Showing 60001 words to 63000 words out of 177840 words

Chapter 21 - FITAR TSIRO COMPLETE HAUSA NOVEL BY RUFAIDA UMAR

11 Jul 2024

79165

ajiye mana abin nan idan mun zo tafiya sallar taraweeh sai mu ci."

Faɗin Safina murya a ɗan sama don har Haulatu ta sanya ƙafa za ta fice. Ta amsa mata da toh kawai ta bar su Haidar da tambayar Safina mene abin da za'a ci ɗin?

Tana tafe kamar wacce ƙwai ya fashewa a ciki don gaba daya takun ma ba ta son yi, kallo ɗaya za ka yi mata ka fahimci azumin na wahalar da ita. Idanunta a lumshe tana shaƙar ƙamshin turaren da ledar ke yi, can kuma ta buɗe idanun, ta kai ga gefenta inda ta ji ƙarar hon. Sosai motar ta burgeta kalar maroon ce. Gilasanta duk sun sha tinted. Sabuwa dal sai sheƙi take yi, ba ta taɓa ganin irin motar a gidan ba don haka ta fi zaton baƙi suka yi, aka ƙara yi mata hon, ta juya ta ga motar a saitinta ta tsaya an zuge gilashin.

"Ƴar ƙauyen Kano, duk azumin ne haka? Please idan kin shiga ki ce Hajja a ajiyemin kayan shan ruwa ina nan shigowa."

Sam ba ta kula da na gefensa ba ta taɓe baki.

"Gaskiya ɗan birni ina goyon bayan Hajja, ta nemo maka wata zankaɗeɗiyar budurwar ƙauyen mu aura maka. Kullum ƙa..."

Sauran zancen ya maƙale a fatar bakinta sakamakon wanda ta ga ya ɗan ɗago kai daga saman kujerar da ya kwantar na gaban motar ya ɗan yi rigingine. Bacci ne ya soma ɗaukarsa saboda gajiyar wurin aiki ga azumi a baki. Ya kalle ta da rinannun idanunsa mai cike da gajiya. Fatarsa ta ƙara gogewa kamar ba shi ba.

"Wuce ki tafi."

Yanayin muryarsa can ƙasa don haka sum sum ta juya ta cigaba da tafiyarta ya bar Mu'az da yi mata murmushin mugunta, dama yasan ba ta ga Sadaukin ba. Shi kuwa bayan ta wuce ya ja guntun tsaki.

"Ban san sadda ka soma jan yaran nan a jiki ba, sun soma rainaka."

Mu'az murmushi ya ƙara yi karo na biyu bai ce uffan ba ya ja motar suka wuce Haulatu dake tafiya kamar za ta kife. Haka kawai ta kasa yi mishi musu ko tsiwa. Ta bi motar da harara kamar su na ganinta. Koda ta isa ledar kawai ta jibge saman kujera, Hajja ba ta falon ta shiga alwala don haka ta isar da saƙon Mu'az ga Umma.

"Ah yau dai ƴan shan ruwan namu suna da yawa kenan, ɗan gidana ma ya cemin yana tafe."

Haulatu ba ta san sadda ta miƙe zaune gami da ɗan zaro idanu ba. Khaleefa da Mu'az a wuri daya? Mutanen da ba sa wani jituwa?

"Taɓ din! Akwai kallo." Ta yi furucin a fili, Umma ta ce "Me kika ce?" Sai ta yi saurin cewa ba komai gami da haɗiye dariyarta. Ta rantse ba za ta sanar da Mu'az ba, za ta rama muguntar da ya shirya mata yanzun. Su zo su haɗu da Khaleefan ta ga gudun ruwansa.

***
In sha Allahu gobe zan muku posting.
Kiran sallar magriba ne ya miƙar da Haulatu daga kujera da sauri ta yi saman ƙatuwar dardumar da Umma suka shimfida aka jera kayayyakin shan ruwa a samansa. Kai tsaye ruwa da soma sha duk da dabinon da Umma ke miƙa mata, ita yau kam ƙishin ruwan ta ke ji. Daga haka kuma ta miƙe ta shige bandaki. Alwala ta ɗauro, sai da duka suka idar da sallah kafin Umma ta shiga zubawa Hajja kunu a kofi. Haulatu kuwa filas ɗin wainarta ta ɗauka da haɗaɗɗen yajin da aka daka mata ta yi gefe bayan ta tsiyaya kunu. Ta sani dama can Umma ba ta damu da wainar fulawa ba, Hajja kuwa ko tayi ba'a yi mata ba don haushin Haulen da take kiranta take yi, dama kuma ita ma ba cimarta ba ne. Sosai ta so hayewa sama ta sha ruwanta a tsanake kafin wannan Khaleefan ya shigo sai dai kuma tana son kallon diramar da zasu yi da Mu'az. Ta soma ci kenan sai ga Khaleefa ya yi sallama, can babu jimawa da zamansa shi ma Mu'az ya shigo. Haulatu dai daga kallon da ta yiwa Khaleefa da kuma gaisuwa sai ta kauda kai, Mu'az ya ji gaba daya fara'ar da ya shigo da ita ta ragu. Kamar ya juya sai kuma ya dake ya ƙaraso ciki, madadin ma zama kusa da Khaleefan sai ya koma gefen Hajja inda Haulatu ke zaune daga can gefen kujera.

"Taso ki zuba musu Haule, kunun za ku sha ko shayi? Ga ƙosai mai zafi, ga farfesun kifi ga kuma dankali da ƙwai." Hajja ke koro wannan bayanin, ta miƙe kasancewar tana cike da farin cikin haɗuwar Khaleefa da Mu'az sai ba ta ko ji zafin Haulen da Hajja ta kira ta ba. Khaleefa ya ce bai son dankalin, ta zuba masa farfesu a ɗan ƙaramin bowl sai kuwa kunu da ƙosai. Sai kayan marmari a ɗan farantin tangaran ƙarami. Koda ta zo kan Mu'az, dubansa ta yi da zummar tambayar me za ta zuba masa, aikuwa ba ta san sadda dariyar da ta ke maƙalewa ba ya fito, ta shiga yi abin ta.

"Ke, mene haka?" Muryar Umma ta katse ta. Shi kuwa Mu'az sanin da ya yi ta san cewa ya sha faɗamata hakanan ba ya son abu ya haɗa shi da Khaleefa saboda girman kai da jin shi ya isa, ya gane sarai dariyar me ta ke yi. Ai kuwa ya shaƙa.

"Za ki zubamin ko na tashi na bar wurin?"

"Aa, me ya yi zafi? Yi hakuri ɗan birni. Kai na san ba ka shan kunu ko? Bari a zubamaka shayi sai farfesu da dankalin. Ƙosai da kunu ai sai ƙauyawa irin mu."

Khaleefa ya ɗan ɗago kai ya kalle ta, wai dama tana magana har haka? Koda dai ba zai ce magana ba, tunda a ganin farko ma da ya yi mata, tsiwa take yi. Amma yaushe suka yi sabo da Mu'az da har ta ke mishi irin wannan zolayar? Sai kawai ya maida kai ga kallon tashar Saudia da ake hasko ɗakin Allah, a gefe kuma suna ɗan taɓa hira da Umma. Shi sam haɗuwarsa da Mu'az din a wuri bai fiye damunsa ba, kamar yanda bai nuna akwai wani rashin jituwa tsakaninsu sakamakon bambancin halayya. Ya sani dai shi ɗan baruwansa ne, idan aka sanya shi a zance, to fa zai shiga, idan kuwa babu shi ciki, ba ruwansa da mutum.

Har ya kammala bai bar jin Haulatu na hira da Mu'az ba, shi ma Mu'az din ganinta a wurin ya sanya shi watsar da batun Khaleefa, har ma zamansu wuri guda ya dame shi. Umma dai tana lura da yanda ba su kula juna, ba yau ta soma gani ba, amma a baya ba ta kawo komai ba sai da Haulatu a hira ta taɓa labarta mata dagaske wai jininsu ne bai hadu ba kamar yanda Mu'az din ya fadi mata. Suna yawan samun matsala da juna, yanzu za su hadu, amma kuma rabuwar zai iya zuwa da fushi ko jin zafin maganar ɗayansu. Sam abin bai yiwa Umma dadi ba, ta kuma ci ɗamarar gyara alaƙarsu da taimakon Allah. Wannan ya sa ta duban Mu'az.

"Nikam Mu'azu ba na ji kana ƙorafin yawan ciwon baya ba kwana biyun nan? Me zai haka ka faɗawa ɗan uwanka yanda ka ke ji ko yana da shawarar da zai ba ka?"

Daidai nan wayar Khaleefa ta yi ƙara, ya ciro ya ɗaga, Mu'az kuwa kallon Umma ya yi kafin ya ɗan dubi Khaleefan wanda ya yi tamkar bai ji mai ake cewa ba, da alama da Sadauki ma yake waya saboda ya ji shi ya ambaci Saraki. Muddin ka ji Khaleefa na waya ya ce Saraki to ba da kowa yake wayarnan ba face Sadauki.

"Ni fa na warke Umma. Dama ba wani ciwon a zo a gani ba ne."

"Ke ma dai Na'imatu da neman magana kike, ai shi wannan ya gwammace ko zai nakasa ya yi akan dai Dakta ya duba shi. Wannan baƙin ran nasa irin na uwarsa ban san ina zai kai shi ba. Dakta ya ba ka shekara guda amma daga kai har shi babu aikin da ku ka saka a gaba sai sha wa juna ƙamshi, to ku je ku ƙarata."

Khaleefa dai kallonta kawai ya yi bayan ya kammala wayar, idan Hajja ce ba yau ta saba yi musu caa akan rashin jituwarsa da Mu'az ba. A ganinsa yaron ba sa'ansa ba ne sam, to na mene ne zai tsaya yana wani shiga sharo ba shanu? Ai yaron ma sai ya ƙara raina shi fiye da yanda ya yi a yanzun.

"Please Hajja, ba na son irin haka."

Haulatu ta saci kallon Khaleefa, aka yi rashin sa'a shi ma lokacin ya ɗan dube ta, hararar da ta samu ne ya sa ta kauda kai tana ɗan yamutsa fuska.

'Mutum kawai ya baro matarsa ya zo kwaɗayi.' Ta furta a ƙasan ranta.

Mu'az ne ya fara miƙewa ya yi musu sallama da zummar zuwa shirin tafiya masallaci, tsabar Hajja ta gama ɓata ransa har wayarsa ya bari a saman kujera, da sauri Haulatu ta ɗauka ta bi bayansa. Khaleefa ya bi su da kallo kawai, nan ma bai ce komai ba.

Sai bayan tashin Hajja da hayewarta sama ne Umma ta maida duba ga Khaleefa.

"Ɗana, meyasa da girmanku ku ke yin abu irin na yara? Shi yanzu Mu'azu idan ma za'a yi mishi uzuri ganin kamar yana abu wasu lokutan irin na ƙuruciya, kai ai mai hankali ne, ka fi shi sanin rayuwa da yanayi na zamantakewa. Don Allah a yi kokarin kai zuciya nesa, idan ku na nuna wa juna irin wannan hali na ko in kula, me na ƙasa da ku za su gani su yi koyi da shi? Babu dadi ma a ji mutane na cewa jininku bai hadu ba, a ina ne jininku bai hadu ba alhalin duka tsatso guda ku ka fito, uwa uba ma musulunci da ya haɗa ku? Ni dai ban jin dadin wannan abu naku. A ƙoƙarta a gyara."

Khaleefa ya jinjina kai yana mai gamsuwa da maganganun Umma, sosai kuma ya ji har ransa matsayinta ya ƙaru. Ko mahaifiyarsa ba ta taɓa nuna wata damuwa akan rashin jituwarsu ba, asalima sai dai ta ce ya cigaba da jan girmansa kar ya kusa ya sakarwa Mu'az ya raina shi. Ya kuma danganta hakan da cewa watakila kawai saboda ba sa ga maciji da Mamin Mu'az ne. Dagaske suke kishin facaloli a tsakaninsu.

"In sha Allahu zan yi kokarin gyarawa Umma. Sai dai fa ƙarfe ɗaya ba ya amo. Ni a iyakar sani na, babu abin da ya taɓa yi min, kawai ni ban damu da shiga sabgar wasu ba."

Murmushi Umma ta yi.

"Ɗan uwanka ne shi, gaisuwa ma ta sakin fuska koda ba hira ku ka yi mai tsawo ba yana da dadi. A daure a kai zuciya nesa. Na kuma ji dadi da ka ce babu abin da ya taɓa haɗa ku. Ya wajen ɗiyata? Jikin dai da sauki ko?"

Sai a sannan ya tuno ma dalilin zuwansa nan shan ruwa, ya je ya tarar gidan kaca-kaca, dama kwanakin nan hakuri kawai yake yi don tun goma ga azumi ƴar aikinta ta tafi gida wai za'a yi mata aure bayan sallah shi ne dalilin da yasa ita kuwa ko tsinke sai ya yi mata jan ido ta ke kawar wa. Girki kuwa sai dai ya siyo a waje, abin ya ishe shi ya kai ƙara wurin Mamarsa madadin ta dauki zafi sai ta nuna ai ba komai laulayin ciki ne kuma ma ba ta saba da aikace-aikacen gida ba, da wanna ta tura musu yar aiki ɗaya cikin biyu da take da su. Sai ta zo ba ta iya girki ba, gidan dai ba laifi takan gyara, yau dai aka yi katari hatta da gyaran bai samu ba dalilin wai ta je gidansu an yi rasuwa, to Hafsat kuma kwanciyarta ta yi dama tun kamawar azumi ba ta yi ko guda ba acewarta ita ba za ta iya ba saboda laulayi bayan jikin ta samu sauki sosai. A fusace ya bar gidan ya kira Umma da zummar zai sha ruwa a wajenta.

"Lafiya dai ko?"

Tambayar Umma ta katse mishi tunani. Ya yi ɗan murmushin yaƙe, bai fiye son yawan ƙorafi ba musamman akan na kusa da shi don ko Maama sai ta ɓaci sosai yake iya furzar mata.

"Bakomai Umma, lafiyarta kalau. Ai dayake ma ba ta samun yin azumin saboda yanayi na jiki. Amma da sauki Alhamdulillah."

Umma ta jinjina kai, ta ɗan karanci damuwa a fuskarsa amma sai ta bi shi da hakan tunda ya nunamata babu komai.

***

Haulatu ta iske Mu'az na tafe kamar zai tashi sama.

"Ah, ɗan birni saurin me kake har ka na mance wayarka?"

Ta ƙarashe tana mai miƙa masa gami da haɗiye dariyarta. Ya ja guntun tsaki, yanayin fuskarsa babu ɗigon fara'a.

"Dama kin san da zuwansa shi ne ko ta waya ba ki sanarmin na fasa shigowa ba?"

Ta taɓe baki gami da ɗan ɗaga kafaɗa.

"Ina ruwana to? Ɗan uwanka ne fa, tare na gan ku. Ƙiyayyar ai ba ta yi zafin da ba za ku zauna inuwa ɗaya ba."

Ya jinjina kai kawai. Bai ce mata komai ba ya juya ya cigaba da tafiya.

"Allah ya huci zuciyarka. Sai na taɓo ka whatsapp sai mu shirya."

Bai ko juyo ba, ita kuwa dariya har da riƙe ciki sannan ta koma ciki. Ganin magana Umma ke yi da Khalifa yasa kai tsaye ta nufi hanyar sama.

"Ina za ki je? Maza dawo ki kira Bushira ku tattare wajen nan."

Jin haka Khalifa ya miƙe da zummar wucewa. Suka yi sallama da Umman ya fice.


"Wai ke ko a gaida gida ba ki iya yiwa mutum ba?" Fadin Umma tana duban Haulatu baki sake don gani ta yi yarinyar kamar ita ma tana son ɗan uwanta Mu'az wurin basar da lamarin Khalifa.

"Lah, ni fa Umma ko na yi magana bai cika amsawa ba. Ai kin ma gani sau nawa zan gaida shi ya dinga amsamin kamar yana shan kunun tsamiya."

Girgiza kai kawai Umma ta yi ta tattare shirginta ta haye sama ita ma don ɗauro alwala da niyyar zuwa masallaci. Babban masallaci ne kusa da su kaɗan, ɓangaren maza daban da na mata. Nan suka tafiya gaba daya idan ka dauke su Hajja wadanda ke zama su yi na su a gida.

Haulatu kuwa idanunta na kan ledar nan, sai ta ji tana son ganin me ya kawomata amma lokacin sallah ya taho kuma ta sani nan kusa za ta ga su Safina da Radiya sun biyo mata tafiya sallah. Da sauri su na gama tattarawa ta dauki ledar ta nufi sama. A daki ta zazzage ledar saman gado, Umma lokacin tana saka kaya ta yi wanka yanda za ta ji dadin gudanar da ibada.

"Wannan duka tsarabar taki ce?" Fadin Umma tana ɗan mamaki, lokaci guda tana mai karasowa ta kalla. Riga doguwa mai laushi na kwalliya ko yawo a tsakar gida sai na bacci mai kauri guda daya, sai turare mai ƙamshi a wani ɗan gida mai kyau. Sai kuwa agogo da wani set na sarƙa da ɗan kunne kalar silver. Sai ko takalmi irin na yawo tsakar gida mai kyau. Sosai tsarabar ta burge su.

"Masha Allahu, lallai Sadauki Allah ya bar zumunci toh. Idan mun dawo daga sallah ko a waya ki kira ki yi misho godiya. Ki hanzarta an soma kiran sallah." Umma ta ƙarashe tana mai nufar sif son fiddo doguwar riga marar nauyi ita kuwa Haulatu har ta tattara kayan ta shiga banɗaki ta yo wankan ita ma ta fito ba ta bar mamakin wannan kaya ba. Ita a farko ma ta yi zaton ko har da na Ummanta a ciki.
Koda ta fito ma Umma tuni ta fice, tana shirin saka kaya su Safina suka shigo don haka da gaggawa ta shirya suka fice zuwa masallaci.

A hanya suke tambayarta me da me Yaya Sadauki ya kawomata tsaraba, ta ƙi sanar da su ta ce sai ta ji na su tsarabar tukunna. Nan Safina ta ce duka dogayen riguna ya kawo musu, wasu kuwa takalma ne. Sai ta ɗan yi turus, to meyasa na ta ya fi na su yawa?

"Ke kuma me ya kawo maki?"

Ta kara saurin tafiya, layin duka fitilu ne masu haske sosai ga kuma mutane masu parking motocinsu har ma da masu tafiya a ƙafa don tuni an tayar da sallar isha'i. Da wannan ta samu damar fadin

"Sai ku zauna har mu rasa wannan raka'ar ku na tambayar abin duniya."

Ganin haka suka mara mata baya da sauri, da wannan ta samu aka bar tambayar don ko bayan sun dawo gida, wainar fulawa suka yi zaman ci sannan suka kora da lemun zoɓo, tana ba su labarin diramar da aka yi tsakanin Mu'az da Khalifa, ita da Radiya suka dinga dariya yayinda Safina ta dan ji babu dadi wai an ɓata ran masoyinta.

***

Washegari...


"Wallahi kurwar ɗana kur! Ni dai ina maki gargadi da babbar murya, daga ke har mayyar ɗiyarki ku fita hanyar ɗana! Idan ba haka ba zan nunamaku daidai nake da ku. Wato tsabar an shanye shi, ya kasa zuwa wurina shan ruwa, amma ya iya ya dinga safa da marwa a hanyar wajenku neman abin da zai ci! Wannan uban nacin da masifa da me ya yi kama? Barikin da ku ka saba yi a inda ku ka fito shi ne yanzu ku ke gwada shi kan ɗana? To na ga Zakiyya (Maama) ma, ita ma ta yi ta gama! Haka nan ta rabu da ni! Ballantana kuma ke da ba a gama sanin asalinki ba!"

Waɗannan zantukan da suke fitowa daga bakin Momin Mu'az, su ne suka farkar da Haulatu daga baccin ranar da ya kwashe ta. Ƙarfe uku da motoci, Hajja ba ta nan, Najeeb ya kai ta asibiti wurin likitan ido. Ta murtsuƙa idanunta, Momi na tsaye ta riƙe ƙugu ko rufin mayafi ba ta yi a saman doguwar rigar atamfar dake jikinta ba, Umma na daga zaune ta yi shiru kawai fuskarta dauke da tsananin damuwa yayinda Baba Saude da Bushira ke a gefe sai ko wata fitsararriya a cikin ƙannen Mu'az, Nusaiba dake tsaye daga ƙofa kamar wacce ke gadi kar wani ya taho. Kan Haulatu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login