Showing 153001 words to 156000 words out of 177840 words

Chapter 52 - FITAR TSIRO COMPLETE HAUSA NOVEL BY RUFAIDA UMAR

11 Jul 2024

79170

tashi fadi yake.

"Cikinta fa? Yana nan ko ya fita?"

Sai da Mansur ya ɗan yi shiru, bai wuce don mamakin yanda bai tambayi lafiyar matar ba sai na cikin da take ɗauke da shi.

"Komai lafiya."

Wata doguwar ajiyar zuciya Ɗan Mutuwa ya yi yana mai dafe motar jin kamar zai kife.

"To shikenan, gani nan zuwa yanzu."

Daga haka ya shiga motar ya ba da umarnin su nufi asibitin. Kasancewar asibitin ba ɓoyayyen asibiti ba ne, ya sa bai bace musu ba.

Mansur wanda shi ya taimaka wurin kawo Hindatu asibiti, ya tarbe su. Bayan sun gaisa ya musu jagora har dakin da take, Duna ya tsaya a kofa tare da shi, Dan Mutuwa kuwa ya shiga  dakin. Jin an taɓa ƙofar ne ya sa likitan dake tsaye yana tambayar Hindatu ko akwai inda ke mata ciwo ya waigo, nos da Hindatu duk suka dubi wanda ya shigo. Hawaye ne ya zubowa Hindatu a fuska, ga farin cikin rabuwa da cikin dake jikinta, ga kuma na takaicin kanta na auren mijin aminiyarta ba tare da ta sani ba. Kuma na rashin dace a samun mijin ƙwarai. Ta sani wannan duka har da laifin Mominta.

Shi kuwa Ɗan Mutuwa bayan sun yi musabaha da likitan yake sanar da shi mijinta ne. Nan ya buƙaci su je ofishinsa su yi magana. Ɗan Mutuwa ya dubi Hindatu ya dan shafi gefen fuskarta.

"Sannu kin ji? Allah ya baki lafiya." Ta kauda kai gefe ɗaya zuciyarta na tuƙuki don ji ta yi kamar ya ɗoramata garwashin wuta.

Daga haka ya juya ya fita.

A ofishin Likitan ne ya ji abin da ya kusan zautar da shi, wato na ɓarin cikin Hindatun. Ya miƙe ya hau faɗan wai makirci ne ya sa likitan zubar da cikin matarsa kuma ya rantse sai ya yi shari'a da shi. A karshe ya fita yana sababi kamar zautacce har da cire hula ya yi wurgi da ita. Ɗakinnda Hindatun take ya koma wannan karon da ƙarfi ya bugi ƙofar ta buɗe. Ya yi tsaye yana huci a kanta, ita kuwa kallonsa kawai take yi, kallo na tsana.

"Ba ki isa ba Hindatu! Ni za ki kawowa iskanci da rainin wayo? Ni za ki nunawa bariki! Toh ni Ɗan Mutuwa ni ne barikin da kansa! A cikinta aka haife ni! Kin cuce ni kin zubarmin da burina da mafarkina! Allah ya isa tsakanina da ke!"


Daga haka ya kada kai a gigice ya fice daga asibitin har da haɗawa da gudu-gudu. Duna ya bi bayansa da sauri shi ma yana mamakin abin da ya hargitsa uban gidan nasa har haka.

Tun komawarsa gida ya kasa zama balle sukuni, meeting din da bai samu zuwa kenan ba, babban burinsa dare ya ratsa gari ya yi duhu ya samu zuwa ga mai sharemasa kuka, wato Uban Dodo. Shi ya sani ya ɗebo ruwan dafa kansa. Sai ga hawaye suna fita a idanun Ɗan Mutuwa na jin raɗaɗi da takaicin wannan asara da Hindatu ta jawo masa a rayuwa. Dare na kara nisa ya fice zuwa ga Uban Dodo inda suka haɗu baki daya ƴan ƙungiyar saboda taron gaggawa da ya tashi na hukunta Ɗan Mutuwa akan asarar da ya jawo wa ƙungiya na rashin ɗaya daga cikin ƴaƴanta.

Wannan kenan.

***
Kano...

"A yau rana ta Alhamis ne, sha biyu ga watan Junairu, jami'an tsaro suka cafke wata jamshaƙiyar mace mai suna Hajiya Adama Loma, wacce ta kwashi tsawon shekaru tana harkar safarar yara da miyagun ƙwayoyi, wanda a ƙarshe ƙungiyar nan mai yaƙi da safarar mata da yara wato Naptip ta yi nasarar kuɓutar da ƴanmata masu ƙananun shekaru sha biyar zuwa ashirin da ake ƙoƙarin fitar da su ta ɓarauniyar hanya ta Nijar. Ɗaya daga cikin yaran tana kuka ta shaidawa manema labarai cewa ita ƙanin babanta ne ya kawo ta har gidan Hajiyar inda suka yi cinikinta kamar wata dabba, aka cika masa lalitarsa ya yi gaba ya bar ta. Wata kuwa, cewa ta yi dama da niyyar karuwanci ta fito daga gidansu, a cewarta iyayenta ne suka hana ta saurayin da ta ke so."

Girgiza kai kawai Hindatu ke yi tana salati, tana daga ɗaki amma duk wannan labaran da ake watsawa a rediyon da makwafciyarsu ta kunna babu ɗaya da bai shiga kunnuwanta ba. Tabbas ta san wace ce Hajiya Adama Loma, ta kuma sha ganinta ta hanyar tsohon mijinta Ɗan Mutuwa. Godiya ta ƙara yiwa Allah da ya kuɓutar da ita daga cikinsu ba tare da sun yi nasarar gurɓata rayuwarta ba. Har aka ƙare labaran ba ta ji an sako muryar Hajiya Adama ba don a cewar ɗan jaridar ta ƙi yarda a yi hira da ita. Shigowar makwafciyar tasu ce da zummar yi mata wanka irin na jego ya katse tunaninta. Sunanta Asabe amma mace ce mai kirki kuma ba wata babba ce ba sosai. Tun zuwan Hindatu gidan ita ke ɗawainiyar kula da ita hatta abinci idan ta dafa sai ta zubamata. Momi har lokacin ba su dawo ba, ta kuma ji dukkan abin da ya faru amma sam ta nunawa Hindatun ba ta yarda ba sharri ne ta ke wa Ɗan Mutuwa don kawai tana so ta rabu da shi. Don ɓacin rai ma ba ta ƙara bari sun yi magana ba ko Momin ta mata a whatsapp ba ta amsawa. Babban burinta jikinta ya ƙara kyau ta tafi wajen mahaifinta.

***
Su uku ke tsaye a falon, Maada, Ɗan Aljan da Duuna, kowannensu na busa karan sigari, Ɗan Mutuwa sun kai shi asibiti sun ajiye, Maada ya yi amfani da akwatin kuɗin da Ɗan Mutuwan ke yawo da shi a mota ya biya kudin gado da na magunguna daga haka suka fito a cewarsu za su je su dawo.

"Ni fa kawai mu kwashe abin da za mu kwasa mu samfe kawai. Wannan garan ba tashi zai yi ba, idan ma ya tashi ba wani abun arziƙi za mu yaga a jikinsa ba. Ko ya kuka gani?"

Ɗan Aljan ke wannan kalamin yana dubansu. Wata dariya Duuna ya yi.

"Daɗina da kai akwai ja sosai. Kamar ka san tunanin da nake yi kenan. Ya dace mu yiwa kanmu gyaɗar dogo mu kwashi ganima mu yanka gabas."

Maada dake sauraronsu ya yi murmushi. Dama tunaninsa kenan sai aka yi sa'a nasa da abokansa ya zo ɗaya. Nan suka tsaida shawarar farawa da korar ma'aikatan sannan su yiwa gidan kankat a cikin daren nan su fice da komai su siyar. Da wannan kuwa suka yi nasarar sallamar duka ma'aikatan da cewa umarnin Maigidan ne. Su dai babu abin da ya sha musu kai tunda an musu kyakkyawar sallama don sif guda cike yake da kudade a dakin Ɗan Mutuwa.
A wannan daren suka nemo babbar motar da ta yi musu lodin kaya, babu wani abu da suka bari kama daga kayayyakin sanyawa har kayan furnitures da sauran tarkace. Hindatu dama tun sadda za ta bar gidan ta kwashe komai nata mai muhimmanci don ta saka a rai cewa ta gama aure a gidan, lefenta ba ta ɗauki ko tsinke a ciki ba, haka suka kwashe dukkan komai suna jin dadin wannan arziƙi da suka yi a dare guda. Takardun gidan suka nema ba su samu ba, ko kuma ace sun gani amma ba su san shi ne ba, tunda cikinsu kaf babu mai ilimin bokon balle ya karanta, dama-dama ma Ɗan Aljan, shi har sakandire ya fara zuwa kafin shaye-shaye da bin ɓata garin abokai ya lalata masa rayuwa.

Motar har ta yiwa kayan kaɗan don dma farfajiyar gidan suka shigo da ita, daga nan suka yanke cewa Ɗan Aljan da direban su soma yin gaba su kai ma'adana su ɓoye waɗannan ɗin sannan su dawo a kwashe sauran. Da haka suka fice aka bar Maada da Duuna na zaman jira. Sai dai kuma har asubahi ta kawo kai babu su babu labarinsu. Wayar Ɗan Aljan ma a kashe, hankalinsu ya tashi. Duuna ya ƙunduma ashariya ya bugi katakon kujera.

"Kada dai ace wannan saunan yaudararmu ya yi ya gudu?"

Maada dake aikin cigaba da dannawa Ɗan Aljan ɗin kira ya koma ga direban, amma ina kowannensu wayar a kashe. Nan da nan suka ƙulle ƙaton ƙyauren gidan suka mara musu baya a ɗaya daga cikin motocin Ɗan Mutuwa, dama tuni sun yi cinikin sauran biyar ɗin tun da haske a gari suka fice da su ɗaya bayan ɗaya, kudaden aka zuba a asusun Maada tunda shi ne Ogansu. Ma'ajiyarsu babu Ɗan Aljan ba dalilinsa. Suka koma har inda direban ke parking ɗin ƙurƙurarsa. Nan ma aka ce ai yana asibiti, can aka tsince shi a gefen titi jikinsa duk sara. Suka kuwa iske shi yana kuka yake roƙon su masa aikin gafara Ɗan Aljan ne ya ce ya yi parking daga nan ya nemi ya fita a motar, gardamar da ya yi ce ta sanya ya sassare shi a jiki. Wannan maganar sam ba ta yi musu dadi ba. Haka suka fice kowannensu na cin alwashin irin kisan da zai yiwa Ɗan Aljan tunda har ya ci amanarsu. Nan da nan suka dinga kiran duka abokan dabarsu da suka sani a wuri-wuri kan cewa duk wanda ya ci karo da Ɗan Aljan ya shaida musu. Daga nan suka koma gidan Ɗan Mutuwa don jira dare ya yi su kwashe abin da ya rage. Sai dai a wannan ranar jami'an tsaro na yaƙi da miyagun ƙwayoyi suka mamaye gidan don kama Ɗan Mutuwa wanda Hajiya Adama ta ce bakinsu ɗaya tare suke aikata dukkan munanan ayyuka. Maada da Duuna ba su tsira ba, haka aka kwashe su, babban jami'in cikinsu da wasu yaran suka nufi asibitin da su Maada suka ce Ɗan Mutuwa na can yana jinya.

***
Katsina...

A wannan daren dai duk yanda Sadauki ya so ganin Haulatu hakan bai samu ba dalilin neman da Daddy ke masa akan zancen lefe da ma shirin biki wanda daƙyar suka roƙi Baba Dakta ya amince ya maida nan da wata biyu, sati takwas kenan. Koda ya fito dare ya riga ya yi don haka kawai sai waya suka ɗan yi ba wata doguwa ba suka yi sallama.

A gefen su Hajja kuwa jin biki wata biyu ya sa ta shiga hada-hadar gyara Haulatu hakan ya sanya ta neman layin Maama, bayan sun gaisa ta ke shaida mata batun auren. Maama ta yi dariya.

"Na ji labarin komai Hajja, ai Alhamdulillah sai fatan kawai Allah ya nunamana."

Hajja ta washe haƙora.

"Amin amin Zakiyya. Sai ki tasarwa shirya ɗiyartaki."

Dariya karo na biyu Maama ta yi.

"Ah wannan kam ai dolena ne. Zan yiwa Ummu Deedat waya, duk radda take da lokaci zan ce ta leƙo gidana, idan mun kammala magana sai na yi magana da Haulatun. Amma fa aronta za ki bani Hajja na ƴan satika."

"Ai ko na wata ne Zakiyya ba ki da matsala idan jikata za ta fito ras da biki."

Suka yi dariya da yiwa juna fatan ganin lokacin sannan suka yi sallama.

***
Barr Dawud ne zaune a chamber ɗinsu na lauyoyi, bai jima da fitowa a kotu ba inda ya kare wani maraya da ake zargin shi ya kashe iyayensa ƙarshe gaskiya ta bayyana cewa Yayan mahaifinnasa ne ya kashe shi. Yau aka yanke hukuncin shari'ar aka kama masu laifi. Zuciyarsa cike da farin ciki na wannan nasara amma damuwar da ya shiga a ɓangare guda ya hana shi bayyana wannan murna gaba daya. Ya gama fahimtar kansa a kwanakin nan, shi ba yaro ba balle ace ya kasa gane kauna ce da soyayya ta aure ya ke yiwa Na'imatun Hajja. Kamalarta, haƙurinta kai har ma da kyawun halittar da Allah ya yi mata, su ne suka haifar da wannan son nata da yake ji. Ba ya jin kuma zai yi shiru, zai gwada sa'arsa tunda su ɗin ba yara bane. Zai yi dai ƙoƙari ya danne zuwa sa'in da bikin ɗiyarta zai kammala. A yau dai ba ya jin zai iya komawa gidansa ba tare da ya je ya ga koda fuskarta ba don haka kamar wanda aka tsikara ya miƙe ya haɗa ƴar jakarsa. Koda ya fito, yaronsa ya zo da sauri ya karɓi jakar zuwa mota. Shi kuwa ya ƙara yin sallama da abokan aikinsa suna ƙara taya shi murnar wannan nasara da ya yi a yau ɗin.

A gidan kamar yanda ya tsammata, hakan ce ta faru. Rikici irin na Rahma har bai san yaushe zai ƙare ba. Zaune ya iske ta a falonsa sai cin magani take tana kumburi, bai ce mata uffan ba ganin ko sallamar da ya yi ba ta amsa ba kai tsaye ya shige ɗakinsa. Sai da ya fara rage kaya ya yi wanka ya fito ya tarar ta shigo tayi zaune bakin gado tana girgiza ƙafafu. Kallo ɗaya ya bi ta da shi ya nufi sif ya fiddo jallabiya.

"Wai Dawud ba za ka cemin komai ba kake nufi?"

Ransa na ɗaci amma bai yi magana ba, daidai da miskilancin nan, Khaleefa ya ɗauka a wurin Baban.

"Wallahi Dawud ba na son wulakancin da ka ke yimin, kuma ka bayar da fuska yan uwanka ke neman tozarta ni, suna nema su kashe min yarinya su jefa ni cikin tashin hankali da masifu!"

Sai a sannan ya dube ta.

"Fitarmin a ɗaki Rahma tun ba ki kai ga ɓatan rai ba."

Mamin Khaleefa ta shaƙa iyaka, sai kawai ta shiga kuka.

"Eh dama haka za ka ce Dawud, wai ni yarinyar nan ba jininka ba ce ne? Kana ji kana gani rayuwarta na nema ta salwanta amma ka zuba ido ba ka ce komai ba? Shi Sadaukin ba mijin mace huɗu ba ne? Don me za ka kasa roƙon alfarma akan ya aure ta su zauna tare da matar so ɗin tasa?"

Duk yanda ya kai da ɓacin ran sai da ya ɗan ji babu dadi, a duniyar idan da abin da ya tsana bai wuce ya ga mace na kuka ba don haka ya kama hannunta suka zauna gefen gado.

"Share hawayen, ya isa hakanan, nutsu ki saurare ni dakyau."

Ba musu ta bi umarninsa, ita yanzu ai babu abin da ba za ta iya aikatawa ba muddin ɗiyarta za ta samu abin da take so. Akan farin cikin yaranta za ta iya koma mene ne.

"Rahma, shi auren nan da kike ganinsa, nufin Allah ne. Wannan koke-koke da kwanciya ciwo da Jannat ke yi, ba shi zai sa ta auri Abeed ba. Na kira ta na mata faɗa, kenan duk abin da nace mata ta bayan kunnenta ya bi? Ta sanya ƙafafunta ta shure? Ai babu abin da za ka same shi ta ƙarfi, da ace namiji ne ma ke son, ana iya cewa ƙila a gaba zai iya siye zuciyar matar ta haƙura su rayu tare. Amma fa ni ba zan kai Jannat inda ba'a sonta ba duk da cewa ina yiwa yaron kyakkyawan zato ba zai bari ya cuci ƴarmu ba, sai.."

"Sai me? Me kuma ya yi saura da ba ki faɗi ba Dawud? Fito a mutum kawai ka ce ba za ka iya samarwa ƴarka cikar burinta ba. Shikenan, muje a hakan, ni kuma yanzu na fara faɗi tashi akan yarana!"

Tana kai wa nan ta fice fuu kamar za ta tashi sama.

***
Ta ɗaga hannu ta wanke fuskar ɗan nata da lafiyayyen mari. Fuskarta kaca-kaca da ruwan hawaye ta nuna Zaid da yatsa.

"Kai ashe marar hankali da tunani ne ban sani ba? Zaidu akan mace za ka dubi tsakar idanun iyayena ka ci musu mutunci?! Da wane idanun zan dubi Baba Alhaji?"

Kawai sai ta saka salati ta koma mazauninta tana fitar da ƙwalla. Zaid wanda ke daga tsaye don shigowarsa ko zama bai yi ba ya yi karo da tsarabar mari daga Malama. Ya durƙusa jikinsa a matuƙar sanyaye ganin irin hawayen da mahaifiyarsa ke fitarwa a kansa, Bebi autarta dake gefe kuka kawai take yi ganin haka Juwairiyya ta ja hannunta zuwa ɗaki.

"Ki yi haku..."

"Haƙuri na me? Me ka yi min? Rayuwar da ka zaɓarwa kanka kenan akan soyayyar mace, ka yi duk yanda ka so Zaidu. Amma ina maka rantsuwa ko bayan raina ka auri Haulatu ban yafe maka ba! Shashasha marar tawakkali. Iliminka ya tashi a banza kenan! Ai alhaki kwuikwuiyo ne, da ace ba ka da saurin mantuwa, da ka tuna alhakin Zaituna ke cinka a yanzu. Kuma a gobe ka tattara ka koma Abuja. Ban yafe maka ba idan koda wasa ka cutar da Matarka."

Tana kaiwa nan ta miƙe a fusace da zummar wucewa ɗaki sai dai ba ta ko yi taku biyar ba ta zube a wajen. A gigice ya kira sunanta.

"Umma!" Kafin ya yi wurinta yana salati, hakan ya yi sanadiyyar shigowar samarin ƙannen Zaid din. Nan da nan ya miƙawa mai bi masa muƙulli akan ya kunna mota, shi kuwa ya cicciɓi Malama ganin ya zuba ruwa amma ba ta farfado ba suka fita. Gaba daya suka shiga motar, Juwairiyya da Bebi ya ce su zauna a gida bayan Al'amin dake gefe ya karɓi hijabinta da Juwairiyya ta kawo.

Kai tsaye asibitin Baba Dakta suka nufa, ba ya nan sai Khaleefa suka iske tare da wata Dr Aisha. Nurses suka karɓi Malama da gaggawa a ka shiga da ita ɗakin duba marar lafiya. An yi sa'a bayan dabaru na likitoci ta farfaɗo daga doguwar suman da ta yi. A ƙarshe dai bincikensu ya tabbata da jininta ne ya ɗan hau dalilin damuwa da ɓacin ran da ta shiga. Abin sosai ya motsa zuƙatan yaran tunda ba su taɓa sanin mahaifiyartasu da hawan jini ba. Ƙannen suka dinga jin zafin Zaid har suna ɗaure masa fuska don sun sani silarsa ne komai ya faru. Shi kuwa wata irin nadama sosai ta shige shi, jikinsa ya yi sanyi. Malama kuwa ta dage akan ba za ta kwana asibiti ba dole suka sallame ta bayan ba da shawarwarin a kara kula sosai. Khaleefa har mota ya rako su yana kara yi mata sannu. Sai da suka tafi sannan ya koma bakin aikinsa.

Daren ranar Zaid bai iya bacci ba, ya dinga nafila da addu'o'i kan Allah ya cire masa wannan soyayyar da ke wahalar da shi da ma makusantansa. Har ya yi sallar asubahi bai runtsa ba, yana idarwa kuma ya haɗa ƙaramar jakarsa ya shiga suka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login