Showing 57001 words to 60000 words out of 177840 words
ke ta nuna masa hanya har suka soma keta daji, sai da suka kai ga wani gida tafkeke mai ƙaton ƙyaure sannan tace ya yi hon, motarta da aka gani bai sa an bude ba sai da ta sauke gilashi wani jibgegen ƙatti su biyu masu gadin ƙyauren suka zuro kai, ganin baƙon fuska yasa su dubanta.
"Kar ku damu, mun samu ƙaruwa ne."
Suka ƙyaƙyace da dariya idan ka cire sannan suka karasa aka wangale ƙyauren, suna shigewa da motar aka maida aka rufe ta gam har da manyan padlocks.
"Ka cire takalmanka ka bar su a mota." Faɗin Hajiya Adama cike da nutsuwa, zuwa sannan gaba daya hatta a fuska ta sauya, wani irin ladabi ta soma kamar tana gaban Uban Dodon. Ɗan Mutuwa ya amsa da toh. Har zai fita ta ce.
"Ba a ɗaga murya, ba kuma a shiga da wayoyi, ba ka isa ka ɗaga kai ka kalli sararin samaniya ba. Ladabi, ladabi, ladabi."
Tana kai wa nan ta ajiye mayafinta, dankwali, da jaka da wayoyi, ta cire takalminta ta fito a sannu sannu. Yanda ta yi, haka ƙawarta Haj Zulaihatu ta yi. Ɗan Mutuwa ya cire takalmi shi ma ya fito, ya ga ba ma su kaɗai ne a farfajiyar wurin ba, manyan mutane da jallabiyoyi wasu kuwa da manyan riguna sai masu sanye da coat haka suke tafe suna nufar cikin gidan. Madadin ya ga falo, sai ganin wani babban fili ya yi a tsakar wajen da wani ƙaton wuri zagaye kamar rijiya an jera kyandir masu ci sai fararen ƙyallaye da kuma ja da baƙi an yiwa kyandiran ado.
Hajiya Adama suka tsaya can wani ɓangare mai ɗan tudu, zai bi bayansu aka dakatar da shi. Da wata murya marar dadi aka ce.
"Kai! Koma can baya! Ba ka da darajar zuwa wurin can!"
Ba musu ya ja baya ya koma can gefe, sai ga jikinsa yana rawa, bai san yana da tsoro har haka ba a duniya.
Wani ihu suka fara yi suna kiran sunan Uban Dodo, can hayaƙinya turnuƙe wajen sai kuma a hankali wani bango daga kusurwa ya soma buɗewa, wani mutum ne ya fito jikinsa duk gashi babu kaya, zirr yake. Sai wasu mata su ma tsirara su na take mishi baya har gaban wannan wuri mai kyandira. Gani ya yi ana zubewa ana kai goshi ƙasa ana kwasar gaisuwa, ba musu ya yi irin yadda suka yi. Sai Ɗan Mutuwa ya ga wasu ƙatti tsirara sun shigo riƙe da wata ƙatuwar ƙwarya sun ajiye gaban Uban Dodo, can kuma wasu yan mata suka soma zuwa su na rarrabawa kowa wani jan ƙyalle ana ɗorawa a saman goshi. Ana zuwa kansa Uban Dodo ya ce a dakata. Da kakkausar murya ya ce.
"Adama! Fito nan da baƙon ki!"
Jiki na rawa ta bi umarni ta fito tana tafiya a saman gwuiwarta har ta iso gabansa kanta a duƙe, shi ma Ɗan Mutuwa sai ya yi irin na ta da ya ga ta yi.
Yana zuwa aka ba shi wani abu a ƙwarya aka ce ya sha. Ɗan Mutuwa ya zaro idanu.
"Kai! Jini?!" Ya faɗi a gigice har bai san sadda ya saki ƙwaryar ba amma bai kai ga zuwa ƙasa ba Adama ta riƙe da sauri.
Tsawa Uban Dodo ya daka masa.
"Kai!! Anan ba a yi mana musu! Buƙatar duniya ce ta kawo ka! Dole ka bi dukkam umarninmu! Idan kuwa ka ƙi! To haka yana nufin ka zaɓi mutuwarka akan rayuwarka!!"
Jin haka Ɗan Mutuwa ya ji hanjin cikinsa ya kaɗa.
"Ka bi umarninsa kar ka sake ka ƙara musu. Idan ka ƙara yi kashe ka za'a yi. Koda ka fasa tunda ka shigo nan ka sani cewa mutuwa ce za ka yi ta don haka ka yi duk abin da aka sanya ka."
Hannu na rawa haka Ɗan Mutuwa ya kurɓi wannan jan abun, zai yi yunƙurin amai ya ji an watsa masa bulala a gadon baya a dole ya haɗiye abin da ya yi niyyar yi ya fasa. Uban Dodo ya matso ya shafa masa wani jan abu a goshi sannan ya ɗaura masa jan ƙyallen da kansa. A nan wurin aka fiddo wata akuya aka ce Ɗan Mutuwa ya kusance ta. Ji ya yi kamar an ɗaure masa baki, duk abin da aka ce ya yi, shi kawai ya ke aikatawa da rawar jiki. Sai da ya yi ta yi har ya gama kafin kuma Uban Dodo ya ba da umarnin a yanka akuyar. Jinin akuyar aka ba Uban Dodo ya shanye shi tas. Nan fa aka hau yin wani ihu mai nuni da taya Ɗan Mutuwa murnar shigowa ƙungiya.
"Za ka yi kudi Ibrahim Ɗan Mutuwa! Za ka samu arziki don kana da sa'a a rayuwa! Za ka yi aure! Sai dai ka sani! Abin da ka fara haifa da matarka zai kasance mallakinmu! Ya kasance ƙarƙashin ikon mu!"
Kan Ɗan Mutuwa ya ƙulle, jiki na rawa ya ce.
"Ai ni ba ni da wacce zan aura yanzu."
Wani kalar dariya Uban Dodo ya yi kafin ya murtuke fuska.
"Kana da mata kana da ɗiya! Abin da yasa bamu ce ka kawo ɗiyarka ba! Saboda namiji muka fi buƙata a farko da zamu salwantar, ko makusanci ko dan uwa ko babban amini! Kai kuwa ba ka mallaki ko daya ba! Mun hango cewa nan gaba kadan za ka yi wani auren! Za ta haifamaka namij! Daga ranar da ya zo duniya za ka dauko mana shi ka kawo ko wanka kar ka kusa ka bari a yi mishi! Wannan shi ne kashedin! Abu na gaba kuma! Ka je ka tono sabon kabari ka ciro mana harshen wannan gawa! Zamu yi maka babban aikin da za ka samu duniya a tafin hannu!"
Ɗan Mutuwa ya yi turus, tabbas sau daya ya taɓa yiwa Adama aikin zuwa saka layu a bakin gawa, amma ciro harshe? To idan kuma haƙansa bai cimma ruwa ba a ka kama shi?! Sai kuma dai ya ji zuciyarsa ta bushe! Ya ji babu abin da za'a ce ya yi ya kasa! Ya shiryawa komai muddin zai yi wannan kuɗin. Nan take ya cire wasi wasi ya amince da buƙatar Uban Dodo. Daga nan aka yi abin da ya tara na jin matsalar kowa tare da ba su mafita, sai ma Dan Mutuwa ya ji na sa ma da sauki don ciki har da wanda aka ce ya kawo kan matarsa. Wata kuwa cewa aka yi sai ta sadu da Surukinta mijin ɗiyarta sannan ta kawo musu maniyyin za ta cimma wani burinta na duniya.
Haka aka watse daga taro, sai dab da Asubahi suka shigo cikin gari, Hajiya Adama na jinjina yanda aka ƙara mata matsayi ta ƙara zama a sahun mutanen da ake ji da su a wurin saboda ta kawo sabon ɗan bauta. (Wa'iyazubillah).
***
A kwana a tashi ba wuya a wurin Allah, aka wayi gari azumi an kai ashirin da biyar.
Tsakanin Haulatu da Hajja kuwa sai sam barka don tun fara azumi ba jimawa sosai sai sabo ya shiga tsakaninsu. Kamar wani abu bai taɓa faruwa ba. Hajja har hawayen farin ciki ta yi, ita kuwa Umma hamdala ta shiga yi ga Allah da ya karɓa mata addu'arta na dare da rana. Ba wannan kaɗai ne abin burgewar ba, har ma da sauyawar ɗabi'u da dama na Haulatun. Ta ƙara maida hankali ga karatu, a baya da ba ta damu da kai hadda ba makaranta, yanzun ita ce koyaushe cikin tilawa, ga kuma litattafai da ta sani. Yanayin maganarta ta fara sauyawa, zaman da take yi na yau da gobe wajen Alhaji da ma kuma Umman dake kokarinta har Baba Saude wajen gyara mata wasu lafuzzan idan ta yi, ya sa a hankali ta fara koya gami da gano inda ta kuskure. Wasu abubuwan dai sai a hankali za ta koya. Ita ma Umman tana zuwa na matan aure nan kusa da su kaɗan. Tun kuma kamawar azumin, har da Haulatu a wajen zama gudanar da aikace-aikacen girkin shan ruwa, wataran idan yana jin wahalar azumin kuwa sai ta wuni a kwance tana bacci cikin iskar fanka ko ta AC. Zuwa sannan sun yi wata irin shaƙuwa da Mu'az, su ne hira a whatsapp na zolayar juna, haka idan ya shigo gidan suke yi. Sabon da suka yi da junansu hatta Safina wacce a baya yake ganin sun saba, sai Haulatu ta ture ta. Ko a rai ba ta masa kallon saurayi kamar yanda wasu a gidan musamman masu haukan sonsa bayan Safina su ke gulmar shaƙuwar tasu. Ita har ga Allah kallon ɗan uwa kuma babban yaya take mishi, tana ganinsa tamkar ciki ɗaya suka fito, ta sha ce masa ba ta san daɗin ɗan uwa namiji ba sai da ta haɗu da shi. Shi ma kuwa ya riƙe wannan girman, ya na kokari wajen ba ta shawara idan ya gan ta da wata damuwar da ba ta taka kara ta karya ba. Ko kuwa idan suka gangaro batun da ya shafi Mahaifinta, ganin irin tsanar da ta yiwa uban, yana kokari sosai wajen bin ta da nasiha. Idan ta gaji ta yi ta sauya darasin da sako wata hirar. Ba ta taɓa karambanin yi mishi hirar Safina ba don ba ta ga dalilin da mace za ta karya bille ta ce tana son namijin da kamar bai ma san tana yi ba. Ita ma kuma Safinar ta goyi bayanta akan yin shirun, ta kuma gane girman alaƙarta da Mu'az, tana ji a rai babu soyayya tsakanin Haulatun da Mu'az din kamar yanda magulmata ke zuwa zuga ta akan ta bari Haulatu ta nuna ta fi ta iya bariki har ta raba ta da abin kaunarta.
Yau ma ta kama Juma'a, suna zaune da yammaci a falon ƙasa daga Hajja har Umman sai Haulatu, sai ko Baba Saude da ɗiyarta Bushira suna aikace-aikacen azumi. Haulatu sanye cikin riga doguwa mai ƙaramin hannu ruwan toka. Kanta ta rufe da hular cikin ƙaramin hijabi. Sosai ta dage tana faman yanka albasa tana hawaye, ita a yau babu abin da ta ke sha'awar ci sai wainar fulawa. Hajja na tsokanarta da cewa a duk abubuwan kwaɗayi na duniyarnan ta rasa mai take so sai wainar fulawa? Ita dai turo baki kawai ta yi ba tare da ta tanka ba musamman jin Hajjar ta kira sunanta da Haule. Umma kuwa shirin yin ƙosai ta ke yi don haka tana kammala yanka albasa ta miƙe tana dariyar sunan Haule da Hajjar ta ambata ta faɗa kicin. Safina ce ta yi sallama ta shigo da rawar jiki. Suka dube ta ganin yanda ta ke washe haƙora.
"Ƴar gidan Zakiyya? Lafiyarki ko? Kin shigo ki na washe mana haƙora kamar wacce aka yiwa albishirin zuwa Umrah. Ko su Ridwanun za ki hau jirgi ki bi?"
Hajja ta faɗi, tana nufin Alhaji Ridwan da Hajiya Nuratu sai ko Baban kowa da matarsa Haj Hussaina da kuma Baba Dakta wadanda duk Alh Ridwan ne ya dauki nauyinsu, su ne wannan karon suka tafi Makkah sauke farali.
Safina cike da rashin sabon wasa da raha da Hajja ta ɗan rage fara'arta ta nutsu don a farko ma ba ta lura da Hajjar ba hankalinta kacokam yana ga Haulatu dake zaune.
"Am, ba komai Hajja, dama na zo cewa Haulatu, ta zo Maama na kiran ta, za ta karɓi tsarabarta na wajen Yaya Sadauki."
Banbarakwai Haulatu ta ji maganar. A safiyar jiya Alhamis ne ta ji labarin dawowar Sadauki garin, amma ko kusa ba su hadu ba, asalima koda ya zo gaisawa da Hajja ita ɗaki ta shige ba ta yarda sun haɗu ba.
"To, ah masha Allahu. Maza Haule, au Haulatu, jeki ki karɓo mu gani idan irin namu ne na ƙwace."
Dariya ya so kubcewa Safina, ita har lokacin takan yi mamakin yadda Hajja ta sake da Haulatu har haka. Cikin daure fuska Haulatu ta ce.
"Uhm um, gaskiya nidai sai an sha ruwa ba zan iya fita ba. Allah kuwa har wani jiri-jiri nake ji. Wainar ma a zaune zan soya."
"Bar shi idan dai wainar ce, ga Bushira nan, ai ta kammala ferar dankalin sai ta soya maki."
"Aa ni da kaina zan soya abi na."
Ta yi saurin tarar numfashin Hajja, ita fa zuwan ne ba ta son yi amma Hajja ta ƙi fahimta. Nan fa ta dage ita za ta yi suyarta, Hajja kuwa na aikin rarrashi akan ta je ta karɓo. Safina na tsaye tana kallon ikon Allah, mamakin riƙo irin na Haulatu take yi, kada dai tun abin da ya faru na kwacen waya da Yaya Sadaukin ya yi mata shi ne ta ke ƙin zuwa karɓar abin da ya fito daga hannunsa? Amma idan riƙo ne da ita har haka, tabbas halinsu ɗaya da Yaya Zaid.
"Ke, tashi ki je. Don iskanci ita da ta dage tana roƙonki sa'arki ce da ba za ta ba ki umarni ki bi ba? Maza tashi kafin na ƙaraso na kai maki bugu."
Umma ce ta fito daga kicin ranta a ɓace don duk ta ji diramar da suke yi tun farkon zuwan Safinar. Ba shiri Haulatun ta miƙe ranta duk a jagule ta kama hanyar fita. Umma ta ce.
"A haka za ki je babu mayafi ko hijabi?"
Ta juya ta koma falon ta dauki hijabin da ta yi sallar la'asar da shi ta zura suka kama hanya tana ta mitar wai Sadauki ya ja Umma ta mata faɗa. Baki sake Safina ta dube ta.
"Kai Haulatu, wai dagaske har yanzu kina kallon Yaya Sadauki matsayin mugu? Mutumin da har ya tuna da mu ya yo mana tsaraba baki daya? Don Allah komai ya wuce mana."
Ta juya duk da cewa tana dafe da kafaɗar Safinar saboda jirin da ke kwasarta ba don rashin ƙwarin jiki, bai hana ta harare ta.
"To sannu gwana ta gwanaye, ni nace maki ina wani son tsarabarsa ne? Kuma ƙarya aka yi ba mugun ba ne? Ke ni raba ni da batunsa ma, kuma ma tsarabar wayasani ko Maama ce ta yi mishi dole akan ya kawo. Na sani ma ko ku kaɗai ya kawo wa shi ne za'a yi min kara? Oho."
"Wallahi aa, Maama ita kanta mamaki ta yi da ta ga tsarabar, Yaya Sadauki bai taɓa tafiya ya dawo da tsarabar da har za ta shafe mu jikoki ba. Bar shi dai idan zai zo gidan nan duk abin da ya kawo na tsarabar kayan marmari ko kuma kayan abin sha, za ki ga ya ce har mu a ba mu namu. Zai ce ma wanda bai samu ba ya je can wurin Maminsa ya karɓa. Hakanan da sallah, idan dai zaune kake a babban gidan nan to fa sai ya ba ka naka kayan sallahn. Ke Yaya Sadauki hatta da masu hidima a gidan nan sun mishi shaida da kyauta. Kuma batun wannan tsarabar, Maama har kiransa ta yi a waya da ta ga manyan ledoji Yaya Haidar ya shigo da su don ta ji na waye da kuma wa, kuma koda ta kammala wayar ta ce shi ya ce a ba duk wadanda suka dace, kuma da kansa ya ce kar a manta da jikar Hajja da ta zo. Kin ga kenan ba Maama ce ta faɗi ba."
Haulatu dai idanunta har lumshewa take ga wani ƙara da cikinta ke yi.
"Ke, ni rabu da ni, maganarsa ma ta ƙara sanya ina jin yunwa. Ko mene ne dai shi ya sani." Safina ta dube ta.
"Au, ba za ki dai fidda komai a ranki ba ko? Shikenan."
Ta yi murmushi ba ta ce mata komai ba, ita ina ruwanta ma da wani Sadauki da har za ta tsaya ɓata lokacin tuna shi balle ya tsaya mata a rai? Kawai dai ta sani idan aka yi zancensa ne take tuna abin da ya haɗa su da kuma kallon da ya ke mata fuska haɗe kamar hadari. Har suka ƙarasa ba ta ƙara cewa uffan ba, can ɗakin Maama suka shiga ba ta nan, don haka suka fito zuwa zagayen da ake aikin azumi. A can suka iske ta suna ta aiki tare da ƴan aikin ɓangaren Baba Dakta su biyu. Sai Gwaggo Amarya matar Baba Dakta, uwa ga Maama. Tsohuwa mai ran ƙarfe tana daga gefe tana sauraron tafsiri a rediyo.
Haulatu ta gaishe su, gaba daya aka amsa fuska a sake.
"Ga dukkan alamu kina jin azumin nan ɗiyata. Muje na sallame ki."
Ta yi murmushi tana ɗan dafe bango kaɗan. Koda suka ƙarasa wata ƙatuwar leda ta ga Maama ta miƙo mata
"Ga shi nan, duka naki ne ke kaɗai inji Yayanki. Sai ki yi mishi godiya."
"Kai kai, lah Maama, ya na ga ledarta kamar ta fi ta kowa cika?"
Fadin Safina da ƴar shagwaɓa a ranta kuwa sosai ta ji dadi ko ba komai watakila wannan tsaraba ta wanke Yaya Sadaukin a zuciyar ƴar uwarta. Maama ta yi murmushi.
"Ke ma ai nakin mai kyau ne. Kuma ina ce Haulatu ta ba ki watanni uku?"
Nan fa Safina ta dage ita Haulatu ba ta girme ta ba, Haulatu kuwa kanta ya fasu, sun saba musun wanda ya girmewa wani tsakaninsu. Tana so ta ji an ce ta girmi Safina da Radiya.
"Toh yau dai ƙawar taki ba bakin magana azumi ya sha mata kai. Je ki abinki Haulatu. Kya bude idan an sha ruwa."
Maama na maganar tana nufar wajen aiki ganin lokacin shida da rabi ma ta gota lokacin shan ruwan na gabatowa. A lokacin kuma samarin yaranta suka shigo tare da su Najeeb da Haidar sai Nura yayan Radiya.
"Ah, yau da alama wata na jin azumi, kai ku kawo wuƙar mu yanka kawai ba za ta kai ba." Fadin Najeeb kenan cike da zolaya. Ita kuwa ta daure fuska ta harareshi, ba ta da ƙwarin tanka masa sai kawai ta ce.
"Oho dai, ni ba a dauko ni a sume ba daga filin ball."
Aka yi dariya, Najeeb na ƙwafa da mitar wai ita Haulatu har yana son jawo ledarta shi sai ya ga tsarabar da Yaya Sadauki ya loda mata. Ita kuwa ta riƙe gam, ƙarshe ta saka ƙara da kiran sunan Maama saboda jikinta babu kwari, ganin haka da sauri ya saki ledar ta yi gaba tana dariya.
"Yar uwa ki