Showing 72001 words to 75000 words out of 177840 words

Chapter 25 - FITAR TSIRO COMPLETE HAUSA NOVEL BY RUFAIDA UMAR

11 Jul 2024

79135

ya sa Mommy nunamata kar ta sake ta damu, dama masu arziki haka suke kyauta na bajinta kuma na fitar hayyaci. Kar ta sake ta damu. Haka dai har ta yi nasarar fidda Hindatu daga shakku tare da kwaɗaita mata kalar rayuwa irin na manya da za ta gudanar a gaba.

***
Katsina kuwa, sallah na wucewa sai mutanen gidan aka shiga shirin auren su Raudha da Batulu. Ana saura sati biki gida ya cika da baƙi har da mutanen Malaysia. A filin jirgi na garin Kano suka shiga, a mota aka dauko su zuwa Katsina. Hajja sosai aka tashi da gyara a sashinta ranar. Su Ihsan da mamanta Hadiza sun iso. Hakanan ɗan Hajja Abba dake zaune a Yobe da iyalinsa su ma duk ranar za su iso. Wannan yasa bangaren Hajja duk ya hargitse da kacaniyar gyara da girke-girke. Tsakanin Haulatu da Fahima sai harara da kauda kai amma babu wanda ke kula wani, hakanan Ihsan ba ta shiga harkar Haulatu, Umma ma idan ta ɗan saka ta a zance sama-sama take mata wannan dalilin ne yasa Umman jan bakinta ta kama girmanta ta fita sabgarta tun da ba sa'arta bace. Gwara Maimunatu ma ita ce ta saki jiki da su sosai, sam ba ta da matsala ba ta ma da yawan magana.

A gajiye ta shiga ɗakinsu tana mitar aikace-aikacen sun yi yawa kamar ba a taɓa baƙi a gidan ba sai a kansu. Ta zube saman gado tana maida numfashi. A haka bacci ya yi awon gaba da ita, can ta ji waje ya cika da hayaniya da ihu wanda shi ya yi sanadin farkawarta.

Ji ta yi ana sannunku da zuwa lale marhabin da mutanen Malaysia. Aikuwa ta yi wuf ta miƙe daga saman gadon ta shiga bandaki ta wanke fuskarta ta fito zuwa falon.
Wata mace ta gani mai haske tamkar buzuwa don duk a yaran Hajja, Hajiya Nafisa ta fi su hasken fata balle kuma da ya haɗu da hutu da rayuwa a wuri mai kyakkyawan yanayi. Yaranta uku, babbar budurwar wacce Haulatu jikinta ya ba ta cewa ita ce Zaituna, ta sha doguwar abayarta ruwan madara mai ɗan karen kyau da ɗaukar ido. Sai da ta saki baki wajen kallon baiwar da Allah ya yiwa Zaituna, doguwa mai ɗan jiki kaɗan sai kuwa hanci har baka ga ƙaramin halittar baki. Sai ko idanunta kalar na Haulatun masu ɗan girma. Uwa uba kuma ga dirin jiki don koda abayar da ke jikinta bai ɓoye halitta na cikar ƙirji da mazauna da Allah ya ba ta ba. Sai mai bi mata namiji da ƙaraminsu shi ma namijin. Dama ta ji a bakin Hajja yaran Hajiya Nafisa su uku ne. Babu abin da ya burge Haulatu har ya sanya ta murmusawa face yanda ta ga Hajiya Nafisa ta rungumo Umma a jikinta har tana ɗan hawaye. Ta san sun sha gaisawa da Umman ta waya idan ta kira Hajja, amma sai ba ta yi zaton kaunar da ta ke yi ga Umman ya kai har haka ba. Nan kuma aka zauna tana ji Hajiya Nafisa ta soma tambayar ina yarinyar da aka ce ta zo da ita, sai kuwa Baba Saude ta yi caraf ta amsa.

"Kin gan ta can tana ƴar laɓe. Haulan Hajja ƙaraso ku gaisa mana."

Ta ɗan ji nauyi ganin gaba daya sun kallo inda ta ke, ta soma tafiya ta ji an sanya tattausan hannu cikin nata. Koda ta duba ta ga Zaituna ce take sakar mata murmushin da har gefen kumatunta na lotsawa.

"Assalamu alaiki."

Ta amsa mata sallama gami da maida mata martanin murmushin. Ita kuwa Hajiya Nafisa rungumeta ta yi bayan ta ƙarasa wajenta kafin ta zaunar da ita a gefenta.

"Masha Allahu, wannan dai ni za'a bar wa ta yi karatu a wurina ko? Ki samo mana ɗan Malaysia?"

Aka yi dariya har Haulatun. Aka gaggaisa, tana kula da mutanenta su Ihsan yanda suke cika da batsewa, su sam ba su so ganin wannan tarbar ga su Umma ba daga wurin Hajiyar Zaituna. Hajiya Hadiza ita kanta abin ba haka ta so ba, so ta yi su haɗa kai da ƙanwarta su ware Umman. Ita kaɗai ba za ta iya yin yaƙin ba ko don shakkar Hajja, amma fa da ace Haj Nafisa ta biye mata to fa lallai ko ba su yi nasara a wani ɓangaren ba, za su iya yi a wani. Ita har gobe ba ta son Umma, ta kuma tsani Haulatu fiye da zaton mai zato musamman da ta ji labarin ɗinkunan da Hajja ta ce Sadauki ya ɗinka mata na sallah da ma tsaraba na bajinta wanda dole sai da Umma ta fiddo su ta nunamata. Fahima ta ke yiwa kwaɗayin zama matar Sadauki, wannan ne burinta. Maza irin su Sadauki wahala suke yi, ba ma haka ba, samarin yanzu sun zama mayaudara. Fahimta duk wanda zai zo wajenta da zummar yaudara ne. Ta fi kaunar yi mata auren gida na zumunci, irin auren da ka riga ka san girma da halayyar mutum. Sai dai shakka babu ta tsorata da wannan giggiwar da acewarta Sadauki ke yi akan Haulatun, meyasa ko kyautar turare bai taɓa haɗa su da Fahimar ba? Ƙarƙari dai na barka da sallah wanda kowa ma yiwa ya ke.

"Haj Hadiza  kin yi shiru ana hira." Faɗin Maman Zaituna kenan. Sai ta yi dariyar yaƙe.

"Uhm, kin ga hankalin ne ya tafi a wani tunanin. Ai ya kamata ku ɗan huta sai ku ci abinci ko?"

"Um um, nikam sai Autan Hajja ya iso ma ci tare. Sai dai ko yaran. Haneef?"

Ta kira sunan Autanta tana ɗan rungume shi da yi mishi yaren Malaysia. Ya kuwa taɓe baki ya ba ta amsa da shi tare da ita zai ci. Ta yi dariya sannan ta tambayi ɗan uwansa wanda ta ke kira da Sayyeed. Shi ɗin ma ya ce sai da ita.

Zaituna dai ɗakin su Haulatu ta nufa sanin da ta yi nan ne masaukinsu duk sadda suka zo, sai Hajja ce ta dakatar da ita gami da nunamata ɗakin dake gefenta. Ba musu ta juya ta nufi ɗakin.

Ba su yi ko awa ɗaya da zuwa ba sai ga Abba da iyalinsa sun iso. Ya sha coat abinsa, ɗan boko na gaske. Tare da matarsa da ƴan ukun yaransu da matar ta haifa duka maza ƴan kimanin shekaru tara. Matar dai fuskar babu alamun fara'a, Hajja ta fi ba Haulatu mamaki, duk irin yanda surukar ke wani tamke fuska tana shan ƙamshi amma rawar jikin yi mata hidima ta ke. Koda dai ance dama matar ba kirki ta cika ba sai dai kaunar da Hajjar ke nunawa Autanta Abba ya sa har matarsa ya shafa. Ko kaɗan Haseenah ba ta laifi wajen Hajja.

Kafin dare, sai ga Zaituna da Haulatu na hira tamkar sa'annin juna, za ta girmi Haulatu da shekara, ko kusa Zaituna ba yarinya ce mai ji da kai ba. Ba ta da ɗaukar kai kamar su Ihsan da Fahima. Mahaifinta hamshaƙin mai kuɗi ne mutumin ƙasar Misra da aiki ya kawo shi Malaysia. Sun haɗu da Haj Nafisa ne a Umrah. Soyayya ta ƙullu kamar wasa sai ga shi har ya tako Nijeriya karo na farko a rayuwarsa dominta. Bayan binciken asali da komai Allah yasa aka yi auren har suka haifi su Zaituna, Muhd Sayyid da kuma Haneef.

Haka Haulatu ta yi ta shan hira a wajen Zaituna da hausarta da ba ta yi tarr irin nasu ba. Ta ce tana jin larabci, turanci da kuma yaren Malay.

"Yanzu wai duka waɗannan yarukan kina ji?"

Zaituna ta yi murmushi tana lumshe idanun da suka zame mata jiki muddin tana magana ta amsa wa Haulatu tambayarta.

"Na'am, ina ji duka."

Jinjina kai Haulatu ta yi, sai ta ji ta ƙara burgeta. Ita tana son ta iya yaruka daban-daban amma kamar ma ba ta da wannan kwakwalwar da za ta ɗauka.

"Kina zuwa makaranta ne?"

Tambayar Zaituna ya katse tunaninta.

"Eh, yanzu dai results nake jira na exams da muka yi, an ce Waec ya fito ma. Ban duba ba dai."

Ta ɗan girgiza kai kamar mai ɗan tunani kafin ta ɗan ce.

"Oh, Masha Allah. Allah ya taimaka."

"Amin."

Har suka kammala hirar Haulatu ta yi mata sallama ta tafi don kiraye-kirayen sallar Isha'i da aka soma ita dai Haulatu ba ta bar mamaki ba. Shi kuwa Yaya Zaid me ya kai shi ƙin Zaituna? Yariny mai nutsuwa da daɗin hira, ga yawan murmushi. Sai ma ta ji ya ba ta haushi, a duniya duk namijin da zai wulaƙanta mace ba ya burge ta sam. Za ta so ta ji labarin yanda lamura suka faru daga bakin Zaitunan, sai dai ta sani tayar da zancen kamar yi mata fami ne da abin da take da yaƙinin zai wahala idan bai wuce ba a zuciyarta wannan yasa ko kusa ba ta yi karambanin haka ba.

***
Tun shigowarsa falon ya ji wani irin ƙarni ya buso hancinsa. Ransa ya ɓaci sosai ganin an yi shara da guga amma fa tiles ɗin ƙarni ya ke yi. Ba yau ya saba da haka ba, sai ƴar aikin ta yi gyara amma fa ƙarni ya dinga tashi. Har liquid detergents ya kawo kala kala masu ƙamshi daban daban akan ta dinga amfani da su wajen gugar, amma sai ta ce wai kumfar yawa yake yi ta kasa gogewa yanda ya kamata. Amma a lokacin sai ta ba da haƙuri da cewa za ta gyara.

"Sannu da zuwa. Lafiya ka tsaya a bakin ƙofa?"

Ya dubi Hafsat wacce shigowarta falon kenan daga ɗaki, ransa ya ƙara yin baƙi ganin ita ta cakare ta ɗau wanka cikin riga da wandon da ba su kama ta sosai ba don ya hana ta saka abu matsastse saboda cikinta, dama a nan yake samun sauƙin kuma nan ɗin ma sai da ya rantse mata muddin ba za ta dinga gyara jikinta ba to fa babu abin da zai hana ya ƙara aure. Wannan jan idon ne ya sa ta saitu, sai ko ƴar aikin da ta ke rufarsa da masifa da rashin mutunci idan ba ta kammala gyara ba kafin dawowar Khaleefa. Tana son mijinta matuƙa amma ta rantse ita ba ƴar wahala ba ce. Ba za ta yi girki ko aikin da zai jigatar da ita ba balle har fatar hannunta ta yi kaushi madadin taushin da yake da shi.

"Why ki ke min haka? Meyasa ke tunda kin nuna kin fi ƙarfin ki yi, ba za ki saka masu yi makin su yi abin da ya dace ba? Ace kusan koyaushe sai na yi zancen ƙarnin da ke tashi a gidan nan?"

Ta ɗan marairaice fuska.

"Ƙarni kuma Khaleefa? Ni ban ji komai ba. Kodai hancinka ne?"

Takaici ya sa shi zarcewa ɗakin kawai ya bar ta tsaye tana ware hanci, tabbas ta ji amma ita toh ya za ta yi tund mai aikinta ta tafi tun kafin magriba? Kawai sai ta ɗauki room freshner da ke a can lungun kujerunta ta hau fesawa a falon tana mitar tsirfa irin na Khaleefa.

Shi kuwa hatta banɗakin sai da ya ji yana ƙyanƙyami tunda abu ne a rubuce, mai aikin ce ta wanke, kamar kullum sai da ya zuba hypo lungu da saƙo ya kora ruwa kafin ya zuba dettol a ruwan wankansa.

Koda ya fito ya zura jallabiya, bai koma falon ba, tuni ya ciko cikinsa a gidansu wajen Umminsa. Ita kuwa Hafsat dake falo tana chatting jin shiru bai fito don ya ci abinci ba dai ga ta kamar an jefo ta ɗakin babu ko sallama.

"Wai Khaleefa mene ne haka? Kwanaki nawa ka jera ba ka cin abincin gidannan? Haka za mu yi ta rayuwar ka ƙi ci sai dai ka je waje ka cika cikinka? Salon ka cigaba da jawomin zagi wurin yan uwanka a ga kamar kana cefane ba'a girkawar?"

Duk yanda ya kauda kai ya yi banza da ita sai da maganarta na ƙarshe ya sa shi ɗago kai ya dube ta.

"Ina gargadinki, ki kiyayi harshenki da faɗamin duk abin da ya fito daga bakinki. Kaf cikin ƴan uwana babu sa'an yin ki. Stay within your limits."

Yanda ta ga yanayin fuskarsa da kaushin da muryarsa ta yi ya sanya ta turo baki kawai ta fice daga dakin, ta san halinsa, tabbas sau daya ta taɓa kuskuren faɗin wata magana akan Umminsa aikuwa a ranar ba ta kwana gidansa ba don dai Ummin da kanta ta je biko ta nuna lallai ya yi hakuri tunda ita aka yiwa ita ma ta yafe to shi ma ya yafe mata. Shi ne dalilin da yasa take takatsantsan amma abin na mata zafi. Ai koda ba ita ke girkawa ba a ganinta wulakanci ne ya ci abinci a gidansu. Akwai sadda ta ji har wurin Hajja yake tarewa yana cin abinci daga bakin Fahima don ita din ƴar gidanta ce sosai. Fahima ƙawa ce ga ƙanwarta. Wannan ne dalilin sabon su. Takan zo gidan tare da ƙanwar Hafsat din su wuni ana hirarraki.

***
Ɗan Mutuwa cike da walwala ya dubi Hajiya Adama.

"Sai fa a soma shiri, aurena za'a yi shagalin da ba ku taba haskowa ba."

Ta yi dariya bayan ta miƙa masa wayarsa inda ya buɗo mata hoton Hindatu wanda musamman ta je ta ɗauka kala-kala a gidan hoto ta turamasa.

"Ba laifi, ta gaban mota ce. Ina fatan ka yi wa komai tufka gudun samun matsala?"

Ɗan Mutuwa ya yi dariya.

"Kar ki damu Hajjaju, ai nan zuwa anjima zan je ba ga mahaifiyarta. Komai na tafiya daidai. Ganin farko kar ki so ki ga yanda uwar ta ruɗe a kaina. Idanunt fes ya ke."

Suka sa dariya.

"Ai irin su an fi cin riba a kansu. Kai dai a wannan ganin da za ka yiwa Uwar ka tabbatar ka jiƙa ta yanda ta dace."

"Ba sai kin faɗa ba, gida na siya mata ma, zan kai matar takardun gidan. Daidai da ma'aikata zan zuba mata."

Hajiya Adama ta yi wata shewa.

"Ɗan Mutuwa shegen kaya. Ko tsinanne haka ya gan ka ya ƙyale."

Suka yi dariya kafin ya ɗan tamke fuska.

"So nake na shigar da batun Na'imatu da wancan shegiyar yarinyar gaban mai alfarma."

Ta jinjina kai

"Hakan daidai ne. Amma me zai hana ka bari ka gama da babin auren nan da ka cicciɓo. A gani na gwara koda zuwa wajen Na'imatun za ka yi, ta gane cewa ba zaman jiranta ka tsaya ba. Na gaba ya yi gaba. Ai ni zan fi kowa farin cikin maido Na'imatu rayuwarka. Koda kana da kyau ka ƙara da wanka nake gayamaka, ɗiyarnan taka babbar kadararka ce. Ka samu ka aurar da ita ga wani mai faɗa a ji ɗin. Ko nan gaba sai ka ga an ci gaba da damawa da kai fiye da haka. Za kuma ka ƙara shiga cikin manyan mutanen da ba ka taɓa kawowa a kai ba."

Haka ta ci gaba da rura wutar lamarin a wajen Ɗan Mutuwa har sai da ya gamsu ya kuma yi amanna da dukkan huɗubobinta.

***
A Katsina kuwa, washegarin ranar da su Zaituna suka iso garin. A yammacin suka shirya don zagayawa sakamakon Zaituna da zaman ɗakin ya ishe ta. Tafe suke da Haulatun don zuwa ɓangaren Daddy Ridwan, Zaitunan ce zasu gaisa da iyalansa da kuma na Baban Kowa, iyakacinta dama wurin Baba Dakta da Baba Alhaji sadda suka zo gidan. Safina ba ta nan sun fita kasuwa da Maama ita kuwa Radiya tana ɓangarensu.  Hajja ta dube su tana washe baki.

"Inyee, ke Nafi dube su kamar dama can sun san juna."

Haulatu da Zaituna suka dubi juna gami da yin dariya.

"To ai Hajja haduwar jinin kenan. Allah ya ƙara haɗa kawunansu."

Faɗin Maman Zaituna, Umma da su Hajja suka amsa da amin. Hajja ta dubi Fahima  wacce ta zo gidan kenan sai bayan biki.

"Ke ba za ki tashi ku je yawon tare ba? Ke meyasa kike da baƙar zuciya ne irin na ubanki?"

Fahima dake kwance tana danne wayarta wacce Sadauki ya maida mata ita bayan Haj Hadiza ta saka baki, gaba daya sai ranta ya ɓaci da batun Hajja. Dama can ba wani jituwa ta ke yi na sosai da Zaituna ba, don ita Fahima a duniyarta ta tsani koda ƙawance ne da wanda ya fi ta kyau, ta fi kaunar inda ta fi mutum ta yanda za ta wulaƙantaka son rai. Haɗewae kansu da Haulatu tun zuwansu ya tsayamata a maƙoshi sai da ta ji kamar ta arce ta koma gidansu amma Haj Hadiza ta yi mata jan ido. A cewarta ta ina za ta saka idanun ta kula da takun Haulatun da Sadauki idan har ta ƙi zama ta koma? A dole don tasan tana son Sadaukin yasa ta danne ta haƙura. Yanzu kuwa maganar Hajja sai ta ji ranta ya yi zafi har ta kasa ɓoyewa a fuska.

"Haba Hajja, ƙila dai ba ta son hayaniya ne. A ƙyalemin ɗiyata ta huta."

Faɗin Umma kenan cikin son nuni da goyon bayan Fahimar, ita kuwa Haulatu ta ji inama Umma ba ta saka baki ba a shigarwa wacce ba ta san ƙimarta ba. Aikuwa Fahima ta ƙara jin zafi na don me Umma za ta kira ta da ɗiyarta? Kawai sai ta miƙe tana tura baki ta yi ƙasa, gwara ta fice daga sashin Hajjar ta ba su wuri.

Zaituna ta yamutse fuska tana mai zaginta cikin yaren Malay ƙasa-ƙasa yanda ta san Mamarta ba za ta ji ba. Haulatu dai ba ta san me ta furta ba, suka kama hanya suka sauka. Zaituna na mata mitar dama sam Fahima ba ta da hali. Tun can wai ba su jituwa. Ita ta rasa ma dalilin da yasa har mamarsu ba su kwanta mata a rai ba. Wai kamar ba jinin ƴan gidan ba. Halayyarsu ta sha bamban. Ita dai Haulatu murmushi kawai take yi tana duban wayarta ganin missedcall din Hindatu.

Daidai lokacin da suka isa ga ƙofar fita daga falon, a lokacin shi kuma ya sanyo kai da sallama. Gaba ɗaya suka yi turus, Haulatu ta ɗan yi saroro, ta kalli wancan ta maida idanunta ga wannan. A hankali kuma ta ga Zaituna ta sauke kanta ƙasa. Gaida shi ta yi da harshen larabci, shi ɗin ma cike da basarwa ya amsa mata yana tambayar yaushe suka iso. Ta ce jiya. Daga nan ta ja hannun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login