Showing 33001 words to 36000 words out of 177840 words

Chapter 12 - FITAR TSIRO COMPLETE HAUSA NOVEL BY RUFAIDA UMAR

11 Jul 2024

79136

na mayar ma bayan sallar isha'i, hakan zai fi."

"Haba Baba Alhaji, kafin lokacin ai mun suma mun farfaɗo, so muke mu san komai. Dagaske ne waccan matar, oh sorry, Autarku ta taɓa haihuwar shege?"

Daƙuwa Alhaji ya yiwa mai maganar, saurayi ne da bai fi shekaru goma sha takwas ba, sanye da wando 3 quarter da riga marar hannu. Kansa kuwa wani shegen aski ne, kai daga kallo ɗaya ma za ka fahimci akwai fitina tattare da shi.

"Ko uwarka Zaituna ba ta isa ta yimin wannan zancen banzan ba ballantana uban naka da kake taƙama shi Soja ne. Kar kuma ku ƙara sheganta matar da aka haifa ta hanyar aure. Maza ku tashi ku ba ni guri, na kuma mayar bayan isha'i, ni da iyayenku zan yi ba da ku ba."

Sum sum suka miƙe, ya bi su da kallo kafin ya girgiza kai cike da jin takaici a ransa. Laifin duka na Hajiya Babba ce, da ace ba ta ɓoyemusu ba tun farko, hakan duk ba zai faru ba.

***
  Haulatu na zaune tana danna ƙaramar wayar Umma, ƙoƙari take ta cika umarnin Umman na kiran su Abban Bahijja ta sanar musu cewa sun isa gidan. A lokacin Hajiya Rabi tuni ta yi musu sallama ta tafi bayan ta ci abinci, yamma ta yi sosai, Umma na kwance dai idanunta rufe, ga dukkan alamu kan ya matsa mata da ciwo. Haulatu ma ta sha mamakin kwanciyarta da la'asar don ba ɗabi'arta ce ba, asalima ita ke hana ta. Aka turo ƙofar aka shigo babu ko sallama, Haulatu ta ɗaga kai ta kalle su. Su uku ne, ɗaya babbar mace ce, sai wata da za ta girmi Haulatun riƙe da bebi a hannunta cikin shawul sai ko budurwa da ba za ta fi sa'arta ba. Suka ƙarasa shigowa su na musu kallon tara saura, Umma ta ɗan miƙe zaune jiri na kwasarta daga kwancen, Haulatu ta ɗaure fuska ta yi tsai da idanu tana kallonsu, a shirye take da duk wacce suka zo don ba ta ga alamun rahma a saman fuskarsu ba.
Budurwar ido waje ta dube su.

"Kai! Unbelievable! Wallahi sun yi mugun kama fa Adda."

Wacce aka kira da Adda mai riƙe da bebi ta yamutsa fuska idanu saman Haulatu wacce ta maida kai ga danna wayar da a wajensu ko ƴan aikinsu sai haka.

"Sannunku." Faɗin Umma da raunanniyar murya.

"Yauwa." Babbar matar ta amsa kafin rai a cunkushe ta juya ta fita.

"Aikin banza, da alama wahalar rayuwa ce ta koro su wajenmu."

Faɗin wacce aka kira Adda kafin ta ja tsaki. Haulatu ta yi murmushi.

"Kuma dole a karɓe mu ba."

Baki sake Adda ke kallon ikon Allah, ita kuma wannan da ƙarfinta ta shigo gidan?

"Da me kike taƙama?" Faɗin Adda zuciyarta na tafarfasa, dama can ga ƴan adawar ɗakin nasu suna musu dariyar wannan mugun abu da ya faɗo ɗakin nasu.

Dariyar rainin hankali Haulatu ta yi kafin ta watsamata wani kallo da manyan idanuwanta masha Allah.

"Da me zan yi taƙama? Ai koyaushe Allah ke bamu ya rufa mana. Kuma gidan nan mun shigo shi kenan, abin kunya dai Asma'u ta riga ta yi. Ta bar muku baya da ƙura tunda ta haifi ɗiyar so Umma Na'imatu babu yanda ku ka iya karɓa dole. Ku godewa Allah ma da ba a gidan rediyo ku ka sha labari ba."

Umma juya kai kawai take idanunta a runtse.

"Haulatu." Shi ne kawai abin da ta iya furtawa bayan haka radadin da kanta ke yi ya hana ta magantu. A harzuƙe budurwar nan ta soma magana.

"Kut! Sunan Hajiya kike kira kamar ki na magana da sa'arki?"

Itama a fusace ta amsa.

"Ke kika san ta a Hajiyar."

Kafin su yi wani yunƙuri na magana ko rashin ta ido, Hajiya Babba ta faɗo ɗakin. Ta dube su a fuska a daure, kasancewar ana shakkarta ya sa duk suka nutsu idan ka cire Haulatu da ta haɗa su tana watsa musu harara.

"Ku fice min a nan." Ba musu suka fice rai a ɓace. Ta ƙarasa shigowa ba ta ko bi ta kan Haulatu ba ta dubi Umma cike da kulawa, murya na ɗan rawa ta ce.

"Na'imatu meke samunki?" Ta ƙarashe tana kai tafin hannunta saman goshin Umma. Aikuwa ta ji ya ɗauki zafi rau.

"Innalillahi, ai ba ki da lafiya. Bari na kira Khaleefa."

"Daga baya kenan, sau nawa tana yin cutar a duniya kin taɓa kulawa? Sai yau?"

Faɗin Haulatu tana harararta, nasihar Umman ta ɗazu ce akan abin da ta aikata a falon Alhaji yasa ba ta yi gigin ture hannunta daga jikin uwarta ba. Hajiya Babba ta kalle ta, wai yau ita ce ake faɗawa baƙar magana? Dama akwai ranar da za'a yi jikar da za ta gasamata mai zafi haka? Tana kallo Umma na girgizawa Haulatun kai, ita kuma ta juya a sanyaye ta fice don kiran Khaleefa ya zo dubamata ɗiyarta.

Bayan fitar ta Umma ta dubi Haulatu, kafin ta kai ga magana rai a tunzure Haulatu ta katse ta.

"Don Allah Umma kiyi hakuri, wallahi idan na gan ta raina baƙi yake yi. Kuma na rantse ba zan iya cusa kaunarta cikin zuciyata ba."

Kawai sai ta fashe da kuka ta miƙe ta shige banɗaki. Umma dai ajiyar zuciya kawai ta yi. Ta sani dama ya lafiyar kura ballantana an jefe ta da kashi? Fatanta Allah ya yayyafawa lamarin ruwan sanyi domin ita kam ba ta ma san yanda ta dauki Hajiya Babbar ba a yanzu. Haƙiƙa tana buƙatar ko na lokaci ne kafin ita ko Hajiya Babba wani ya riga kwanciya a dama, su rayu cikin aminci da zumunci. Ko ba komai ta nuna nadamarta a fili.

***
Fuska a ɗaure ya bi wayar da kallo, sunan Hajja da ya gani ya sa shi fahimtar mai kiran. Ya dubi nurses din dake tsaye kansu na kallon ƙasa sakamakon faɗa da yake kan sakacin da suke yi mishi da marasa lafiya. Da muryarsa tausassa ya nunamusu hanyar waje da yatsa gami da fadin.

"Out."

Suka ƙara furta Sorry Sir, kafin su sa kai sum sum kowannensu ya fice.

Khaleefa Dawud S Malumfashi kenan.
Bai kai ga ɗaukar wayar ba, ta ƙara ringing karo na biyu, sai a sannan ya ɗaga.

  "Yes Hajja."

Abin da ya furta kenan murya can ƙasan maƙoshi, yana mai ɗan runtse idanu da ɗan dafe goshi alamun gajiya.

"Khaleefa, maza ka zo gida yanzu ka duba Na'imatu ba ta jin dadi."

"Wace haka?" Ya furta ya na yamutse fuska tamkar tana kallonsa.

"Na ce dai ka zo yanzun nan. Don Allah, jikinta ya yi tsanani sosai."

"Ok." Iyakar amsar da ya ba ta kenan kafin ya sauke wayar daga kunnensa ba tare da ya katse ba sai can Hajja ta yanke.

Sai da ya kwashi mintuna uku cikin yanayi na shiru da tunani, abubuwa biyu ne a ranar yau suka sosa ransa, a gida Madina ta yi mishi nata kalar laifin, ya zo asibiti nan ma ya iske marar lafiya cikin halin neman taimako amma nurses kowa na harkar gabansa. Wannan abubuwa biyun sun yi matuƙar kai shi bango. Sarai ya na da labarin abin da ke wakana a gidan nasu, bai dauke shi wani abu na tashin hankali ba ko na a zo a gani, shi mutum ne da ya fi damuwa da matsalar dake gabansa. Wannan na daga cikin ɗabi'arsa da kowa ya sani.

Miƙewa ya yi ya dauki waya da muƙullin motarsa. Koda ya fito daga ofis din sai da ya biya ofishin abokin aikinsa suka yi magana kafin ya dinga keta mutanen dake zirga-zirga a asibitin ya fice zuwa filin parking.

***
Umma sosai zazzaɓi ya rufe ta, tana kwance rufe da bargo. Baba Saude ta shigo ta kashe Ac sakamakon sanyin da Umman ta yi ƙorafin tana ji. Har aka yi sallar Magriba, Haulatu ba ta ko motsa daga gefen Umma ba. Ta cika ta yi fam, ita so ta yi ta fita ta je ko wurin Baba Dakta ne ta fadamasa Umma ba lafiya a kai ta asibiti amma kuma Umman ta hana ta har da haɗa ta da Allah ta zauna tunda a cewarta Hajiya Babba na ta zirga-zirga kuma ta kira likita zai zo.

  "Tashi ki je ki yi sallah. Idan kin fito sai na shiga." Ta tsinci muryar Umman tana magana dakyar. Ta miƙe tana ɗan ɓata rai ta shiga bandakin, bayan ta fito Umma ta miƙe da taimakon Haulatun ta shiga ta ɗauro alwala ta fito. A zaune ta yi sallar. Abincin ma da aka kawo ko loma ɗaya ba ta sanya a baki ba.

***
A babban falon Hajiya Babba kuwa, ita ce zaune cike da damuwa da sanyin jiki, ta yi shiru tana jin muryar ɗiyarta Hadiza da suke kira Anti Dije tana famam sababin ba ta kyauta musu ba sam. Ita ce dai ta shiga dakin Umma a dazu tare da yaranta domin tabbatarwa kanta abin da ake fadi.
   "Haba Hajiya, yanzu fisabilillah kin jazamana magana a zuri'a, dama ya muka ƙare? Gaskiya nidai ki lallaɓa ki saka matarnan ta koma can inda ta fito, ta fadi nawa take so sai a ba ta."

"Atoh." Fadin Ihsan tana ƙara zaman bebinta gami da cigaba da shayar da shi. Kallon da Hajiya Babba ta watsa mata ya sa ta kauda kai tana ɗan shan mur.

"Tashi ki ficemin a nan tun kan ranki ya ɓaci." Ba musu Ihsan ta miƙe tana ƙunƙuni. Ita kuwa Hajiya Babba duban tsanaki ta yiwa Hadiza.

"Ke yanzu Hadiza ni kike fadawa duk abin da ya zo bakinki gaban yara? Madadin ki taya ni neman gafarar Na'imatu na gyara kuskuran da na aikata a baya, shi ne ki ke kokarin mayar mini da hannun agogo baya? Dakyau, to ki sani, girma ya riga da ya kama ni, ba zan kuma bari son zuciyata ta sanya ni jefa rayuwarta cikin hatsarin da ya fi na baya ba. A shirye nake na gyara kura-kuraina duk yawansu. Ai farkon zuwanta nima tunanin nawa bai wuce na sallamarta da kudade ba ta yanda zan ƙara nesanta kaina da ita. Amma kuma cikin ikon Allah na fahimci kuskurena musamman da na ji irin ƙalubalen da ta fuskanta a rayuwar da ta yi ba tare da ni ba. Ba kuma zan bari hakan ta ƙara faruwa ba muddin ina da sauran numfashi a gaba."

"Amma Hajiya kun ce tana da aure, yanzu da auren Na'imatun za ta zauna a gabanki?"

Rai a ɓace Hajiya Babba ta ƙara ba ta amsa.

"Auren jeka na yi ka? Auren da babu abin da ta tsinta a ciki face baƙin cikin ɗa namiji? Toh babu inda za ta je. Daga ita har Haulatun a nan za su zauna. Ki kuma sani kaf ta girmeku, ku kira ta da Maman Haulatu kamar zai fi akan Na'imar."

Baki buɗe kawai Hadiza ta saki tana kallon Hajiya Babba. Sallamarsa ce ta katse maganar da ta lanƙwasa harshenta da zummar furtawa uwar. Suka dube shi, dogon saurayi fari ƙal, yana sanye cikin farar tshirt dinsa sai kuwa wandon jeans kalar sararin samaniya. Fuskarnan tasa a ɗan ɗaure ba kuma don komai ba sai don ɓacin ran da ya ci karo da shi a falon Hajiyar dake ƙasa, ƙannensa ke cece kuce kamar za su kaure da dambe. Tsawa ɗaya ya sanya duka suka shiga taitayinsu.

Mu'az Faisal S Malumfashi kenan. Matashin saurayin da ke girgiza zuƙatan yanmatan zuri'ar tasu. Mutum mai sakin fuska, sai ko idan rai

Hajiya Babba ta dube shi.

"Mu'az, maza kira min Khaleefa a waya. Tun ɗazun na ce ya zo ya duba jikin Na'imatu ka ji shi shiru. Ko kuma dai mu wuce da ita asibitin?"

Ita kadai ta yi kiɗa da rawarta, shi kuwa sai ma ya nemi wuri ya zauna gami da yin filo da baby bag din Ihsan dake ajiye a gefe.

"Toh Hajja a kai ta mana."

Ta kai mishi duka a cinya.

"Aush." Ya mike zaune.

"Wai me Hajja?" Ya fadi yana yamutse fuska.

"Tashi za ka yi a kai ta da motarka. Haka take nufi Mu'az. Bari na fiddo ta." Faɗin Hadiza tana mai miƙewa ta kama hanyar ɗakin da Umman ke kwance. Hajiya Babba ta yi mamakin wannan saukowa lokaci guda na Hadizar, sai dai ita ta san wace ce ita. Mace ce da ta iya shirya abu a rai, ko ita da ta haife ta ta san halinta, abu zai iya taɓa ran Hadizar ta shanye a gaban idanunka, amma hakan ba yana nufin ya wuce ba, tabbas akwai abin da ta ƙullata da za ta yi ramuwa a kansa. Yanzun ma ta fi tunanin da walakin goro a miya don haka ta bi bayanta. Shi kuwa da kallo kawai ya bi su kafin ya maida idanunsa ya lumshe. Ya ji labarin komai, ya tarar da Mommynsa na ta farin ciki da walwala, a bakinta ma ya soma jin maganar. Jin dadinta kuwa bai wuce sanadin takun saƙar da take yi da Hajiya Babbar ba tun sadda Hajiya Babba ta yiwa Engr Faisal umarnin ƙara aure bayan ta kawo masa wata yar uwa daga Malumfashi a sanadiyyar saɓani da aka samu da Mommyn a sannan ta yi yaji. Aure dai na huce haushi, wannan abu ne ya tsaya a ran Mommyn, hatta da sabon da ya yi da Hajiya Babba ba kaunar hakan take yi ba. Ya ji a bakin Mommyn, shegiya ce Hajiya Babba ta haifa, a bakin Alhaji kuwa, ya ji gaskiyar abin don haka shi kam bai ga abin tada jijiyoyin wuya ba.

***
Haulatu ba ta tsaya wani ja in ja ba da su Hajiya Babba don hankalinta na ga Umman wacce ta gama sheƙa amai ba jimawa. Haka ta mike ta zura nata hijabin tana kuka, Hadiza na tallafe da Umman suka fito. Fitowarsu daga dakin zuwa falon, ya yi daidai da shigowar Khaleefa da sallama dauke a fatar bakinsa. Jin muryarsa ya sa Mu'az ƙara lumshe idanu yana mai amsa sallamar murya can ƙasa. A zuri'ar kusan kowa zai ba da shaidar rashin haɗuwar jinin mazajen biyu. Za'a hadu a gaisa idan ta kama, hira ce dai Khaleefa bai yi da shi, kamar yanda Mu'az din bai damu da sanya shi a shirginsa ba. Shi Khaleefa na masa kallon mutumin da ya girma amma bai san ya girman ba saboda son yawace-yawacen wurare na bude idanu da more rayuwa da yake da shi, yayinda Mu'az ke masa kallon mutum mai zafi da nuna isa da gadara a komai.

Ko kallonsa Khaleefa bai yi ba, ya maida hankali ga Hadiza wacce ta fito riƙe da Umma. Ganinsa ne ya sanya ta ɗan ja burki.

"Ah, kinga ma Khaleefan ai. Bismillah zo ka duba ta, ta jiga ta sosai."

Ya dubi Umman da kyau, ko ba a fadi ba dama ga kamannin Hajiya Babba a fuskarta. Ta juya suka koma ciki tana ba Hajiya Babba amsa cewa ga Khaleefan ya zo. Haulatu da ba ta ji me suke fadi ba ganin sun dawo da Umma ranta ya yi zafi.

"Au kun dawo da ita dakin kenan idan ma mutuwar ce ta ƙarasa a ciki?! Ni dama nasan babban burinku bai wuce ku ga gawarta ba. Toh ni zan fita na kai Uwata asibiti, ko ba komai na san ciwonta!"

Tana fadin haka ta yi kan Hadiza dake ƙoƙarin ajiye Umma saman gado da zummar tallafawa Umma ta ƙara miƙarta. Umma ta riƙe hannunta amma babu bakin magana.

"Will you excuse me?"

Jin muryar namiji ne ya sa ta waigo fuskarnan jage-jage da ruwan hawaye, suka dubi junansu ido cikin ido, shi tasa fuskar a tamke tamkar an aiko masa da saƙon mutuwa, ita kuwa kallonsa take da tunanin shi kuma waye don ba ta cikin wata nutsuwa ko hayyacin yin wani lissafin.

"Likita ne, Khaleefa duba ta don Allah mu ji meke samunta haka. Gyara a wurin ya duba ta."

Sai da ta juya ta watsawa Hajiya Babbar wani kallo ganin yanda ta riƙe mata gwuiwar hannu kafin ta matsa ta ja baya. Khaleefa ya dubi Hajiya Babba.

"Ku na iya fita baki daya."

Suka fice, Hadiza ta hadiye ɓacin ranta na hararar da Haulatu ta yi uwarta.

"Mu je Haulatu, duba ta zai yi."

Ta so yin gardama amma irin kallon da Khaleefan ke watsa mata mai kama da harara ko kuma ta ce na tsana, sai kawai ta hadiye suka fita gaba daya.

Sai da ya yiwa Umman tambayoyi, ya yi rubutunsa a takarda sannan ya fiddo abin gwajin jini ya ƙara duba Bp dinta, nan ya ga ya hau. Ya dubi Umma, kawai sai ya ji matar ta kwanta masa a rai, ciki ciwo take amma sunayen Allah kawai take kira madadin sambatu na mai fama da zazzaɓi.

"Sorry." Ya furta a tausashe. Ta ɗan gyada kai.

"Ki rage tunani, damuwar ba ta kawo wa bawa mafita a dukkan matsalar da zai shiga."

Daga haka ya miƙe ya fito, ko ta kan Haulatu wacce ta ke tsaye bakin ƙofar ɗakin bai yi ba ya dubi Hajiya.

"Hajja zan je zan ba da magungunan a kawo. A kula da abin da zai sanya ta tunani ko ɓacin rai. And please, tana buƙatar mai hankali a kusa da ita."

Ya ƙarashe, sai a nan ya dubi Haulatu dake kallonsa da nata dara-daran idanun kalar nasa. Ta yi kasa da kai, Hajiya Babba na amsa mishi da toh. Mu'az tun shigar su ya fice a falon saboda zuwan Khaleefa.

Ran Haulatu ya ɓaci, wato da ita ya ke? Allah ne ya taimake ta dai ba ta furta komai ba, sai kawai yana matsawa ta sanya kai ta shige dakin. Ya maida dubansa ga su Hajiya Babba ya ce a samu abinci marar nauyi a ba ta ta sanya a cikinta. Daga nan ya wuce.

***
Bayan sallar Isha'i Alhaji ya tattara yara da jikokinsa wadanda ke kusa. Ya ce a sanar da na nesa. Sai da ya fara da addua kamar koyaushe, ya dan yi ƙaramar nasiha sannan ya ba su labarin Umma da Haulatu a taƙaice. Ya kuma nuna musu ita din haifaffiya ce ta hanyar aure, ba wai zina ba. Kar ya ƙara jin wasu a ciki na sheganta Umma. Daga nan ya gargaɗe su akan ko kallon banza kar ya shiga tsakaninsu da su

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login