Showing 99001 words to 102000 words out of 177840 words
za ki je ki yi ki goge a turanci ya na neman gagararki? Maza Hauleta ɗiyar albarka jeki, tun ɗazu Gali ya zo, ke kawai yake jira ya kai ki."
Ta ɗan yi murmushi, ta yi sallama da Umma sannan ta nufi ƙasa. Ƙarar wayarta ne ya sa ta ciro ta daga cikin jaka tana amsa addu'ar Allah ya tsare hanya da Baba Saude ke mata. Sunan Yaya Sadauki ne a fuskar wayar. Ta ɗaga da sallama, ya amsa sannan ta gaida shi.
"Lafiya lau, are you ready?" Ita ce tambayar da ya jefa mata.
"Yes. Na fito ma yanzu zamu wuce."
"No, ban ganki ba, ki fito, ni zan kai ki. Ina son magana da Malamar ne."
Ta ɗan yi mamaki don shi ne a jiya ya ce Gali ne zai kai ta yasan wajen amma yau kuma ya sauya ra'ayi?
"Ba ki ji ba?" Ya katse mata tunani. Ta ɗan numfasa.
"Toh, ga ni nan."
Daga nan ya katse kiran.
Ya dubi Mu'az dake tsaye a gefensa fuskarnan babu walwala. Duk wata hira da suke yi sai ya fice a ransa.
"Are you okay?" Ya tambaye shi. Mu'az ya ɗan yi yaƙe.
"Yes."
Girgiza kai Sadauki ya yi.
"Ban yarda ba, ka faɗamin meke damunka? Kwanakin nan ka chanza gaba ɗaya. Ba wannan zolayar, ba wasa da dariya. Tsaya ma, yaushe ka fara min ɓoye-ɓoye?"
Sadauki ya ƙarashe da mamaki, shi kuwa Mu'az sai ya kauda kai daga Sadaukin ya maida ga Haulatun dake nufo su. Kwalliyarta ta masa kyau a ido, sai kuma tunawa da furutan Mominsa ya sanya shi kauda kai daga dubanta yana jin sabon radadi, to gwara ma ya fidda rai a kanta, ko ba don kalaman Momin ba, ita kanta uwar gayyar ba sonsa take ba, ta kuma furta masa.
"Wacce ka ke jira ta fito. Bari na je sai kun dawo."
Bai ko saurari me Sadauki zai ƙara cewa ba ya yi gaba, ya kula da yanda ita ma Haulatun ta haɗe girar sama da na ƙasa ganin Mu'az ɗin. Ta ƙaraso daidai lokacin da shi kuma Mu'az ya fice.
"Akwai abin da ya haɗaku da ɗan uwanki?"
Tambayar da ya watsomata kenan bayan ya harba motar saman kwalta sun soma tafiya. Ta ɗan dube shi, hankalinsa na ga tuƙi.
"Wane ɗan uwana?"
"Mu'az."
Ta ɗan maida kai gefe.
"Aa, babu komai."
"Ok." Shi ne abin da ya ce kawai daga haka bai ƙara uffan ba. Can kuma wayarta ta yi ƙara, ta fiddo daga jaka, yana kula da ita sai dai bai iya ganin sunan mai kiran ba, ya ga dai ta katse kiran kuma ta saka a flightmode, ya ɗan waiga ya ga yanayin fuskarta ta ɗan sauya. Sai ya ji ransa ya sosu, kawai sai ya kawo ko ya makara ne wani ya mishi shigar sauri? Watakila ma faɗa ta yi da masoyinta shi ne dalilin ƙin amsa wayar a yanzu. Ba ya son yin katsalandan ga rayuwarta, kar ta ga kamar ya takura mata wannan dalili ne ya sa ya shanye bai nemi jin ba'asi ba.
Malamar tana da kirki, ta karɓe su hannu bibbiyu don dama akwai sanayya tsakaninta da Sadauki, sai da suka ɗan tattauna da shi sannan ya dawo ga Haulatu dake tsaye tana kallon ajin wanda ƴan tsiraru ne a ciki, har da masu aure, sai dai duka mata ne ma, a ido ma ba su fi a ƙirga ba. Ta dube shi, ta kasa jure irin kallon da yake bin ta da shi ta kauda kai.
"Shikenan, sai an tashi?"
Ya furta a ƙasa-ƙasa, yana ji kamar zai tafi ya bar zuciyarsa ne. Ita ma sai sallamar ta shige ta, ta ratsa jikinta, ba wani hira suka yi ba ko a tahowar, amma ta ji dadin hakan a ranta, ta gyada kai a hankali tana duban dogayen yatsun ƙafafunsa.
"Please kalle ni kaɗan mana."
Da mamakin abin da ya fito daga bakinsa ya sa ba ta ma san ta ɗago ɗin ta kalle shi ba. Wani murmushi ya jefamata sannan ya soma ja baya.
"Thank you. Wish you all the best. Ki kunna wayarki ki saka a vibrate, kar a kira ba ki sani ba." Daga haka ya juya ya bar wajen, ta bishi da kallo ranta na mata daɗi kafin maganar Malama Ruƙayya ya maido ta cikin nutsuwarta. Da murmushi ta dube ta.
"Oya, shiga ko?"
Ta fadi tana nuna mata hanyar ajin, ba musu ta shiga. Sallama ta yiwa abokan karatunta sannan ta ƙarasa can gefe guda bayan wata ta zauna, kai tsaye jakarta ta buɗe ta ciro wayar gami da bin umarninsa wajen kunnata da maida ta vibrate mode. Daga haka ta maida hankali yayinda Malamar ke ba ta umarnin gabatar da kanta. Babu laifi ta miƙe ta yi kokari, inda ta kuskure kuma aka yi mata gyara, abin da ya burgeta, babu wanda ya yi dariya ko nuna wani yanayin na daban wannan ya ƙara ƙarfafa mata gwuiwa. A na darasin idan ta tuna murmushin da Sadauki ya jefe ta da shi, sai ta ji murmushi ya suɓuce mata.
'Wai meke damuna?' Da kanta ta watsawa kanta tambayar, ba shiri kuma ta ɗan saita fuskarta, ya dace ta bar tunanin Yaya Sadauki hakanan tunda dai ba wani abun ke tsakaninsu ba. Ita ba ta soyayya, kawai ɗabi'unsa, kallonsa da komai yana jefa zuciyarta cikin shauƙi.
***
A ɓangaren Sadauki kuwa, haka ya isa gidan yana jin zuciyarta wasai. Da ace kullum zai kasance tare da ita bai kuma san ya zai ji ba. Kai tsaye ɓangarensa ya nufa don tura wasu saƙonnin a email, bai kammala ba sai wuraren sha ɗaya da rabi, ya nufi falon Daddy, ya tarar da shi zaune ya kammala kari har ya yi wanka ya shirya. Bayan sun gaisa ya ce.
"Fita za ku yi ne?"
Daddy ya girgiza kai yana duban lokaci.
"A'a, baƙi zan yi ne. Sanata Hashim ne zai zo kawomin ziyara."
Abin ya ɗan ɗaurewa Sadauki kai. Sanata Hashim kuma? Ya san dai ba wani kusanci suke da shi da Daddyn ba, toh wani abun ne ya tashi da ya tuna da Daddyn nasu?
Sallamar Momi Nuratu ce yasa suka dube ta suna amsawa. Sun riga sun hadu da Sadauki tun safe da zai fita kai Haulatu, ta dube shi.
"Aa, har ka dawo kenan? Ƴar makaranta tana can."
Ya shafi suma yana murmushi kaɗan tuno masa da Sahibarsa da aka yi sai kuma ya basar.
"Eh."
"Masha Allah. Yallaɓai an kammala haɗa komai, an kai falon."
Ta maida akalar zancen ga Daddy dake lura da ɗansa yana murmushi. Ya dube ta shi ma.
"Masha Allah, Allah ya yi albarka. Wace ƴar makarantar da kike magana?"
"Oh, Haulatun Hajja ce fa. Lesson ta soma zuwa kafin su fara karatu. Wai saboda harshenta ya goge da turanci da ma wasu darussan."
Daddy ya jinjina kai.
"Hakan dabara ce. Ni na jima ban gan ta ba ma."
Momi Nuratu ta yi ƴar dariya.
"Ai kam dai nan ɗin ma ba kullum take shigowa ba, shi ne rannan da suka zo karɓar shaidar admission ɗinsu, nake mata tsiya, nace ta mayar da ni tamkar wata surukarta ba uwa ba, ba ta shigowa a gaisa."
Sadauki ya ɗan dubi Mominsa kafin ya sauke kai don jin wani nauyi. Daddy kuwa ya yi murmushi.
"To wayasani ko hakan ne? Abeed me ka ce?"
Ai da sauri ya miƙe.
"Amm..Daddy bari na je wurin Baba Alhaji, ya kira ni a waya yana nemana."
Momi Nuratu ba ta fahimci zancen ba, ta ga dai ɗan nata ya ji kunya har ya fice da sauri, shi kuwa Daddy ƴar dariya ya yi nasu na manya. Ta dube shi.
"Ban fa gane yaren da ku ke yi da ɗan naka ba."
Shi kuwa waya ya dauka ya yi kiran Sadauki akan kar ya jima ya zo yanzu ya ta ya shi tarbar baƙi sannan ya maida duba ga Momi Nuratu yana mai amsa tambayarta.
"Ki ka sani ko surukar taki ce?"
Ta ɗan yi jim cikin sanyin jiki amma ba ta ce komai ba. Wayar Daddy ta yi ƙara ya duba, ganin Sanata Hashim babu ɓata lokaci ya ɗaga gami da sanyawa a kunne. Sun gaisa ya sanar da shi ga su sun shigo farfajiya, nan ya ce ga shi nan fitowa. Dama Maigadi ya san da zuwansu daga bakin Daddy wannan dalilin ne ya sa suna zuwa ya buɗe ƙaton ƙyauren dake a can baya ɓangaren Daddy Ridwan ɗin ba na can gidan gaba ɗaya ba. Koda suka fito a mota, Daddy tuni ya fito wajen, su biyu ne. Da Sanata Hashim sai Ɗan Mutuwa da yake baƙon fuska wurin Daddyn. Nan aka yi musabaha fuska a sake sannan ya ba su umarnin shigowa ciki, shi kuwa Ɗan Mutuwa bin sa da kallo ya yi, ko ba a fadi ba akwai kamanni na jini tsakaninsa da Na'imatu. Suna ƙarasawa falon bayan an zauna ne kuma aka ƙara gaisawa da hirar bayan rabuwa. Har suna jajantawa juna rashin da aka yi kwanaki na wata tsohuwar alƙaliya kuma abokiyar karatunsu. Shi dai Ɗan Mutuwa na zaune yana jin su don ya matsu a zo wurin. Sai can aka ɗan yi shiru Daddy cikin baza kunnen sauraron da me Sanata ya zo. Sanata Hashim ya gyara zama ya ce.
"Amm..Alhaji Ridwan, na san ba ka san ko waye wannan mutumin da muke tare da shi ba ko?"
Daddy ya ƙara duban Ɗan Mutuwa duba na nutsuwa da tattara hankali sannan ya maida ga Sanata yana jinjina kai.
"Gaskiya ne, yau na fara ganinsa ma ina tunani."
Sanata ya girgiza kansa.
"Ba tunani ba ne, hakan ne yau ka fara ganinsa. Sunansa Alhaji Ibrahim, mijin ƴar uwarka Na'imatu, mahaifin Haulatu."
Waɗannan zantukan su ne suka yi dirar mikiya a kunnuwan Sadauki wanda ya sanyo ƙafa guda a falon, sallamarsa ta maƙale a fatar baki lokaci guda ya sanyo kai sosai, ya yi daidai da miƙewar Daddy tsaye shi ma ransa a tsananin ɓace.
"Ashe yana da kunyar da zai zo gabanmu? Cemin za ka yi Ɗan Mutuwa ba Alhaji Ibrahim ba."
Daddy ke zancen ransa na suya, Sanata cikin sauri ya tari numfashinsa.
"Haba Alhaji Ridwan, abin bai kai zafin haka ba, don Allah ka koma ka zauna ka ji da abin da muka zo. Shakka babu duk wani abu da ku ka ji daga bakin Na'imatu gaskiya ne sai dai akwai rashin fahimta a wasu wuraren. Sai kuma sharrin asiri wanda aka yi domin shiga tsakaninsu da matarsa. Don Allah ka zauna zamu warware muku zare da abawa."
Daddy ya girgiza kai.
"Aa Sanata, ba ni kadai ya dace na ji da me ya zo ba, ya kamata ƴan uwana da ma iyaye su san da zuwansa da kuma abin da za ku ce."
Daga haka ya dubi Sadauki dake tsaye ya na ƙarewa Sanata da Ɗan Mutuwa kallo, shi mutum ne wanda da kallo kaɗai yakan gane ƙarya ko gaskiyar mutum, jikinsa ya ba shi maƙaryata ne na gaske, babu ɗaya daga kalaman Sanata Hashim da suka yi tasiri a zuciyarsa.
Daddy kuwa umarni ya ba su akan su zo su je can wurin Baba Alhaji a tattauna a can, ko ta kan liyafar da aka shirya musu bai ƙara bi ba. Su ɗin ma ba shi ne a gabansu ba face fatan haƙansu ya cimma ruwa. Ɗan Mutuwa na kula da kallon banzan da Sadauki ke watsa mishi don ko arziƙin gaisuwa ba su samu daga gareshi ba tun da ya ji ko waye. Bai yi ƙasa a gwuiwa ba shi ma ya bi bayan su Daddy ɗin.
Alhaji na zaune a falonsa sai ga Daddy ya shigo, bayan sun ƙara gaisawa karo na biyu ya ce masa tare yake da mijin Na'imatu ɗiyar Hajja. Alhaji kansa ya sha mamakin yanda Ɗan Mutuwa ya iya takowa ya zo wajensu. Nan ya kira Baba Dakta a waya ya shaida masa. Hakanan ita ma Hajja aka ce ta zo tare da Umma sai dai su din ba su san dalilin kiran ba.
***
Umma ta dubi Hajja kirjinta na duka. Ba dai mafarkin da ta yi na wai Ɗan Mutuwa ya zo ba ne zai tabbata?
"Hajja, lafiya wannan kira haka?"
Hajja ta taɓe baki tana gyara zaman gilashinta.
"Ina fa lafiya, ko wani abun ne ya faru idan mun je ma ganewa idanunmu. Ni kaina na yi mamakin wannan kiran na Yaya Usman. Alheri ne in sha Allahu."
Ta ƙarashe tana sa ƙafa a waje, ita ma Umma ta bi bayanta tana ambaton sunayen Allah a zuci hakan ya haifar mata da nutsuwa.
Suna ƙarasawa Hajja na shiga ta bi bayanta da sallama a bakinta ita ma. Ɗago kan da za ta yi, suka yi ido huɗu da Ɗan Mutuwa, kallonsa take ido waje nan da nan bakinta ya ɗauki rawa ta kasa magana balle ta motsa daga inda take tsaye a bakin ƙofa. Shi ma kallonta yake, ta sauya ta yi kyau gaba daya ta zama kalar ƴan gayu.
"Na'imatu." Faɗin Ɗan Mutuwa yana mai miƙewa tsaye da soma takawa, ba zato ya ga Sadauki tsaye a gabansa ita kuwa Umma har ta koma bayan Hajja ta tsaya, jikinta na rawa tana ambaton Allah gami da runtse idanu. Suka yi kallon kallo shi da Sadauki, ya kula yaron na neman yi mishi shige da ƙudundune a hanci, ya kula da mugun kallon da yake bin sa da shi tun a farkon ganinsa.
"Kar ka kuskura ka yi wannan gangancin." Faɗin Sadauki kenan yana nuna shi da yatsa.
"Kai Sadauki, ya isa hakanan, ka ji ko? Bar shi ya koma ya zauna ai magana dai ta fatar baki ba ta karya wuya ko?"
Fadin Baba Dakta kenan, wannan ya sa Sadauki ja gefe gami da neman wuri ya zauna, Hajja dake tsaye ta yi sororo ba ta gane komai ba ta ƙara riƙe hannun Umma dake jikinta.
"Wai meke faruwa Yaya? Su kuma waɗannan daga ina? Su waye?"
Ta yi tambayar tana kallonsu.
"Zauna Hajiya Asma'u. Magana ce ta kawo su. Yanzu za ki ji ko su waye."
Ba musu ta ja Umma suka zauna gefe guda saman kujera. Ɗan Mutuwa sai bin Umma da kallo yake yi kamar ya yi me? Shi dai bai taɓa jin kaunarta na gaske a ransa ba sai a yanzu da ya yi ido huɗu da ita yanda fatarta ta murje ta yi kyau ainun. Sai ya ji tabbas da ace ya zo musu ne a Ɗan Mutuwarsa na lokacin baya wanda talauci ya nuna har a sutura da fatar jikinsa ya san babu ta yanda za'a yi ya samu kallon arziƙi tun daga bakin ƙaton ƙyauren shigowa gidan balle a kai ga wajen mazauna ciki. Alhaji Ridwan ne ya yi gyaran murya bisa umarnin Baba Alhaji ya soma magana.
"Toh Alhamdulillah, wannan da ku ke gani dai ba kowa ba ne face mijin ɗiyarku Na'imatu. Ibrahim Ɗan Mutuwa kenan."
Ya kwashe duk yanda suka yi da Sanata Hashim ta waya har zuwa yanzu da suka zo. Ya ƙara da faɗin.
"Amma dai waƙa a bakin mai ita ta fi daɗin sauraro. Bismillah, muna ji, mai ke tafe da ku?"
Hajja da ta fusata ta yi caraf ta ce.
"Me ku wa ke tafe da su idan ba sharri da makirci ba? Kai yanzu Ridwan har za ka ce wai meke tafe da su? Ai ganin wannan yaron Ɗan Mutuwa ba alheri ba ne. Macuci azzalumi..."
"Ke Asma'u, yi shiru haka ya isa. Kar na ƙara jin ta bakinki, dukkanmu nan mu ma mun damu da Na'imatu ba ke da ki ke uwarta ba. Ki yi shiru har mu ji me zai ce. Kar ki yarda na ƙara jin ta bakinki."
Baba Alhaji ne ya katse ta da wannan zancen, Hajja ta saki huci ta furzar gami da watsawa Ɗan Mutuwa kallonta mai kaɗawa jikokin gidan ƴaƴan hanji idan ta yi musu sai dai ba ta ce komai ba shi kuwa har da wani sunkuyar da kai fuskar na nuni da tsantsar nadama.
"To, muna sauraronka."
Madadin Sanata Hashim da ya ɗauko magana a ɗazun, wannan karon Ɗan Mutuwan da kansa ne ya fara bayan ya yi ƴar gyaran murya.
"Da farko dai zan soma da ba ku haƙuri musamman Na'imatu. Don Allah ki yafemin dukkan abin da ku ka ji daga gareta da ma wanda na sani ita ɗin mai iya rufan asiri ce ta ɓoye wasu. Haƙiƙanin gaskiya nasan na zalunci rayuwarta, na kuma cutar da ita ta hanyoyi da dama masu yawa wadanda wasunsu ba yin kaina ba ne, ban kuma aikata su ina cikin hayyacina ba."
Umma ta yi tsai tana dubansa, tsoro da shakkar duk ta kau, sai mamakin kalamansa na rainin hankali da ya ɗauko, wai ba yin kansa ba ne. Babu wanda ya ce komai face kallonsa da ake musamman Hajja da Sadauki dake watsa masa kallon banza. Wannan ya sa shi ɗorawa daga inda ya tsaya.
"Akwai wata tsohuwar budurwata mai suna Ramatu, da muka yi rayuwa ta so da kauna tun ma kafin nasan zan auri Na'imatu, na yi mata alƙawarin aure a mabambantan lokuta sai dai ganin da na yi wa Na'imatu karon farko a rayuwata na ji nan duniya ita nake so. Aka kuma yi katari na dace jininmu ya hadu da na mahaifinta marigayi Saleh Maikalangu, shi ya duba nagarta ta ya damƙa min amanar Na'imatu bayan an ɗaura mana aure. A farkon zaman mu na kaunace ta na kuma nuna mata babu ya ita, sai dai dawowar Ramatu cikin rayuwata ta ci alwashin sai ta raba ni da Na'imatu. Ta ce na ci amanarta, na tozartar soyayyar da ta ke yi min don haka ni ma ba za ta taɓa bari na runtsa ba. Ni dai ban san me ya faru ba, na wayi gari kawai da mugun tsanar matata, ko magana bana so ya haɗa mu. Har ta kai idan ta yi wani abun nakan buge ta sosai. Sai bayan na aikata na fita daga gidan na samu wuri na yi kuka kamar yaron goye, na rantse muku duk abin da na aikata ga Na'imatu ba a hayyacina na yi shi ba, sannan ni ba ni da masaniyar sace Haulatu da aka yi yunƙurin yi. A lokacin idan za ku tambayi Na'imatu, ta san zamantakewarmu ya sauya, na dawo yanda nake a baya tun farkon aurenmu. Muna