Showing 54001 words to 57000 words out of 177840 words
rabuwa ki ke magana wai?"
Kuka Hindatu ta saka a wayar.
"Ya sake ni wallahi. Mun rabu da Badamasi. Shege dan iska. Allah ya isa tsakanina da shi."
Jin kukan Hindatun itama sai nata zuciyar ya karye, ko babu komai Hindatu ta kaunace ta, aminiyarta tun yarinta, hawayen ta shiga fitarwa tana fadin.
"Kin gani ko? Kin ga abin da ya sa na tsani na yi aure. Yaudara ce zallah a cikinsa, ya zo ya nunamaki so kamar gaske, ashe dama son a baki ne. Wai me kika yi masa?"
"Maganar akwai tsawo Haulatu, kuma kudin wayata ba.."
"Kar ki damu bari na kira ki, kashe."
Hindatu ta amsa da toh gami da yanke kiran.
"Ina jin ki, amma don Allah ki bar asarar hawayenki akan banzan nan." Cewar Haulatu bayan ta bi bayan kiran.
"Uhum, ba za ki gane ba. Na aure shi ba don kudinsa kawai ba, aa, saboda ina son shi. Amma bayan auren duk ya sauya, wannan kashe kudin da yake yimin ashe duka na yaudara ne don a waje ne. Sati biyu kacal a gidan ya sauyamin daga kyakkyawar cima zuwa cimar da ko a gaban Momi bana yi. Wai ni ke cin fara da mai babu ko salad ballantana su tumatur? Shi ke riƙe da muƙullin store ɗinsa na abinci, kullum shi yake auno abin da zan girka. Ko baƙo na yi sai dai kar na ba shi abinci. Ga neman mata na masifa. Ashe duka wannan zantukan nasa da ustazancin na ƙarya ne. Tun fara laulayi da na yi ya ke zagina, wai kamar wata akuya duka duka yaushe aka yi auren da zan dau ciki, shi ba ya son haihuwa, yaran da uwargidansa ta haifar mai ya ishe shi. Ya dage akan ɓarar da cikin, na faɗawa Momi. Nan fa ta zo suka yi zagi na uwa da uba tsakaninsu ƙarshe dai wannan ne silar da na bi Momi gida don ba zan juri ya zagarmin uwa ba. Shi kuma ya ce ya sake ni ba kuma zan dauki ko tsinke daga gidansa ba. Komai mallakinsa ne idan kuwa mun ƙi zai shigar da mu kotu kan a biya shi kudaden da ya kashe kafin aure. Hum. Yanzu zancen da nake maki, tsabar tashin hankalin da na riski kaina a ciki ya yi sanadin zubewar cikin, kin ga na kammala idda. Hum, Haulatu na kasa daina jin zafin wannan abu, mun zama abin gulma da zunɗe, wai har da su Baraka a masu yi min habaici sanadin da yasa Momi tashin dukkansu daga gidan kenan."
Labarin ya girgiza Haulatu, ta dai taya ƙawarta jimami sosai, ƙarshe kuma ta nuna mata kar ta damu kansa ya yiwa. Ta shiga ɗebe mata kewa har tana ba ta labarin ta yi waya har ta yi mata magana a whatsapp ba ta hau ba. Hindatu ta taya ta murna sosai.
"Zan hau kuwa yau din nan, don Allah ki aikomin hotunanki, kwana biyu ba a hadu ba."
Haulatu ta yi dariya.
"Sha kuruminki, zan aikomaki kuwa yanzu don kar na manta."
Daga nan suka yi sallama, aikuwa a take Haulatu ta zaɓi hotunanta wadanda Safina ta yi mata a gidan gona da ma kuma wanda ta dauka a gaban swimming pool na gidan ta tura mata. Daga haka ta miƙe ta haye saman tana mai son ba Umma labari sai dai ganin Khaleefa ya sanya tana mikawa Umma waya ta gaishe shi ya amsa ciki-ciki sannan ta shige dakinsu.
***
Kano...
Hindatu na kwance saman tabarma a tsakar gidansu, ba ta jima da saka data a wayarta ba ta shiga whatsapp. Saƙonni rututu ne suka faɗo har sai da ta zo kan baƙuwar lambar da take kyautata zaton na Haulatu ne ganin shaidar kamar hoto ne aka turo. Ta bude su duka tana kallo. Waro idanu ta yi tsabar mamaki. Momi da ke zaune a gefe ta kalli fuskar wayar itama.
"Wace ce haka ƴar gayu ki ka samu?"
Ta dubi Uwar baki bude.
"Momi, ba ki gane ta ba wai? Haulatu ce fa? Haulatu Khalil ta aminiyata."
Momi ta karbi wayar tana mata kallon ƙurilla. Ita ma ta sha mamaki tsantsa.
"Ikon Allah, ita kuma da suka bar nan, karuwanci ta faɗa?"
Hindatu wacce ta rasa bakin magana na dan lokaci sai a sannan ta magantun.
"Kai a'a, ni na san har abada Haulatu ba za ta bi wannan layin ba. Dama karshen wayar da na yi da ita kwanaki can da na matsa mata akan ina suke, ta cemin tana wurin yan uwan mahaifiyarta. Kar dai ace yan uwansu attajirai ne?"
Suka dubi juna da Momi.
"Aikuwa ya dace dai mu tabbatar. Wane gari ta ce suke?"
"Wai Katsina."
"Maza kira wayarta ku yi hira ko tambaye ta. Idan ma da hali ai kin ga sai muje mu ganewa idonmu."
Jin haka Hindatu ta jinjina kai, har ranta ta yi wa ƙawarta murna muddin ya kasance abin da take tunani ne ba wai zargin da mahaifiyarta ta yi ba. Ta dannawa Haulatu flashing, bai kai ko mintuna uku ba ta biyo bayan kiran. Ba su ko gaisa ba ta ce.
"Ke Haulatu, ke ce kika zama haka? Dagaske ke na gani a hoton da kika turomin?"
Dariya Haulatu ta yi.
"Ni ce Hindatu. Kin ga ikon Allah ko?"
"Na gani tabbas. Amma dai don Allah ina ne wurin da kika yi hoton nan?"
Haulatu daga can ta yi ɗan jim kafin ta yi dariya.
"Gidan wasu ne fa inda Umma ke aikatau. Suna da kirki dai, duk wani gwanjon kaya da ma cima mai kyau suka ba mu."
Ajiyar zuciya Hindatu ta sauke. Ta dan dubi Mominta kasancewar suna da wutar solar. Girgizawa uwar kai ta yi, Momin ta yi murmushi don dama ta sani ina Na'imatu suka ga wasu dangi masu arziƙi? Duk buge ce.
Bayan sun gama wayar, Hindatu ta labartawa Momin, dariya sosai na mugunta Momi ta yi.
"Ahaf, ni da na sani. Ke dai ki sha kuruminki, arzikin da muka ɗanɗana a baya, na yanzu zai ci ubansa. Bari a kwana biyu magulmata su rage tattaunawar nan zan je wurin Na Gangare ya haɗomana wani aikin. Kuma Badamasi na yi alƙawarin sai na sa an karya masa arzikin nasa mu ga ta tsiya."
Ita dai Hindatu shiru ta yi ba ta ce uffan ba.
***
Ɗan Mutuwa fa???
A can Kaduna kuwa, Ɗan Mutuwa ke zaune a falon gidansa da Hajiya Adama ta mallaka masa halak malak dake unguwar Malali. Hatta da kujeru da labulaye babu abin da ba ta saka ba, farko ma da ya bude ya shiga ya ga irin kayan da aka zuba a gidan sai da ya rikice ya fidda waya ya kira ta dom tabbatarwa da kansa ko tana sane da kudaden da kashe na zuba kayan furnitures, a cewarsa idan ma mantuwa ta yi ba ta saka an kwashe ba kafin zuwansa, toh ta aiko a kwashe mata kar ta bi shi bashi. A lokacin dariya ta sakarmasa.
"Kar fa ka damu, wannan gida da duk kayayyakin da ke cikinsa ba komai ba ne a cikin dukiyata. Ko kaɗan bai girgiza ba. Kai dai ka yi nazari sosai ina jiranka, gida irin wanda na mallaka maka, muddin ka bi shawarata na rantse maka sai dai ka zuba haya ko ka bayar sadaka. Amma kai kam sai ka fi ƙarfin shigarsa."
Zaro idanu ya yi a sannan, bai kai ga cewa komai ba ta yanke kiran.
Tun sadda suka yi waya ya nemi wuri ya sheme saman kujera yana ta saƙe-saƙen zuci. Kai kuɗi sun fa yi a rayuwa.
'Za ka zama abin da ba ka taɓa kawo wa ba. Hatta siyasar da ka jima kana kwaɗayi, koda ba ka shige ta ba, za fa a dama da kai tunda kana da silalla.'
Haka zuciyarsa ta dinga raya masa abubuwa da dama ya ji sosai son lamarin ya shige shi don haka jiki na rawa ya dau waya ya kira Hajiya Adama. Tana ɗagawa tun kafin ya kai ga cewa wani abu ta amshe.
"Ka amince kenan?"
Jinjina kai ya yi kamar tana gabansa.
"Kwarai na amince. Yanzu ya za'a yi?"
Yana jin sadda ta sauke ajiyar zuciya, murya cike da tsantsar farin ciki ta amsa.
"Ka zo Kano jibi, akwai taron da zamu yi, zan gabatar da kai a nan. Nima kuma na san hakan zai sa na ƙara samun matsayi fiye da wanda nake da shi yanzu a ƙungiyar. Ka yi kyan kai da ka zaɓi hanyar jin dadin duniya cikin sauƙi. Ƙwarai na taya ka murna Alhaji Ibrahim Ɗan Mutuwa."
Wannan sunan da ta faɗi a ƙarshe ya ƙara jin zumuɗi da wani ƙarfin gwuiwa kan hukuncin da ya yanke na ba da kai bori ya hau. Dariya suka saki cike da jin dadin nasarar da kowannensu zai yi nan ba da jimawa ba. Har suka yi sallama wannan suna da Hajiya Adama ta yi kiransa da shi ya na ta yawo a kwanyarsa, ya furta a baki ya kuma nanata a zuciya yana mai cike da jin annashuwa. Sai ya ji ma jibi ya yi mishi nisa, ya sani kafin nan da jibin tunani da mafarkan cikar burinsa sun ramar da shi.
***
Katsina...
Umma ta dubi Haulatu bayan ta saurari duka labarin hirarta da Hindatu daga bakinta.
"Kin kyauta da ki ka ɓoyemusu ainahin inda muke."
Ƴar dariya Haulatu ta yi.
"Ai Umma nifa duk hanyar da mijinki zai samu labarinmu ba kaunarsa nake ba. Ballantana kuma Hindatu da Mominta idon cin naira, ni na san muddin Mominta ta zo ta ga gidan nan to fa sai ta ƙulla wani makircin. Sanin hali ai ya fi sanin kama."
Murmushi Umman ta yi ba tare da ta ce komai ba. A ƙasan zuciyarta dai tana ƙara godewa Allah da ya fara shiryamata ɗiyarta, duk wasu shirme da caɓa magana da ta ke yi sun ɗan ragu duk da kuwa wasu lokutan idan ta yi wata kwaɓar sai ka fahimci da sauranta.
"Umma." Kiran sunanta da Haulatun ta yi ya katse zancen zucin da take yi.
"Ni kam me zai hana kema ki koma makaranta, zai ɗebe maki kewar zaman nan. Baba Alhaji ya ce ba a girma da neman ilimin addini."
Wannan magana ta Haulatu ya ƙara saka Umma jinjina girman nisan da ta soma yi wurin koyon ɗabi'un rayuwa da ma ilimin addini. Ita kam tana kara jin kaunar Baba Alhaji a ranta, mutum mai hangen nesa da hakuri da halin yara, zai yi wasa da su kuma su yi raha. A yaransa kaf Baban Kowa shi ne ya dauki dukkan waɗannan ɗabi'u nasa. Shi ma akwai son jama'a ga ilimin addini daidai gwargwado.
"Umma kin yi shiru." Cewar Haulatu cike da magiya.
"Farin ciki nake ji a zuciyata ganin ɗiyata ta soma hankali. Yau dai ke da kanki da nake shan fama a baya akan ki je makaranta, ke ce ki ke kokarin nusar da ni na je? Allah abin godiya."
Murmushi mai bayyana haƙora Haulatun ta yi tana mai ɗora kai a kafaɗar Umma na dama.
"Umma ba burinki kenan ba? Kar ki samu damuwa, zan dinga iyakar kokarina wajen ganin na maida hankali. Baba Alhaji ma ya yi alkawarin muddin jarrabawarmu ta fito zai sa a nema min admission a Al-Qalam na cigaba da karatuna. Ke dai ki taya ni addu'a kin ji?"
Ita ma Umma murmushin ta yi tana mai kauda kwallar da ta cika idanunta ba tare da ta yarda sun zubo ba. Idan wasu lokutan ta dubi wannan sauyi na rayuwar da suka samu, sai ta ƙara fahimtar a rayuwa ba a fidda rai da rahmar Ubangiji. Komai kuma yana da lokaci idan bawa ya yi haƙuri to fa babu wani abu da ba zai zama tarihi ba. Babban burinta na gaba a duniya bai wuce ta ga auren Haulatu ba.
***
Shirye-shiryen azumi ya kankama, ana gobe za'a ɗauki azumi, Haulatu na zaune sashin Baba Dakta suna hira da Maama da Safina sai Radiya da wasu yan mata su biyu na gidan wadanda ba wani sabo ta yi da su sosai ba sai dai a wannan ranar sun dan sake koda sun tsoma baki a hira takan amsa idan an sanya ta ciki. Batun ankon ƙanne da yayyu mata suke yi da aka fitar na bikin su Raudha, ɗayar mai suna Saddiƙa ta na aikin kushewa a cewarta sam kalar atamfar bai mata ba. Kowa dai na faɗin ra'ayinsa a haka suka ji sallamar sa ya shigo falon. Gaba daya suka waiga suna masu amsawa. Haulatu suka haɗa idanu ta yi saurin kauda kai. Ita kam ta shiga uku, me kuma ya kawo wannan mai nacin kallon garin a yanzu? Tana ji ya karaso ana gaishe shi amma kallonsa ma ba ta yi ba. Kusan shi ne ya kula da ba ta gaida shi ba don duka baki suka haɗa wurin gaishe shi, a zaton Maama, har da ita. Maama ta kalle shi fuska a sake daidai sadda yan matan ke mikewa su duka a kokarinsu na fita a falon.
"Mutanen Abuja, dama kana tafe ba sanarwa? In ce dai lafiya?"
Zaid ya yi murmushi, ya dakatar da yan matan.
"Kai ina za ku je? Ku yi zamanku."
Suka ɗan dubi juna jin abin wani banbarakwai, sam ba su saba da zama a wuri idan yana nan ba, kusan kamar wasu dodonni haka suke ganinsa shi da Khaleefa da Sadauki, gwara Mu'az yakan sake idan ya ga dama. Idan kuwa sun kula ranar babu walwala tattare da shi, to fa sukan kama kansu su ja baya daga shiga sabgarsa.
Haulatu kamar ba ta ji ba ta yi gaba yayinda su kuma suka dawo wajen zaman su.
"Ke, ba ki ji me aka ce ba?"
Ya yi maganar cikin dakiya don ba ya son fallasa abin da ke ransa.
"Haulatu ina za ki je? Zauna mana ku cigaba da hirar ku." Fadin Maama.
"Maama zan je ne lokacin shan maganin Umma ya kusa, ni ke tunasar da ita."
"Toh, je ki idan kin ba ta kya dawo."
Daga haka ta juya ba tare da ta ƙara kallon Zaid ba wanda ta ji a jikinta ita ya ke kallo. Gaba daya sai ya ji ransa ya ɓaci, ya bi ta da idanu har ta fice a falon. Shi kam ba abin ya bi bayanta ba saboda Hajja, bai ga me zai sa ya shiga ɓangarenta ba.
"Are you ok?" Ya ji tambayar Maama a tsakar kai, lumshe idanunsa ya yi kafin ya dube ta yana mai ƙaƙalo murmushin da bai kai zuci ba, tsaf ta karanci akwai wata damuwar binne a zuciyarsa, sai dai kuma me nene? Ba ta da masaniya, har Safina ta kawo ruwa da lemo da kofi a tray ta ajiye a gabansa bai ce uffan ba, ganin haka sai Maama ta dube yaran ta ce su ba su wuri. Dama su hakan ya fi musu dadi don ba wani sabo suka yi da shi ba. Da sauri suka mike suka yi ɗaki.
"Meke faruwa? Ko wani abu ya faru tsakaninka da Jalilah?"
'No Zaid, you have to control your feelings, zai zama abin kunya wani ya ji kana son jikar Hajja.' Wani ɓangare na zuciyarsa ya kwaɓe shi. Nan da nan kuwa ya saita kansa gami da wayancewa da bude gorar ruwa yana murmushi.
"Ko ɗaya Maama, kawai dai na gaji kaina ke ɗan ciwo. Haka yau na tashi da shi."
Maama ta bishi da toh gami da tambayarsa ko ya sha magani don ita kam ba ta wani gamsu da abin da ya ce ba. Ai ba ta jin ko iyayensu sun yi musu karatun da ita ta yi musu.
"Yau ka shigo garin amma ko? Don jiya da dare ma mun yi waya da Malama ban ji ta ce kana hanya ba."
"Eh yau na shigo, anjima zan bi jirgi na koma, akwai wasu bayin Allah da nakan sallama a wani ƙauye kusa da Malumfashi duk sadda azumi ya kusa, nakan yi musu alheri haka, wannan karon na mance da batunsu shi ne silar zuwa na ba shiri. Amma har na je na dawo."
Ya fadi hakan ne don Maama ta yarda babu wani abu da ya faru wanda ya yi silar zuwansa ba sanarwa, ya kuma ci sa'ar ta yarda da wannan don daga yanayin fuskarta da furucinta na cewar yanzu ta ji batu yasa ya gane. Shi kuwa dai ya sani ƙarya ce kawai don tun a na saura sati guda ma ya yi waya da wani yaronsa dake ƙauyen, ya aikamasa komai ta asusun banki, sun kuma tabbatar masa matashin ya kai musu kayan masarufi na azumi har suka dinga godiya sai da ya katse kiran. Zuwa ya yi musamman don ganin Haulatu kuma ya gan ta din amma ba irin ganin da yake so ba. Ya na so ya faɗi abin da ke ransa sai dai ya gwammace ya yi shiru gudun zubewar girmansa. Ba ya son raini sam.
Sun ɗan taɓa hira da Maama kaɗan kafin ya yi mata sallama ya tafi don samun zuwa ya yi shirin komawa a nutse. Ya fito ya kai duba ga sashin Hajja, ya ji zuciyarsa na neman raunana, wai wannan wace irin jarrabawa ce haka yake fuskanta? Yarinya kamar wacce ta yi masa wani aikin, daga gani sau ɗaya shikenan ya bi ya susuce? To ko dai ya samu Alhaji faɗamasa komai?
"No, ba zai yiwu ba." Ya ba kansa amsar a fili. Haka ya bar gidan da saƙe-saƙen zuci.
***
Kano...
Ranar da duniya aka wayi gari da azumin Ramadhan, a wannan ranar ce Ɗan Mutuwa ya shiga Kano ba tare da ya ɗau azumin ba kamar yanda Hajiya Adama ta yi masa kashedi. Koda ace ma ba ta yi ba, ta sani bai damu da ibada ba amma gudun ma kar a yi din ya sa ta yi wa abin tufka. Daidai lokacin kuwa da bayin Allah suke haramar zuwa masallaci don yin sallar isha'i bayan an kai azumi na ɗaya, a wannan lokacin suka shiga shirin tafiya can wani ƙebantaccen wuri a dajin Allah don gabatar da uzurorinsu na duniya. Wuri ne mai nisa da zai kwashe su awanni uku zuwa hudu, hakan ce ta sa Ɗan Mutuwa ke tuƙin sai Hajiya Adama a gefensa sai kuwa wata aminiyarta ƴar ƙungiya, Zulaihatu. Suna tafe su na ƙara kwaɗaitawa Ɗan Mutuwa irin alfarmar da zai samu da kwarjinin da zai dinga yi wa mutane nan da wasu lokuta. Shi kuwa ban da washe baki babu abin da yake yi. Hajiya Adama