Showing 36001 words to 39000 words out of 177840 words

Chapter 13 - FITAR TSIRO COMPLETE HAUSA NOVEL BY RUFAIDA UMAR

11 Jul 2024

79144

Umman, su riƙe su hannu bibbiyu su koyawa zuƙatansu kaunarsu tunda a yanzun dai an zama ɗaya. Engr Faisal ne ya ce ya kamata ace taron har da Umma, amma uzurin rashin lafiyarta ya sanya aka bar zancen. Bayan an kammala Alhaji ya sallami yaran sai iyayen, nan ya kara yi musu nasiha da nunamusu kar su kusa su gwadawa yaransu ƙyamar abin da Allah ya kaddaro cikin rayuwarsu daga baya. A cewarsa muddin suka fa iyayen sun riƙi Umma da Haulatu hannu bibbiyu, su ma yaran dole su karɓe su. Suka amsa da toh su na masu biyayya ga Alhajin. Daga haka aka yi addu'a aka shafa.

***
BAYAN SATI BIYU...
BAYAN SATI BIYU...

Jikin Umma ya yi sauki ta warware tamkar ba ita ba. Kulawa sosai ta ke samu wurin Hajiya Babba da Haulatu. Zuwa lokacin tsegumi ya lafa, ƴan uwa masu zirga-zirga a gidan don son ganewa idanunsu Umma da Haulatu sun yi safa da marwarsu a gidan sun gaji domin Hajiya Babba ta hana kowa takurawa Umma sadda take fama da jinya. Asalima ba ta bari a shiga wurinsu, shakkarta da ake yi ya sanya kowa ya ja bakinsa.
  Dr Khaleefa kuwa, bayan zuwansa na farko sai da ya ƙara zuwa har biyu don tabbatar da samun sauƙinta. A duk zuwan da zai yi kallo ɗaya ke hada su da Haulatu take gane mamufarsa a dole ba don ta so ba take ficewa ta bar shi da Umman a dakin tana ƙunƙunin da bai isa ya ce ga abin da take faɗi ba.
   Gaba daya zama wuri daya ya ishi Haulatun, Umma dama tuni ta ɗan soma fita falon Hajiya Babba ta ɗan zauna, tun kwanciyarta rashin lafiya yanda ta ga Hajiya Babba ta sadaukar da lokacinta duk da jiki na girma da tsufa tana takowa ta zauna tana jinya duk kuwa da irin waƙe-waƙen habaici da kuma gwatsalewar da take sha daga Haulatu hakan bai sa ta fasa ba, dalilin keman da ya sa zuciyar Umma sanyi, ta ji kuma tausayin tsohuwar, ta saka a ranta kawai duk wani abu da ya faru a rayuwarta, nata ƙaddarar kenan. Haka kuma Allah ya tsara mata babu yanda ta iya ta kaucewa hakan. Da wannan ta kwaɓi Haulatu ta kuma bi ta da gargadi sosai akan koda wasa kar ta ƙara faɗawa Hajiya Babba baƙar magana, da ma dukkan wani abu da ta ke yi da zummar ɗaukar fansa ta haƙura ta watsar da makamanta.

"Ni ta haifa ta watsar, ni ta yiwa ba ke ba. To hatta ni ɗin da ta yiwa, ki sa a ranki na yafemata. Ya wuce a wurina, na kuma fidda shi a zuciyata, yanzu ta lafiyata nake yi, ke a matsayin na mai ƙaunata ai na yi zaton taya ni kula da lafiyata ya fiye maki duk wani rikici da ke ƙasan ranki a kan baiwar Allahn nan."

Wannan magana ta Umma yasa Haulatu ta ɗan yi sanyi amma ko kallon Hajiya Babba ba ta yi ballantana ta ci arziƙin gaisuwa. Hajiya Babbar ce ma ke son ganin Haulatun ta saki jiki ta dinga matsawa da son yi mata magana tana amsa mata daƙyar kamar an mata dole. Har auna su aka zo aka yi za'a yi musu dinkuna, Hajiya Babba har siyayyar mayuka da kayan amfanin ƴanmata masu kyau ta saka aka yiwa Haulatun, ta dai karɓa ganin idanun Umma yasa ta yi godiya. Yar budurwar da aka aika jikar Baba Dakta ce kuma sa'ar Haulatun da ake kiranta Safeena. Sosai take son ƙulla zumunta da Haulatun amma babu fuska, kusan ma ba ta bari ta fito falon.

Yau ma kamar koyaushe tana kwance a ɗaki tana latse-latse a wayar Umma, yayinda Umman ke falon Hajiya Babba su na hira. Wayar ta yi ƙara, ta duba dakyau, baƙuwar lamba ce, sai da ta ɗan yi tsai cike da tunanin wa zai kira Umma da baƙuwar lamba kafin ta danna ta kara a kunne ba tare da ta ce uffan ba don so take ta ji ko waye.

"Hello, Umma ina yini."

Jin muryar da ba ta yi zato ba yasa ta miƙewa zaune tana washe haƙora. Jimawar da suka yi ba a gaisa ba ya sa Haulatu ta nemi wancan fushin da take yi da Hindatun ta rasa shi.

"Toh ƴar guguwa, ba Umman ba ce, wai dama kina duniya?"

Daga can Hindatu ta yi wani ihu na farin ciki, suka kara sakin shewa da nanayensu. Rabon da Haulatu ta tsince ta cikin walwala har haka ba za ta iya tunawa ba.

"Kee shegiya, kina nan don wulakanci shi ne ba kya ko nema na a gaisa ko?"

Sai a sannan ma ta tuna da abinda ta riƙe Hindatun da shi a baya, ta dan taɓe baki.

"Bar maganar Malama. Ya kike to, ya amarcin? Ina Alhajin naki? Ba ku tafi shi honeymoon din da kike ta mafarkin zuwa ba?"

"Uhm, wane honeymoon ina shiga nayi tuntuɓe da ciki. Mts. Wallahi kin ga laulayi nake fama da shi mai ɗan karen wahala, kusan koyaushe muna hanyar asibiti."

"Lallai, ki ce abin nema ya samu, matar ɗan sanda ta haifi ɓarawo. Momi sai ta zuba ruwa a ƙasa ta sha."

Haulatu ta karashe tana wata dariya.

"Me kike so ki ce? Dama burinmu samun cikin ko me?"

Hindatu ta watsamata tambayar, kawai sai kuma ta waske.

"Aa, ina ruwan biri da gada? Ni wani abu nace? Yo wace uwar ce ba ta so ta ga jikanta na farko a duniya?"

"Uhm, ke kika sani dai. Wai kina ina ne? Kinsan fa rasa lambobi nayi tun sadda na yi Iphone, sai da muka hadu da Momi ne na dauki lambar Umma a wayarta."

"Au dama tana da lambar Umma?"

"Ji wani zance, to sau nawa nake kiranki a wayar Momin? Ni na yi mata saving. Wai yaushe za ki zo gidana? Kuma yanzu kina ina? An kama wadanda suka so sace ki? Me kika yi musu ma ne?"

Ita Haulatun dariya ma ta yi kafin ta ja guntun tsaki. Abu ne da ta bar shi a ranta da zummar duk wuya duk runtsi sai ta daukarwa mahaifiyarta fansa da ma ita kanta a wajen Ɗanmutuwa. Ba ta son tattauna zancensa da kowa, hakanan ba ta kaunar tattauna abin da ya shafe shi a yanzun.

  "Ina Katsina fa. Mun zo gidan family din Umma."

"Katsina? Dama kun san su? Amma ba ki taɓa ban labari ba."

"To ai komai yana da sila. Ma yi maganar dai. Zan kira ki."

Ba tare da ta jira amsar Hindatu ba ta katse kiran tana kallon Baba Saude wacce ta shigo dakin da sallama.

"Ƴar gidan Umma, ki zo tana kiranki."

Ta ɗan yi murmushi da fadin toh. Zuwa lokacin ta saki ranta da duk wanda ya nuna musu ƙauna idan ka cire Hajiya Babba. Ita kadai ta ke jin kamar ba za su yi sabo ba musamman da ta kula kamar ma ana shakkarta ne  a gidan.  Idan ta tsawatar ba musu suke bi, wannan ma na daga cikin dalilin da yasa ba ta zama falon, a ganinta iko da nuna gadarar Hajiyar ma ya yi yawa.

Sai da Baba Saude ta fita da minti kusan daya kafin ta mike ta fito kanta babu ko kallabi sai gashinta dake a tsefe babu kitso da ta tufke a ƙeya. Tana ɗan buɗe ƙofar ta hango Umma tare da matar da ganinta da ita kusan na uku kenan a gidan, Hajiya Zakiyya kenan wacce ta ji ana kira da Maama. A sashen mahaifinta, Baba Dakta ta ke zaman zawarcinta. Ita ke fuskantar ƙofar dakin hakan yasa dole Haulatu ta tura gaba daya ta fito. Umma ta bi ta da kallo ganin babu ko ɗankwali a kanta, Hajiya Babba na daga gefe ɗaya suna magana da Baba Saude, lokacin ƙarfe uku da mintoci na yamma.

Ta ƙarasa ba tare da ko ta kalli inda Hajiya Babba take ba, ta gaida Maama. Ta amsa fuska a sake gami da fadin.

"Zo nan ɗiyata, kya dinga zama ki ƙunshe kanki a ɗaka ke daya? Ai zaman shirun ba shi da dadi."

Haulatu ta ɗan murmusa kawai.

"Ato, ki yi mata faɗa ko za ta ji." Faɗin Umma kenan.

"Shirya maza ki yimin rakiya unguwa."

Jin haka Haulatu ta saki fuskarta sosai, ta dubi Umma da zummar ta ji amsar da zai fito bakinta, Umma ta gyaɗamata kai. Aikuwa da murnarta ta miƙe ta faɗa dakin.

"Kai Zakiyya amma kam kin kyauta. Ni na rasa irin wannan yarinya koyaushe tana ɗaki a ƙulle kuma na sani don ni take wannan shaƙiyancin. Toh ai kuwa dolenta ta sake da ni tunda dai na haifar mata uwa."

Aka yi dariyar maganar Hajiya Babba har Umma.

"Hakane Hajja, ai nima ba nisa zamu yi ba. Matar Khaleefa ce ba ta jin dadi kwana biyun nan shi ne zan leƙa mata. Jibi ne kawo lefen Raudha ko?"

Ta ƙarashe da tambayar Hajiya Babba.

"In sha Allahu. Ita Batulu sai sati na sama."

"Allah ya sanya alheri, ya sa zamu gani."

Aka amsa addu'ar Maama Zakiyya da amin.

Anan take ƙara yiwa Umma bayanin, ai Raudha diya ce ga Alhaji Ridwan, ita kuwa Batulu ɗiyar Barista Dawud ce. Gidan iyayensu duka na kusa da su ba tazara sosai. Umma ta dan murmusa.

"Ai na ga yaran, Hajja ta nunamin su da suka shigo kwanaki. Su ma iyayen mun gaisa. Allah ya nuna mana."

Aka ƙara amsawa da Amin. Daidai nan Haulatu ta fito cikin wata doguwar rigar abaya samfurin dubai. Blue black mai adon farin duwatsu, ta yafa mayafin a kanta, sosai ta yi kyau fatarta ta ƙara murjewa da kuma haske kai ka ce dama can ta saba da rayuwar jin dadin. Maama sai nazartarta take yi, tabbas yarinyar Allah ya mata baiwa na musamman. Nan gaba za ta gwara kan samari idan ta ƙara wayewa. Mutum ɗaya ta yi wa sha'awarta, ta sani kuma zai wahala ma ya kalle ta da sunan so da kauna. Ajiyar zuciya ta yi kafin ta miƙe tsaye.

"Masha Allah Haulatu kin fito tsaf. Muje kafin yamma ta ƙara yi."

Fadin Maama tana gyara zaman ƙaramin mayafin da ta ɗora saman doguwar riga ta yadi da aka yiwa ɗinkin bubu. Maama doguwa ce kuma kakkaura, ba ta da muni, baƙinta mai kyau ne. Idan ka gan ta ba za ka ce ta haifi yara samari har uku ba, koda alama jikinta bai nuna tsufa ba. A karon kanta ta ƙi bada dama ga maneman aurenta sai dai a ƴan kwanakin nan akwai wanda ya matsa har ya ja su Alhaji na maganar ta ba da dama ya fito ta yi aure. Ita kuwa a nata lissafin, ta rufe babin aure a rayuwarta.

Haulatu ta yi sallama da Umma, Hajiya Babba na a dawo lafiya, ganin idanun su Umma da Maama yasa ta amsa da Amin. Daga haka suka fice.

***
  Tafe suke a motar Maama tana tuƙi cike da nutsuwa har suka iso unguwar Modoji inda anan ne gidan Dr Khaleefa ya ke. Wani ƙerarren gida ne a cikin gidajen dake kan layin da suka shiga, nan ta ga Maama ta saka hancin motarta gami da yin hon. Maigadi yana ganin motar ya gane da sauri ya tura ƙaton ƙyauren gidan ta shiga.
Flat house ne mai ɗan karen kyau, wurin parking bai fi na motoci hudu ba. Anan Maama ta adana motarta ta fito tana mitar ta san wancan agogo sarkin aikin ba ya gida. Ita dai Haulatu tun a hanya ma da ta gane gidan wanda za su je ta ɗan tsuke fuska. Maama ta rasa inda za ta zaga da ita ganin gari a Katsina sai gidan Dr Khaleefa?

Haka ta bi bayanta tana tura baki kaɗan, mutumin da kullum cikin harararta yake yi, ya za su ƙare yanzu tunda ta tako ta zo inda ya ke rayuwa? Amma jin Maama ta ce da wuya idan yana gidan, ya sanya ta ɗan ji wasai. Yanzu burinta ma ta ga matarsa ta ga ya take? Ta san dai tana haƙuri da shi don daga ganinsa masifaffe ne kuma zai yi mugunta.
'Falon ƴan boko.' Faɗin Haulatu a ƙasan ranta bayan ta bi ko'ina da kallo. Babu tarkace sosai amma fa an zuba kaya masu kyau kalar fari da ruwan zaiba. Zama ta yi saman kujera mai fuskantar wani ɗan corridor inda ta fahimci a can ne ɗakunan matar gidan suke don hanyar da ta ga Maama ta nufa kenan. Dama ta ji ance auren gida Khaleefa ya yi da matarsa. Duk da dai ba zuri'arsu ɗaya ba amma ɗiyar abokin mahaifinsa ne, Barr Dawud. Sun zama tamkar yar uwa na jiki a irin zumuntar dake tsakaninsu da zuri'ar ma baki ɗaya. Taɓe baki ta yi kamar a lokacin ta ji Hajiya Babba na labartawa Umman. Ita a duniyarta ta rasa dalilin mutane masu ƙaƙabawa kansu son auren zumunci ita dai ba ya burgeta kuma ta ƙudurce a ranta koda a duniya za ta yi aure, ba ma za ta yi irinsa ba musamman a irin wannan gidan nasu da ta ga ba ya rabo da ƙananun magana.
Maama ce ta dawo ta zauna gefenta.

"Wash! Sannu Haulatu na bar ki ke ɗaya. Meyasa ba ki kunna tv ba? Ai da sai ki kunna ya ɗauke maki hankali. Kin ga ashe Hafsat na sauƙi ya samu sai fatan Allah ya raba lafiya."

Ɗan murmushi ta yi, ina ita ina ƙarfin hali a gidan mugun mutum irin Khaleefa? To a zancen Maama hakan na nufin ciki ne da Hafsat din? Kuma ai ta ji ance suna da ɗa guda daya, amma ba ta ga alamun wani a gidan bayan ƴar aiki ba. Ta dubi Maama, Kafin ta ce wani abu sai ga matar gidan ta taho, Haulatu ta kalle ta. Baƙa ce, irin baƙin nan mai sheƙi da kyau. Tana ɗan tsayi sai dai ba ta kai mijinta ba. Siririya ce, ba laifi daidai gwargwado tana da ɗan karan hancinta da ƙaramin baki wanda ya ƙawata fuskarta. Ga dukkan alamu ita din mace ce mai fara'a don har ta ƙaraso ta zauna fuskarta a sake take. Suka haɗa idanu da Haulatu ta sakarmata murmushi, ganin hakan yasa Haulatun ma maida mata martanin murmushin.

"Ina wuni. Ya jikin?"

"Lafiya kalau ƙanwarmu. Ya baƙunta? Koda dai yanzu kin zama ƴar gari ko?"

Ta yi dariya kawai ba ta ce uffan ba. Sai take mamaki, a hakan mace mai sakin fuska da komai, amma Maama a mota take cewa matar ba ta da hali, mijin haƙuri yake yi da ita? Nan da nan kawai ta saka a ranta shi ne ma mugun, shi yake zaluntarta. Dama mazan ai su ke cutar da matayensu a zamantakewa.

"Atine! Atine!!"

Ta shiga ƙwalawa ƴar aikinta kira. Da rawar jiki yarinyar da ba ta wuce shekaru goma sha uku zuwa huɗu ba ta fito daga wani ɗaki dake jikin falon tana mai durƙusawa a gefe.

"Naam Anti, gani."

"Kawo musu ruwa mana, ke komai sai an faɗamaki?"

"Aa ta bar shi ma, sallah kawai zamu yi mu kama hanya. Yamma ta yi ai. Haulatu da alwalarki ne ko za ki ɗauro?"

Haulatu ta gyaɗa kai. Hafsat ta nunamata bandaki da yatsa, ta mike ta shiga. Koda ta fito tuni har Maama ta tayar da sallah. Itama ta gyara zaman mayafin abayarta ta tayar.

Suna idarwa kuwa suka yiwa Hafsat sallama suka tafi tana ta godiya.

A hanya Haulatu ta kasa haƙuri ta dubi Maama.

"Maama, ni na ji kina cewa matar nan ba ta da hali, kuma sai na ga kamar ba haka ba. Dubi yanda ta karɓe mu da fara'arta da komai fa."

Hankalin Maama na kan titi, murmushi ta yi.

"Haulatu kenan, ki dinga ce mata Momin Annur, haka yan uwanki ke ce mata. Abu na biyu, ki sani, ba a saurin yankewa mutum hukunci a farkon haɗuwa da shi. Ki bari zama ya yi zama, ko kuwa wata mu'amalar ta haɗa ku, anan za ki gane waye ɗan adam. Hafsat tana da fara'a idan ta ga dama, da ace na bar ki a gidan ki kwanar mata biyu za ki gane halinta. Ba ta son kowa ya raɓe su ita da mijinta. Ba kuma ta yin aiki ko na kawar da tsinke a gidan, wannan dai ƴar yarinyar da kike gani Atine, ita ke shan wahalar aiki. Tana da dattijuwa mai zuwa yi musu girki ta tafi. Abin da ke baƙantawa Khaleefa rai kenan, mace a gidan mijinta, amma ba ta iya girki ba sai dai ƴar aiki ta dafa ta ba shi ya ci. Ga fita aiki da take yi tun safe sai yamma, aikin banki, rashin lafiya ce ta sa kika gan ta a gidan. Ba laifi muna shiri da ita tun farko, mai yiwuwa kuma ganin Khaleefa ɗan gidana ne ya sa itama tamu ta zo ɗaya. Duk shawara ta duniya kafin ya nufi mahaifiyarsa da ita, ni ya ke zuwa mu kashe mu binne ba tare da wani ko wata ya ji ba. Shiyasa za ki ji wasu lokutan ana ce masa Ɗan Maama."

Ta jinjina kai, ta kuwa ji sunan a bakin Baba Saude, duk sadda ta shigo da haka take kiransa idan zasu gaisa. Wayar Maama ce ta yi kara, ba tare da ta duba ba ta cewa Haulatu ta ɗaga ta ga waye. Ba musu ta ɗauki wayar daga gefen Maama ta duba sunan.

"Zaid."

Ta furta a fili. Da sauri Maama ta karɓi wayar har fara'arta na ninka na farko.

"Mutanen Abuja, jiyan nan nake samun shigowarku."

Ko me aka ce, ta yi dariya kafin su gaisa take fadin "Ina Amarya?"

Daga nan ko me aka ce. Ta amsa da fadin.

"Yes na fita ne, gidan Khaleefa na shiga duba jikin Hafsat."

Can kuma kamar magiya yake mata akan ta biyo yana son su yi magana mai muhimmanci ita kuwa fadi take ba za ta zo ba, ya tako gida ya same ta. A karshe dai Haulatu ta ji Maama ta amsa da toh ga ta nan zuwa. Daga haka suka yi sallama.

Madadin su yi gida Maama sai ta dauki wata hanyar ta daban, ta dubi Haulatu.

"Kifin rijiya, ke fa aka bar ki sai na kai ki na siyar ma ba ki sani ba ko?"

Dariya suka yi a tare, yau dai ita

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login