Showing 78001 words to 81000 words out of 177840 words
ta ji babu wasa a ciki sai ta juya ta tako tana kumbura fuska. A ranta tunani take yanzu kuma me zai ce mata?
"Ina wuni." Ya amsa yana kallon ledar da ke hannunta. Shi har ya manta ma da abinda ya faru jiyan.
"Ina za ki je?"
Da ɗan mamakin tambayar ta dube shi sai kuma ganin ita yake kallo ta kauda kai tana duban ƙawayen Raudha da suka zo wucewa zasu nufi gidan Daddy Ridwan da duka amaren nan zasu kwana. Su ɗin ma kallonsu suke yi da mamaki na ganin Sadauki tsaye da wata macen, sai kuwa suka shige ciki bayan sun gaida shi ya amsa ya kauda kai, babban burinsu su je su fesawa Jannat wacce duk wanda ya zauna da ita ko na sakanni ne sai ya san tana son Sadaukin.
"Amsa?"
Ta dube shi don ita ta tafi kallon ƴanmatan da suka shige suna waigensu. Haka kawai yanayin kallon da ya bi ta da shi sai ta kasa jurewa ta kauda kai. Ta ɗan yi gyaran murya.
"Gidan Baban Kowa wajen Radiya."
Ya jinjina kai.
"Ok, gobe ki kawomin results dinki na Jamb. Idan ba ki gan ni ba, ki kira ni a waya."
"Na dauka sai bayan biki."
Ta tambaya. Ya yi murmushi don sai a sannan ma ya tuna diramarsu ta jiya.
"No, ina son ganin score dinki na..."
Ai da sauri ta juya za ta bar wurin lokaci guda shi kuma ya riƙo hannunta ya dawo da ita baya, kusancin da har numfashinsu na cuɗanya da juna. Da sauri ta ja baya amma fa ta kasa ƙwatar tsintsiyar hannunta da ya riƙe.
"Kar ki damu, ba wanda aka haifa da iya wa. Gradually, ke ma wataran za ki iya idan kin maida hankali a inda zan kai ki. Na yarda da ke."
Daga nan ya saki hannunta yana mata murmushi, wannan murmushin shi ne Jannat ta gani da kuma kalmar ƙarshe da ya ce ya yarda da Haulatu. Haulatu wacce mamakin kalmar da ma murmushin nasa ya kusan sanya ta suman tsaye, ba ta farfaɗo ba sai da ta ji ya soma tafiya yana kiran sweet dreams.
Ta dube shi inaa, sai ƙeyarsa, tuni ya bar wurin da taku irin na wanda ya amsa sunan namiji.
"B...uban can! Kai!!! Kun ji kuma kun ga abin da na gani?"
Muryar wata ce a gefen Jannat, ya dauki hankalin Haulatu, a nan ne ta ankara da su, ba ta ce musu uffan ba ta kauda kai ga kallon banza da hararar da ta ga Jannat na jifanta da shi ta sa kai ta nufi sashin Baban kowa. Ita a zatonta ma ko za su biyo bayanta ne ta nunamusu daidai take da kowacce a cikinsu sai dai kuma ta ji shiru. A can ne ta labartawa su Safina duk abin da ya faru. Sakin baki suka yi suna kallonta kafin su kwashe da dariya. Radiya faɗi take.
"Kai kai kai! Ki ce akwai kallo a gidannan. Anti Jannat ta ganku? Kin san irin mutuwar son Yaya Sadauki da ta ke yi? Toh wallahi na ta haukar ina ga ya fi na Anti Zaituna. Gwara ma ita Yaya Zaid ya san da zamanta, ita kuwa wannan Momi Nuratu ce kawai ta sani kuma ta ce ba ruwanta a cikin sha'anin."
"Ni sai na ga ma kamar sonki yake yi." Faɗin Munira tana duban Haulatu. Haulatu ta dube ta sai ta ji gabanta ya fadi.
"Sona kuma? Kin ga ki yi shiru ma kar wasu su ji ki. Ni ban iya abin soyayya ba. Duka duka ma nawa nake?"
Harararta Safina ta yi.
"Jimin ke. Kin kusa ashirin kina batun nawa kike. Tab, ai bana fatan soyayya ta yi maki ma irin kamun hauka na Aunties dinnan namu, ni kinga da sauki ko ba komai yawan addu'a ya sanya na rage damuwa hankalina kan shagalta da wasu abubuwan. Amma fa son yana nan babu ƙarya. Kai, ina ma dagaske Yaya Sadauki yana sonki, wallahi kun yi masifar dacewa."
Haulatu za ta yi magana kenan wayarta ta yi ƙarar shigowar saƙo. Ta duba, ganin baƙuwar lamba ya sanya ta maida hankali.
_*If I could give you one thing in life, I'd give you the ability to see yourself through my eyes, only then would you realize how special you are to me.*_
(Idan ace zan iya ba ki abu ɗaya a rayuwa, da na baki damar ganin kanki ta cikin ƙwayar idanuna, a nan kaɗai za ki gane yanda ki ke ta daban a wurina).
Ta karanta ya fi sau biyu, ta dai fahimci kalaman soyayya ne amma kuma ta ƙaryata yanda ta fassara su kamar ma ba daidai ba, sai kawai ta miƙawa Safina.
"Ɗan karanta."
Safina ta karanta a fili, suka dube ta kafin su dubi juna su sa dariya.
"Inyee, waye wannan don Allah? Bari na ga ko nasan lambar." Faɗin Radiya tana kara kai a fuskar wayar su na dubawa.
Ita dai Haulatu sai ma ta miƙe tana mitar su tashi su dafo indomie da kifin da suka ce za'a ci ita yunwa take ji. Haka suka gama duba lambar har da sanya wa a nasu wayoyin amma ba su canki ko na waye ba, ga Haulatun ta ce musu ita ba ta ba kowa lamba ba. Wani murmushi Radiya ta yi.
"Oh ni, Allah yasa Yaya Sadauki ne. Kai da na yi maki murna wallahi."
Ta ja guntun tsaki gami da faɗin.
"Wai ku ina muku maganar yunwa nake ji kun tsaya mafarkin gaibu."
Sai a sannan suka miƙe suka fito zuwa kicin hirar dai ba ta ƙare ba. Mai yanka albasa na yi mai gyara kifi tana cire ƙayar tana yi, a haka suke aikin suna hirarsu har Munira kai ka ce ma ta san Haulatun tun jimawa.
Da daddare kuwa koda ta zo kwanciya, wani saƙon ne ya ƙara faɗowa ɗan guntu.
_*Good night princess. Sweet dreams.*_
Ta tuno ɗazu da Yaya Sadauki ya furta mata kalmar saƙon nan na ƙarshe, to ko dagaske suke yi shi ɗin ne?
'Kai aa, ina da lambarsa ai." Ta faɗi a ƙasan rai gami da ɗan buɗe contact lists dinta ta duba, tabbas akwai lambarsa. Wayarta ta yi ƙara ta ga Yaya Mu'az ne, sai da ta ɗan dubi su Safina kowacce hankalinta na ga waya tana danne-dannenta babu ma alamun bacci a idanunsu kafin ta ɗaga.
"Ɗan birni." Jin sunan da ta ambata ya sa hankalin Safina komawa kanta duk kuwa da cewa idanun suna kan waya amma tuni ta rasa nutsuwarta. Sai da ta ji faɗuwar gaba sakamakon saƙe-saƙen zucin da ta faɗa, kada dai ace Yaya Mu'az ne mai turo wa Haulatu saƙon? Zarginta ya kau da ta ji Haulatu ta ɗan yi dariya ta ce.
"Ni na sauyamaka a ina? Kawai dai ka watsar da lamarin ƙanwarka shiyasa ni ma na ja jiki."
Har dai suka kammala hirar ba ta ji alamar ya turo saƙo ko makamancinsa ba. Sai da suka yi sallama da zummar gobe zasu haɗu a gidan su yi magana ta fahimta kafin Safina ta samu nutsuwa. Koda Haulatu ta kammala wayar ma ba ta ce musu uffan ba face chaji da ta jona wayarta ta shiga ta ɗora alwala wanda a dole Umma ta sabar mata da yi kafin kwanciya har ya zame mata jiki idan ma ba ta yi ba sai ta ji ba ta da nutsuwa komin dare idan ta tuna sai ta tashi ta yi.
***
Zaid ya zubawa wayarsa idanu, bai taɓa zaton ba zai ga kira ko amsa ba don a tunaninsa yarinta ma ba zai sa ta ƙyale ba ta biyo bayan lambar ta ji ko waye ba. Zai so ya ji muryarta koda kuwa shi ɗin ba zai ce uffan ba. Shigowar Juwairiyya da sallama ne hannunta riƙe da faranti mai ɗauke da ruwan shayi da sugar da kofi ya maido shi hayyacinsa. Jalilah har a sannan tana gidansu sakamakon rashin lafiyar da ta fara tun bayan sallah wanda zuwan farko da suka yi asibiti aka tabbatar da cewa juna biyu gareta.
"Yaya ga shi nan."
Ya gyada mata kai.
"Nagode. Ki tura ƙofar idan kin fita."
"Toh, sai da safe."
Ta amsa a ladabce kafin ta miƙe. Har dai ya kammala shan shayin ya yi shirin kwanciya babu amsa, anan ne ya ƙara aika saƙon sai da safe amma shiru don haka ya haƙura ya bi lafiyar gado.
***
Washegari aka sanya Amare a lalle, wannan karon a farfajiyar gidan Abba Ridwan aka sanya ƙaton rumfa sai kafet da aka shimfiɗa amare aka yi musu lalle hakanan ƙawayensu. Masu ƙunshi ne har mutum uku, don haka bayan ƙawayen Amare ma har ƴan uwa sai da suka samu na su rabon. Ga kiɗan ƙwarya a gefe yana tashi masu rawa na yi.
Haulatu kuwa sau ɗaya ta je wurin sai ta fita ta shiga wurin Momi Nuratu ta gaida ta daga nan ta fice zuwa ɓangarensu.
Tana shiga ɗakin Umma bayan sun gaisa da mutanen falon, wayarta ta yi kara. Dafe goshinta ta yi gami da yin salati ganin sunan mai kiran. Hindatu ce. Ita shaf ta manta ma da kiran da ta yi mata dab da biki kuma ko ta whatsapp ta ga ta yi mata magana amma a ranar sun je gidan kitso ya sa ba ta buɗe ba.
"Wai Allahna, ƙawas yi haƙuri ni wallahi har ma na ji kunya." Abin da ta ce kenan ba ta ko jira cewar Hindatun ba don ta san ta yanzun za ta cikamata kunne da faɗa da mita. Sai dai saɓanin hakan ta ji muryarta a sanyaye.
"Hum, ba ki da kirki ai Haulatu. Wato ke ko mutuwa zan yi ma sai bayan ta faru ta ƙare za ki biyo sahu ko? Kin kyauta ai."
Ta zauna gefen gado.
"Wayyo, ni dai ki yi haƙuri. Gidan da nake aiki ne suke hidimar biki, kin ga tun fara shagulgulan babu zama, ni ce goya yaron wance, ni ce shara nan tattara can. Ya garin? Ya Momi?"
Hindatu ta sauke numfashi.
"Lafiya kalau muke. Sai ki shirya zuwa Kano ya gan ki, ni ma aurena nan da sati ɗaya."
Zaro idanu waje ta yi.
"Kai Big Mama kin san bana son irin wannan wasan ko?"
"Na rantse maki dagaske nake Haulatu."
Ta kwashe labari tun daga haɗuwarta da Alhaji Ibrahim da ma irin hidimar da ya yi musu ita da Mominta har zuwa batun neman auren da ya yi can wurin wasu dattijai a dangin Momi har da saitin akwati ɗaya da ya ciko ya kawo na saka rana ba wai lefe ba, duka ta sanar da Haulatu. Ta ƙara da faɗin.
"Haulatu yanzu kam ba tsora ta, ga shi gobe za'a kawo lefe. Wallahi duk sona da abin duniya ba ki ji yanda ƙirjina ke lugude ba a koyaushe, ga mafarkai da nake yi masu ban tsoro akan Alhaji, kuma ni nasan ina sonsa, amma kudin nan da yake min hidima da su tsoro suke bani. Ina kuma ji cewa idan ban aure shi ba mutuwa zan yi saboda ina sonsa."
Duk da fankar da ke kaɗawa a falon bai hana Haulatu gumi ba.
"To ai ba ke ba Big Mama, ni kaina da nake gefe a nan ba ki ji yanda na tsorata ba. Kin rikita ni, ga shi nan dai kin ce kina tsoro amma kuma kina sonsa ba za ki iya fasa aurenshi ba. Wannan wane irin abu ne? Tsaya ma, ni ban ji kin ce ga sana'arsa ba."
"Ɗan kasuwa ne. Yana da babban gareji na gyaran motoci nasa na kansa, kuma yanzu haka yana gina wani katafaren Mall a nan wuraren gidan gwamna."
Ajiyar zuciya Haulatu ta saki.
"To ai da sauƙi ma Big Mama, don Allah ki kwantar da hankalinki. Kawai ki saka a rai babu komai, addu'a ita ce mafita ke dai. Kar ki zuba idanu ki bari kanki ya ƙulle ganin dukiya, ki tsaftace zuciyarki daga zargin wanda za ki aura tunda kina sonsa. Ki miƙa dukkan lamuranki ga Allah. Kin ji?"
"Toh Haulatu. Amma fa na yi mamakin jin wadannan kalaman daga bakinki, yaushe ki ka zama mai hankali har haka wai?"
Dariya suka yi kafin Haulatu ta ja tsaki.
"Me kika maida ni?"
Daga haka suka ɗan taɓa hirarsu kaɗan sannan Hindatu ta ce.
"Bari na kyale ki hakanan kar a neme ki a gidan. Ki gaishemin da Umma don Allah sannan ki turon da lambar akawun na saka maki wani abun."
Haulatu ta zaro ido.
"Ni ƴar Ummana."
"Au ba za ki turo ba?"
Sai a sannan ma ta fahimci suɓul da bakan da ta yi. Ta yi maza ta saita bakinta.
"Aa fa, nufina ina ni ina mallakar akawun na banki?"
Sai dai a zahiri ta buɗe akawun har Umman ma bisa umarnin Hajja. Ita dai kuɗin Hindatun ne ba ta buƙata balle ma da ta ji ita kanta tsoronsu ta ke amma don ta kwantar mata da hankali ta ce za ta nemi na wani ko cikin ma'aikata maza na gidan ne ta aikomata. Da wannan suka yi sallama.
Shigowar wani kiran ne ya sa ta ɗaga wayar don a zatonta ma Hindatun ce sai ta ga lambar Yaya Sadauki ai ba shiri ta mike tsaye, ita shaf ta mance ma da zancen kai mishi takardar jarrabawarta ga shi nan kuma yanzun yamma ta yi, ko ɗazu sun haɗu da Mu'az sun tattauna ya ba ta haƙuri da nuna mata dalilin Mominsa ne ya rage shiga sabgarsu. Ta fahimce shi sosai saboda sanin girman mahaifiya. Ai da ta sani ma ɗazun ta damƙawa Mu'az din ya ba shi kawai ta huta da haɗuwarsu.
Ta ɗan yi gyaran murya kafin ta ɗaga gami da sallama. Ya ɗan ja fasali kafin ya amsa sallamar.
"Ki kawo takardar ina gida."
Daga nan ya katse kiran. Ta ɗan harari wayar kafin ta nemo wani file da ta ajiye dukkan takardunta masu amfani ta ciro na Jamb ta fito. Su Umma duka ana falon ƙasa, ta karasa har wajen Umma saitin kunnenta ta faɗamata umarnin da Sadauki ya yi mata, Umma gyaɗa kai kawai ta yi, dama tana da labarin Baba Alhaji ya ce ta kai wa Sadaukin takardunta. Bayan fitar ta, Hajiya Hadiza ta dubi Umma.
"Oh ni Na'imatu, wannan ɗiyar taki akwai kinibibi, ko me ta raɗamaki haka? Oho."
Umma ta yi murmushi.
"Ni kuwa yarinyar ta a burgeni. Na faɗa da ace za'a bar min ita can Malaysia zamu wuce ta yi jami'ar har Allah ya kawo mijin aure." Cewar Maman Zaituna, wannan magana ta yi mugun yi wa Haj Hadiza zafi, dama tun sadda Maman Zaitunar ta soma furtawa sam abin bai mata ba, wato ita nata ɗiyar ba ta da farin jinin Haulatu. Kowa ya zo a ƴan uwa zai ce Haulatun na burgeshi, wannan sam abu ne da ke cin zuciyarta. Da ace ta san yanda za ta yi da Haulatu ai da tuni ta yi abin da zai jawo mata baƙin jini a gidan baki ɗaya.
A fili kuwa dariyar yaƙe kawai ta yi. Maman Safina ita ma sai yabon ɗabi'un Haulatun take yi, anan ne Haj Hadiza ta yi dariya gami da nuna ai a gidan ne ta nutsu. Ta ƙara da faɗin.
"A baya da ta zo yanda ku ka san ita ce haihuwar barikin ba uwarta ba tsabar rashin iya tauna magana kafin ta furzar. Yanzun ma ai takan taɓa kawai dai ilimin addini ne da ta samu wanda ya jawo ta soma yaƙar jahilci."
"Wace irin magana kike yi ne haka Hadiza? Don Allah wannan ba girma a ciki."
Cewar Hajiya Aishatu ƙanwa ga Abba Ridwan dake zaune a garin Kano.
Hadiza ta yi shiru kawai ganin sun mata caa, Umma kuwa kamar ba ta wajen don ci kanki ba ta ce mata ba. Sai ma ta maida hankali ga autan Maman Zaituna, Haneef wanda ya miƙo mata robar lemu wai ta buɗe mishi.
***
"Yallaɓai na fa samo labari daga wurin Alhaji Mijinyawa, kamar yanda na faɗamaka ɗansa Mujahid abokina ne. A bakinsa na ji komai."
Jin haka Ɗan Mutuwa ya gyara zama a ɗaya daga ciki ƙawatattun kujerun dake falonsa, ga sanyin Ac ta ko'ina ya na sha yace.
"Ina jinka Audu."
"Yauwa, iyalinka suna Katsina. Mahaifin Uwargida babba ne a Katsina kafin mutuwa ta ɗauke shi. Sunansa Alh Bello S Malumfashi. Wannan sunan ba ɓoyayye ba ne a garin Katsina."
Tsananin mamaki ya mamaye Ɗan Mutuwa. Ba don ya san Audu ba maƙaryaci ne ba tun a baya, da zai iya cewa ƙarya yake yi. Sannan uwa uba Uban Dodo ya ce masa iyalinsa na gida na alfarma ne kuma wuri ne mai cike da tsari na addu'o'i. Amma tabbas ko ma ina ne, gidan manyan mutane ne.
"Lallai an gaisheka Audu, haƙiƙa ka kyautamin da wannan bincike. Ka turomin lambar asusun bankinka. Za ka ji ni yanzu."
Wanda aka kira da Audu ya dinga zuba godiya kafin Ɗan Mutuwa ya katse kiran. Bai jira komai ba ya ƙara dannawa wani ɗan ƙungiya kuma Sanata a garin Katsina waya. Bayan sun gaisa ya sanar da shi buƙatar sanin waye Alh Bello S Malumfashi. Nan ya tabbatar masa shi kansa yana harkar kasuwanci da yan gidan, ya san Alhaji Ridwan sosai. Wata dariya Ɗan Mutuwa ya yi kafin ya yi mishi sallama da zummar zai neme shi bayan biki.
Wato Na'imatu daula ta samu, har ta yi ƴancin da zai mantar da ita matsayinsa na mijin aurenta kenan? Ya yi ƙwafa kawai. Babban burinsa yanzu Hindatu ta shigo hannunsa sai kuma ya koma yaƙin dawo da Na'imatu rayuwarsa.
***
Mu haɗu gobe in sha Allahu....
Da sallama ta shiga falon Momi Nuratu, tana jin hayaniyar su Raudha da ƙawayensu a can falon na biyu. Ta iske ta zaune suna hira da Mamin Khaleefa da Amaryar baban Mu'az (kishiyar mommynsa) sai ko wasu daga yan uwa na Malumfashi. Gaishe su ta yi gaba daya suka amsa fuska a sake. Ta ƙarasa ga Momi Nuratu tana tambayar inda Yaya Sadauki yake, ta ƙara da yi mata bayanin results din da Baba Alhaji ya sa ta kawo mishi. Momi Nuratu ta kira wata yarinya cikin ƴan aikinta ta ce ta kai ta ɓangaren Sadauki. Bayan fitarsu Mamin Khaleefa ta dubi Momi Nuratu.
"Wannan kamar jikar Hajjar nan ko?"
Da murmushi ta amsa.
"Haulatu ba, eh ita ce. Ɗiyar Na'imatu."
Da mamaki Mamin Khaleefa ta ce.
"Kai, kinsan Allah da farko