Showing 129001 words to 132000 words out of 177840 words

Chapter 44 - FITAR TSIRO COMPLETE HAUSA NOVEL BY RUFAIDA UMAR

11 Jul 2024

79179

Sadauki ya fice bai yi mata wata tsiwa ba, sai ga su kamar irin an saba ɗin nan har ya shiga ba ta labarin wani test da aka yi musu a aji sadda ba ma ya jin dadi kuma bai yi karatu ba a ranar amma ya taɓa karantawa ya riƙe. Amma da aka tashi hatta Malamin sai da ya fiddo shi gaban aji har ya bi shi da kyautar dubu ɗaya da ma ƙarin maki saboda jin daɗin bayanin da ya rubuta. Ita kuwa ta yi ta murmushi, Zuhra da ke hararar Fu'ad ganin ya mance ma da wacce ya ke sai ta ja guntun tsaki, Haulatu ta kalle ta kawai kafin ta maida duba ga Fu'ad cike da nishadi ta yi mishi godiya ta tattara kayan karatunta ta yi musu sallama ta fice. Bayan fitarta Zuhra ta kalle shi.

"Wai dama karatun na tsakani da Allah ka koyamata? Maimakon ka zura ta a kwalba ta je ta kwaso zero?"

Fu'ad ya taɓe baki gami da ɗan ɗaga kafaɗa.

"Ke ni rabu da ni, idan fagen course dina ne mancewa nake yi da wata ƙiyayya. Balle ma ni wannan ba abinda ta yi mana hakanan muka ɗorawa kanmu wahala." Daga haka ya dauki wayarsa ya fice zuwa ɗakinsa dake kusa da na Yayansa Sadauki.

Zuhra dai ta bi shi da kallon mamaki sannan ta yi ƙwafa ba ta ce uffan ba.

A ɓangaren Haulatu tana tafe tana jin wani sanyi a ranta, ta san a hankali waɗanda ke nuna mata tsana za su gaji su bari, ga dai Fu'ad ya watsar da makaman ya sake mata har yana cewa duk abin da ma ba ta gane ba daga yau ta zo, kuma zai kwaso mata tsoffin handouts dinsa ya ba ta.

"Kun kammala ne?"

Sai da ta ɗan firgita don sam ba ta ji tahowarsa ba face magana a saitin hannun damanta. Ganin haka ya ɗan ɗaga hannuwa.

"Afuwan. Na tsorata ki ko?"

Sauke ajiyar zuciya ta yi sannan ta gyaɗa kai.

"Bakomai."

Ta amsa da ɗan murmushi bayan ta ja ta tsaya. Sadauki ya ƙurawa fuskarta idanu yayinda ita kuwa ta ke kallon hanyar fita daga ƙaton gate ɗin gidan, ta kasa kallon inda yake domin tana ji a jikinta ita ya ke duba. Ji ya yi kalmar ina sonki bai wadatar da shi gurin bayyana yanda ya ke jin ƙaunarta a ransa ba. Sai kawai ya sauke ajiyar zuciya ya ƙara magana.

"Mu je na taka maki tunda na kula akwai ki da tsoro."

Ta soma tafiya ita dai ba ta ce masa uffan ba. Yanayin tafiyar tamkar ba su son rabuwar haka ake yin ta.

"Kin fahimci karatun sosai?"

Ta gyada kai.

"Eh na gane."

"Good. Please ki maida hankali a karatun, ba na so na ji wata aba da ta shafi zancen saurayi ko hira da samari."

Ta ɗan dube shi kamar ta yi kuka shi ma kuwa ya kai dubansa gareta kafin ya kauda kai gami da ɗan taɓe baki da ɗaga kafaɗu.

"Oh, na dameki da batun samari ko? Saboda na damu nima."

Haulatu ta kasa fahimtar inda zancen ya dosa don haka cikin ƴar rawar muryarta ta amsa.

"Ni fa Allah kuwa Yaya na fadamaka karatu ne gabana. Ba ni da lokacin ma soyayyar balle na saurari wani."

Sadauki ya yi shiru, yana son hakan, amma kuma abin da ke ɗan damunsa da amsar, toh ko shi ba ta sonsa? Kenan babu ma kowa a gabanta har shi ɗin?

'Kai za ka gina kanka a zuciyarta, kar ka kusa ka bari a yi maka shigar sauri.' Wani ɓangare na zuciyarsa kenan da ya ba sa shawara.

"Masha Allah, hakan ya yimin daɗi."

Amsar da ya ba ta kenan.

"Ni me ne ne ma Jamb Score dinki?"

Ai sai ta hau tura baki da runtse idanu, muryarta cike da ƴar shagwaba ta ce.

"Yaya please mana."

Ya yi dariya. Daidai sadda bai fi kaɗan su cimma ɓangaren Hajja ba, suka hango Mu'az dake tafe. Sosai Mu'az ya ɗan ji wani iri a ransa, sai dai ya zai yi? Tunda dai Mominsa ta mishi tsakani da Haulatu, uwa uba kuma Baba Alhaji da ya nemi a bar komai har sai yarinyar ta nuna ra'ayin ɗayansu don kanta. Kamar babu wani abu, haka Sadauki ya miƙa masa hannu suka yi musabaha, Haulatu kuwa wacce kallo ɗaya ta yi masa ta kauda kai, gaida shi ta yi ya amsa. Sadauki ya bi ta da kallo yana murmushi.

"Shi ke nan, kina iya tafiya. Sai da safe."

Ta amsa da toh, har ta soma tafiya ya dakatar da ita.

"Haulat."

Sai da ta ji wani yarr a jikinta, ta juyo ta na mishi wani kasalallen kallo. Shi ma ya ji shi a jikinsa. Cike da jarumtarsa ya ce.

"Take care."

Murmushi mai tsada ta bi sa da shi tana mai jinjina kai. Daga nan ta juya ta cigaba da tafiyarta zuciyar kamar ta fasa ƙirjinta ta fito don wani irin daɗi da annashuwar da ta ke jin ta ciki. Wai ko dai ta soma son Yaya Sadauki ne? Wannan ita ce tambayar da ta yiwa kanta.

'Toh sai me ma idan son nashi nake? Ya fa kai a so shi.' Ta tsinci kanta da bai wa kanta amsa, ta kasa haƙuri sai da ta ɗan waigo ta kalle shi, tuni ya maida hankali ga Mu'az ba ta san me suke faɗi ba. Juyawa ta yi ta cigaba da tafiyarta ranta wasai. Ita ta mance ma akwai wata alaƙa da ta taɓa haɗa su da Mu'az ɗin.

A ɓangaren Mu'az kuwa, baki kawai ya saki yana kallonsu, ko ba a faɗi ba, ai shi ba makaho ba ne. Idan ma bai gama sanin wace ce Haulatu ba, yana da cikakken sani akan Bestyn nasa. Ya ji wani ɗaci a maƙoshinsa, tabbas ya rasa Haulatu, damar samunta ya kufce masa, Sadauki ya nuna ya fi su wayo kenan? Ta haka yake so ya kafa gwamnatinsa a zuciyarta? To ko ma dai ya kafa ɗin? Haka ya dinga jerawa kansa tambayoyi iri-iri. Sai bayan ta bar wurin ne Sadauki ya dube shi kamar babu abin da ya faru, fuskarnan ɗauke da murmushin da bai gushe ba.

"Blood ya aka yi?"

Ajiyar zuciya Mu'az ya sauke ganin irin wannan tambaya ta Sadauki mai kama da rainin hankali. Ya kauda kai daga kallonsa saboda ɓacin rai.

"No, ba komai, dama Maama ta kira ni bari na je."

"Ok. Goodnight." Amsar da ya ba shi kenan da haka ya juya ya koma inda ya fito, shi ko Mu'az sai da ya bi shi da kallo sannan ya juya, ba ya jin ma a yanayin da yake ciki zai iya yarda su haɗu da Maama. Zai yi mata waya kawai ya ce ya yi nisa. Duk yanda zuciyarsa ke mishi tuni da Maama ce fa, amma ina, wannan kishi na ganin Sadauki da Haulatun ya mantar da shi komai. Ya ji ya tsani Haulatu tun da har ta watsa mishi ƙasa a ido, ta nunawa duniya ba ta ƙaunarsa. Ba zai kuma ɓata alaƙarsa da ɗan uwansa ba saboda mace.

***
Kano...

Hankali a matuƙar tashe Ɗan Mutuwa ya faɗa gidan Haj Adama. Har ƙuryar ɗaki ya iske ta tana tare da wani ɗan matashin saurayi wanda a haife za ta iya haifarsa, daga shi sai gajeran wando da singilet ita kuwa da ɗaura ƙirji. Ba ta yi mamakin ganin Ɗan Mutuwa ya shigo mata a birkice ba. Bai ko bi ta kan matashin ba ya soma yunƙurin magana.

"Adama ni za ki nunawa bariki?"

Haj Adama tana wani murmushi ta dubi Matashin nan.

"Shalelena, ɗan ban mintuna kaɗan na sallama wannan."

Ya amsa da ok sannan ya dira daga gadon zuwa ƙasa ya ɗauki kayansa ya na hararar Ɗan Mutuwa da ya ɓata masa sha'ani ya fita. Yana rufo ƙofar Ɗan Mutuwa ya cigaba da ɓaɓatunsa.

"Ni za ki munafunta? Mun yi cinikin kaya kin sa an riƙe nawa ke kuwa kin bi duk hanyar da za ki yi wajen kuɓutar da naki?"

Ta miƙe ta tako tana mai ɗora hannunta a kafaɗarsa ya kuwa saurin kaucewa.

"Haba Alhaji Ɗan Mutuwa. Ka tsaya ka saurare ni. Ba ka san taƙamaiman maƙudan kudaɗen da na kashe wajen ganin kayanmu duka sun kuɓuta ba. Iliyasu ya ce na bi komai a sannu, yanda ya yi min ƙoƙarin kuɓutar da nawa kayan zai yi hakan a kan naka. Don Allah ka kwantar da hankalinka, duka fa wannan ba abu ne na damuwa ba.."

"Ya za ki ce ba abin damuwa ba ne? Ta ya za ki soma cewa haka alhalin kin sani muddin wancan mugun shi ke mulkar wannan kujera to fa kashinmu zai iya bushewa."

Ta girgiza kai tana murmushi.

"Kamar ba mu ne da ƙasar ba? Akwai Custom ɗin da ya isa ya tsone mana idanu? Kar ma ka ƙara wannan hangen. Kaya za su fito, babu abin da zai faru."

Dan Mutuwa ya bi ta da kallo irin na wacce ta raina masa wayo.

"Ni za ki mayar sakarai? Ko an faɗamaki ban samu labari daga wajen su Duna ba? Ina da labarin komai, kin ce a yi maki duk yanda za'a yi naki a yi clearing, nawa kuwa ko me za su yi toh su yi. Haba Adama, ai ba yau na sanki ba, ke mace ce mai son kanta muguwa baƙar azzaluma. Toh da ni kike zancen."

Ran Haj Adama ya ɓaci har sai da ta nuna shi da yatsa.

"Ni ka ke kallon tsabar idanuna ka ke zagi? Yau ni ka ke zagi Ɗan Mutuwa? Eh lallai! Mutum mugun icce! Yau ni Adama ka ke ci wa mutunci?! Ba don ni ba ina ka ga ma arziƙin shigo da kaya mai yawa har haka?"

Madadin ya yi ƙasa sai ya ƙara ɗaukar zafi.

"Dama ai ku mata ba a raba ku da gori! Mu zuba ni da ke, matuƙar kayan nan ba su kuɓuta ba kamar yanda na ki ya kuɓuta, ni na san mummunan matakin da zan ɗauka."

Yana kai wa nan ya sa kai ya fice kamar zai tashi sama. Haj Adama ta bishi da kallo fuskarnan a ɗaure tamau. Ta yi alƙawarin ɗaukar matakin kafin ya kai ga ɗauka doj haka a gaggauce ta shiga maida suturarta, da haka wanda ta kira da Shalele ya shigo.

"Ah, Sweety ya haka? Wannan wane banzan ne haka da ya ɓata min mood ɗinki?"

Ta numfasa zuciyar na tafarfasa.

"Bari kawai Shalele, ma yi magana yanzu fita ce ta kama ni."

Daga haka ta juya ta buɗe bedside drawer dinta ta fiddo bandiran kuɗaɗe ƴan dubunnai har uku ta cilla masa ya kuwa cafe abinsa yana wangale haƙora.

"Ga wannan ka sha madara kafin mu ƙara haɗuwa."

"Godiya nake." Ya amsa kai tsaye sannan ya fice bayan ya ɗauki wayarsa da tarkacen da ya shigo da su.

Ɗan Mutuwa kuwa, direbansa na tuƙi amma ji yake kamar su na tafiyar hawainiya hakan ya sa har wata tsawa yake yi mishi akan ya yi sauri. So ya ke a gobe ya wuce Abuja don ganawa da tsohon Comptroller-General na Customs, Yahuza Hayatu, wanda yake mutuminsu kuma ɗan ƙungiyarsu ta harkokin miyagun ƙwayoyi, yanzu haka bayan sauke shi da aka yi yana rayuwa ne a Abuja. Ya tabbata shi ba zai rasa hanyar da zai yi a saki kayansa ba. Ya so ƙwarai su yi ta a waya amma Sanata Hashim ya ba shi shawarar takawa ya je da kansa.

Koda ya isa gida ya iske Hindatu zaune tare da Mominta suna hira. Ganinsa ya sa Momi washe haƙora da fadin.

"Ranka ya daɗe sannu da zuwa." Bai ko kalle su ba ya nufi ɗakinsa. Abun ya yiwa Hindatu zafi wanda ya sanya ta miƙewa. Da sauri Momi ta riƙo hannunta.

"Ke, ina za ki?"

"Momi rabu da ni, na gaji da wulaƙancin da ya ke yi maki. Ban ga dalilin da mijin da nake aure zai raina uwata ba."

Baki sake Momi ta ce.

"Haba Hindatu, ke yanzu mijinki har yanzu ba ki gama karantarsa ba? Dubi fa yanda ya shigo rai a ɓace amma ki ke son ki je masa da zancenki na shirme? Ina ki ka ga ya wulaƙanta ni idan ba neman magana ba?"

Zuciyar Hindatu babu dadi ta ke kallo da sauraron Momin har ta kai aya a zancenta kafin ta amsa.

"Yanzu Momi ke kenan koyaushe cikin mara wa Ibrahim baya don kawai yana da kudi ai ba zai zame masa hujjar da zai ci zarafin uwata ba. Ni kam ba zan aminta da wulaƙanci ba." Daga haka ta tafi fuu, Momin na kira har da haɗawa da zagi amma ina tuni Hindatu ta bi hanyar da zai sada ta da ɗakinsa. Tana shiga ta iske yana waya yana zazzaga masifa da ɗura-ɗuran ashariya. Ba yau ta soma jin sa yana zage-zage ba da girmansa, abun ma kamar bai ta'azzara ba sai da ya gayyato mata wasu ƴan iskan ƴan daba gida suke kwana wai su Duna. Bai ko kula da tsayuwarta ba sai da ya ɗan ɗago ya gan ta ya haɗe rai ya katse kiran.

"Ke ya za ki shigo ki yimin tsaye ina waya?"

Hindatu ta ɗaure fuska.

"Ai kai zan tambaya, ta ya ya za ka shigo mana falo babu ko sallama kuma wai mahaifiyata na gaisheka tunda kai ba ka gaida ta, shi ne za ka bi mu da kallon banza ka shigo ɗaki?"

Ɗan Mutuwa ya saki baki.

"Ke! Da ni ki ke wannan maganar?"

"An.."

Ai ba ta ƙarasa ba da ya yi wani taku da bai fi uku ba ya cimmata ya hau jigba yana ashariya, dama neman inda zai huce fushinsa yake sai Allah ya yi ta faɗo tarkonsa.

Jin ihun Hindatu ya sa Momi ba shiri ta shigo kamar an wurgo ta. Ganin jinim da ke bin ƙafafun ɗiyarta ya sa ta sakin ƙara.

"Wayyo na shiga uku! Shikenan ka kashe ta! Shikenan ka ɓarar da cikin!"

Tuni Hindatu ta sume, shi kuwa jin batun ɓarar da ciki sai ya tsaya cak! Ya bi ƙafafun Hindatun da kallo, jinin da ya gani ya sanya shi jin wani irin faɗuwar gaba. Kashedin Uban Dodo ne ya shiga amsa kuwwa a kunnuwansa.

_"Idan ka bari muka rasa abin da ke cikin matarka lallai ka sani za ka rasa dukiyarka!"_

Ai bai san sadda ya kinkimi Hindatu ba ya yi hanyar waje a guje, Momi ta bi bayansu ita ma babu batun ɗaukar mayafi balle takalmi.

***
Katsina...
Matashiyar ƴar aikin Momi Nuratu mai suna Ummi, ta kammala haɗa komai na farfesun a wuta bayan tafasa kazar, jira ta ke yi kawai ya ƙarasa ta jiye a flask ta ba Fu'ad ya miƙa kamar yanda Momi Nuratu ta umarta. Tana nan tsaye ta kafa waya a kunne tana sauraron labarin wani littafin hausa da aka tura mata audio ɗinsa Jannat ta shigo kicin ɗin. Ita a farko ma ba ta kula da ita ba sai da ta ƙaraso sosai. Cikin sauri Ummi ta kashe sautin gami da fadin.

"Sannu Anti, wani abun ki ke buƙata?"

Jannat ta dube ta, kamar ta watsa mata harara sai ta danne ta jefamata murmushin yaƙe don ita a duniya ba ta taɓa sakarwa ɗan aiki fuska, ba ma iyaka na gidansu ba, ko a nan ƴan aikin na gulmar irin girman kanta da ma yanayin yanda ta ke wulaƙanta su kai ka ce ba mutane ba ne. 

"Yes, am..ku na da quaker oat a store?"

Ummi ta ɗan gane me take nufi tunda cimar Fu'ad ce, tana yawan dafamasa da safe. Ta gyaɗa kai.

"Eh akwai."

Jannat ta kai duba ga tukunyar farfesun wacce ƙamshinta ya karaɗe kicin din sannan ta dubi Ummi.

"Ok, je ki daukomin bari na taya ki ɗora ruwan."

"Lah, ai akwai ma a kicin ɗinnan, kin gan shi. Ɗazu na damawa Yaya Fu'ad da safe, na mance ban maida ba."

Jannat ta ji kamar ta shaƙo wuyanta. Sai ta basar da cewa ok. Ita dai Ummi mamaki ke ɗawainiya da ita, matar da tun zuwanta sai dai ta yi ta ba ta umarnin aiki kamar ita ta ajiye ta a gidan, amma kuma yau ita ke kokarin yin abu da kanta. Ita dai ta karasa ta duba farfesunta ya yi, hankalin Jannat na kan Ummi dake kwashe farfesun tana zubawa a foodflask. Ta kammala ta ɗora saman tray ta ɗauraye ɗan bowl da serving spoon sai cokali duk ta goge ta ɗora saman tray din.

"Na waye?" Cewar Jannat.

Ummi da girmamawa ta amsa.

"Na Yaya Sadauki ne."

"Kawo na miƙa masa, dama yau ba mu gaisa ba ashe ba ya jin dadi."

Kamar kar ta bayar tunda ga umarnin da Momin ta yi mata amma kuma ai ba ta isa ta hana Jannat ba. Ba ta shiryawa cin mutuncinta ba don haka ba musu ta miƙa mata.

"Idan ya tafasa ki haɗamin kafin na dawo."

"Toh." Ummi ta amsa. Bayan fitarta ba jimawa sai ga Fu'ad ya shigo.

"Ummi, ina saƙon Yaya Sadauki? Ya kira yana faɗa ban kai masa ba."

"Yanzun nan Anti Jannat ta tafi ta kai."

Ya ɗan bugi bakin ƙofar kafin ya fice yana mitar Jannat za ta jazamasa faɗan da ya fi na farko kenan, ai shi Yaya Sadauki muddin ya sanya ka aiki bai ga ka yi ba wani ya yi, to fa kawai ba ya maka uzuri sai dai ya ce dama ba ka yi niyya ba. A ƙarshe kuma ya hukuntaka. Wannan dalilin ya sanya Fu'ad sauri-sauri wajen bin bayan Jannat. Har ya kusan cimma ta, sai ya ga ta dire tray din a hankali tana waige-waige, ganin za ta juyo ya yi saurin laɓewa a jikin ginin da ya raba corridor ɗin da barandar shiga wurin.  Mamaki ne ya cika shi ganin ta buɗe murfin ta kunce wani gari ta barbaɗa da sauri kafin ta ɗan gauraya ta hanyar jujjuya flas din sannan ta maida ta rufe. Garin kuwa ta yi azamar ƙullewa ta jefa a inda ta ciro. Sosai Fu'ad ya razana, tana soma tafiya ya yi saurin ƙarasowa amma ya yi iyakar kokarinsa wajen shanye mamakinsa da firgicin da ta jefa sa ciki.

"Sis." Kusan a firgicen ita ma ta waigo, sai kuma ta sauke ajiyar zuciya.

"Kai amma ka tsorata ni. Sam ban ji tahowarka ba."

Ya yi dariyar yaƙe.

"Oh, ina ta sauri na cimmaki, uhm, don Allah bani na kai, na rantse idan Yaya ya ga ba ni ne na kai ba faɗa zan sha. Yanzu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login