Showing 132001 words to 135000 words out of 177840 words

Chapter 45 - FITAR TSIRO COMPLETE HAUSA NOVEL BY RUFAIDA UMAR

11 Jul 2024

79164

ma haka ba jimawa sai da ya kira ni yana tambayar wai ina saƙonsa da Momi ta ce na kawo? Shi ne na ƙarasa kicin Ummi ke cemin kin karɓa. Taimaka please."

Daga yanayinsa ta gamsu da cewa bai gan ta ba don haka ta ɗan yi murmushi.

"Shikenan, karɓi ka kai. Dama na so mu gaisa ne na ji ba ya jin dadi. Amma idan ya shigo ciki na gaishe shi."

Ya sa hannu ya karɓa yana maida mata martanin murmushin.

"Yauwa godiya nake."

Daga haka ya ƙarasa zuwa ƙofar ɗakin Yayan nasu ya ƙwankwasa kafin murɗa ya shige da sallama. Sai da ta ga ya shige ya rufo ƙofar sannan ta yi wani tsalle har da rawa don jin dadi, da sauri ta fice son ta sanar da Maminta a waya.

A ɓangaren Fu'ad kuwa, zaune ya iske yayan nasu a falo yana share hanci da tissue, saman hancin nan ya yi ja ga dukkan alamu yana jin jiki don ko a muryarsa za ka fahimci lallai yana fama da mura. Bayan ya ajiye tray din ya tsaya, shi bai zuba ba kuma bai miƙe ba. Har sai da Sadauki ya rage ƙarar tv dake aiki ya dube shi.

"Lafiya?"

Fu'ad bai yi nauyin baki ba ya labarta masa duka abin da ya faru. Sadauki ya yi mamaki shi kansa, ya sani dama bai wani yarda da yarinyar ba har da zamanta a nan, sai dai bai kawo har wuyanta ya yi wannan kaurin ba. Ajiyar zuciya ya yi.

"Dauka ka je ka ba masu gadi."

A ɗan tsorace Fu'ad yace.

"Yaya, kar ya cutar da su."

Murmushi Sadauki ya yi.

"Kar ka damu, ba abin da zai faru. Ai ba su aka yi wa ba. Na kuma sani, ko mene ne ba zai wuce don abu ɗaya ta yi shi ba. Jeka ka kai musu, koda Momi ta tambaya ka ce ka zubamin na sha kawai."

Daga haka ya kwantar da kai, yunwa yake ji ba kuma ya jin ɗanɗanon komai, amma ya gwammace ya haƙura zuwa gobe.

"Ko a yi maka wani abun?"

Tambayar Fu'ad ta sanya shi ɗago kansa ya kalle shi.

"No, kar ka damu, i'm ok."

Daga nan Fu'ad ya dauki flask din ya bi ta ƙofar da za ta sada shi da farfajiyar gidan nasu kai tsaye ba ta ɗayan hanyar da ya shigo ba. Ba jimawa ya dawo ya ajiye kwanukan gami da yi wa Sadauki sallama, har zai fita ya ji Sadauki ya dakatar da shi ta hanyar kiran sunansa. Dawowa ya yi.

"Na'am." Ya amsa.

"Bana son kowa ya san zancen nan. Koda Momi."

"Toh Yaya." Ya amsa ba don haka ya so ba domin jikinsa har tsuma ya ke yi don ya je ya sanar da Momin tasu. Amma kuma tunda har Yayan nasu ya taka masa burki ya sani idan ya aikata zai yabawa aya zaƙinta.

Shi kuwa Sadauki ko bayan fitar Fu'ad lamarin ya yi ta juyawa a kwanyarsa, duka-duka nawa Jannat take da har ace ta san hanyar gidan ƴan tsibbu? Waye ya koyamata? Anya kuwa a gida an sani?

Haka ya yi ta watsawa kansa tambayoyin da rashin mai amsawa ya sa kawai ya rufe da addu'ar Allah ya shirye ta.

A ɓangaren Jannat ko, tana can cikin zullumi a falo, Zuhra na mata hira amma ita rabin hankalin ya na ga ƙofa, so take ta ga shigowar Fu'ad, aikuwa yana zuwa ko zama bai yi ba ta ce.

"Ya jikin Yaya Sadaukin? Ya kuwa samu ya sha farfesun?"

Fu'ad ji ya yi kamar ya zage ta, sai kawai ya daure ya ce eh.

"Kai Yaya Fu'ad, maimakon ma ka tsaya ya kammala ka kwasomana sauran mu sha?" Cewar Zuhra. Harara ya banka mata sannan ya ja guntun tsaki yana mai miƙewa lokaci guda, shi ba ya ko son kallon Jannat din.

"Au kodai tare ku ka sha ne ma?"

Zuhra da ba ta haƙura ba ta ƙara furtawa.

"Ki tashi ki je ki tambayi mai shi ba ni za ki tsaya yiwa tambayoyi ba."

Daga haka ya mike ya bar wurin don shi ko kallon Jannat din ma haushi yake ba sa. Jannat dai dadi kamar ta yi me, ta tabbatar burinta ya kusa cika akan Yaya Sadauki. Tabbas idan ta aure shi ta gama morewa. Wadanda za ta yiwa ɗagawa suna da yawa.

Da wannan ta yiwa Zuhra sallama ta shige daki don ta ce bacci ne a idanunta. Zuhra kuwa ta amsa da toh kawai don hankalinta ma ya koma lan waya.

***
Kano...

Hindatu zaune ta yi shiru cikin yanayi na tunani, tun faruwar lamarin da ya kusan yin sanadiyyar zubewar cikin jikinta, ta soma ganin kulawa ta musamman fiye da baya a gurin mijinta Ɗan Mutuwa. Ita ba wannan ke damunta ba a yanzu face wayar da ya yi a kan kunnenta sadda tana kwance a gadon asibiti, duk a iya tunaninsa bacci take yi sai dai tun soma wayarsa ta motsa a lokacin amma kuma ta ƙi nuna komai. Da wani Honarabul suke waya inda yake fadin.

"Kai bari Honarabul, farko na kaɗu ai, duk a zatona cikin nan ya fice, da ban san me zan faɗawa Shugaba ba. Ai yanzu dole zan yi takatsantsan har zuwa sadda zan cika umarnin ƙungiya. Batun Na'imatu kuwa na haƙura tunda dai kana gani Shugaba ya tabbatarmin idan na dage akan sai mun ga bayanta, to karfin addu'ar da take yi zai sa komai ya juya kanmu."

A lokacin jin motsin za'a shigo ne ya sa shi gaggawar katse kiran, ita kuwa ta yi kamar tana bacci har sai da Nos ta ɗan taɓa ta za ta yi mata allura sannan ta motsa. Gaba ɗaya ta kaɗu da abin da ta tsinta yana faɗi, ta ma kasa tuna wace ce Na'imatun a kwakwalwarta tsabar ruɗani. Wato dai ya tabbata zargin da take yi wa Alhaji Ibrahim tun farko hakan ne? Ko kuwa ita ce ba ta fahimta ba? Cikin ta shafa wanda ko watanni uku bai cika ba, cikin jikinta yake so? To wane ne shugaban da zai ba? Tun sadda ta ji wannan zantukan ta ke yawan zama cikin tunani da firgici, ta kuma kasa sanar da ko Momi ce don ta sani zai wahala a yanda idanunta suka rufe ta amince.

"Bebina, tunanin me ki ke yi?" Yadda ta zabura ta rikice ta miƙe sai da shi kansa Ɗan Mutuwa da ya yi furucin ya tsorata.

"Lafiya?" Sai ta yi saurin girgiza kai da sauke ajiyar zuciya.

"Babu komai, ban san ka shigo ba ne shiyasa."

Ya yi murmushi ya kamo hannunta ya maida ta mazauninta.

"Ni wannan tunane-tunanen naki sam ba na kaunarsu, ko har yanzu ba ki haƙura kin yafemin ba?"

Yaƙe ta dan yi.

"Komai ya wuce, dagaske nake."

Ya shafi gefen fuskarta.

"To ki kwantar da hankalinki, ina nan ina nema mana visa, zan kai ki Dubai ki ɗan buɗe idanu ki huta abinki."

Ita sam abin bai burge ta ba sai ma sabon tsoro da ta shiga, ta girgiza masa kai.

"Aa, nagode amma ni dai na fi son garin nan. Ba na son zuwa ko'ina."

Ya ɗan haɗe fuska.

"Mene ne haka? Au, watsamin ƙasa a ido za ki yi?"

Hindatu kamar ta yi kuka don ita komai na gidan ma ba iyaka maigidan ba, tsoronsu take ji. Balle kuma abin da zai fito daga hannunsa.

"Allah kuwa dagaske nake, ni bana ra'ayin zuwa ko'ina."

Ya yi dariya gami da ɗan rungumota kaɗan.

"To mene ne abin tayar da hankali? Shikenan ya isa kar ki yi min kuka."

Tuni ta soma hawaye don ji take kamar ya ɗosana fuskarta a kan wuta. Ba ta so ta dinga gudunsa da yawa ya zargi wani abun don haka ta share fuskarta kafin ta ce.

"Ni dai ka bar ni na je gidan Momi na yi kwanaki."

Ɗan Mutuwa ya ɗan yi shiru, sai kuma ya tuna zai fi samun damar aiwatar da shirinsa akan Hajiya Adama shi da su Duna a nutse. Ya rantse sai ya dauki fansar kayansa da ta saka aka kama wanda har Abuja ya je amma bai ci nasarar da suka fito ba, sai dai ya samu sunansa bai fito ba kwata kwata don yaron da aka kama da kayan ko za'a mutu ba zai taɓa tona asirinsa ba, yanzu dai sai an kwana biyu zai san yanda zai yi yaron ya kuɓuta a hannun hukuma. Dalilin kenan da ya dauki alƙawarin illata kayayyakin Hajiya Adama koda hakan na nufin ƙone ɓoyayyen store ɗinta da ke can cikin daji inda take ajiyar kayan ne.

"Shikenan, kar ki damu, ki shirya gobe ki je sai ki kwana biyu. Sati ɗaya ya yi maki?"

Ta girgiza kai bayan ta ɗago daga ƙirjinsa tana dubansa.

"Please na yi sati biyu?"

Ya ɗan yi shiru yana dubanta, ya kula kamar a tsorace ta ke da shi, bai kawo wai ko ta samu wani labari ba ne face ta tsorata da irin dukan da ya yi mata, wannan ya haifarmata da shakkarsa. Don haka ya riƙo hannunta da ya ji har wani rawa suke yi. Ya bi yatsun da kallo kafin ya dube ta.

"Bebina kamar tsorona ki ke ji? Na fa yi maki rantsuwa akan ba zan ƙara taɓa lafiyarki ba. Ko ba ki yarda ba?"

Yaƙe ta yi.

"Na yarda."

"To nidai ki bar wannan tsoron, kuma batun sati biyu a gidan Momi, na amince. Yi murmushi na gani?"

Ta kuwa saki fuskarta sosai don ta ji dadi. Za ta samu damar yiwa Momi zancensa. Ita ta saka ma a rai idan ta taka ƙafa ta bar gidan har abada ta bar shi kenan. Wannan dalilin ne yasa koda ta tashi shirya kaya, akwati babba ta ɗauka ta haɗa komai da ta san yana da muhimmanci a wajenta ciki har da takardun makarantarta.

***
Katsina...

Haulatu da Safina sun yi nasarar ƙona layar da suka tsinta a ɗakin Maama, hankalinsu ya kwanta hakan ya sa koda suka tashi dawowa daga Islamiyya zuƙatansu fes saboda jin dadi.

"Wai ku shi ne ɗazu ko ku jira ni ku ka yi ficewarku ko?" Faɗin Radiya tana harararsu.

"Kai Radiya, ke da ban sanki da ƙorafi ba? Zama da Haulatu ta sa kin koya kenan."

Haulatu ta kai wa Safina dundu ta kuwa kauce suka yi dariya.

"Ai shikenan, na yi shiru tunda kun ɗauke shi matsayin ƙorafi. To goben dai zamu ke gidan ƙunshin ko?"


"Me zai hana? Bikin Maamanmu guda? In sha Allahu. Kinga Safina don Allah ki tashi da wuri ke ce dama mai shegen nawa idan kin so. Sai a shirya a yi ta jiranki. Ni har kitso ma zan yi a gobe in sha Allahu."

"Kawai kin san idan na tuna ranar bikin sai mun shiga makaranta haushi nake ji fa." Faɗin Safina tana yamutse fuska.

Haulatu ta bi garin da kallo yanda hadari ke faman haduwa kafin ta ce.

"To ai kuwa zuwa kinsan dole ne, akan biki dai nasan ba za'a bari mu yi fashin makaranta ba sai dai ko idan zamu nuna ba mu da lakca ranar."

"Ni kam da sauki, English ne kawai zamu yi kuma da safe ne, daga shi ba ma komai. Malam Bilal ya maida ajinsa ran Friday da safe." Fadin Radiya tana musu dariyar mugunta, suka bi ta da harara kawai. Haka suna tafe suna hirarsu da tsokanar juna har suka karaso gidan.

"Ke, ga mutuminki can tare da Yaya Khaleefa."

Jin abin da Safina ta ce har tana ɗan zungurinta ya sa Haulatun kallon gaban ƙaton ƙyauren gidan. Suna tsaye a gefe kusa da shukoki, motar Yaya Khaleefa a fake, Yaya Sadauki sanye da jallabiya baƙaƙirin mai adon golden din zare a wuya da bakin hannu. Irin mai mannewa a jiki da ya taimaka wurin fiddo tsarin halittar da Allah ya yi masa na ƙirar namiji. Sam hankalinsu bai je garesu ba, ga dukkan alamu abin da suke ta tattaunawar mai muhimmanci ne. Ta kauda kai daga kallonsa ƙirjinta na harbawa da sauri-sauri. To mene ne na fitowa bakin titi salon ƴan matan makarantarsu su yi ta kallonsa? Sai ta shiga waige, ta ga kuwa wata budurwa dale tafe tare da ƙannenta uku hankalinta na kansu, saboda tsabar kishi da ta ji ya tokare maƙoshinta sai ta ke ganin kamar ma murmushi budurwar ke jefamasa. Shi ta ke kallo, ba shi take kallo ba, ita dai Haulatu kawai tunaninta ya ba ta hakan. Don haka nan da nan ta tamke fuska, wai sai ta ji Yaya Sadaukin ma na ba ta haushi.
Sai da suka kusan isowa dab da su sannan ne idanunsu ya kai garesu. Sadauki na kula da irin yanda mutuniyarsa ke faman cin magani da hura hanci. Khaleefa kuwa kauda kai ya yi don ba ma ya so ya cika kallon Haulatun, ya yi nasarar fara mancewa da ita, dama bai zurfa da yawa ba, ba ya son abin da zai maido mishi hannun agogo baya.

"Yaya Khaleefa ina yini, Yaya Sadauki ina yini." Haka suka jero gaisuwar kusan duka lokaci guda, su ma suka amsa musu da lafiya lau. Har za su shige Sadauki ya yi magana yana duban Haulatu.

"Ita kuma wannan wa ya taɓa ta?"

Safina da Radiya har Khaleefa suka dube shi kafin su maida duba ga Haulatu, Khaleefa ya kauda kai yana ɗan murmushi, ya kula dagaske dai Sadauki yake son Haulatu, sam shi bai wani kula da sauyin fuskarta na a zo a gani ba. Haulatu kuwa kallon Sadaukin ta yi sai ta ga kamar ma har wani haske ya ƙara, irin kallon da yake jifanta da shi ya sanya ta kauda kai cike da jin kunya. Ba su amsa ba sai ita ce ta ce.

"Bakomai."

"Are you sure?" Bai damu da kallon da Khaleefa ke bibiyarsa da shi ba ya ƙara tambayar, Haulatu ta gyaɗa kai.

"Ok, ku shiga gida."

Daga haka suka wuce cikin bin umarninsa. Ya maida kai ga Khaleefa wanda ya ƙuramasa idanu yana ɗan murmushi mai ɓoye abin da ke ransa.

"Me nayi toh?" Fadin Sadaukin shi ma ya na murmushi.

Ɗan taɓe baki Khaleefa ta yi.

"No, ka ji na tanka? Kawai sai ka tsargu?"

Suka yi ƴar dariya.

"Have you confess?" Cewar Khaleefa.

Har lokacin bai bar murmushin ba ya ɗan dubi hadarin da ke ƙara haɗuwa ga iska mai daɗi dake kaɗawa ya amsa.

"Not yet."

"Ka na jiran me toh? For how long za ka tsaya kana fama da abu guda? Ba ka tsoron wani ya yi maka shigar sauri?"

Da mamaki Sadauki ya ce.

"Tun yaushe ka sani?"

Khaleefa ya yi ƴar dariya gami da dukan kafaɗarsa kaɗan.

"Ka ga bari na tafi kafin ruwa ya tare ni. Sai mun yi wayar ko?"


Murmusawa Sadauki ya yi, ya san ko zai ƙara tambayar idan dai Khaleefa ne ba zai samu amsar ba don haka ya bar maganar shi ma. Suka yi sallama shi kuma Sadauki ya koma ciki.

***
Washegari kuwa da wuri suka ɗunguma gidan ƙunshi. Sun ci sa'a babu wani layi, don matar ta iya ƙunshi, kusan ko ba lokaci na biki ko sallah ba, gidan Hasiya Mai Ƙunshi yakan zama da mutane. An yi musu ja mai ɗan karen kyau sai baƙi a iyakar hannu, sai dai sun zaunu don ba su suka bar gidan ba sai da aka idar da sallar isha'i. Ga gajiya ga yunwa, Haulatu kanta har wani sarawa yake yi. Hajja ta kira ya fi a ƙirga tana masifa wai ita wannan wane irin ƙunshi ne haka ace har yanzu ba su dawo gida ba ga hadari ya haɗu a garin.

Sadda Hajja ke wayar ƙarshe da Haulatun bayan sallar isha'i tana mitar dare ya yi su jira za ta sanya a zo a ɗauko su, Sadauki na nan ya shigo kawo wa Hajja saƙo daga Daddynsa ya tsaya suna ɗan taɓa hira da Umma da kuma Haj Hadiza da ta shigo gidan tun safe anan ta yini an kira mata mai ƙunshi ta yi mata. Hankalinsa na ga Hajja har ta kammala wayar ta ajiye ta cigaba da sababi.

"Saude, maza zo nan, ko kuma ke Na'imatu karɓi ki bincikomin lambar Gali, ya zo ya ɗaukomin yaran nan."

Jin haka Umma ta miƙe ta ƙarasa ga Hajja, shi kuwa Sadauki duban Hajja ya yi.

"No Hajja, bari na ɗauko maki su. Wane unguwa ne?"

"Kai Allah ya yi maka albarka Sadaukin Alhaji, daɗina da kai akwai kirki. Nan unguwar Sabon Gida. Idan ka je kwa yi waya su maka kwatance."

Haj Hadiza ba ta ce musu uffan ba har Sadauki ya miƙe ya musu sallama ya fita Hajja ba ta bar sa mishi albarka ba, ta kalli Umma dake faman murmushi, ta watsamata kallon banza a ranta faɗi take.

'Makira, kin ƙullo wani surƙullen nasu na bariki dole ki yi murmushi tunda kwalliya ta biya kuɗin sabulu.'

A fili kuwa miƙewa ta yi tana fadin.

"Hajja bari na zo na tafi kafin ruwan nan ya sauka tun da na kammala, sai kuma jibin idan Allah ya kaimu."

Hajja ta amsa.

"Toh shilenan, ki gaida gida. Jibin dai ki shigo da wuri, kuma a yiwa wancan mai kunnuwan kashedi, muddin ya hana min Maimunatu shigowa sabga da kaina zan kira shi a waya tunda shi dai bai san mutunci ba."

Dariyar da bai kai zuci ba Hadiza ta yi.

"Ah Hajja ai ke ce daidai da wannan ɗan naki."

Umma kuwa cewa ta yi.

"Hajja kenan, idan har ya hana ai babu yanda za'a yi sai haƙurin tunda dai ya fi mu iko da ita."

Haj Hadiza kamar ta buge Umma haka ta ji, ta san watakila ma Umman a ranta dadi take ji. A kwanan nan har matsala sosai Maimuna ta samu akan ta je bikin dangin Musbahun mijinta ta kai dare shi ne fa ya sanya mata takunkumin fita. Sun yi fada sosai har kokarin dukanta ya yi, magana dai har gaban mahaifinta ƙarshe aka yi sulhu ta koma. Yanzu kuwa ya ce babu inda za ta ƙara fita idan ba larura ba sai ya hora ta.

"Ni da kaina zan yi kiran Musbahun."

Umma dai kallon Hajja kawai ta yi gami da girgiza kai ba tare da ta ce uffan ba. Hadiza ta harare ta karo na biyu sannan ta shige ɗakin Hajjar ta kimtsa ta fito, sallama ta yi musu ta fice tana ƙara maimaitawa Hajjar batun zuwan Fahima a gobe.

Bayan fitarta Umma ta Hajja magana sosai kan rashin dacewar yi wa suruki kutse gudun raini, ba girma a ciki. Hajja ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login