Showing 27001 words to 30000 words out of 177840 words

Chapter 10 - FITAR TSIRO COMPLETE HAUSA NOVEL BY RUFAIDA UMAR

11 Jul 2024

79126

fiye da sauran yayyunta maza. Yau dai ga babban sirrin da ba ta taɓa gigin sanar da shi ba. Bayan ita da wasu bayin Allah biyu da ta rayu da su a can wani gari, sai ko uban gayyar Saleh Mai Kalangu, babu wanda ya san da batun cikin Na'ima balle a san da wanzuwarta a doron ƙasa a dai nan garinsu Katsina.

Shiru ma magana ce inji Hausawa, tabbas shirun da Hajiya Babba ya tabbatarwa Dakta zarginsa.

"Innalillahi wa inna ilaihir raaji'un." Ya maimaita a karo na biyu. Wayarsa ya fiddo ya danna kira, yayansu babba da ya rage ya kira ya ce masa ga su nan zuwa da baƙi, magana ce mai muhimmanci.

Yana katsewa ya dubi Hajiya Babba, gaba daya idanunsa sun kaɗa.

"Ku muje can ɓangaren Alhaji a yi magana. Wannan ba ni zan yi hukunci ba."

Ya ƙarashe da jin ɗaci a maƙoshi. Daga haka ya sa kai ya fice daga falon bayan ya ba Maimuna umarnin ta yiwa su Umma jagora sashin Alhaji.

***
Babban falo ne mai dauke da ababen mora rayuwa daidai gwargwado. Tsaruwarsa ya shafe na sashin Hajiya Babba. Wani tsoho ne zaune saman dardumarsa ta ibada. A gefensa wasu matasa ne biyu wadanda duka ba su wuce shekara ashirin da takwas ko tara ba. Hira suke yi kafin wayar da Dakta ya yiwa Alhajin ta katse su. Ko bayan kammala wayar shiru suka yi baki daya domin da yawan lokuta Alhajin yana amsa waya ne ta hanyar sanya ta a handsfree. Wannan ya ba samarin damar jin abin da ya ce. Ɗaya a cikinsu wanda ya fi ɗan uwannasa jiki da kuma hasken fata ya miƙe.

"Bari na ƙarasa ofis kafin wancan Baturen ya kore ni."

Jin haka ɗayan ya yi dariya gami da faɗin.

"Kai Haidar, ka iya bakinka fa, ko ka mance a gaban amininsa ka ke? Wannan ɗan tsohon ko tusa aka yi sai ya fesa mishi."

Alhaji ya kai mishi duka da sandarsa dake ajiye a gefe. Aka yi dariya baki daya. Ya amsa.

"Ja'iri, kun fi kowa sanin ai Sadaukina daidai yake da ku. A hankali zai saita ku kowannenku ya shiga taitayinsa tunda na kula ku kam ba ku da aiki sai kashe-kashen kuɗi. Kai kuma mai kiransa da Bature kamar a kunnensa."

Wanda aka kira da Haidar ya kama kunne.

"Tuba nake tsoho mai ran ƙarfe, Ango kuma miji gurin Hajja Bilkisu mai gadon zinare. Allah ya ja da ranka, idan ka mutu kuma Allah ya haɗaka da ita a aljanna."

"Amin, amma mutuwa kam ba yau ko gobe ba da yardar Allah. Ɓacemin kafin ka kashemin jiki."

Matasan suka tuntsire da dariya karo na ba adadi. Kafin su kai ga tashi sai ga sallamar Dakta, wannan ya sa duka suka ɗan nutsu. Dakta da Hajiya Babba suna daga cikin kakannin da sam ba su sakin fuska yadda ya dace ga jika. Babu ma kamar Hajiya Babba wacce ake masifar shakka idan ta tubure ta hau faɗa da bala'i akan duk abin da aka yi bai yi daidai da ra'ayinta ba. Ita ce ƙaramarsu amma su na ji da ita sosai don suna yawan cewa ita ɗin amana ce ta iyayensu, kuma sun musu Allah ya isa idan har sanadinsu ta shiga wani yanayin. Wannan ya sa ba a komai suke tsawatar mata ba sai idan sun ga tura ta kai bango.

Samarin suka gaida Dakta cike da girmamawa. Kafin su maida duba ga wadanda ke shigowa falon. Duban junansu suka yi da tsantsar mamaki. Bayan sun zauna sai ga Hajiya Babba itama ta shigo.

Idanun Baba Dakta ya rufe bai ma nemi su Haidar su tashi ba ya korawa Alhaji komai da ya je ya tarar a sashin Hajiya Babba. Ya yi mishi nuni da Umma gami da ba ta umarnin ta tashi ta matso kusa.

Umma ta miƙe ba musu har jiri take ji tsabar damuwar da ke cinta ga wani zafi da take ji daga ƙirjinta sai kuwa kai dake sara mata lokaci guda. Har Umma ta ƙaraso ta durƙusa gaban Alhaji ta ƙara gaida shi bakinsa bai bar furta sunayen Allah ba. Alhaji ya dubi Dakta kafin ya maida kai ga Hajiya Babba wacce ke faman kuka na takaicin wannan ranar.

"Ya Allahu, Sule, ai wannan Asma'u ce zaune a gabana."

Dakta ya yi ƴar dariyar baƙin ciki.

"Ita ce Yaya, ɗiyarta ce ta cikinta. Ta ɓoye mana bamu da labarinta. Haka iyayenmu ba su san da wanzuwarta ba har ƙasa ta rufe idanunsu. Watakila ba don Allah ya yi zamu san gaskiya ba, da har ƙasa ta rufe namu idanun ba mu da masaniya a kanta."

Haidar dai sun yi mugun kaduwa da jin wannan labari, wayarsa da ta yi ƙara ce ta sanya Dakta ankara da su. Nan ya ce maza su fice. Suka miƙe don su dai kam sun gama jin kan labarin.

Suna fitowa Haidar ya dubi ɗan uwana Jabeer.

"Kai! Don Allah ɗan mintsile ni na ji ko dai mafarki nake?"

Jabeer da shima ya yi mutuwar tsaye don mamaki ya kuwa girgiza kai bakinsa a bude, can kuma ya yi wata ƴar ƙaramar ashariya ya ce.

"Kai! Yau akwai labari a gidan nan. Wai Allah, wa ya kamata na fara kira?"

Haidar ya yi wata dariya.

"Amma ashe tsohuwarnan ma ta buga duniya har haka take neman shigar mana hanci da ƙudundune? Kalli fa kamanni kamar ta yi kaki. Ai wallahi wannan ta fi kama da ita akan Anti Maryam. Kai! Akwai fa labari a gidannan! Ai mu shiga group kawai."

Suka yi dariya, dariya irin ta mamaki da kuma ganin bala'i da masifar da abu kaɗan Hajiya Babba ta jefa akan jikokinta da ma wasu a yaran ƴan uwannata, sai ga su nan sun bayyana a tattare da ita. Suna da yaƙinin cewa labarin nan zai girgiza wannan zuri'a ta su.

***
Hajiya Babba ta dubi Alhaji bayan ta gyara zama. Alhaji ya jefamata tambaya har sau kusan uku akan dagaske ɗiyarta ce amma ta kasa amsawa, sai a yanzun da ya haɗa da tsawa cikin muryarsa ta tsufa kafin ta yi yunƙuri na ba shi amsa. Haulatu kawai harararta take yi don a farkon ganin tsohuwar ta ji ta burgeta, sai dai a yanzu kam ji take yi babu wacce ta tsana sama da ita tun daga yadda ta nunamusu da farko.

"Eh, ɗiyata ce da na haifa tare da Saleh."

Ta ba da amsa kai tsaye, Umma ta sunkuyar da kai gami da lumshe idanu, hawaye kawai ke fita daga idanunta. Alhaji ya yi salati.

"Ɗiyarki ce dai kenan Asma'u. Garin ya ya haka ta faru? Kin ce mana guduwa kawai ki ka yi daga gida kuma kika dawo bayan zuciyarki ta yi sanyi. Kin nuna mana ke ba Saleh kika bi ba, Asma'u wannan maganar kuma daga ina ta ɓullo?"

Girgiza kai Hajiya Babba ta yi, wannan masifa da me ta yi kama? Meyasa asirinta bai tashi tonuwa ba sai bayan da tsufa ya zo mata? Kai, ita ta ma yi zaton tunda har labari ya risƙeta na mutuwar Saleh tun a baya, to ɗiyar itama ta mutu. Ashe dai dama akwai sauran rina a kaba? Ta sauke ajiyar zuciya ta ƙara duban Umma karo na barkatai sannan ta maida duba ga yayyunta.

"Ranar wanka haƙiƙa ba a ɓoyon cibi, saboda ita Na'ima, zan ba da labarin komai tun farko har zuwa lokacin da na dawo gida wajenku. Da kuma irin rufi na asiri da marigayi mijina Yusufa ya yimin sadda muka yi aure."

Gaba daya hankali sai ya koma kan Hajiya Babba har Umma.

***
Fitar tsiro
Page 15
"Bayan na kai minzalin da ya dace na shiga makaranta, a lokacin ne na tayar da hankalinsa kan lallai nima ina so na dinga zuwa makaranta tunda ina ji ina gani wani yaro ɗan wata a gidan da ake kira Farida Kulɓa yana zuwa. Yaro ne da ya girme ni da kadan a lokacin, kuma shi ya kasance shege, amma tana ji da shi kamar me. Ganin haka a dole Baba ya sanya ni, tare muke zuwa da yaron nan, Huzaifa. Mu sha zagi kala-kala a wurin ɗalibai har da wasu malaman da ke yawan kiranmu su na bugar cikinmu don jin ko bamu da wasu yan uwa ne muka yarda da zama hannun iyayenmu a gidan ƴan bariki? Wasu lokutan har kuka nake yi, a sannan shi Huzaifa yana firamare aji na hudu. Shi zai yi ta lallaɓa ni yana nunamin nayi hakuri ai tunda dai iyayenmu na son mu shikenan. Hatta makarantar islamiyya ina zuwa. Alokacin ne kuma Baba ya yi aure da wata ƙabila mai suna Iyabo. Ya maida ni hannunta, a gaban idanunsa ta nunamin kauna da so, a bayan idanunsa kuwa babu kalar azabar da ba ta yimin. Har wankin kaya take saka ni, tun ban iyaba saboda ƙarancin shekaru har na koya don dole. Iyabo sai ta hana ni abinci tun safe har sai na galabaita kafin ta ba ni. Ga shi nan idan Baba ba ya gida sai ta yi ta kawo mishi wasu mazan, idan sun tafi ta kama ni ta ja min kunnuwa tare da kashedi akan muddin na sake na faɗamasa sai ta kashe ni. Na kuma amince za ta aikata tunda har cokali ta taɓa sanyawa cikin garwashi ta manna min a cinya kawai don na Baba ya tambaye ni batun karatuna nace masa na fi sati ban je ba. Wasa-wasa Iyabo sai da ta kashemin karatu, tun Baba na maida hankali ga tambaya, na rasa dalili har shima ya yi watsi da maganar. Makarantar islamiyya kam shi ma tana bari naje ne a dole saboda ina yi mata cinikin cincin. A ƙarshe ma ta hana ni zuwa ta koma ɗoramin tallah. Shi Baba idan ya kaɗa harkar barikinsa sai ya kwashe sati biyu ma bamu sanya shi a idanu ba. Haka har na kai shekaru goma sha uku a duniya cikin wahala da ƙuncin rayuwa. Ance ba'a sabo da wahala ba don haka ba sai ince na saba da wahalar Iyabo. Idan zan mutu ina rashin lafiya kallo ban ishe ta ba. Duk tsananin ruwa idan Iyabo ba ta so ba, ban isa na shigar mata ɗaki ba sai dai na kwana a waje. Idan naji ruwan ya yi ƙarfi ne nake komawa zauren gidan kusa da tumakanta na keɓe. Babu zato ba tsammani, watarana da daddare ana muku-mukun sanyi, ina zaure na ƙudundune sakamakon Iyabo ta yi wani baƙon watsewarta suna ɗakin. Ta kuma rantse ko kwakkwarar motsina ta ji sai ta fito ta yankamin wuya. Wannan ta sanya tari kwakkwara ma na kasa yi. Ba zato Baba ya bude gidan da mukullinsa ya shigo. Haske ni ya yi sosai da tocila yana tambayar.

"Wace a nan? Na'imatu! Me kike yi anan cikin wannan uban sanyin? Maza tashi."

Ya ƙarashe zancen nasa yana mai sa hannu ya kama nawa hannun da sanyi ya kama tamkar an jefa cikin ƙanƙara, haƙorana kuwa kar-kar kawai suke yi suna gugar da juna. Sam Iyabo ba su ji motsi ba, ya ga na tsaya ƙyam na ƙi yarda mu shiga koda falonta ne, kafin ya kai ga yimin magana ya ji muryar wani namijin ba shiri ya saki hannuna ya faɗa ɗakin. Can ba jimawa mutumin ya fito a guje har ya a tunkuɗeni ina zubewa a ƙasa. Ba jimawa kuma na ji ihun kukan Iyabo na tashi, Baba na jibgarta. Haka har ya fito da ita waje, runtse idanuna nayi ganin babu ko kaya a jikinta, a kan kunnuwana ya yi mata saki ya kuma dura mata ashar kala-kala.
Da wannan aurensu ya ƙare, zamana ya ƙara komawa gidan ƴan bariki. Rayuwar a sannan ta zama mafi hatsari gareni fiye da baya saboda maza da dama na kawomin hari amma Allah yana tsallakar da ni. Fir na ƙi makaranta saboda habaici da zagi da ɗalibai ke yimin. Wasu na kira na ƴar iska wasu kuwa shegiya kai tsaye.
Da na ƙara shekaru na ƙara yin hankali na shiga damuwa sosai, rayuwar gidan ta ficemin a kaina. Kullum cikin takurawa Baba nake yi kan ya kai ni ga Mamana ko yaya take zan zauna da ita. Da dai ya ga abin ya ishe shi ya zaunar da ni ya cemin ai ta tsane ni ba ta sona. Ya kuma ce koda na je wajenta ba za ta taɓa kallona ba. Hakan ya ƙara sanya mini tsanarta cikin raina. Ban ƙara tada maganarsa ba. Ina da shekaru sha shida ne aka soma kawomin hari fiye da baya. Cikinsu har da Ibrahim Ɗanmutuwa, mahaifin Haulatu. Su na cikin samari masu ji da kai da kuma gayu da kudaden da suke burge yanmatansu na bariki. Ba su da aiki sai caca, Babana na daga cikin masu zama a gefe suna waasa su, su kuwa hakan yana ƙara fasamusu kai. A duniyar ƴan caca babu wanda Babana ke so da yawan kurantawa kamar Ɗanmutuwa. Koda dai an masa shaidar cewa babu wata caca da za'a buga tare da shi bai ci ba. A lissafe ma bai fi sau biyu rak! Aka taɓa nasara a kansa ba.
Sanadiyyar wani wawan cin ganima da Ɗanmutuwa ya yi a wurin wasan su na caca, shi ya ja Baba yi masa alƙawarin aura masa ni. Wannan magana ta fi komai yiwa Ɗanmutuwa daɗi, a duniyarsa dama ya ɗauke ni kamar wata abar wasansa, abin nufi, tun sadda abokansa suka hau cin alwashin aurena, wasu kuwa na su bai wuce samun galaba a kaina ba, shi ma ya dauki nasa alwashin sai dai wayo da dabara bai sa ya furta musu ba. Lokacin da suke daukar alwashi a kaina, ina daga zaure ina jinsu, ban mance ba ma fita nayi zuwa kanti siyo sukari, a hanyar dawowa suka fara zancena, koda na karasa shigewa gida sai da na dakata na ji inda zancen nasu ya tsaya don ina tsoron su ƙulla wani abun da za su cutar da ni ba tare da na sani ba.

Maganar aurena da Ɗanmutuwa ba ƙaramin tayar da hankalina ya yi ba. Duk irin roƙo da koke-koken da na yi bai sauya komai daga ɓangaren Baba ba. Kai kusan ma dai kyauta aka ba shi ni, don duka-duka kudin sadaki kawai ya bayar aka ɗaura aurenmu a wani masallaci. Baba shi ya zama waliyinsa. A cewar Baba, Ɗanmutuwa asalinsa shima Bakatsine ne, amma iyayensa sun mutu. Danginsa kuwa ba su damu da rayuwarsa ba shi ne dalilin shigowarsa Kano neman kudi. Ni dai ba ni da ta cewa. Babu abin da kuma ya kaɗamin ƴaƴan hanji sai ganin tun ranar farko da aka kai ni, na so na yi gardama ya zanemin jiki tas ya yi kuma abin da ya ga dama da ni. Wannan ya haifarmin da mugun shakkarsa, ga shan kayan maye. Haka na rayu da shi cikin ƙunci da rashin galihu, ciki kuwa da na samu yake ba ni magani ya zube. A cewarsa sam, bai kai shekarun tara iyali ba. Ban mancewa har mata yake kawomin cikin gida, ranar da ya fara na nunamasa fushina ya kama ni ya jibga ya kuma ƙulle a ɗaki tun dare bai buɗe ni ba dai washegari da rana. Alokacin na galabaita babu ci babu sha balle a yi batun sallah. Kai tsaye ruwan wanka ya sanya na ɗora musu, a dole jikina har rawa yake yi na kunna risho na dora, ga jiri da nake sakamakon yunwa.
Babban takaicina bai wuce yadda Baba bai taɓa takowa don duba lafiyata ba kamar dama shi ɗin ma ya gaji da ni neman hanyar rabuwa kawai yake yi da ɗawainiyata. Sai da na shafe shekara ban sa Baba a idanu ba, ko na tambayi Ɗanmutuwa cemin yake yi yana bariki. Wannan amsar ba ta yimin dadi sam, hakan ya sa na ja bakina na yi shiru ban ƙara maganar ba.
Ɗanmutuwa bai fasa zubarmin da ciki ba, sai a kan Haulatu ne Allah ya yi ikonsa domin jan bakina nayi na yi shiru ban faɗi ba. Kuma sai Allah ya taimake ni cikin har ya shiga watanni bakwai hankalinsa bai kai gareni ba, kusan ma ya fi maida hankali da harkokin gabansa. Sadda ya farka da cikin kuwa, ranar na sha baƙar azaba kai ka ce kashe ni zai yi. Cikin wannan halin baƙin cikin na haifi Haulatu, makwafciyata ce ta taimakamin da zuwa asibiti da komai. Wannan taimako da na samu shi ya jawo muka tashi daga unguwar muka koma wata, acewarsa makwaftan sun masa shishshigi kuma har suna ikrarin haɗa shi da hukuma kan ya bar ni a gida ina naƙuda tsawon sati bai ko damu ba. Su ne suka siyamin kayayyakin amfani na jariri da ma nawa. Sosai ya ji haushinsu.
Fitar tsiro
Page 16
Haulatu na da wata biyu a duniya, Ɗanmutuwa yace na shirya zamu yi ƴar tafiya. Nidai ban san dalilin da yasa na dinga ji gabana na faɗuwa ba, tasha muka nufa muka shiga motar Kaduna. Wani gida ya kai ni bai ko damu da ya shiga ba sai ma cikin hali na ko'in kula ya sanar da ni wai Baba ne a ciki ba shi da lafiya, na zauna zuwa gobe zai shigo mu tafi gida. Jin haka hankali tashe na faɗa ciki da sallama. Ɗan ƙaramin gida mai ɗakuna falle biyu sai banɗaki. Baba na kwance saman ƴar katifa cikin hali na ciwo, sallamar da na yi ce ta fito da wata mace daga wani ɗaki. Itama dai babu alamar cikakken lafiyar tattare da ita. Tana tambayar ko wace ce ni sai dai na kasa ba ta amsa har na ƙarasa makwancin Baba na tabbatar shi ɗin ne, shima kuma ni ya ƙurawa idanu can cikin rawar murya ya kira sunana. Na ƙarasa na zauna kawai sai na fashe da kuka. Anan yake bani labari ai tun bayan aurena babu jimawa ya auri matar da na gani mai suna Falmata. Sai dai babu jimawa ya kamu da cuta mai wuyar magani amma a sannan ya ma ƙi faɗin sunan cutar. Ya cemin koyaushe ina ransa, ya ba da saƙo sau ba adadi ga Ɗanmutuwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login