Showing 117001 words to 120000 words out of 177840 words
matsayin wacce zai aura? Dama abin da ya jefa ta cikin tunani bai wuce jin wai ita Haulatun ce ta amince Mu'az ya yiwa iyaye magana ba. Yanzun ta fahimci shiri ne da kuma son zuciya irin na sa.
"Ni fa Maama yanzu Safina nake tsoro kar ta ji wannan maganar ta kasa fahimta na, ban taɓa ba su labarina da Yaya Mu'az ba. Kuma duk saboda kar Safina ta ji babu dadi. A zatona zancen ba zai taɓa fitowa ba."
Maama ta yi murmushi.
"Kar ki damu, in sha Allahu za ta fahimce ki kamar yanda na fahimceki. Ni ma a farko ai kin ga ban fahimceki ba amma kuma dama ina tunanin ba lallai hakan ya kasance gaske ba, kin san zuciya da saƙe-saƙe dai. Ku na da kyakkyawar alaƙa ta zumunci tsakaninku, babu abin da zai hana ta yi maki uzuri."
Cikin narkar da murya ta ce.
"To Maama ki fadamata komai sai daga baya na yi mata magana."
Maama ta girgiza kai.
"A'a, da kanki nake son ki sanar da ita. Idan da hali ma ki ja Radiya ku same ta har gida ku yi magana. Na san dai Umma ba za ta hana ki ba."
Cike da gamsuwa ta gyada kai. Maama ta ce ta kwantar da hankalinta komai zai zo da sauƙi. Daga nan suka yi sallama, Haulatu na jin kaso saba'in na damuwarta ta ragu. Ko babu komai Baba Alhaji ya ce zai takamusu burki, kuma Maama ita ma ta ƙarfafa mata gwuiwa.
Tana zuwa ta ba Umma da Hajjah labarin komai har na Yaya Zaid. Nan Hajja ta shiga zazzaga ruwan masifa. Fadi take.
"Ni ban taɓa ganin cikakken marar kunya ba irin Zaidu, shi ya na da idon da zai dubi jikata ya ce yana so? Eh lallai, da walakin ashe, wai goro a miya, shiyasa ya ke ta safa da marwar zuwa ya gaishe ni? To aikuwa daidai nake da su. Ke Na'imatu, lalubomin lambar wayar Safiyya ki bani nan, ni ɗanta zai nunawa iya shege?"
Umma ta ɗan numfasa.
"Ki yi hakuri Hajja, ai kin ji yanda suka yi da Baba Alhaji, tunda ya tabbatar da cewa zai takawa abin burki, don Allah kar ki kira Malama ki tada hankalinta. Kuma yin haka zai sa Baba Alhaji tunanin kamar bai isa ya yi hukunci akan naki ba ne."
Hajja ta yi kwafa.
"Ashe zuciyar tasa ta banza ce, ai da sai na nunamasa ni Asma'u karr nake kallonsa. Dama jikina ya ban ba don Allah ya ke jelar zuwarmin ba. To ahirr dinsa, shi ma Mu'azun da ya ke wani raragefe, anƙi a ba shi ita tunda ba ta so, haka kawai uwarsa ta salwantarmin da rayuwar jika? Ke Haule ki kwantar da hankalinki, daga kaina aka bar yunkurin yiwa kowa auren haɗi a zuri'armu kin ji ko? Yanda Yaya Usman ya fadi hakan ce za ta faru, ki maida hankali ga karatunki kamar yanda ki ke so."
Haka Hajja ta yi ta sababi ita dai Haulatu ɗan murmushi kawai ta ke yi, jikinta dai a sanyaye yake, har yanzu maganar na ba ta mamaki. Yaya Mu'az ya cika mugu mai son kansa da yawa. Shigowar Radiya ce ya sanya ta sulale ta bar falon suka yi ɗaki. Ta sani, zancen ta ji ga dukkan alamu. Dama kuma ta yi niyyar ta je wurinta.
***
A gefen Sadauki kuwa, wuni ya yi a waje bai shigo gidan ba sai bayan sallar isha'i don a waje ma ya sha ruwa, koda ya zo ma ɓangarensa kawai ya shiga ya watsa ruwa sannan ya nufi falon Mominsa. Su Fu'ad dake zaune su na hira ana buga musu su na ganinsa gaba daya aka nutsu suka gaida shi, ya amsa fuska ba yabo ba fallasa ya tambayi Momi Nuratu. Suka ce tana sama. Daga nan ya haye saman ya iske ta zaune tana waya. Bayan ta kammala ya gaida ta. Ta amsa tana mai jin tausayinsa a rai. Wato dai shi ke son Haulatu amma ita ba ta sonsa? Ko kuma dama tunaninsu ne ya ba su kamar yana sonta? A bakin Mamin Khaleefa ta ke jin komai, takanas kawai ta kira ta da yamma ta hau ba ta labarin wai auren Mu'az da Haulatu za'a yi don magana ta je kunnen manya.
"Ya aikin? Daddynka ya ce kun yi meeting ko?"
Cike da alamun gajiya ya yi ɗan ƙas-ƙas da yatsun ƙafa.
"Eh Momi, yau na gaji sosai."
"Allah ya huta gajiya. Bari na sa a hadomaka abinci."
Ya ɗan lumshe idanu kafin ya bude.
"No, ba zan iya cin abu mai nauyi ba. Kun yi fruitsalad?"
"Ai fa, aikin kenan, ba ka son cin abinci, ba don ma jikin naka ba a ganewa ba ai da tuni ka zama kyandir tsabar siranta. Bari a haɗomaka."
Ya yi murmushi kadan, wai shi zai zama kyandir? Bayan ta gama waya da bayar da umarnin haɗamasa ta dube shi.
"Kana da labarin maganar auren Mu'azu da Haulatu?"
Bai san lokacin da gajiya da kasalar da yake tattare da shi ta tafi ba.
"What? Ban fahimta ba Momi."
Jikinta ya ɗan yi sanyi, ko dai yana son ta? A sanyaye ta ke fadamishi yanda aka yi. Ta kara da fadin.
"Amma fa ban sani ba ko dagaske manyan sun ji, ni dai ban ji daga bakin Daddynku ba."
Ya rasa ma abin cewa don haka ya miƙe.
"Ina zuwa."
Ba ta dakatar da shi ba, ta gama karantar yanayinsa, ransa a ɓace yake. Shi kuwa kai tsaye ɓangaren Baba Alhaji ya nufa wurin Maama. Ya yi nasarar iske ta a falo tare da su Najeeb da Haidar yaranta. Suna ganinsa suka gaishe shi, ya amsa yana mai musu alamar su fice da hannu. Ba shiri duk suka miƙe suka fita, ya karasa ya zauna gefen Maama, idanunsa har sun kaɗa. Maama ta san dama za'a rina, wai an saci zanin mahaukaciya. Kafin ya yi magana ta katse shi.
"Ka samu labarin abin da ƙaninka ya aiwatar kenan ko?"
"Maama, me hakan ke nufi?"
Haka kawai ya iya faɗi don magana na yiwa Sadauki wuya idan yana cikin ɓacin rai. Haka yanayinsa yake shi.
Ya ji zuciyarsa ta yi sanyi, fargabar kada ya rasa abar kaunarsa ta kau. Ko babu komai ya samu tabbaci daga harshen da bai taɓa faɗamasa ƙarya ba, wato daga bakin Maama. Ya ji duk abin da ke faruwa, a gefe guda ga zafin Mu'az da Zaid da ya ji. Maama ta miƙa masa ruwan gora mai sanyi tana murmushi.
"Oya, ga shi nan ka sha ka ƙara samun nutsuwa. In sha Allahu Haulatu rabonka ce ka ji ko? Kai dai ka ƙara miƙawa Allah lamuranka."
Sadauki ya karɓa ya buɗe gami da yin bismillah ya soma sha. Haƙiƙa sai yanzu ya samu nutsuwar.
Bai wani jima sosai ba ya tashi, ya ƙudirta a ransa yanzu ne zai soma yaƙi akan Haulatu, irin yaƙi na bi a sannu, ba zai yi saurin furta mata kalma ta so ba, amma fa zai yi iya yinsa wajen kyautata mu'amalarsu ta yanda ya ke fatan a hankali ta koyi sonsa.
Momi Nuratu ta sha mamakin ganin yanayin da ya dawo mata da shi, cikin nutsuwa ta dube shi.
"Ina ka je haka? Daga magana ka sauya ka fice a hargitse yanzu kuma kamar ba kai ba."
"Ba komai Mami." Iyakar abin da ya furta kenan don ya ma rasa amsar bayarwa, shi fa har gobe yanda yake sakin jiki ya yi zantuka da Maama ba ya iya hakan da Momi Nuratu, ita ma ganin ba shi da niyyar ɗorawa daga faɗin haka sai ma murmushi da ya ɗan yi kawai sai ta rabu da shi tana miƙewa.
"Bari na shiga ciki. An kusa ƙarasa maka, ko can wajen naka Fu'ad zai kai maka?" Ta ɗan dakata tana dubansa ya amsa da eh, daga nan suka yi sallama ganin dare ya yi, dama shi Daddy sun gaisa tuntuni.
Ita kuwa Haulatu koda suka shige ɗaki da Radiya, Radiya ta dube ta.
"Ke Haulatu, wata magana na ji fa ta a yawo shiyasa ba shiri ki ka gan ni."
Ajiyar zuciya Haulatun ta yi cikin yanayin damuwa.
"Ko ba ki zo ba dama na yi niyyar
***
Washegari Umma ba ta hana Haulatu zuwa wajen Safina ba musamman da ta ji komai na irin son sa Safinar ke yiwa Mu'az. Ita ma ba ta son rashin fahimtar juna ya shiga tsakaninsu. Don haka wuraren sha ɗaya na safe duk da hadarin da ya haɗu a garin bai hana Haulatu jan Radiya da ta san gidan su tafi tare ba. Babu direba hakan ya sa madadin su koma su sanar da Hajja kamar yanda ta ce idan Gali ba ya nan su sanar mata sai kawai ta ce su nemi napep.
Da Yaya suka soma cin karo tana zaune falo tana raba faɗa tsakanin Ahyaan da ɗan uwansa Hayat akan wai shi Ahyaan din ya ga sadda Hayat ke shan ruwa a banɗaki ya karya azumi, shi kuwa Hayat idanun sun yi kwal kwal yana afkin rantsewa Yaya shi bai sha ba. Sallamar su Haulatun ce ta katse hayaniyar, Yaya ta amsa tana dariyar yaran nata.
"Ah ƴan ukun Maama, hala kun biyo ƴar uwarku ko?"
Suka yi murmushi. Gaishe ta suka yi ta amsa kafin su Ahyaan su gaishe su. Hayat dake kuka Haulatu ta jawo hannunsa.
"Kai da wa?" Nan Ahyaan ya yi caraf ya hau basu labari wai Hayat ne ya sha ruwa a bandaki ya karya azuminsa. Yaya kuwa girgiza kai take don ita tsokana irin ta Ahyaan ma har mamaki yake ba ta. Koda dai barewa ba za ta yi gudu ɗan ta ya yi rarrafe ba, Dakta Hashim shi ma haka yake da son tsokana.
Haulatu ta sharewa Hayat idanu.
"Yi shiru abinka, ai mantawa ka yi na sani. Kuma idan mutum ya manta ya sha ruwa, babu komai ko?"
Ya gyaɗa kai, ta murmusa. Radiya ke tambayar Safina, Yaya ta ce.
"Tana ɗaki tun safe da ta fito ta shige wai kanta na ciwo. Na ce ma ta ajiye azumin ganin kamar har da zazzaɓi amma ta ce ita za ta iya kai wa."
Sauke ajiyar zuciya Haulatu ta yi yayinda wani fargaba ya ɗan shige ta, to kodai ta ji zancen ne?
"Allah Sarki, Allah ya ba ta lafiya, bari mu shiga mu gan ta." Faɗin Radiya kenan. Suka amsa da amin sannan suka fice zuwa dakin.
Da sallama suka shiga, tana zaune gefen gado, daki ne da ya sha adon komai pink kalar mata. Da ace a gidan take rayuwa, za ta samu kulawa da jin dadi sosai duk da a can ma tana samu fiye ma da haka, amma Dakta yana ji da yaransa, yana kuma kokarin kulawa da sauke nauyinsu dake rataye a wuyansa. A can din ma ba ya fasa yiwa Safina komai. Radiya ce a gaba sai Haulatu biye da ita, ta kurawa Haulatu idanu, tunani take wai ita ce ta yi mata irin wannan rufin? Daga yanayin kallon da Haulatu ta kula Safina na mata yasa ta fahimci komai, tabbas ta samu labari. Radiya ta zauna gefenta ita kuwa Haulatu ta ja kujera dake ajiye a gaban tebur mai fari da pink na karatu ta zauna tana fuskantar Safina. Hannunta na dama ta kama.
"Yar uwa, sannu. Yaya ke faɗamana ba kya jin."
Murmushin yaƙe kuma na zallar takaici Safina ta yi tana duban Haulatu da idanunta da suka cicciko da ƙwalla.
"Da sauƙi."
Radiya ta dubi Haulatu wacce duk ta sha jinin jikinta, sai kuma ta maida duban ta kan Safina ta ce.
"Amma zazzaɓin ya sauka ko? Da kin ajiye azumin nan kin sa wani abu a cikinki ko kyanji ƙarfin jikin tunda kin ga ko azhar ba ta yi ba, kar ki wahala."
Safina ta jinjina kai kawai, lokacin tana kallon yatsun ƙafafunta sai kuma ta dubi Haulatu.
"Na ji abin alherin da ya same ki, ashe kuma Yaya Mu'az za ki aura. Allah ya tabbatar maku da alheri."
Ɗan dafe kai Haulatu ta yi tana ambaton Allah. Ta kalli Radiya da na ta manyan idanun da su ma suke barazanar zubar da hawaye don tuni sun cicciko.
"Kin ji wani ya riga mu sanar da ita ko?"
Jin abin da ta ce ne ya sanya Safina yin wata dariya kaɗan ta kalli Haulatu.
"Ba ki so wani ya faɗamin ba sai dai na ji daga bakinki kenan? Haulatu kenan. Mamakin da ki ka bani bai wuce na wai ashe soyayya kuke yi da Yaya Mu'az ba, ki ka maida ni sakara marar wayo, na zauna na saki baki na yi ta amayar maki da abin da ke raina, ashe wai ke..."
Ta kasa ƙarasawa ta ciji leɓɓanta saboda kukan da ya ci ƙarfinta. Haulatu wacce ita ma hawayen ta ke fitarwa ta yi saurin tarar numfashinta.
"Na rantse maki babu komai tsakanina da Yaya Mu'az. Duk abin da ki ke tunani ba haka ba ne, yanzu ma zancen da nake maki, an kashe wannan magana."
Daga haka ta yi shiru saboda kallo na kin rainamin hankalin da Safina ke watsamata ga dukkan alamu kuma ƙin yarda da hakan ne ya jawo. Radiya ce ta karɓe zancen ta warwarewa Safina komai. Safina ta cika da mamaki, tuni dama hawayenta sun tsaya, ta kalli Haulatu.
"Amma meyasa ba ki taɓa ba ni labari ba?"
"Saboda gudun hakan, ba na so na ƙara karya zuciyarki ne. A baya kin rayu da sonsa cike da jin ƙarfin gwuiwa tunda kin shaida babu kowace budurwa a rayuwarsa, idan na fito na ce maki ya furta yana sona, ban san halin da zan jefa zuciyarki ba. Na rantse, ban ɓoyemaku da gangan ko wata manufa ba, ni na fadamaku daga shi har Yaya Zaid din babu wanda nake so. Ni karatu ne a gabana kamar yanda na faɗawa Baba Alhaji kuma ya mara mini baya. Don Allah kar ki bari saboda wannan mu samu saɓanin fahimta, na yi kuskuren rashin sanar da ke a baya, kuma ni ban taɓa son Yaya Mu'az ba, so irin na masoya, ni ina masa kaunar ɗan uwa ina kallonsa kamar Wa namiji a wurina, idan ma ba ki manta ba na taɓa faɗamaki haka Safina."
Safina ta jinjina kai, akwai sadda suke hirar kusancin Haulatun da Mu'az ta ke cewa ita tana jindadin yanda ya riƙe ta kamar ƙanwarsa Nusaiba, ba kuma ta sani ba ko don ta tashi ba ta da wani ɗan uwa namiji ko mace shiyasa. Sai jikin Safina ya yi sanyi, wato dai Anti Jannat makirci ta so haɗawa a jiyan, so ta yi ta shiga tsakanin kyakkyawar alaƙar da ke tsakaninta da ƴar uwarta.
"Amma Yaya ta sani kuwa?" Tambayar da Radiya ta watsowa Safinar kenan. Ta girgiza kai.
"A gidan nan ban ga alamar wani ya sani ba ma, ni ɗin ma Anti Jannat ce ta zo jiya, wajenta nake ji."
Da tsananin mamaki Radiya da Haulatu suka kalli juna.
"Anti Jannat?"
Safina ta amsa da eh sannan ta labarta musu dukkan abin da ta ce har ma da amsar da ta ba ta. Sai ga su suna dariya baki daya.
"Kai Safina, ni wallahi kin burgeni. Ai jira nake yi kawai ku sauke zancen na rufu a kanki da faɗan yanda ki ka bamu kunya gabanta, ashe ba haka ba. Sai da na ji ƙarashen zancen na samu nutsuwa." Radiya ke wannan batun, Safina ta harareta tana murmushi.
"Ji, wai ke din da ba ki da wani faɗa har wani abu za ki iya aikatawa? Da sai Haulatu ce ma nasan yanzu zan sha faɗa da zagi."
Suka ƙara darawa. Nan fa sai ga Safina ta wartsake, ta nemi ciwon kai ta rasa, dama tun sadda ta yi bacci ta farka zazzaɓin ya sauka. Yaya koda ta leƙo ta gansu suna hirarsu da dariya, sai ta fice tana murmushi. Dama ta yi tunanin Safinar akwai wata damuwa a ranta, sai a yanzun tunaninta ya bata watakila ƴar matsala suka samu da juna yanzun kuma aka ɗinke. A ranta ta dinga bin su da addu'ar Allah ya dauwamar da zumuntarsu har jikoki, ya fito musu da mazaje nagari.
Haulatu ba su ne suka tashi barin gidan ba sai da suka sha ruwa. Dakta ma a farko cewa ya yi sai sun kwana, sai dai ba yanda ya iya tunda Hajja ta riga ta aiko Gali ya dauke su. Sun sha dai dariya kamar cikinsu zai ciwo, don idan mutum ya na tare da Dakta Hashim to fa ba zai kamu da hawan jini ba, ko ya hau ma zai sauka.
***
Bayan kwana biyu...
Malama ranta a ɓace ta ke duban Zaid dake tsugunne gabanta, a dazun ne Baba Alhaji ya kira shi ya ce ya yi hakuri kar ya ƙara tayar da zancen Haulatu tunda yarinyar dai ta nuna ba ta sonsa, kuma karatu za ta yi to kar ya matsa mata. Ita kuwa Malama, Hajja ce ta kira ta ta yi mata tas tace Zaid ya rainata ba shi da kunya har ya iya kallon idanun manya ya ce yana son jininta, to idan har ta isa da ɗanta, ta gaggauta taka mishi burki. Har ta ke ikrarin ba lallai Malamar ta iya hakan ba tunda ba ta tilasta mishi auren Zaituna ba, to wannan ma ba za ta iya ba. Don haka ita tana can tana jiran ranar da Zaidun zai kwaso jiki ya shigo mata gida. Maganganun dai sam ba su yiwa Malama dadi ba, ta yarda Hajja matsayinta na Uwa a gareta komai ma ta iya faɗa, kuma ba laifin kowa ba ne sai Zaid mai masifar kafiya da naci idan ya sa abu a gaba.
"Me kuma ya kawo ka wurina yanzu?"
Wannan ita ce tambayar da ta watsa masa, dama tana son magana da shi, amma ganin yanda ya kawo kansa har ya durƙushe ta kyautata zaton wani abun zai ce. A iyakar sanin da ta yiwa ɗanta ya kasance mai kafiyar da ba ta jin haƙuri ya zo bayarwa mai nuni da ya bar maganar Haulatun. Aikuwa ya tabbatar mata da tunaninta sadda ya karya bille ya soma magana.
"Na yi maki laifi ne, kin ce na haƙura amma na kasa har na fiddo zancen ga Maama, sai dai ba ni na kai maganar ga Baba Alhaji ba. Ki yi hakuri, ina