ci.
***
Safina kuwa tana shiga ɓangaren Baba Alhaji ta iske a na ta hayaniya, Najeeb da Haidar ake riƙewa su kuwa suna ta botsarewa musamman Haidar akan a bar su su daki Anti Mabruka wai ta zagi Maama a gabansu. Maama na gefe tana hawaye, ƙarshe ta taso ta daka musu tsawa. Duk suka nutsu, Haidar jikinsa har rawa yake yi. Autan Maama, Nazifi ba ya nan, dama shi hannun Haj Fatima dake Kano, koda yana nan shi yana da sanyin zuciya kamar na Maama ba lallai ne ya ce uffan ba.
Jin hayaniyar ta yi yawa ne Baba Alhaji ya fito yana tokare sandarsa, nan ya dubi kowa ya kuma ba Anti Mabruka da Maama umarnin su zo ɓangarensa. Sai a sannan Najeeb da Haidar suka fice zuƙatansu babu dadi. A bakin mai kula da Nene, Yahanasu, Safina ke jin tun farkon abin da ya hada. Wai Anti Mabruka ce ta iske Maama a falon tana zaune da su Najeeb ta hau yi ja mata Allah ya isa tana kuka tana cewa ita ta yi mata asirin da ta rasa mashinshini kuma har ga shi nan babu kunya ba tsoron Allah duk da ta hayayyafa tana da budurwar zuciya. Abin dai babu dadin ji don har da zagi, dalilin fusatar su Najeeb kenan. Su da a baya ba sa goyon bayan auren Maama, sai suka ji wani kwarin gwuiwa kan ta yi auren bisa kalamin Anti Mabruka.
Baba Alhaji sosai ya yiwa Anti Mabruka tas, ya kuma rantse muddin ta sake yiwa ƴar uwarta munanan ƙazafi sai dai ta nemi wani uban ba shi ba. Kuka sosai ta saka wai dama can Baba Alhaji ya fi son Maama a kanta. Maama dama da hawayenta ta shigo, sanadiyyar baƙaken kalaman da Anti Mabruka ta shiga jefowa ya sanya Baba Alhaji jin wani jiri na kwasarsa daga zaune, dama ba wani cikakken lafiya ba, kirjinsa ya hau zafi nan da nan ya sume a wajen, a gigice Maama ta yi kansa tana salati, jin ihunta ya sa su Safina shigowa, duk da ruwan da ake bai hana sautin Maama fita ba, ganin har ruwa an yayyafa amma Baba Alhaji ba shi da niyyar farfadowa ya sa Maama karɓar wayar Safina bayan ta fidda nata password, ta kira Alhaji Ridwan. Ita kuwa Safina sheƙawa ta yi a guje kirawo su Najeeb. Su ma a gigice suka shigo falon Baba Alhaji, babu wanda ya bi ta kan Anti Mabruka da ta yi likimo a gefe kamar wacce aka tsoma a randa. Ba jimawa sai ga Daddy Ridwan tare da Sadauki duka hankulansu a tashe. Ba a sanar da Baba Dakta ba gudun kar a tada hankalinsa don shi ma yana fama da matsalar ciwon sugar sai kawai a wannan ruwan suka yi asibiti da shi.
Dalilin da ya hana Sadauki kiran Haulatu a daren kenan. Hajja ma ba ta sani ba, Umma ce kawai Maama ta kira ta sanar da ita bayan an jima har ma an shawo kan Baba Alhaji, hankalin Umma ya tashi sai dai bisa umarnin Maama ba ta sanar da Hajja ba ta ce a bari zuwa safiya tunda dare ya yi. Umma dai duka ba ta samu nutsuwa ba duk da an ce ya samu sauki har ya yi bacci ma. Haulatu koda ta ji sai ita ma ta shiga damuwa.
Washegari kuwa da safe labari ya baza gida Baba Alhaji na asibiti ba lafiya, hankalin yan uwansa, Hajja da Baba Dakta ya tashi. Nan da nan aka ɗunguma zuwa asibitin duk kuwa da Dakta Hashim (mahaifin Safina) ya hana kowa shiga wurinsa don kar a takura masa amma Hajja da Baba Dakta sai da suka shiga suka gan shi hankalinsu ya kwanta. Ba wani abu ba ne ya haifarmasa da tashin hawan jininsa ba face damuwar da ya shiga, shi faɗan da yake yi ma a zo a sallame shi kar a sanya mutane zaryar zuwa dubiya amma Dakta Hashim, ya ce a bar shi ya samu hutu.
Bayan sun fito ne Baba Dakta ke tambayar Barr Faisal dake gefensa abin da ya faru. Shi da bai da labarin ya yi shiru sai a bakin Sadauki ya ji komai. Maama ta labartamusu a jiya, hakanan ya samu ƙarin bayani daga bakin su Haidar din. Ran Baba Dakta ya ɓaci.
"Mutuniyar banza, ashe shiyasa ban ga ƙeyarta a asibitin nan ba. Mabruka anya tana son gamawa da duniyarnan lafiya?"
Haka ya yi ta faɗa ita kuwa Hajja na taya shi. Dama Hajja yanlafiyar giwa... Dakyar dai aka taushe su suka haƙura suka bar zancen.
A yanda Baba Alhaji ya matsa dole aka sallame shi don ya rantse shi fa a kansa ba za'a ɗaga auren Maama ba. Haka aka tattara aka koma gida sai dai a yammacin sai da Baba Dakta ya tara meeting na iyaka yaransu babu jikokin gidan. Ya wanke Mabruka tas a gaban su Maaman da su Daddy Ridwan, ya kuma sassauta a ƙarshe da yi mata nasiha kan imani da ƙaddara da nunamata komai ai yana da lokacinsa. Anti Mabruka dai ba don ta saduda ba sai don tilas, ta nemi gafarar Maama, har a zuciya kuma Maama ta amsa da ta yafemata. Daga nan dai aka rufe zancen da addu'a. Koda aka fito, Mabruka ji ta yi ta ƙara tsanar Maama, abin sam ya ƙi fita a ranta, wato yanzu ba iyakar iyayensu ba, hatta ƴan uwa kowa ya tsane ta sanadin Maama, ta ci alwashin koda Maama ta yi auren nan, babu ita ba kwanciyar hankali har abada. Da wannan ta shige ɗakinta ranta na susa.
Haulatu dai kitson da ba ta je ba kenan, hakanan ta haƙura saboda wannan tashin hankali. Fahima ta iso a ranar sai ko wasu baƙi daga Malumfashi. Kirki da mutunci irin na Maama yasa gidan ya cika kamar wannan ne aurenta na farko don ita ɗin ta kowa ce sannan abin hannunta sam bai rufemata idanu ba.
***
Washegari...
Tun safe Haulatu ta fice makaranta amma hankalinta gaba ɗaya yana ga bikin Maama, babu yanda ta iya don ba ta son ta yi tsallaken rana. Safina ma kanta ta riga ta tafiya don ko sadda ta aiko mata saƙo cewa ta tafi gida, ita sannan ma suna tsaka da ɗaukar lakca. Ba su ne suka fito ba sai wuraren ƙarfe uku da rabi, gaba ɗaya kuma hankalinta ya yi gida. Ko bi ta wayarta dake faman ruri a jaka ba ta yi ba har ta tako zuwa titi. Tsayuwar jiran abin hawan ma aiki ya zame mata. Can sai ga wata jan mota ta taho har ta gifta ta, ta yo ribas ta tsaya daidai saitinta. Ganin haka Haulatu ta daure fuskarnan tamkar hadarin kaji karshe ma ta taka ta soma tafiya don ta gwammace ta fara rage zango da dai wannan tsayuwar motar da ba ta san ko ta wace ce ba a gabanta tunda ba ka hango na ciki ba, balle yanzu da duniyar ta zama abin tsoro.
"Assalamu alaikum." Ta ji sallama a gefenta, juyawa ta yi, wani matashin saurayi ne kakkaura, sanye da shadda. Baƙi ne mai ɗan gemu. Ba ta taɓa ganinsa ba sai a ranar, wani murmushi ya ke mata. Ta kauda kai fuska daure ta cigaba da tafiya.
"Afuwan, na maki sallama ba ki amsa ba. Nasan ba daidai ne na tsaida ki a titi ba. Idan ba damuwa don Allah ki taimake ni da kwatancen gidanku da lambar waya."
Haulatu kamar ta yi me don ta takaici, ita gaba daya ma ya ishe ta.
"Ni ba ni da waya kuma an sanya min rana don Allah ka bar bibiyata."
Daga haka ta ƙara gaba, Allah ya taimaka bai kuma biyo ta ba, ta samu abin hawa ba ta ma tsaya ciniki ba ta faɗa. Ba tare da sanin cewa mutumin tuni ya koma mota ya bi bayansu ba. Ji ya yi ba zai iya haƙura ba sam. Suna isa ta iske ƙofar gidan nasu da mutane, baƙin Malumfashi ne maza sai ko wasu cikin abokan matasan gidan, sam ita ba ta ma kula da sauran ba don wurin a cike yake, ko ba komai bikin Maama ake yi, mace mai son zumunci kuma ta mutane. Koda ta sauka ta biya mai napep ba ta jira komai ba ta faɗa gida kanta na ƙasa. Sadauki da ke tsaye gefe tare da wasu abokansa suna ɗan taɓa hira, ya gan ya kuma ya ga wata mota da ke bayansu, har saurayin ya fito daga motar bai dauke idanu a kansa ba. Ganin saurayin na waige-waige ya sanya shi ƙarasawa gare shi bayan ya nemi ƴan mintuna daga waɗanda suke tare. Sallama ya mishi, dama jiran wanda zai yiwa magana ya ke don haka da sauri ya miƙa hannu suka yi musabaha.
"Ina fatan lafiya?" Cewar Sadauki yana ƙare masa kallo. Murmushi saurayin ya ɗan yi da shafar suma.
"Lafiya lau, suna na Kabeer Maitama dama wannan baiwar Allah na biyo, sai na ga ta shiga nan shi ne..."
"Matar aure ce."
Shi ne abin da Sadauki ya faɗi kai tsaye kuma fuska a haɗe. Kabeer jikinsa ya yi sanyi, wato dagaske take da ta ce an sanya mata rana kenan? Sai ya ba shi hakuri ya shige mota ya bar wajen. Sadauki koda ya koma ga abokansa ma bai samu nutsuwa ba. Wato dai da gaskiyar Khaleefa da yace idan ya yi sake za'a yi mishi shigar sauri. Aikuwa zai yi kokarin kafa gwamnatinsa tun kan hakan ta kasance.
A gidan kuwa Haulatu ta iske jama'a sai hada-hada ake yi. Yara sun cika wuri suna ta wasanni, dama tun jiya ta ji wai a can babban farfajiyar gidan Daddy Ridwan aka shirya walimar tunda yana da girma sosai don ya fi na ɓangaren kowa ma girma. Koda ta shiga sallar la'asar kawai ta gabatar ta ci abinci sannan ta faɗa wanka. Da ta fito ta kira wayar Safina. Tana ɗagawa ta ji ta cikin hayaniya har ba ta jin me take faɗi saboda muryar Ado Gwanja da ta cika kunnuwanta a waƙarsa ta Warr sai kawai ta katse kiran. So take ta ji sun shirya ko kuwa, ba ta so ace ta riga su sanya kayan. Tana nan zaune da ɗaura ƙirji Umma ta shigo, ta sha ado cikin atamfarta mai gold sai sheƙi take, ba za ka taɓa cewa ta jikinta Haulatu ta fito ba, sai dai ka yi tsammanin ƙanwarta ce. Dama sam ba su ga juna ba sai yanzun aikuwa Haulatu ta washe baki.
"Masha Allah, Ummana kin yi kyau sosai kamar wata ƴanm.."
Daƙuwar da hararar da Umman ta yi mata ne ya sa dole ta katse abin da ta yi niyyar fadi tana dariya.
"Ni sa'arki ce ko Haulatu? Ban hana ki zama da ɗaura ƙirji ba? Ki tashi ki sanya kayanki."
Ta dan turo baki.
"Ni fa Umma ba na so na saka su Safina ba su sanya nasu ba. Ita kuma ina kiranta a waya ba ta ɗaga ba."
Umma ta girgiza kai.
"Ai shikenan, sai ki yi ta jira kin ji ko?"
Ta yi murmushi ta na duban Umma, ba kwalliya a fuskarta don ko hoda ba ta shafa ba, amma duk da haka kayan sun sa ta fita fes. Ganin Umma ta zauna gefen gado ta ɗan yi shiru ya sa ta fadin.
"Umma lafiya?"
Umma wacce maganar da Haj Hadiza ta gwaɓa mata akan wai kamar tana jira, ace ba ta kai ga kammala idda ba amma ta cancaɗa adon atamfa haka? Har tana cewa Maman Safina dake zaune wai toh su bi a hankali dai, Na'imatu ta kusan fara zawarci. Wannan abu ya yiwa Umma ciwo duk da cewa Maman