Showing 168001 words to 171000 words out of 177840 words
ruwa tsundum, ganin abin na neman zarce gona da iri ne ya sanya ta saurin janye fuskarta ta kuma ja baya, shi ma babu wani karfi a jikinsa sai ya jinginar da kai yana sauke ajiyar zuciya akai-akai. Kasa furta sai da safen ta yi don haka a hankali ta sa hannu ta buɗe murfin motar, za ta fita ya ɗan riƙe yatsunta. Murya kamar ba ta Sadaukinta ba ta ji ya ce.
"Allah ya tashe mu lafiya."
A hankali ta zame yatsunta daga nasa ta amsa da amin, amsawar da babu lallai ya fita yanda ya dace.
Ba ta bada fuskar a ja ta da ƙananun tsokana ba amma ina, duk da haka ba ta tsira ba wajen su Safina da Radiya.
Washegari da asubar fari bayan Haulatu ta yi sallah, Umma ta ja ta zuwa ɗakin da babu kowa ciki sai su biyun. Nasiha mai ratsa jiki ta shiga yi mata na ƙara nusar da ita matsayi da girma na miji. Tun Haulatu na dannewa har hawayenta ya shiga fita. Sun jima sosai kafin a ƙarshe Umma ta bi ta da kyawawan addu'o'in shiga gidan aurenta a sa'a ta kuma yi mata nuni da muhimmancin riƙo da sallah, da karatun Alkur'ani mai girma da kuma addu'a.
A ranar dama lakca ce za'a yi akan aure sai kuma dinnerparty da Ango ya shirya wanda daga can zai wuce da Amaryarsa.
KANO...
Tana zaune a ɗaya daga cikin ɗakunan gidan Mahaifin nata Malam Bashir Magaji tana goge kayanta sakamakon wutar nepa da aka kawo, kwananta uku a gidan amma babu wata alama na cin fuska ko mutuncinta a wurin mahaifin sai ma ja a jiki da kuma nasiha. Gida ne na ilimin addini da kuma kyakkyawar tarbiyya. Da Uwargidansa Rakiya, Mominta ta yi zaman kishi. Rakiya ta sha wahala a zaman Momi a gidan. Dalili kenan da ba ta samu wata tarbar arziƙi daga gareta ba, gwara ita ta biyun wacce sai bayan fitar Momi ta shigo gidan. Ba ta wani samu matsala da ita ba. Ita dai ga Hindatu babban farin cikinta yanda mahaifinta ya karɓe ta. Momi har kiranta ta yi bayan dawowarta daga Dubai ta kuwa shaida mata inda take, hankalinta ya tashi ta dinga zaginta. Ƙarshe ta ce za ta zo su tafi kuma sai ta karya dukkan wani sihiri da Baban ya yi don ya raba su. Ita dai ba ta tanka mata ba sai ma hawayen takaici da ta zubar ganin har a sannan abubuwan da suka faru bai sa Momin ta yi nadama ba. Sun yi waya da Haulatu kafin bikinta, nan take jin labarin aure za ta yi. A sannan ne kuma ta zayyane mata gaskiyar halin da suke ciki a Katsina. Ita ɗin ba aiki take ba, hannun dangin Umma suke sannan ɗan uwanta za ta aura. Hindatu ta sha mamaki amma ba ta ji zafin ɓoyon da ta yi mata ba sosai musamman da ta ji dalilin Haulatun cewa ta yi ne don gudun kar Ɗan Mutuwa ya samu labarin inda suke.
"Hindatu! Hindatu! Fito ko na ci ubanki!"
Jin murya kamar na Mominta ya sa ta ajiye dutsen gugar gami da kashe socket din. Wata ƙanwarta dake latsa waya a saman katifa ita ma ta miƙe zaune ta dube.
"A'uzubillahi, wa ke mana ashariya a gida? Kamar ke ake kira kuma ko?"
Jin haka yasa Hindatu ƙara nutsuwa, aikuwa wannan karon sosai ta gane muryar Mominta don haka da sauri ta miƙe kusan a tare suka fita da budurwar nan.
Gwaggo kamar yanda ake kiran Rakiya uwargidan Malam, ita ce ta soma fitowa daga ɗakinta cikin shirin da ta yi na fita unguwa amma ta haƙura sai yamma dalilin ranar da ake yi a garin, wannan ne ma yasa kowa ya ƙume a ɗaka. Momi ta banka mata uwar harara, babu abin da ya fi baƙanta mata irin atamfar da ta gani jikin Rakiyar wanda ita ma a watan ta siye shi, ko wata biyar ba ta yi da fitowa a kasuwa ba, ga kuma irin gyaran da gidan ya sha kamar ba gidan da aka yi shi da jar ƙasa ba a baya wanda ta sani.
"Haba Shatu, ai ko da me kika zo gidan nan, bai kyautu ki shigo mana da ashariya ba. Kar fa ki manta gidan nan na masana ilimin addini ne, ba haka nan ake zaune ba kamar tsoffin maguzawa."
Kamar Momi na jira ta hau kanta da ruwan masifa.
"To sannu rainon Sudais, ni za ki koyawa addini? Kira ni kafira kawai! Aikin banza, ni ba don dalili irin wannan ba ai na fi ƙarfin zuwa gida irin wannan mai kama da akurkin kaji. Ɗiyata na zo a ban na tafi da ita tunda dai ko sisin kwabo na siyan ko sabulu Bashir bai taɓa aiko min don amfaninta ba."
"Momi, mene ne haka?" Muryar Hindatun da suka ji yasa suka dube ta, ita ma Maman Jidda wato Amaryar Malam, ta na daga tsaye ƙofar ɗakinta baki a sake tana kallon abin mamaki. Lallai daga yanayin Momin ta yarda za ta aikata duk abin da aka zayyane mata har ma fiye da haka. Kallo ɗaya ma idan ka yi mata za ka fahimci idanun nan a tsaye suke. Kafin Momi ta ba da amsa Gwaggo Rakiya ta cafe.
"Ko ya aiko ko bai aiko ba, wannan kin fi kowa sanin dalili. Ita kuwa Hindatu da kike ikrarin sai ta bi ki kuma ɗiyarki ce, toh ni Rakiya nace babu inda za ta je. Malam ba ya gari ya yi tafiya kuma amanar gidan a hannuna ya damƙa don haka kin yi kaɗan ki shigo ki mana tijararki na rashin tarbiyya ki tafi da Hindatu."
Wata dariya Momi ta yi sannan ta riƙe ƙugu.
"Rakiya, ke har kina tunanin kin isa ki hana ni tafiya da ɗiyata? Ke a wa? Yaushe ma ki ka samu ƴancin kanki da har ki ke jin kin kai ki mulki wasu? Ko kin mance sadda ki ke durƙusawa ki gaishe ni har ki ɗoran sanwar yini guda curr? Eh lallai, na yarda akuyar ɗaure ta samu sake."
Maganganun sun yi wa Gwaggo Rakiya ciwo, Hindatu ranta ya ɓaci. Ashe dagaske ne dama duka labarin da ta ji wata ƙanwar babanta na bai wa Maman Jidda akan irin zaluncin da farraƙu da Mominta ta yi wa Gwaggo Rakiya tsakaninta da mijinta? Dagaske ne ta juya shi tamkar waina a tanda? Hawaye masu zafi suka zubomata. Ta kasa cigaba da sauraron irin faɗi in faɗar da ake tsakanin Momi da Gwaggo Rakiya wacce har babban ɗanta namiji ya shigo ba a fasa ba. Momi ta dage sai ta tafi da ita yayinda Gwaggo ta ce ko za ta kira DSS ƙarewar ƴan sanda to fa babu abin da zai sa ta tafi da ita a yau. Hindatu cikin zubar hawaye ta fincike hannunta da Momi ta riƙo tana ja.
"Ki kyale ni, ni ba zan biki ba. Babu inda zan je. Kiyi hakuri ki tafi Momi. Shekara da shekaru ina maki biyayya ban taɓa takowa inda mahaifina yake ba, ki bar ni na zauna cikin ƴan uwana nasan dangi kuma na shaƙu da mahaifina. Shi ma yana da haƙƙi a kaina. Don Allah ki bar tara wa kanki mutane ki tafi."
Tana kai wa nan ta shige ɗakin da ta fito. Momi za ta bi bayanta, Gwaggo Rakiya ta sha gabanta, suka kalli juna ido cikin ido. Gwaggo Rakiya na murmushin nasara, tun ma zuwan Hindatu gidan ba ta taɓa ji ta wani burgeta ba sai a yau, ta kuma gane dagaske take ba ta goyon bayan uwarta, ta kuma yi tuba na gaske. Dama babban abin da yasa ta kasa sakin jiki da ita bai wuce tsoron ko wani makircin Momi Shatu ta shiryo ba.
"Na shiga uku na lalace! Hindatu! Me aka ba ki kika sha? Innalillahi! Allah ya isa tsakanina da kai Bashiru. Burinki ya cika Rakiya kin raba ni da ƴata. Ko zan yi yawo tsirara sai na ƙwace yarinyata daga hannunki. Munafuka algungu..."
Ba ta kai ƙarshe ba sakamakon hannun da Rabe babban ɗan Gwaggo Rakiya ya ɗaga da zummar kai mata mari sai dai tuni Gwaggo Rakiya ta riƙe hannun, wani irin rawa jikinsa ke yi. Ba ya tunanin zai ɗauki cin kashin Momi ga mahaifiyarsa. Wanda aka ɗan yi a gabansa yana ƙarami ma ya isa haka. Momi kuwa tsit ta yi dalilin rawa da jikinta ya hau yi tamkar mazari.
"Kar ka kuskura, ashe za ka nunawa duniya ban ba ka tarbiyya ba?"
Abin da Gwaggo ta ce kenan, a dole ya sauke hannunsa zuciyarsa na raɗaɗi, murya a kausashe ya dubi Momi ya ce.
"Fita daga gidan nan."
Ba wani ja in ja ta fice bayan ta makawa Gwaggo harara. Hindatu dake jin komai kuka kawai ta cigaba da yi, har da Gwaggo a wadanda suka shiga rarrashinta. Ko bayan dawowar Malam Bashir, Gwaggo ta zayyane masa duk abin da ya faru. Dariyar takaici kawai ya yi gami da roƙawa Shatu shiriya don ya yi amanna sai dai addu'ar ta kamace ta, amma mai hali ba ya fasa halinsa. Ya kira Hindatu ya ƙara yi mata nasiha akan muhimmancin haƙuri da yarda da ƙaddara. Ya ƙara da cewa zai dinga koyar da ita a gida bayan Isha'i idan ya dawo don a ɓangare na addini kusan babu wani abin arziƙi da ta sani, sai ta share wata da watanni ba ta je islamiyya ba har aka gaji a ka kore ta daga makarantar. Momi ba ta taba damuwa ba.
Hindatu ta ji dadi rayuwa ta sauya, babu abin da ta ɓoyewa Haulatu, sosai ita ma ta ji dadi ta kuma ƙara nusar da ita akan ta dage kar ta yi wasa rayuwarta ta ƙara shiga yanayin farko. Addu'a ce maganin kowace matsala.
Wannan kenan.
***
Katsina...
Babban gida mallakin marigayi Bello Malumfashi ya cika da jama'a mata, waɗanda suka taru a farfajiyar gidan da aka ƙawata da ado don gabatar da lakca dangane da aure. Malamai uku mata ne masana addini da ma zamantakewa suka gabatar da lakcar. Kowa a wurin ya nutsu, Haulatu na daga gaba dab da su a zaune a ƙasa ta rufe kai da mayafi. Sai ƙawayenta da yayyu dake a gefe. Hawaye kawai take yi tana ƙara gane girma da nauyin da ya hau kanta a yanzu. A yanda take ji ko kara ba za ta iya tsallakewa ba matukar ba umarni ne daga mijinta ba. Sosai ta tsorata da misalan girman miji da ma haƙƙoƙinsa da Malaman suke ambata. Ta kuma kara gane cewa Ummanta duk wannan biyayyar da ta dinga yi a baya, har da tsoro da gudun faɗawa halaka tunda babu yanda ta iya a sannan mijin aurenta ne. Taron bai tashi ba sai da ta ƙudurta a rai da yardar Allah ba za ta aikata abin da zai sosa ran mijinta ba da gangan.
Shi ma Sadauki ya sha nasa nasihar da faɗa a wurin Baba Alhaji sadda ya shiga gaishe shi da yammacin, ya yi masa alkawarin riƙe amanar Haulatu da ba ta kulawar da ta dace. Baba Alhaji ya ji daɗi sosai, ya kuma sanya albarkar a auren.
***
Misalin ƙarfe shida da mintoci, Haulatu ta kammala sallama da iyayenta maza, har wajen surukarta kuma uwa Momi Nuratu aka miƙa ta. Ita rungume ta tayi ma ta nunawa kowa ba suruka ce a wurinta ba. Ɗiya take a wurinta. Ita ma addu'o'i ta yi musu na zaman lafiya.
Komai da ya kamata a kai kama daga kayan lefenta da na sanyawa da ma sauran tarkace babu abin da bai yi gaba ba zuwa gidanta. Duk wanda ya je gidan ya dawo sai dai ka ji yana sambatu irin tsari da kyawun gidan. Zaituna kusan da ita aka yi komai, aka ƙara tattara kayan kwalaye da ma sauran tarkacen da aka zubar aka kunna burners aka sa turaren wuta a falo da ɗakunan bacci sannan aka rufe gidan aka tafi.
"Gida babu abin da yake jira sai matar gida."
Abin da Zaituna ta furta kenan tana kallon Haulatu wacce ta idar da sallar Magriba ba ta kai ga miƙewa ba. Kauda kai kawai ta yi tana ɗan turo baki. Tun rana take kukan rabuwa da Hajja da Ummanta. Hakan yasa idanun suka kumbura don har a lokacin ba su gama dawowa daidai ba.
"Kai don Allah Anti Zaituna, daƙyar fa muka samu muka rarrashe ta." Faɗin Radiya kenan kamar ta ɗora wani sabon kukan. Dama ɗazun su ke taya aminiyartasu kuka ita da Safina. Dariya Zaituna ta yi.
"Ba na son gulma fa. Ji wani sabon iyayi. Toh ko a fasa kai ta?"
Ta ƙarashe cike da zolaya tana kallon inda Haulatu take, lokacin tana saman kujerar gaban madubi a zaune mai mata kwalliya na fiddo kayayyakin kwalliyar tana ajiye saman madubi, ba ta kalle ta ba sai wasu sabbin ƙwallar da suka cicciko mata. Ganin haka mai kwalliyar ta hau yiwa Zaituna ido akan ta yi hakuri ta bari. Zaituna na murmushi ta karasa da kanta ta rarrashi ƙanwarta sannan ta fice don soma nata shirin ita ma.
Ba wasu gayya ne za su je Dinnerparty din ba, abu ne na mutane ƙalilan.
Wannan karon Amaryar shigar kaya sky blue ta yi su kuwa Safina babu mai anko kowa da kayan da ya saka. Ta yi kyau ta ƙara, ita kanta ma ciwo yake dalilin kukan da ta ci a ranar. Bakinta ya mutu sai murmushi sanin da ta yi idan ta sa ƙafa ta bar gidan a yanzu shikenan kuma sai gidan mijinta. Daƙyar ta iya daurewa ba ta yi kuka ba. Ta rungume Umma kamar kar ta saki, haka nan aka rabu Umma na mata murmushi da kuma sanya albarka da fatan zaman lafiya. Kowa na fadin ta yi kyau, Hajja ma dai dauriya ta yi, ta godewa Allah da ba ta mutu ba ta ga Na'imatu har ga shi ta ga auren abin da ta haifa. A son Hajja ma sam ba ta so wani dinner bayan daurin aure ba, fada ta dinga yi kawai a wuce a kai Amarya ɗakinta, sai da aka lallaɓata ita da masu taya ta kafin a samu a shawo kanta. Amma acewarta, ai babu wani abu da ya rage na biki wanda ba'a riga an yi ba.
Wata sabuwar mota ta gani fara ƙal sai sheƙi take. Sai a sannan ta tuna Safina ta fesa mata gulmar wai Sadauki ya yi mota sabuwa. Ta sauke ajiyar zuciya har suka ƙarasa, kafin ta buɗe gidan bayan, Sadauki ya kai hannu ya buɗe mata. Angon kaya suka yi, shi ma shaddarsa blue ce. Ya mata kyau sosai kamar yanda shi ma ta masa. Hannuwanta ya matse cikin nasa bayan kafaɗunsu dake gugar juna.
Wurin ya ƙayatu ƙwarai, ba wani abu aka yi ba na raye-raye, abin da zai ba da sha'awa, addu'o'i ne sai ko ɗan nishaɗi da MC ta gabatar, sai Amarya da Ango da suka fito fili suka tsaya aka ɗan yi liƙi. Daga nan aka ci abinci aka watse.
A hanyar dawowa da kansa yake jan motar, Haulatu wannan karon babu ɗigon hawaye don Ogan nata bai bata wannan damar ba, jan ta yake da hira da kalamai masu sanyaya jiki.
Zaituna dake kallon motar Ango da Amarya sadda suka fice a harabar wurin taro ta sa bayan hannunta ta share fuskarta. Murmushi take yi amma hawaye bai bar fita a fuskarta ba. Wani irin murna da farin ciki take taya ƙanwarta da shi na dace da masoyin da yake sonta ita ma ta ke sonsa. Tana ji a jikinta Haulatu ta yi dace da masoyi.
"Muna iya tafiya?" Muryar Khaleefa ta ji, a hankali ta juya suka haɗa idanu yana mata wani murmushi haɗi da miƙa mata hankicif ɗinsa fari ƙal. Ita ma sai ta maida masa martanin murmushin. Tare suka zo a motarsa ita da Radiya da kuma Maama, wannan karon dai babu Maama don direbanta ya zo da mota ta wuce gida. Radiya ita ma ba ta tsaya ba ta fice ta bi su Safina. Sai a sannan ta ɗan wulƙa idanuwa. Motoci na ta fita.
"Radiya tana ina? Da ita fa muka zo."
Tana maganar ne ita kaɗai don haka ya amsa mata.
"Ina tunanin sun tafi, Maama ita ma ta yi gidanta."
Ta sauke ajiyar zuciya.
"Ok."
Daga haka suka taka har zuwa gaban motarsa. A wannan tafiyar dai Khaleefa bai yi ƙauron baki ba sai da ya amayar da abin da ke ransa tare da ba ta damar yin tunani kan yanke hukunci. Ya kuma nuna mata dagaske auren yake so bai zo da wasa ba. Zaituna dai gaba daya jikinta ya mutu, wanda ba ta taɓa hasasowa zai kalle ta ba, ko kuma ya kaunace ta, shi ne da kansa ke miƙa ƙoƙon bara don ta karɓi ƙaunarsa. Tun a sannan ta ji kamar ta amince, amma tunani da kuma tsoron surukata da Maminsa ya sa ta basar ta nuna za ta yi tunanin kamar yadda ya ba ta dama.
***
Ango da Amarya sun isa gidansu cikin ƙoshin lafiya. Tun daga farfajiyar Haulatu ta ji gidan ya burge ta, matsakaicin fili da ɗan madaidaicin rumfa na ajiye motoci uku. Sai gefe da aka yi kwalliya da shukoki. Sadauki dake amsa sannu da zuwan Maigadinsa buzu ya maido hankali gareta.
"Mu je ko?"
Sai a sannan ta dube shi, shigarta babu inda ta nuna tsiraicinta, ko'ina a rufe asalima dinkin mai dogon hannu ne, ta rufe kanta sosai hakanan ɗan abin da ta yafa ba mai nuna tsiraicinta ba ne, wannan zabin Maama ne, sam ba ta yarda ma a yi bikin da Amarya za ta nuna wani sassa na jikinta ba. Hannunta ya kama suka nufi ciki. Sai da ya tsaya a ƙofa ya yi addu'a, ita ma ta yi sannan suka shiga da kafafunsu na dama, da kuma bismilla a bakin kowannensu.
Garin bin wurin da kallo ba ta san ma takalmin ya shige cikin kafet ba wannan yasa ta kusa kaiwa ƙasa, cikin azama ya riƙo ƙugunta da kyau, hannunsa ɗaya ledoji ne, ya ajiye a kujera mafi kusa da shi sannan ya riƙo ta sosai. Kunya ya sa ta ɗauke idanu daga duban nasa. Shi kuwa sosai