Showing 93001 words to 96000 words out of 177840 words

Chapter 32 - FITAR TSIRO COMPLETE HAUSA NOVEL BY RUFAIDA UMAR

11 Jul 2024

79172

su da kallo har suka fice kafin ya girgiza kai da tausayin Haulatu.

***
A hankali suke tafiyar kanta yana ƙasa, sunan Allah kawai take ambato a zuciya, ita kaɗai ta san me take ji. Ga radadin ciwo ga na zuci, sam ba ta ji zafin Hindatu ba sai ma tausayinta da ya lulluɓe ta, ba ta san waye ainahin Alhaji Ibrahim ba tunda dama ba su taɓa karo da juna ba, asalima ba ta san sunansa da ɗin Ibrahim ko inkiya ba, kullum a hirarsu idan ba Mijin Umma ba, to sai Malam Khalil idan ta na ji da iskancin na sosai. Su yi shaƙiyancin su dara haka suke yi. Kai a tunaninta koda ma ace ta taɓa ganinsa, ya yi sauyawar da sai na jikinsa ne za su gane shi, na jikin ma ba kowa ba.

"Babu rayuwar da za ta tafi babu jarrabawa, duk wanda ya yi imani sai an jarabce shi, kar ki bari imaninki ya raunana da ganin tamkar ke kaɗai ce cikin mummunan ƙaddara irin wannan. Ki godewa Allah kina da gatan da wasu ke nema ido rufe. Wani a shege aka haife shi, ya kuma yarda ya yi imani da kaddararsa, ya rungumi rayuwarsa a haka. Kowa da yanayin jarrabawarsa, idan muna kallon wadanda muka fi, zamu kasancewa masu yawan godiya ga Allah, idan kuwa hangenmu yana kan waɗanda suka fi mu, to koyaushe muna cike da ƙunci na zuciya da rashin godewa ni'imomin da Allahu ya yi mana, musamman na lafiya da kwanciyar hankali."

Shiru ya biyo bayan maganganun da Sadauki ke yi idanunsa na ga hanya, ita kuwa jifa jifa tana juyowa ta dube shi har ya kai aya, can kuma ya nisa ya ce.

"Ki ƙara haƙuri, wataran sai labari. Kina da damarmaki da yawa a rayuwa idan Allah ya ƙaddara, kar ki bari sanadin mutum ɗaya da Allahu ya jarabceki da shi, ki rusa rayuwarki da ma burinki. In sha Allahu za ki zame wa zuri'armu abar alfahari wataran. Kin ji?"

Ya karashe da murya ƙasa-ƙasa yana dubanta. Ita ma aka yi sa'a ta juyo ta dube shi, ji ta yi wani abu tun daga yatsar ƙafarta har tsakar kai, nan da nan ta kauda idanunta tana gyada masa kai. Sadauki ya kauda nasa idanun yana sauke ajiyar zuciya. Tsantsar kaunarta na ƙara mamaye gangar jiki da ruhinsa. Ji yake ina ma yana da damar ɗauke mata dukkan waɗannan matsalolin da damuwa, koda ace bai yi nasarar raba ta da duka ba, to ya zame mata tamkar wani majinginar dafawa. Inuwa yayin da ake tsananin rana, hakazalika bargo a yayin tsananin sanyi.

"Nagode."

Ta furta a hankali. Har suka ƙaraso ɓangaren Hajja babu wanda ya ƙara magana, dab da ƙofar ya ja ya tsaya cikin dubanta.

"Na so na yi mantuwa, daure ki zo daga nan."

Ya furta cike da kulawa yana nuna mata gefe guda da ƙofar Hajja gudun kar wani ya ji. Ta kuwa daure ta ƙarasa hannunta ɗaya riƙe da kai. Idanunta har sun ƙanƙance take dubansa.

"Aminiyar taki kuna tare har yanzu?"

"Eh. Amma mun jima bamu yi magana ba."

Ta faɗi tana tuna yanda suka yi ƙarshen wayarta da Hindatu wacce ke tsoron ma kalar mijin da za ta aura, har take tunanin ko ɗan ƙungiyar asiri ne. Zai yi magana ta yi saurin katse shi.

"Na tuna mun yi magana da ita dab da aurensu."

Ta ba shi labarin duk yanda suka yi, ya jinjina kai.

"Ok, ina so koda ace kun ƙara magana, kar ki gwada mata wani abu. Idan da dama ki binciki inda take da zama da zummar za ki kawo mata ziyara kwanan nan. Na tabbata ba za ta yi zaton wani abu daban ba tunda kin ce ba ta san da alaƙarku da shi ba. Kin fahimta? Sorry."

Ya furta kalmar sorry lura da yanayinta, ta amsa da toh sannan suka ƙarasa.

Hajja na ganinta ta hau sababin meyasa ta fita alhalin ba ta jin dadi, sai bayan ta gama faɗan, Sadauki ya gaishe ta ta amsa fuska sake. Ya gaida Umma wacce ta fito daga kicin hannunta riƙe da jug na kunun gyaɗa. Ta zuba wa Hajja shi ma ta sa Baba Saude kawo kofi ta tsiyaya mishi. Wannan ne ya zaunar da shi, sha yake yi amma hankalinsa na ga Haulatu dake kwance, kunun ma ta ce ta ƙoshi da sha.

Hajja duk ta damu sai lallaɓawa take don ta samu ta sa wani abu a cikinta.

"Ni youghurt nake so."

Ta faɗi a hankali yanda Hajjar ce za ta ji, Hajja ta ce.

"To anya akwai shi a firij? Sai dai fura. Kin ji wai yagwat za ta sha."

Ta ƙarashe da maida zancen ga Umma. Umma ta taɓe baki.

"Tsirfa ne fa irin na Haulatu, ko an kawo ni na san ba lallai ta sha ba."

Jin haka Sadauki ya miƙe.

"Umma in sha Allahu za ta sha. Bari na je zan aikomata yanzu ba jimawa. Ta sha maganin kafin nan ko kan zai sauka tunda ta ci abinci ɗazu ku ka ce."

"Yauwa Sadaukin Alhaji. Allah ya yi maka albarka."

Tuni ya fice, Umma kuwa ta dubi Haulatu.

"Sai ki tashi ki sha maganin, Allah yasa kar ki ba shi kunya ya kawo ki ƙi sha."

Ta miƙe zaune jikinta a sanyaye, ledar maganin ta janyo daga saman tebur ta buɗe ta shiga ɓallowa.

Aikuwa can ba jimawa sai ga saƙo daga Sadauki, Najeeb ya kawo. Leda ne na manyan robobin youghurt sai kuwa wata ledar daban na gashin kifi mai dankali da sauce a gefe. Ita kanta ta yi mamakin yanda ta ci sosai, kusan rabin kifin nan sai da ta cinye shi a cikinta, youghurt din ne ba ta sha ba wai tsoro take ji kada ta kutirce, an ce ba a son haɗa nono da kifi lokaci guda, Hajja dai dariya ta yi.

Wayarta take kallo tana duban lokaci ko Sadauki zai kira ta da labarin yanda suka yi da Alhaji Tasi'u sai dai shiru, ga Umma ta hana ta fita ko'ina, ita kanta ba ta jin za ta iya fitar duk da cewa kan nata ya bar ciwo hakanan zazzaɓin ya sauka sai rashin ƙwarin jiki. Ƙarfe bakwai da mintoci ta ji wayarta ta ɗau ƙara, da sauri ta zabura ta dauka har Umma dake gefe tana jan casbaha sai da ta dube ta, duban tuhuma. Sai ta ɗan waske ta saita fuskarta. Madadin Yaya Sadauki, ta ga Zaid ne, guntun tsaki ta ja gami da latse kiran. Bai gaji ba ya kuma kira, sai ta katse kiran ƙarshe ma ta saka wayar a airplane mode ganin Umma na ta dubanta. Koda Umma ta idar da laziminta ba ta ce mata uffan a kai ba ta fita zuwa falo, ita ma zaman shirun da tunane-tunane marasa kan gado ya sa dole ta miƙe ta bi bayanta. Nan ta zauna kusa da Hajja dake kallon tashar Arewa har aka yi kiran sallar isha'i. Kasancewar ba ta da tsarki ya sa ta miƙewa ta shige ɗaki. Daga kwanciya kuma bacci ya yi awon gaba da ita ba ta farka ba sai wuraren sha ɗayan dare, nan ma Umma ta tashe ta akan ba ta sha maganin dare ba. Ta daga wayarta da tunanin ko Yaya Sadauki ya kira tana bacci, abin takaicin ta ga ashe ba ta kunna ba tun ɗazu.

"Af, yauwa, Sadauki ya kira ni ya ce ya jikin naki, ya ji wayarki a kashe. Khaleefa ma ya kira ya ce a maki sannu. Sai Mu'azu da ya shigo kina bacci."

Umma ta ƙarashe tana tsaida idanunta kan ɗiyar don nazarinta. Sai ta ga kawai ta amsa da toh ta kauda kai, duk ta tsargu da kallon da Umman ke yi mata. Babu saƙon da ta ji ciwo irin na Sadauki, meyasa ta kashe wayarta alhalin dama ta san zai iya kira ya ba ta labarin halin da ake ciki. Miƙewa ta yi ta shige banɗaki don kama ruwa da sauya auduga.



A ɓangaren Sadauki kuwa, ya samu tabbacin ƊanMutuwa ba ya ƙasar gaba ɗaya ya yi tafiya Dubai. Hatta da adireshin gidansa sai da aka samo mishi. Ya yi wa Alhaji Tasi'u godiya suka yi sallama. Daga nan ne ya kasa sukuni ya kira Haulatu, ba don ba ta labari ba sai domin tuntuɓar lafiyarta sai dai a kashe. Dole ya kira Umma ya ji ya jikin har tana mishi godiyar abin da ya aiko, ta ce Haulatun ta ci sosai. Hakan ba ƙaramin daɗi ya yi mishi ba.

***
Momin Mu'az ce ta shigo falon sai dai har ta tsaya daga bayansa bai sani ba a dalilin ya buɗe hoton Haulatu a wayarsa yana kalla. A gigice ta daka mishi tsawar da sai da ya juyo har wayar na neman suɓucewa daga hannunsa. Ba iya tsawar ce ta firgitashi ba, har da jin magana a sama tunda bai san da shigowarta falon ba. Zuciyarta har wani tafasa ya ke yi ta nuna shi da yatsa.

"Me kake kallo? Wace ce nake gani kamar waccan ƴar barikin marar cikakken asali?"

Ya sunkuyar da kai yana mai jin zafin kalaman Mominsa a kan Haulatun.


***
Za mu ɗora gobe in sha Allah ko ba yawa.
*Littafin nan na kudi ne. Ki siya ki karanta hankalinki kwance gudun shiga haƙƙin marubuciyar.* *Ibrahim Rufaida Umar, *9034973645 Opaybank.* *₦500* *Idan kin biya ki aiko shaidar biya ta 09034973645*



******

"Na yi magana ka sunkuyar da kai tsohon munafuki, ka ɗago ka faɗamin uban me kake yi da hoton wannan ballagazar."

Sai a lokacin ya magantu cikin sanyin murya ya ce.

"Momi please ki bar aibata mutum haka. Ko ba komai jinina na ce."

Ta saki baki galala tana kallonsa kafin ta ce

"Ni kake faɗawa jininka ce? Toh don ubanka baku haɗa komai da ita ba. Kai ɗin na haifeka a ƙarƙashin inuwar aure. Kai ɗan sunnah ne, ita kuwa har gobe bamu da tabbacin labarin ƙanzon kuregen da uwarta ra zo ta shimfiɗa mana. Ba wannan ba, zan maka kashedi da babbar murya, wallahi tun wuri idan ka san cewa wani abu ka ƙulla a rai dangane da yarinyar nan toh ka gaggauta warwareshi. Matuƙar ni dai uwarka Jamila ina raye ban yarda kuma ban amince ba da wannan haɗin gambizar. Don haka tun muna shaidar juna ka fita hanyarta. Kai idan ka yi kuskuren furta mata wata kalma ma da ta dangancin so ban yafe maka ba. Allah ya isa."

Kalaman suka yi mishi nauyi a kai, ya dube ta da idanunsa da tuni suka kaɗa. Ta watsa mishi harara gami da faɗin.

"Yes Mu'az, dagaske nake babu ja a furucina, ko bayan raina ka yi kuskuren neman aurenta Allah ya isa ban yafemaka ba. Tunda kai ba ka san ciwon kanka ba."

Daga haka ta miƙe fuu ta bar falon tana sababi da fadin Na'imatu da ɗiyarta sun zame musu annoba a gida.

Sai da ya ci mintuna kusan talatin a zaune ya kasa motsi sai tunanin kalaman da Mominsa ta yi, Haulatun da kullum kaunarta sabuwa ta ke a zuciyarsa ita dai ake nufi ya rabu da ita? Wannan wace irin jarrabawa ce mai nauyi? Dakyar ya iya miƙewa ya ɗauki wayarsa ya bar falon jikinsa a mace.

***
Washegari sosai Haulatu ta samu sauƙin jikinta sai dai ba ta bi su Safina makaranta ba don Hajja ta ce ta bari jikin ya ƙara ƙwari ko kuma idan ta kammala shan magungunanta. Umma ba su nan sun je Malumfashi biki ita da su Maama da Mabruka sai ko Momi Nuratu da Haj Hadiza. Bikin wani ne a dangi da Baba Dakta ya ce lallai su je su wakilce su, kwana ɗaya kawai zasu yi su dawo. Ita kaɗai ce zaune a falon ƙasa tana kallon wani shiri na series din India da ake haskawa a tashar Zee World. Sanadin Zaituna ta koyi kalla, a baya sam ba su dame ta ba. Baba Saude na sama suna shan hira da Hajja. Ya yi sallama ya shigo falon. Ta daga kai ta dube shi kafin ta miƙe tana amsa sallamar. Khaleefa ne. Gaishe shi ta yi ya amsa kamar koyaushe yana ɗan haɗe fuska.

"Ya jikin naki?"

Ya yi tambayar yana daga tsaye bayan kujera.

"Da sauki Alhamdulilah."

Gyada kai ya yi sannan ya ce.

"Hajja da Umma fa?"

"Umma sun je Malumfashi, Hajja kuwa tana sama."

"Oh, hakane, jiya ta faɗamin na so na manta."

"Ko ka manta ba." Ta furta a hankali, bai ji ba amma ya ga bakinta na motsi tana magana ƙasa-ƙasa.

"Kin ce wani abu?" Ya nemi sani. Ta girgiza kai gami da kallonsa ido a ɗan waje, kodai ya ji ne? Ta tambayi kanta. Ga mamakinta ma sai ta ga ya ɗan yi murmushi kafin ya juya ya nufi  bene.

Ta bishi da kallo sai ta sauke ajiyar zuciya. Yau dai ɗan Umma ne ya yi mata murmushi haka? Lallai a yi ruwa da ƙanƙara. Wayarta dake gefe ta yi ƙara, ta duba, ganin baƙuwar lamba sai ta tsargu, ko dai Zaid ne? Wannan yasa ta ƙi ɗagawa har ta katse, ba jimawa aka sake kira, dole ta jawo wayar ta amsa da sallama a bakinta. Wanda ta yi zato kuwa shi ɗin ne, ya amsa mata sallamar.

  "Ki na cutar da ni Noor, kina cutar da zuciyata akan abin da ba ni ke da ikon ɗoramata ko hana ta ba. Meyasa ki ka zaɓi yanke dukkan alaƙa da ni koda kuwa na iyaka zumunta ne ba soyayya ba?"

Ranta ya ɓaci, wai shi Yaya Zaid ko kunya ba ya ji wannan nacin da yake yi mata? Sam ba ta kula da Khaleefa dake saukowa daga bene ba ta shiga ba shi amsa.

"Yaya Zaid don Allah ka rabu da ni, ka fita hanyata. Na ce maka har abada ba za ka taɓa samun goyon bayana ba, wallahi koda ace ina sonka to ka haramta a gareni saboda Anti Zaituna ballantana kuma ni na fadamaka babu soyayya a gabana, babu soyayyar kowa a zuciyata. Ni bana soyayyar ba kuma ta burgeni balle a kai ga aure. So please ina roƙonka ka fita a hanyata. Kar ka ƙara sauya layi ka kirani idan kuwa ba haka ba na rantse maka sai na sanar da Hajja halin da ake ciki, ni na san za ta yiwa abin tufka."

Daga haka ta katse kiran ta ma saka wayar a plane mode gami da jan guntun tsaki ta jingina kai jikin kujera, idanunta ne kawai a daman talabijin din amma fa hankalin gaba ɗaya ta fi ga tunani. Shi Yaya Zaid meyasa ba ya abu da lissafi, gwara ma shi Mu'az da yake yana da raha kuma ga fushi, ta ga alamun fushin yake yo tunda bai ƙara gigin kiranta ba sa dai yawan shigowa ɓangaren Hajja don kawai ya sanya ta a idanu. Amma daga amsa gaisuwarta idan ya yi babu mai ƙara cewa wani uffan sai dai ya yi ta bin ta da kallo kamar zai haɗiye.

Khaleefa kuwa a hankali ya ƙarasa step uku da ya yi mishi saura ya sauko daga benen, ya ɗan kalle ta kaɗan, ba ta ko kula da shi ba don gaba daya ta tafi duniyar tunani, ya ɗauke kai ya juya ya fice. Dama duk ya shiga sun gaisa da mutan gidan don haka motarsa kawai ya nufa. A hanya ma tunanin kalaman da ya ji sun fito daga bakin Haulatu ya ke yi. Kenan Zaid ma yana sonta? Ba ma duka wannan ba, kalaman da ta yi akan ba ta soyayya kuma aure ba ya burge ta su ne suka fi tsayawa a ƙoƙon ransa. Hakan na nufin Sadauki shi ke so, amma ba su tare. Ko kuwa shi ma Sadaukin ba wai sonta yake yi ba, zumunta ce kawai ta haɗa?

'Lallai idan hakan ta tabbata, kar ka yi saken da za ka zo ka ciji yatsa.'

Wani ɓangare na zuciyarsa ya tunasar da shi. Ya jinjina kai yana jin ransa na daɗi, nan da nan fuskarsa ta cika da annashuwa da jin dadi. Bai kallon wani Zaid a abin da zai tokareshi daga neman auren Haulatu. Dama shi duk a zatonsa soyayya ce tsakaninta da Sadauki wanda ya ba muhimmin gurbi a rayuwarsa, ya sani, ƙarfin alaƙarsa da shi ya kai su iya hakura da abu don farantawa ɗayansu rai. Babu ma kamar Sadaukin, abubuwa da dama tun suna yara ya sha haƙura ya bar mishi. Dalilin yawan sadaukar da abu da yake yi ga ƴan uwansa shi ya ci girma ya samu sunan can daga Baba Alhaji. Har ya kasance ana manta ainahin sunan yankansa, wato Abeed.
  Da wannan kyakkyawan ƙudurin neman soyayyar Haulatu a sannu ba ta ƙarfi ba, ya rufe babin tunane-tunanensa.

***
  Ta gaji da zaman jiran Yaya Sadauki ya neme ta a waya, don haka kawai sai da daren wurin takwas na dare ta danna mishi kira. Ta runtse idanu jin ya soma ƙara, tsoronta kar ya ce don me ta kira. Ji ta yi ya yanke kiran madadin ya ɗaga. Ta dafe kai cike da jin haushin kanta, meyasa ma ta kira ba ta yi haƙuri har su haɗu ba? Ba ta kai ga gama zantukan zuci ba wayarta ta ɗauki ƙara. Ganin sunan Yaya Sadauki ya bayyana ne ya sanya ta sauke numfashi. Bayan ta ɗaga da sallama ya amsa.

  "Ya ƙarfin jikin naki? Ina fatan kin warware?"

Cikin jin dadin tambayar ta amsa.

"Eh Yaya, Alhamdulillah."

"Masha Allah."

Shiru ya ɗan biyo baya, can ya ce.

"Na'am, ina tare da ke. Kiranki na gani."

Sai ta gyaɗa kai kamar ya na kusa da ita.

"Oh eh, dama akan maganar da muka aka yi kwanaki ne na Mijin Umma. Ina so na ji ko..."

"Kar ki damu please, komai zai zo da sauki in sha Allah. For now dai, ba ya ƙasar an ce sun je Dubai. Da zarar ya dawo zamu san matakin ɗauka. Kin gane ko?"

"Eh."

"Good, ki bar sanya abin a ranki. Muna nan tare da ku, babu abin da zai iya yi maku na cutarwa in sha Allah."

Ta yi murmushi tana ɗan kama gefen gado da hannunta na dama saboda jin daɗin kalamansa masu nuni da kwantar da hankali.

"Soon za ki ji kyakkyawan labari akan karatunki. Ina fatan za ki yi murna?"

Haulatu ta miƙe tsaye don jin dadi.

"Sosaima."

Sautin murmushinsa ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login