Showing 45001 words to 48000 words out of 177840 words
musu hotuna a duk inda ya burge su a wayarta. Sosai hotunan suka burge Haulatu fadi take.
"Kai nima dai Allah ya nunamin na mallaki wayarnan ta zamani. Irin wannan wanki haka?"
"Ka ji fa ƙauyancin ko?"
Suka juya don jin muryar Mu'az, yana tafe a bayansu ba su san ma da zuwansa ba. Haulatu ta turo baki.
"Wallahi ni ba ƴar ƙauye ba ce, ai wanda ya fito dga Kano shi zai yiwa wasu gorin ƙauyanci. Ka ma taɓa zuwa Kano kuwa?"
Ya yi murmushi.
"Tun kafin ki zo duniya na san garin Kano. Bai taba burgeni ba. Ƙauyawa ne ku tiƙis."
Nan fa ta biye masa suka fara musu, ita a dole tana faɗamasa haɗaɗɗun wuraren da akwai a Kano duk kuwa da cewa da yawa ba ta je ba amma tana jin su a bakin Hindatu da ma Bahijja. Shi kuwa yana nuna mata wannan duk ba wani abin a zo a gani ba ne. Haulatu ta tsani tana magana ana nuna abin da take fadi bai wani taka kar ya karya ba don haka nan da nan ta cika ta yi fam. Karshe ma shiru ta yi, Mu'az kuwa ya dinga yi mata dariya. Safina har sakin baki ta yi ganin irin dariyar da yake yi, za ta iya rantsewa makamancinta ma ba ta jin ta taɓa ganinsa yana yi ko tare yake da mutuminsa Sadauki balle kuma su.
"Safina, na ƙure yar uwarki ta yi tsit."
Itama sai ta yi dariyar jin dadin Mu'az ya kalleta yana dariya, ta ji inama zai yarda su ɗauki hoto tare. Haulatu ta yi gaba, shi kuwa ya jera da Safina suna tafe yana murmushi ita kuwa tana satar kallon abin ta kamar ta haɗiye shi take ji don so. Daga ta ga zai kalle ta sai ta yi saurin juya kai.
A hanyarsu ta komawa ma haka Haulatu ta yi ta ƙunci, bai ce mata komai ba shi ma.
***
Ina labarin Ɗan Mutuwa???
Ɗan Mutuwa bai yi tsammanin za'a shafe sama da sati ba balle har a tunkari wata ɗaya bai ji labari cewa Umma ta dawo gidansa neman inda yake ba. Kansa ya ƙulle baki ɗaya, ya kuma rasa mene ne abin yi? Shi ba wai neman Umma yake da zummar yana kaunarta ko son cigaba da zama da ita ba a rayuwa, aa, ko kadan, sai dai yana so ne ya koyamata hankali daga ita har Haulatun da bai taɓa jin ƙauna irin na ƴa da uba ba a kanta. Duka wannan kwanakin ya yi su ne a gidan gona a can Gwarzo. Ya kuma gaji da zaman, ya ƙosa komai ya lafa ya san inda dare ya mishi. Ya ji labarin an yankewa su Maada hukuncin zama a gidan yari na wasu shekaru wanda ya sani babu inda zancen zai je za'a sallame su, su fito tunda su ke da manya a sama.
Yau ma waya yake yi da Hajiya Adama Loma inda yake mata ƙorafin shi fa ya gaji da zaman marinar nan da yake yi.
"Toh yanzu kai Ɗan Mutuwa idan ka fito ina ka dosa? Kar fa ka manta har yanzu wutar can ba ta mutu ba. Ana nemanka ruwa a jallo."
Ya ja guntun tsaki ransa a ɓace yake fadin.
"Ana nema na, ai ba Kanon zan koma ba. A san yanda za'a yi dai ko wani garin nesa da Kano ne na koma can na shimfiɗa sabuwar rayuwata. Kuma kina sane da cewa ina da labarin zuwan Oga a satinnan. Ya kamata ki yi duk abin da ya dace nima na samu halattar zuwa taron nan, akwai burin da nake son Oga ya cikamin shi. Ko ba komai, ai na jima ina nawa ƙoƙarin wajen tafiyar da harƙallar mu."
Ta yi ƴar dariya ta cikin wayar.
"Wannan ne kaɗai damuwarka? Toh ka kwantar da hankalinka, jibi ne dai za'a gudanar da taron, zamu san yanda za'a yi ka halarta. Har yanzu babu labarin matarka ko?"
Ya ƙara jan tsaki karo na biyu, ta sosa mishi inda ke mai ƙaiƙayi.
"Babu, amma ni na sani wancan munafukin makwafcin nawa da sanya hannunsa a kuɓutar su. Kuma ya san inda take, ban kuma san dabarar da zan yi na sani ba."
"Babu wani wuri da kake tunanin za ta je? Ko dangin uba ko na uwa?"
Ya yi wata dariya ta zallar rainin wayo.
"Ke ma dai Adama da mantuwa kike. Na'imatu fa ɗiyar Mai Kalangu, toh har wani dangi gare ta? Haihuwar bariki rainon karuwai? Ko ni nan da nake mata kurin na san asalinta ƙarya ce kawai da kuma barazanar kada ta yi gangancin guduwa ta bar ni. Abu daya da na sani, ubanta da uwarta ƴan Katsina ne. Ke bar wannan batu fa, amma ai har ta mutu ba za ta samu wani a danginsu ba. Na dai fi tunanin duniya ta shiga. Idan kuwa nan ne, samunta ba zai wahala ba. Mu ne barikin."
Suka kwashe da dariya.
"Shegen sama, wai kura ta hangi biri. Ɗan Mutuwa namu kenan. Wato idan ana neman baƙin mugu aka same ka a shafa fatiha."
"Af, ai kifin ruwa ba ya gasa da na kogi. Na'imatu da ni take zancen, duk inda take dai ai ba za ta sauya daga matata ba ko? Toh kuwa za ta je ta dawo ta same ni tunda ba ta da gatan da ya wuce ni. Kuma a lokacin zan murza kambuna."
"Atoh. Ka san da hakan ma kake tada jijiyar wuya? Kai da ma za ka yi aure kwanan nan?"
Dan Mutuwa ya yi dariyar nishadi tunawa da abar kaunarsa Lantana,
Daga haka suka tattauna dangane da abin da ya shafi harƙallarsu ta miyagun ƙwayoyi.
Babban Ogansu ne wanda ya ke na kusa da manya manyan kusoshin gwamnati wadanda matsayin Ɗan Mutuwa da ma na Hajiya Adama ba su kai girman su san su ba, shi ne zai bayyana a babban taron da za su gudanar kan matsalar dake shirin tunkaro su, tun bayan zaɓe da ya gudana a ƙasar baki daya sai ya kasance mutanensu da yawa an sauke su daga muƙamansu. Waɗanda ke kai kuwa masu gyara musu hanyoyin ɓarna a baya, yanzun duk ba su da wani ƙarfin ikon a zo a gani. Ga wasu manyan shugabanni masu tsoron Allah da suka fara tono asirin wasu a ciki inda suka kama wasu motoci manya har biyu dauke da hodar iblis da ma codein. A yanzu haka ana kan binciken wani tsohon Sanata a garin Gombe wanda suke ji da shi. Abin da ya sa za su yi taron kenan da ma dai duk wani abu da za su ƙara kiyayewa.
Wannan kenan.
***
Ta murtsuke idanunta ganin wani kwali ajiye gefen gado kamar na waya, ta ƙara murtsukawa karo na biyu ai kawai sai ta miƙe zaune babu shiri gami da kai hannu ta ɗauka. Akwai ƙaramar takarda a jikin kwalin an rubuta.
"Ƴar ƙauye, nasan mafi yawa kanawa ba sa jin turanci ko? Naki ne, daga ɗan uwanki, MM."
Ƴar Ƙauyen da ta gani ya sa ta gane Mu'az ne. Kafin ta kai ga magana sai ga Umma ta shigo dakin. Lokacin sha biyu na rana ya gota.
Umma ta shirya tsaf ta yi kyau, idan ka ga yanda fatarta ta goge kai ka ce ba ta taɓa ɗanɗana wata wahala ta rayuwa ba sai dai a can ƙasan ranta akwai damuwar da ta lulluɓe ta musamman ma da Baba Dakta suka tabbatar mata cewa duk iya binciken da aka yi ba a gano inda Ɗan Mutuwa yake ba , so suke a kama shi a hannu kafin a zartar da kowane hukunci. Rabuwa kam dama sun ce dole a raba aurenta da shi. Ita tashin hankalinta, bai wuce kar ya ƙara yunƙurin raba ta da Haulatu ba. Don batun ma za a iya kama Ɗan Mutuwa a wasa ta dauke shi. Ai ba yau aka taɓa kwata kamensa ba akan zargin siye da siyarwar miyagun ƙwayoyi amma kwanansa biyu kacal aka sake shi. Wannan maganar tsohuwa ce tun ma ba ta san za ta haifi Haulatu ba.
"Kin tashi? Ga waya Mu'azu ya siyomaki, nima ya sauyamin tawa. Sai ki mishi godiya."
Duk da haushin da yake ba ta sai da ranta ya yi sanyi babu ma kamar na Umma da ta ce ya sauyamata. Aikuwa jiki na rawa ta bude kwalin lokaci guda ta dubi Umma tana dariyar farin ciki.
"Umma, Iphone ce fa? Wai Allahna. Kai! Dama zan riƙe wannan wayar a duniya? Umma ke wace iri ya kawo maki?"
Umma ta ɗan yamutsa fuska.
"Na ji ance samsan ne ko sansam? Ga ta can dai gefen gadon."
Haulatu ta kwashe da dariya.
"Kai Umma, kar ki bari wannan ɗan rainin hankalin Mu'az ya jiki, a takarda rubutu ya yimin da Hausa, wai kanawa ba mu iya turanci ba. Yanzu idan ya ji kin kasa furta sunan wayar ai sai ya samu abin dariya. Samsung ake cewa."
Ta kai karshe tana saukowa daga saman gadon gami da daukar wayar Umma dake ajiye sabuwa fil sai sheƙi take yi. Da murmushi Umma ta girgiza kai gami da fadin.
"Ki dai tashi ki yi wanka, ace daga sallar asuba ki koma bacci kamar mai baccin mutuwa har sha biyun rana? Yau za'a karɓi lefen ƴan uwanki, kinsan gidan dai baƙi za'a yi."
Ranta fari ƙal ba ta ji komai da wani taro da za'a yi ba. Asalima ita murna take yi wai yau ita ke riƙe da babbar waya, babban burinta kawai ta gan ta a whatsapp yanda za ta ba Hindatu mamaki. Dama ta sha mata mitar wai ba ta hawa whatsapp ballantana su yi hira sosai. Har Umma ta fice tana nan tana sarrafa wayar Iphone wacce komai an saita hatta da layi an saka mata Mtn da Airtel. Shigowar Safina ɗakin da sallama ya sa ta miƙewa kamar wacce aka tsikara da murnarta ta ke nunamata wayar da Mu'az ya kawo mata har da ta Umma. Sosai Safina ta taya ta murna. Daga haka ta shige bandaki don yin wanka ita kuwa Safina takardar da ta gani ta jawo ta karanta. Dariya ta kwashe da ita, Yaya Mu'az akwai tsokana. Wannan halin nasa na sakin fuska na burge ta. Ta ƙurawa rubutun idanu tana kallo, ji take yi ina ma kalaman soyayya ne ya rubuto mata? Ta riƙe takardar a wurinta don ita kam tana son kalar rubutunsa. Har Haulatu ta fito tana zaune ta kira lambarta daga wayar Haulatun bayan ta duba ta ga akwai katin dubu daya a kowane layin. Ta adana lambar Haulatun a wayarta sannan ta adana nata lambar a wayar Haulatun, tana wannan aikin suna hira ita kuwa tana shiryawa gami da mitar yunwa take ji.
Tare suka fito falon Hajja. Nan suka iske Hajiya Hadiza da budurwa ɗiyarta sai Ihsan da kuma autanta Areef. Sai wata farar mace kamar ka taɓa jini ya fito mai jiki, ta tuna kan su fito ta ji Safina tana fadin Mamarta ta zo. Jikinta ya ba ta ita ce ko ba komai suna kama.
Ihsan da ƙanwarta Fahima dake aikin latsa waya, tun shigowar Haulatu falon suke dubanta da mamakin irin sauyawar da ta yi, fatarnan ta ƙara haske ga ɗan cika da ta yi ba kamar a farkon zuwanta ba. Taɓe baki Fahima ta yi ta kauda kai tana huci, ita tun da ta ji Hajja na ba su labarin wai Yaya Mu'az ya siyo musu manyan wayoyi ta ji wani ƙululun baƙin ciki, wato abu ne da bai taɓa haɗa ta da shi ba. Ba ya ma sakarmusu fuska idan ba Safina ba da suke ɗan ɗasawa. Zai yi dai hira da annashuwa idan yana tare da iyayensu amma su kam sai ba da umarni kawai.
Mahaifiyarsu Hajiya Hadiza kuwa, kallon Haulatu take da murmushin yaƙe amma can ƙasan ranta zallar takaici da ɓacin rai ne. Ta yi iyaka kokari wajen ganin ta gasawa Umma magana a bayan idanun Hajja ta yanda Umman za ta fice don kanta ta bar gidan amma haƙanta bai cimma ruwa ba domin Umma hakanan ta shanye dukkan zantukanta, kuma ba ta jin Umman akwai mahaluƙin da ta yiwa zancen. Da ace ta furzar, tabbas za ta fuskanci ɓacin rai wajen Hajja.
Umma kuwa sam ba ta kallonta da komai, ta bayar a ranta kawai zafi ta ji a sannan sakamakon ba kowace zuciya ce dama za ta kaunaceka ba. Ba kowa ne zai yarda da mutumin da rana tsaka zai shigo rayuwarsu da sunan shi ɗin tsatsonsu ne ba. Ta kuma yi mata wannan uzurin, ba ta sa a rai dole Hadiza da ma sauran kannenta yaran Hajja su ba ta girma ba, ko kusa a'a, balle hakan ya dame ta.
"Ina wuninku." Haulatu ta gaishe su da ɗan bada girma. Suka amsa fuska a sake.
"Masha Allah, Na'imatu wannan budurwar ɗiyar taki ai da ina da babban ɗa namiji shi zan aurawa." Fadin Hajiya Fatima kenan mahaifiyar Safina. Umma ta yi murmushi ba tare da ta ce komai ba. Fahima kuwa hankalinta na ga wayar dake riƙe a hannun Haulatun. Ai ba ta san lokacin da ta miƙe zaune sosai ba tana ƙara waro idanunta kan wayar.
"Kutmar! Iphone 13 pro max nake gani wai a hannunki? Shi ne wayar da Yaya Mu'az ya siyamaki? Lallai ma Yaya Mu'az, matar da ba ta san darajar wayar ba ma balle wani pro.."
Ta haɗiye sauran zancen da ke tafe a bakinta sakamakon ganin wanda ya shigo ya kuma yi tsaye a ƙofa yana kallonta fuskarnan a murtuke. Sadauki ne. Shigowarsa falon dalilin Alhaji ne wanda ya nuna ɓacin rai kan ƙin zuwa da ya yi su gaisa da ɗiyar Hajja. Har ya jawo Alhaji Ridwan dake wurin yi mishi faɗa shi ma sosai gami da nunamasa rashin kyautuwar hakan. Yana sanye cikin wani tsadadden yadinsa ruwan toka an mishi ƙaramin aiki a wuya da h ceannuwan bakin rigar. Ya sanya hular da ake kira da Minista kalar yadin sai dai ya ciza.
"Fahima, kina cikin hayyacinki kuwa? Toh ko uwarki ba ta isa ta yi wannan rashin mutuncin a gabana ba balle ke haihuwar yau!" Hajja kert ga wannan sababin a lokaci guda tana miƙewa tsaye har zaninta na neman kuncewa tana ɗorawa. Fahima dai tun kallon da ta bi Sadauki da shi ta ji hantar cikinta ya kaɗa. Kafin shi kansa ko wani ma ya ƙara yunƙurin wani abu, Haulatu da ta fusata ta isa dab da Fahima, ji take yi tamkar ta dauke ta da mari sai dai ta kai zuciya nesa ta dunƙule hannunta na dama ta shiga maida martani ba tare da ta damu ta ƙara kallon Sadauki a karo na biyu ba don a ɗazun katse zancen da Fahima ta yi kowa ya ankara da shi.
"Kin ƙara yunƙurin ci mana mutunci karo na biyu, na rantse maki duk radda ki ka ƙara gangancin yin na uku sai na nuna maki ba ki da wayo. Banza mai warin baki. Ke har kina da bakin kallona ki ce ban kai na riƙe wayar nan ba? Eh ban san darajarta ba kuma na mallaki abin da na tabbata ko ƙamshinsa ba ki taɓa ji ba. Tsabar baƙin ciki da hassada irin naki wato har ki kasa ɓo.."
"Ya isa, Haulatu rufemin baki kan ranki ya ɓa..."
Kafin Umma ta ƙarasa Haulatu ta dube ta ranta na zafi ta katse ta.
"Umma ki yi shiru don Allah, ki bar ni na nunawa wannan.." Ba ta kai aya ba ta ji saukar mari tas! A gigice ta dube shi, duba na tsantsar tsana. Yau ita namiji ya mara? Tabbas ta sani, duka halinsu guda ne. Hajja kira take "A'a A'a Sadauki amma ina! Sai da ya aiwatar da marin. Sam a farko bai yi niyyar hukunta ta ba, ya ji zafi da mamakin maganganun da suka fito a bakin Fahima, sai dai yarinyar ta nunamasa ba ta da kunyar dagaske. Ransa a tsananin ɓace yake dubanta. Murya a kausashe ya ke magana.
"Ƙaryarki, kin ci ƙarya ki zo gaban jama'a kina rashin kunya a zuba idanu a kyale ki. Har ana dakatar da ke kina botsarewa? Wannan koda ba mahaifiya take gunki ba sa'arki ce?"
"Ai bari faɗi ma, mahaifiyarta ce ita ta haife ta." Umma ta sunkuyar da kai jin amsar da Hajiya Hadiza ta bayar. Zuciyarta a cunkushe, wai yaushe Haulatu za ta nutsu ne ta koyi haƙuri a rayuwa.
"Ɓace ki bani wuri." Ta dube shi tana haɗiyar yawu mai ɗaci kafin ta juya da sauri bayan ta saki wayar a tsakar falon ta fice ɗaki cike da zafin rai. Safina da sauri ta sa hannu za ta dauki wayar ya dakatar da ita, ɗauka ya yi ya jefa a aljihun wandonsa, ganin haka ta juya ta bi bayan Haulatu ɗaki. Fahima kuwa kallo ya watsa mata kafin ya ba ta umarnin fita waje ta yi jiransa.
Sai kuma ya dawo daidai tamkar ba shi ba. Hajja ta cika ta yi fam tana mitar don me zai mari wacce aka zalunta alhalin ba ita ke da laifi ba taɓo ta aka yi, bai ko biyewa ƙorafin Hajja ba ya maida hankali ga Umma ya gaishe ta a mutunce. Ta amsa tana murmushin da ta saba yi na danne damuwa wanda ya zamo ɗaya cikin ɗabi'unta. Koda ya yi musu sallama ya fita, Hajja miƙewa ta yi ta nufi ɗakin don rarrashin Haulatu
"Allah yasa kar ta ba ki kunya." Cewar Ihsan tana dariya don ranta ya yi haske da marin da aka wanke Haulatu da shi. Umma dai ba ta ce uffan ba.
Fahima kuwa wayarta yasa ta koma ta ɗauko ya karɓe kafin ya kuma rantse muddin ya kuskura ya ji labarin ta riƙe waya sai ya yi mugun saɓa mata. Wannan hukuncin ya yiwa Fahima tsauri matuƙa, dama mahaifinta mai shegen tsaurin bala'i da ya ya bata wayar? Sai da ya bi ta da ruwan kashedi iri iri na muddin ya kama ta da wani laifin to fa babu ita ba riƙe waya sai a dakin mijinta. Ballantana kuma ya ji Sadauki ne ya ƙwace, ai kuwa ta shiga uku, zai dau lamarin ba na wasa ba tun da ya yiwa