Showing 75001 words to 78000 words out of 177840 words
Haulatu wacce ita gaisuwar ma maƙale mata ya yi a fatar baki suka gifta shi suka fice daga falon. A hanya ta kula kamar Zaituna hawaye take fitarwa don haka ta ce su karasa bayan gidan wajen rumfa su zauna. Aikuwa suna isa Zaituna ta ci kukanta, abin ya ɗan daki ran Haulatu, sai kuma ta tsinci kanta da jin tausayi da haushinta lokaci ɗaya. Namijin me? Akan me za ta tsaya tana zubda hawaye kan wanda bai ɗauke ta komai ba?
"Ki yi haƙuri." Kalmar da Haulatu ta iya furta mata kenan, ta ma rasa ta ya za ta rarrashe ta. Zaituna ta jinjina mata kai kafin ta share hawayen fuskarta, abin ka da farar fata tuni fuskarnan ta yi jazur ga idanun ma sun ɗan sauya kala.
"A duniya idan akwai wanda na so kuma nake so har gobe, bai wuce Zaid ba. Na kaunace shi tun ban san ma me nake yi ba. Kaf a ƴan uwan Mamina babu wanda na shaƙu da shi kamar shi a zamana a hannun Hajja, don a nan na soma karatun secondary. Allah ya yi ni da son zaman Nijeriya, duk ƙin Abeena da haka, saboda son da yake min ya haƙura ya bar ni wajen Hajja. Muna chatting sosai da Zaid koda ba ya kusa, hakanan idan ya zo babban gida muke hira sosai, zai ɗauke ni mu je wurare masu kyau mu sha ice cream da sauransu. Wautar da na yi, ina yiwa hakan kallon so, ashe ƙuruciya da hauka su ke faɗamin ƙarya. Hum, Zaid bai taɓa sona ba, ban fahimci hakan ba sai da na kasa haƙuri na furta masa. Ya fututtuke ya sauyamin jin da ya yi na furta da bakina ina kaunarsa kuma da aure. Ya tabbatarmin shi ba ya kallona da hakan face ƙanwarsa wacce ya ke ji da ita. Ke tun fa daga lokacin ya sauyamin. Ban iya soyayya ba Haulat, haka na yi ta bibiyarsa da kuka da roƙo, na kwanta ciwo. Sanadin wannan ciwon ya sa kowa ya gane halin da nake ciki don har suma na dinga yi. Hajja da kuka wiwi ta ce ita fa kawai a daura auren koda Zaid bai amince ba. Shi kuma a gaban su Baba Alhaji da su Baba Dakta, Zaid ya rantse ba zai aure ni don bai taɓa sona ba kuma shi ba ya kaunar ma auren zumunci sannan har abada ba zai yi shi ba. Sannan fa ina dab da zana jarrabawar fit daga sakandire amma komai ya ficemin a rai.
Anan ne Hajja ta zo wuya, ita ma tace duk wanda ya ƙara roƙon Zaid ya aure ni Allah ya isa ba ta yafe ba. Haka suka yi baram-baram da Zaid da Hajja. Tun daga nan jikina ya yi sanyi, na gane dagaske Zaid ba ya sona kuma kamar yanda ya furta har abada ba zai aure ni ba ya sanya ni haɗiyar maganin ɓera amma Allah ya so ni da rahmarSa ban mutu a wannan yanayin ba. Bayan na farfaɗo su Baba Alhaji suka dage akan lallai sai Zaid ya aure ni, anan kuma na nuna musu na fasa aurensa, na roƙe su akan su janye ƙudurinsu na cewar sai sun auramin shi. Na tabbatar musu muddin aka yiwa Zaid dole akan aurena to na rantse zan kashe kaina kowa ya huta. Nace a zuri'ar ba a taɓa yiwa wani auren dole ba, to kar saboda ni a fara, ƙarshe ma na ce musu ni na daina sonsa. Haka na tayar musu da hankali kan cewa ni Malaysia zan koma. Na kira Mamina na labarta mata komai ina kuka sannan nace kar ta faɗawa Abeena, ita ma ta ce me ya kai ta? Saninsa da muka yi da zuciya da ɗaukar zafi, zai iya cewa ba zan ƙara zuwa Nijeriya ba. Yana mataƙur son yaransa, ba ya kaunar duk abin da zai taɓa mu, akan mu sun sha samun saɓani da Maninmu. Duk da dai na sha tambaya da tuhuma akan rama ta da kuma dalilin da yasa ban tsaya na rubuta jarrabawa ba. Dakyar aka kashe maganar ya aminta da cewa rashin lafiya ce ta hana ni. Hajja ita ma hankalinta ya fi kwanciya da komawata Malaysia don sosai ta kai wuya da Zaid, ta kuma rantse ta kuma muddin tana numfashi wataran sai ta rama abin da ya yi min kuma ya yi mata. Sannan ni kuma ko zan mutu ba za ta bari ya aure ni ba ko mai runtsi. Hum, Haulat ba zan iya misalta maki halin da na shiga ba sadda na ci karo da IV na bikin Zaid da Jalilah, anan cutar sonsa ya dawomin sabo. Ina ƙaunarsa fiye da tsammanin ni kaina Haulat, da wata ce kallonsa ba za ta ƙara yi ba bayan cin fuskar da ya yi mata da wulaƙanci, amma har gobe yana raina, na kasa fidda shi. Ganin da na yi mishi yanzu ya ƙara tayar da tsumin sonsa. Na kasa bayar da dama ga masu sona su fito neman aurena, asalima na cewa Abee sai na kammala karatu, da wannan na samu ya goyamin baya. Yanzu haka ina aji na biyu a jami'a a can, ina karantar pentadbir perniagaan."
Haulatu ta yamutse fuska har ta sa Zaituna yin dariya.
"Sorry, ina nufin Business Admin."
Ita ma Haulatu ta murmusa. Zuciyarta cike da tausayin Zaituna da kuma jin babu daɗi game da halayyar maza waɗanda take yiwa mafi yawa kallon masu son kai da zalunci. Domin a baya dukkansu abu ɗaya ta ɗauke su, mugaye. A hankali yanzu da ta fahimci rayuwa ta kuma gane yanayin zamantakewar wasu ma'auratan musamman a babban gida yasa ta ɗan sassauta, uwa uba ilimin addini da ya soma ratsa ta da kuma tarihin zamantakewar Annabawa da Sahabbai da matayensu a yasa ta gane jahilan cikin al'umma ko masu son kansu su ne da hali irin na azzalumai.
"Don Allah yar uwa ki ƙara watsar da lamarinsa. Kar ki ƙara kuskuren shan guba akan wanda bai san darajarki ba. Ki na da qualities ɗin da kowane ɗa namiji zai kaunace ki dominsa. Ni na tabbata ba ke ce da asara ba, shi ne ya rasa mace. In sha Allahu za ku samu wanda ya fi shi."
Zaituna ta jinjina kai tana murmushinta wanda har gefen kumatunta na lotsawa. Sannan ta miƙe tana amsawa da In sha Allah. Daga haka suka bar wurin.
A ɓangaren Zaid kuwa, ganin Zaituna ya sa shi fasa shiga ɓangaren Hajja, suna barin wurin ya juya ya shiga motarsa ya bar gidan zuciyarsa a cunkushe. Babu abin da yake ƙara tunanowa sai yanda abubuwa suka kacame a baya, yana da yaƙinin za'a yi masa dariya idan ya furta ga wani a gidan cewa yana kaunar Haulatu jikar Hajja. Zuciyarsa ta raya masa akan kawai ya nemi kaunarta, matuƙar tana sonsa to fa babu abin da zai hana aurensu. Balle ma yana ji babu wata ɗiya macen da za ta kalle shi ta ji ba ta sonsa. Ya san wannan ƙarya ne. Da wannan ya yanke cewa zai soma hira da Haulatun ta chat har ya samu ya shawo kanta ta so shi. Abu ne mai sauƙi a cewarsa.
***
Kano...
Mommy ta ruɗe yayinda hannuwanta suka shiga rawa tana mai zaro idanu lokaci guda ta dubi takardun da Ɗan Mutuwa ya sanya a hannunta sannan ta dube shi.
"Dagaske kake Alhaji? Gida fa? Gida suntum ka siyamin a gadon ƙaya? Allahu Akbar."
Ya yi ƴar dariya yana ɗan sunna kai kamar surukin gaske.
"Haba Mommy, ai wannan ba komai ba ne daga abin da na ci burin yi maki a rayuwa ke da Hindatu. Dagaske nake sonta kuma a ƙarshen satin nan zan turo idan kin min izni. Zan rungumi Hindatu da hannu bibbiyu ko don maraicinta."
Washe baki Mommy ta ke yi, sam ta kasa rufe baki, nan ta shiga zuba ruwan addu'a da godiya. A ranta tana ƙara jinjinawa Bokanta, dama ya ce mata babu wani abu da zai hana auren Alhaji Ibrahim da ɗiyarta. Kuma za su samu arziƙi fiye da tsammani. Aikuwa gashinan kafin ma ta kai ga batun turowar shi ya zo da maganar. Ɗan Mutuwa ya yi mata sallama bayan ya dire mata rafar dubu har guda biyu, ai Mommy ji ta yi kamar ta sume a nan don dadi. Ya kuma ce su shirya a gobe direba zai zo ya kai su ganin sabon gidan kafin su yi shirin tarewa. Ya ce ba shi da matsala ko a goben ma suka ga za su tare. Haka ya tafi ya bar Mommy cike da sumbatu.
Hindatu dake gefe ta kasa furta komai tsabar razana, wannan kyauta anya ba ta yi yawa ba? Sai da Mommy ta kai mata bugu a cinya gami da mata nuni akan ta tashi ta yi mishi rakiya kafin ta iya miƙewa jiki a sanyaye. Har ga Allah yanzu tana jin son Alhaji Ibrahim don ta kula ya iya tattalin mace amma kuma tana tsoron wannan hidimar da yake yi musu.
A zauren gidan suka haɗu da mijin ɗaya a cikin mata biyu dake haya a gidan, kamar ya yi me tsabar girmama Alhaji Ibrahim yana washe baki, ita dai Hindatu kallonsa take yi, ta san dalilin bai wuce saboda kyautar bajintar da ya yi musu ba kwanaki ƴan gidan ya gwangwaje kowane magidanci a cikinsu da kayan abinci. Alhaji Ibrahim kuwa ya amsa har da yi mishi kyautar dubu goma nan take. Ya karɓa ya na ta bin sa da addu'ar Allah ya ba shi Hajiya Hindatu. Don yanzu kaf ƴan gidan Hajiya suke kiranta. Ita dai jin su take yi.
Koda suka yi sallama ya tafi, ciki ta koma tana danna wayarta ganin Haulatu ba ta biyo bayan kiran da ta yi mata sai ta yi zaton ko wani abun ne ya hana ta. Mommy sai sumbatu take har da rawa, kasa bacci ma ta yi kwata-kwata a wannan ranar. Daga Hindatu ta fara bacci sai ta ji uwar ta taɓo ta wai ta tashi su soma haɗa tarkacensu wuri guda ita a goben ma zasu iya tarewa a cewar Mommyn.
***
Katsina...
Ana saura kwana uku bikin Raudha da Batulu ne Haulatu ta ciro sakamakon jarrabawarta na Waec a Cafe. Tun sadda ya shigo hannunta bakin nan ya ƙi rufuwa, babu wanda ba ta nunawa ba a saman Hajja. Ƙarshe kuma da rawar jiki ta wuce ɓangaren Baba Alhaji, duk da Umma ta ce ta bari sai bayan bikin sakamakon cikar da aka yi a gidan, baƙi daga Malumfashi har ma da mutanen Kano da Kaduna da dai sauran ƴan uwa na nesa duka sun zo amma ina, rawar jikin da ta ke yi kawai don ta nunawa Baba Alhaji wanda ya yi nata alƙawarin shiga jami'a muddin ta fito da sakamako mai kyau. Ba ta damu da jama'ar dake falon ba ta dai gaishe su a tsaitsaye sannan ta nufi ɓangaren Baba Alhaji. Da sallama ta shiga, ya amsa mata ba tare da ta kula da wadanda ke zaune a tare da shi ba tsabar murna baki ya ƙi rufuwa ta durƙusa gabansa ta miƙa masa result dinta.
"Baba Alhaji, ga result ɗina ya fito na Waec, kuma na ci Maths da English har da sauran topics na Arts dama ka ce idan na fito da sakamako mai kyau to zan tafi jami'a ko?"
Ya karɓa yana ƴar dariyar farin ciki irin nasu na manya.
"Masha Allah, Alhamdulillah. Sadauki maza karɓa ka karantomin idanun nawa ba ƙwari sai da gilashi."
Jin sunan da ya ambata ne ya sa ta saurin kallon gefen da yake miƙa takardar. Caraf suka haɗa idanu, yana sanye da riga baƙa da dogon wandon jeans. A gefensa kuwa wata fuska ce da ba ta san ta ba. Amma dai bai kai shekarun Sadaukin ba, kusan ma bai fi sa'an su Najeeb da Haidar ba ƴan ashirin da huɗu zuwa biyar.
Ta yi gyaran murya ta gaida shi. Ya amsa yana duban takardar. Ita kuwa ta kasa kunne ta ji ko zai yaba da ƙoƙarin da ta yi.
"Ta yi koƙari, amma a yanzu ba a gane ƙoƙarin mutum sai ya soma zuwa jami'a. Mafi akasari makarantun secondary, ana rubuce musu jarrabawar ne a allo. Hakane?"
Ya ƙarashe da duban Haulatu. Ta ji kunya ta kama ta karon farko, gaskiya ya fadi dama kam rubucewa aka yi ta kwafa duk da ta san da yawa cikin tambayoyin da aka yi musu. Ta ɗan turo baki kaɗan tana kallon Baba Alhaji.
"To ai ina da ƙoƙari kuma na san yawancin abin da aka tambaya."
Ya taɓe baki gami da ɗaga kafaɗa.
"Amma ba ƙarya na faɗi ba ko?"
Baba Alhaji ya yi dariya ganin yanda Haulatu ta yi narai-narai za ta yi kuka. Duk wannan murnar da ta shigo da ita ya gushe.
"Sadauki, ka rabu da Amaryata ka ga ka sanya min ita kuka ko? Yanzu dai tunda abin haka ne ma, na ɗora maka ragamar nema mata admission."
Wani ɗan murmushi Sadauki ya yi kafin ya shafi sumar kai ya dubi Haulatu da ita din ma ta kalle shi don jin me zai ce wannan karon.
"Ta yi Jamb ɗin ne? Sannan result din ya yi kyau?"
Haulatu ta ji ta tunzura kamar ta kai masa bugu don haushin rainin hankalin da ya ke mata. Ita kuwa ta yi Jamb, ba ta mancewa daƙyar ma Umma ta bari ta yi don a cewarta gwara ta yi aure a lokacin ta fita daga ƙangin rayuwar da suke ciki na gidan. Daƙyar ta yarda ta biyamata kuma sakamakon ya yi kyau ba laifi ta fito da maki har 177.
"Ah ta yi mana. Har nan ta zo ta nunamin. Ni nawa ma ki ka samu?" Faɗin Baba Alhaji.
Ta yi shiru don ta cika ta yi fam.
"Ba amsa?"
Ta ɗan dube shi, ya ɗan lumshe idanu ya buɗe yana mata murmushin da ya ƙara masa kyau.
"One sebin sebin."
Ta ba da amsa bayan ta kauda kai, aikuwa sai ga Sadauki na dariyar sebin sebin, wanda ke zaune a gefensa na taya shi. Ran Haulatu ya ɓaci ƙwarai, ta ma ture mamakin ganin Sadaukin na dariya sai na haushin dalilin da yasa suke mata dariyar kawai sai ta miƙe tana hawaye ta fice daga falon. Baba Alhaji na tsaida ta amma ina, tuni ta bar musu wuri.
Bugu Alhaji ya kai wa Sadauki da carbi sai ya dube shi yana ɗan dariya ciki-ciki.
"Na taɓa jikarka ko? Sorry."
Baba Alhaji ya mishi daƙuwa.
"Ungo nan. To ya ka ke so ta fadi? Kai ai mai cin gyaranta ne ba ku tsaya daga kai har Rufa'i kuna mata dariya ba."
Sadauki da har lokacin bai bar murmusawa ba, bai ce komai ba sai kallom takardar jarrabawar Haulatun.
***
Gimtse dariyarsu suke yi suna duban juna, Radiya da Safina a zaune gefe ɗaya a falon, gefe kuwa Anti Mabruka ce tare da wata baƙuwa daga Malumfashi suna hira, sai ko yara masu tsalle tsalle a gefe. Can dai duk kokarinsu sai da suka kwashe da dariyar labarin da Haulatu ta ba su. Cike da takaici ta miƙe za ta bar wurin suka yi saurin riƙo ta.
"Don Allah ki yi hakuri."
Ganin hawaye a fuskarta ya sa kuma jikinsu sanyi. Ta zauna gami da yin ƙwafa.
"Don kawai yana ganin ya je makarantar lilo shi ne zai tisa ni a gaba yana min dariyar kuskurena, kuma ku din da nake tunanin za ku fahimce ni shi ne ku ka wani biye masa ku na min dariyar ku ma."
"Mene ne makarantar lilo?"
Faɗin Safina don dagaske ba ta fahimta ba.
"Makarantar masu kudi mana. Ni ai na gwamnati babu lilo. Kuma sai mu je mu ƙaraci zama bai fi malamai uku ne za su shiga ajinmu ba. Mafi yawanci ma da Hausa ake koyar da mu, idan aka yi da turancin ma da yawa daga cikinmu ba sa ganewa. Ni kam daidai gwargwado aka yi wanda bai fi ƙarfina ba, ko ban iya bada amsar ba, ina gane me aka ce. Kuma na iya karantawa."
"Ki sha kuruminki. Idan dai English ne in sha Allahu za ki iya shi. Na yarda da ke. Watarana sai Yaya Sadauki ya sha mamakin yanda za ki turance shi. Akwai Antinmu ta makaranta, Malama Zuhra, lesson ta ke yi duk ran Asabar da Lahadi, dama ki yiwa Hajja magana a sanyaki wallahi, sosai ana gane koyarwar ta, ni na tabbata za ta maida hankali wajen ganin kin koya dakyau tunda tana son ƴan gidanmu sosai. Tana da kirki kuma."
Taɓe baki Haulatu ta yi. Ganin kamar ba ta son zancen ne sai suka sauya hirar har suka mantar da ita wancan.
***
Biki Buduri...
Ranar farko aka fara da wasan ƙwallo na nishaɗi tsakanin dangin Amarya da na Ango. Su Haulatu kaf sun je filin, Najeeb da su Haidar da abokanansu su ne suka wakilci dangin Amarya don dama sun sani koda wasa manyan yayyunsu ba zuwa za su yi ba. Haka aka yi abu cikin nishaɗi da raha inda dangin angon Raudha da na Batulu suka zama team guda amma duk da haka sai da dangin Amarya suka lashe wasan. Aikuwa murna wajen su ba a magana. An yi hotuna kafin kuma a watse.
A gajiye suka shigo sashin Hajja ita da Zaituna, Haulatu jiki na rawa ta ɗibi duk abin buƙatarta a leda don ita kam can ɓangaren Baban kowa za su kwana, gidan su Radiya. Su uku abin su sai ko wata ƴar uwar Maman Radiya da ta zo daga garinsu Daura ana kiranta Munira.
Ko'ina a gidan da mutane, wasu ƴanmata ne tsaye na hira yayinda wata na gefe da wani daga cikin ƴan uwa maza tana hira sai ko yara masu guje-guje kamar ba tara da mintoci na dare ba. Kungiyar su Najeeb kuwa suna can gefe ana buga musu akan ƙwallo da aka yi a ranar. Ita dai ba ta bi ta kan kowa ba ta cigaba da tafiyarta. Ta zo daidai ɓangaren Alh Ridwan inda sai ta gifta shi ne za ta ƙarasa na Baban Kowa, a lokacin Sadauki ke fitowa daga ƙofar gidan, ta dube shi ta da sauri ta kauda kai tunano abin da ya faru jiya. Shi kuwa tuni ya gane ta don haka ya kira sunanta. Yanayin kiran da