Showing 81001 words to 84000 words out of 177840 words
ban gane ta ba. Ni rabon da na sanya ta a idanu ai tun kafin azumi. Sai naga ta ƙara girma da gogewa. Eh lallai, wuya kam ba ta daɗi. Ashe yarinya kyakkyawa ce haka masha Allah."
Dariya Momi Nuratu ta yi.
"Ai kam dai."
"Amma shi Sadaukin har sun yi sabo da shi haka? Ko ba shi na ji tana tambaya ba?"
"Kai Mamin Khaleefa, to idan shi ta tambaya ma ina ce ɗan uwanta ne."
Cewar Amarya. Wata kuwa cikin ƴan Malumfashi mai suna Kubra, ta cafe.
"Aa toh, ki ka sani ma ko shaƙuwar ta kai a yi auren gida."
Mamin Khaleefa ta yamutse fuska. Zancen nan sam bai mata daɗi ba, ita da take fatan ɗiyarta Jannat ta samu cikar burinta na auren Sadauki? Yarinya tun tana tatsitsiyarta take fama da son sa? Ai kam dai ba za ta saɓu ba wai bindiga a ruwa. Ta dubi fuskar Momi Nuratu, ko alama babu wani sauyi tattare da ita sai ma dariya da ta yi aka shiga wani hirar yayinda aka bae ta da tauna zancen da Kubra ta furzar.
***
"Ga hi nan. Nan ne ɗakin." Faɗin yarinyar, Haulatu ta amsa da toh sannan ta ƙwankwasa ƙofar gefe guda ƙirjinta na lugude. Ta ji an murɗa ƙofar an buɗe. Ta dube shi, kallonta kawai ya yi ya juya ya shige ciki yana cigaba da amsa wayarsa. Hararar ƙeyarsa ta yi sannan ta bi bayansa tana kallon yanda ƙaramin falon ya tsaru. Babu dai tarkacen a zo a gani kamar ma ba ɗakin namiji ba komai tsaf. Na'urar sanyaya ɗaki nata aikinta, sanyin da tiles ɗin ya ɗauka ya ratsa tafin ƙafarta, gaba ɗaya ma falon ƙamshin turarukan Sadaukin ya ke yi. Za ta zauna a ƙasa ya yi mata nuni da kujera da yatsarsa don har sannan waya yake yana zuba uban turanci. Ta nutsu kuwa tana ji, ta dai tsinci abin da ta tsinta. Ta kuma fahimci da namiji yake wayar kuma yare mai suna Samuel, magana suke yi akan wasu kayayyakinsu da suka yi oda amma ya maƙale a Lagos. Sai bayan ya kammala ne ya yi gyaran murya kaɗan, ta dube shi gami da gaida shi. Ya amsa yana miƙa mata hannu, ba musu ta miƙa masa takardar. Ya karanta ya yi murmushi.
"Shi ke nan, kina iya tafiya."
Ta amsa da toh. Har ta kama hanyar fita ta ji ya kira sunanta.
"Haulat." Sai ta ji kamar ba ta taɓa jin sunanta a bakin wani mahaluƙi ba sai a bakinsa. Ya fita raɗau ga wani daɗi da ya yi a kunnenta, kallonta kawai ya ke, ita ɗin ma sai ta tsinci idanunta cikin nasa ta kasa magana sai kawai ta sunkuyar da kai ta dawo ta ɗan zauna.
"Gani Yaya." Ta furta kirjinta na bugu ta shiga ambaton sunan Allah, wai ita mene ne haka take ji kwanakin nan? Ta kasa fahimtar komai.
"Kina da riƙo. Hakane?"
Ta dube shi idanuwa a waje.
"No ba zaremin idanu na ce ki yi ba. Koda dai, kin riƙe ni saboda na taɓa lafiyar fuskarki. Ina mai ba ki haƙuri akan hakan. Ina haɗawa har na dariyar jamb score ɗinki da na yi. Hope za ki yafemin?"
Ta ji maganar kamar daga sama, wai Yaya Sadauki ne mai neman ta yafe laifukan da ya yi mata? Ba ta san ma ta shagala da kallonsa ba sai da ya ɗan murza yatsunsa biyu na farko da na tsakiya a gefen fuskarta wanda ya yi sanadin lumshewar idanunta. Ta ɗan girgiza kai.
"Ni na mance ma an yi haka. Ya wuce."
Kamar ya ƙara magana sai kuma ya fasa.
"Kina iya tafiya."
Ai kafin ma ya rufe baki ta miƙe don dama ta gama matsuwa da hakan. Abu ne da ba ta saba ba, kaɗaicewa da namiji ko waye shi. Ballantana kuma Yaya Sadaukin da ba su ko saba wani gaisawa sosai ba. Tana fita ta shaƙi iskar ƴanci, dagaske fa tana ɗan shakkarsa ita ma, kawai dai ta fi su Safina dakiya ne. Tana tafe tana tunano haƙurin da ya ba ta da ma murmushin da ya yi mata, sai ta tsinci kanta da murmusawar ita ma. Wayarta ta yi ƙarar shigowar sako amma ba ta duba ba, sam ba ta bi ta ƙofar falon Momi Nuratu ba sai ta fita ta ƙofar dake a ɓangaren Yaya Sadaukin.
Ba ta ankara ba ta ji an ɗan jawo gefen hijabinta, ta juya don duk a zatonta ma Radiya ce, ita ke yawan yi mata wannan wasan idan ta gan ta a hanya.
"Radiya bana.." Sauran zancen ya maƙale a fatar bakinta ganin fuskar Jannat da ta tsaya ta riƙe ƙugunta da bai gama cika ba tana dubanta rai a haɗe.
"Lafiya?" Ta furta bayan ta gyara tsayuwarta. Wata harara Jannat ta bi ta da shi kafin ta nuna ta da yatsa.
"Kin yi kaɗan, kin yi tsaroro ke ko a bariki aka haifi uwar babanki, ba ki isa kuma ba ki kai girma da ƙimar da za ki iya raba ni da Yaya Sadauki. Abeed nawa ne, kuma ni Jannat tasa ce. Wallahi ki ka kuskura na ƙara ganinki da shi sai na maki abin da har duniya ta naɗe ba za ki mance da fuskata ba."
Tun a farko kalmarnan ta bariki ta sosa ran Haulatu, ta danne dai kawai ta kuma jure don ta ji inda zancen ya nufa. Koda ta ji ƙarashen ba ta san sadda ta yi dariya ba.
"A banza, wanda ki ke yi dominsa bai san da zamanki ba. Ina mace take ma a nan da har Yaya Sadauki zai kalla ta burge shi? Ai ba uwar ubana ce bariki ba, ni ma barikin kaina ce, da ace Yaya Sadauki saurayina ne, na rantse maki ko inuwarki ba ta ishe shi kallo ba don ni da ace ina da ra'ayin wani shirme na soyayya, ai ba ki kai na haɗa saurayi da ke ba. Ina ƙirar take? Abu kamar kyandir."
Daga haka Haulatu ta juya a fusace za ta bar wurin idanunta duk dauriyarta tuni sun soma fitar da hawaye ba don komai ba sai na takaicin kalmar da har yau da ta samu ƴancin kai ba'a bar danganta su da shi ba. Wato Bariki. Sai dai ba ta kai ko ƙofar ƙyauren da za ta yi sallama da gidan Abba Ridwan ba, ta ji Jannat ta yi mata wani wawan fisga gami da kokarin kai mata mari aikuwa a zafafe ta riƙe hannun ta hankaɗa ta baya da ƙarfi ta kuwa zube a ƙasa, daidai nan ƙawayenta suka yo kanta tuni Haulatu ta fice.
Haka ta faɗa falon da su Umma ke zaune fuskarnan jage-jage da ruwan hawaye, ko sallama ba ta yi musu ba ta nufi hanyar bene.
"Ke Haule, zo nan." Muryar Hajja ya tsaida ta, duk yanda ta so ta haye amma ta kasa sai ta dawo jikinta har wani rawa ya ke yi don ɓacin rai, ga wani kuka irin na zuci, babu sauti sai sauke numfashi da sauri sai ko ruwan hawaye.
Hajiya Hadiza na gefe tana sallah amma gaba ɗaya idanunta yana kansu, babu ma nutsuwa a sallar. Ita kuwa Umma da ta idar, kallon Haulatun kawai ta yi ta maida kai ga addu'arta. Maman Zaituna wacce ta fito daga banɗaki ta yi alwala ta ƙarasa ga Haulatun ta ɗago ta daga durƙuson da ta yi gaban Hajja tana kuka babu amsa ɗaya da ta iya ba Hajjar dangane da abin da ya faru.
"Lafiya? Meke faruwa? Yanzun nan fa ta fita da walwalarta."
"Ina na fahimci wannan lamarin ke kam, kuma kin ga ta ƙi cewa komai. Daga ina take ma?"
"Assalamu alaikum warahmatullah...wajen Sadauki ta je, ke me ya faru a can din?"
Wannan magana ta fito daga bakin Haj Hadiza don dama tana ta zuci-zucin ta idar ta amshe. Sai ga Fahima ta shigo falon kamar an wurgo ta.
"Ke Haulatu, ki zo inji Momi Nuratu."
Fuska ba walwala Maman Zaituna ta ce.
"Fahima meyafaru ne?"
Taɓe baki ta yi.
"Wai fa dukan Anti Jannat ta yi har ta tunkuɗe ta ta faɗi saman dutse ta fasa goshi. Kuma akan duka su biyun suna son Yaya Sadauki."
Baki sake Haulatu ke duban Fahima wacce ta kantaro wannan uban sharrin ta jefe ta da shi. Umma dai kanta na ƙasa tana tasbihi ba ta ko ɗago ba tun bayan kallon da ta bi Haulatun da shi na farko. Ita kuwa Haj Hadiza hararar Fahimar ta yi, a ranta tana kiranta da banza gaɓuwa marar wayo, tana gefe tana mata yaƙi na samun shiga wurin Sadaukin amma ita kuma kamar ma ko a jikinta taya ƴar uwarta kishin Haulatu take yi.
"Haka aka yi Haulatu?"
Ba ta kai ga cewa wani abu ba sai ga muryar Momin Khaleefa ta shigo a fusace.
"Ina take? Ina marar kunyar yarinyarnan ta ke? Wato don ta cika fitsararra ta kama min ɗiya da bugu har ta ji mata ciwo akan ɗa namiji ko? Wannan mugunta har ina? To mu kam kaf zuri'arnan ba mu taɓa ji ko ganin abu makamancin wannan ba."
Magana ta ke yi murya a sama, ga tawagar da suka biyo ta a baya ganin yanda za ta kaya sai ko na falon sama su Anti Ihsan da tsararrakinta na gidan.
"Haba Hajiya Rahama, me ya kai na waɗannan zantukan marasa tushe? Ina laifin ma ki tsaya ki ji meyafaru. Sannan duk munin abin ai bai kyautu ki munana kalamai ga Haulatu ba."
Cewar Maman Zaituna cikin ɓacin rai.
"Bar ta Nafisatu, ƙyaleta ta gama. Rahama ko? Daidai nake da ita, bar ta ta cigaba da fitsarar da ta zo yi don an taɓa ɗiyarta."
Shaf Momin Khaleefa idanunta ma sun rufe ba ta ko kula da Hajja ba sai a yanzun da ta ji muryarta. Kawai sai ta juya ta fice daga falon tana sababi. Hajja kuwa tuni ta fusata ta hau faɗa wai don an taɓa Jannat shi ne ita mai ƴa ta zo. Faɗi ta ke.
"Toh yau idan soyayya shi Sadaukin ke yi da Haulatun zan ga uban da ya isa ya hana aurensu yiwuwa. Aikin banza kawai. Ni Rahama har ta kai girman da za ta shigomin wuri ta yimin tsaye a ka tana rashe-rashen kunyarta? Da ni take zancen. Idan ita ban isa da ita ba ai shi Daudan (Dawud, mahaifin Khaleefa) daidai nake da shi. Mahaukaciya kawai."
Haka Hajja ta yi ta sababinta ana rarrashinta, ita kuwa Maman Zaituna sai ta ja hannun Haulatu suka nufi sama. Anan ne ta ji duk abin da ya wakana tsakaninsu har irin amsar da ta ba Jannat, ba ta ɓoyemata ko harafi guda ba. Ta ƙara da faɗin.
"Don me ba za'a bar jingina ni da mahaifiyata ba da kalmar bariki. Mu ne muka yi barikin ko kuwa? A cikinmu babu ɗan bariki, don an ga kana shiru shikenan sai kowa ya kwasa bolarsa ya watsamana?"
Maman Zaituna ta rungume ta tana rarrashi cike da tausayawa kafin ta ɗago ta.
"Ya isa haka my dota, yi shiru abinki. Komai zai wuce. Abu ɗaya nake so na sani, dagaske ku na soyayya da Abeed?"
Girgiza kai Haulatu ta yi tana ɗan lumshe idanu hawayenta na zuba. Babu abin da ke yawo a ƙwayar idanun face kyakkyawar fuskarsa a sadda ya ke mata murmushi da kuma tausassan muryarsa sadda ya furta mata kalmar ban haƙuri.
"Aa, babu komai tsakanina da shi."
"Kin tabbata?"
Ta amsa da eh tana gyaɗa kai. Maman Zaituna ta sauke ajiyar zuciya.
"To Alhamdulillah, na yi murna da jin hakan ƙwarai. Koda ma ace ku na soyayyar ne, Abeed yaron kirki ne ba zan ji rashin daɗi na alaƙarku ba. Kuma na tabbata za ki yi farin ciki da shi daidai gwargwado in sha Allahu. Sai dai ni yanzu na fi ƙaunar ɗiyata ta yi karatu ta san ƴancin kanta. Ba ƴanci na bijirewa fadin Allah da Manzonsa (s.a.w) ba, a'a, a karon kanki ki san da cewa ke ma kina da wani matsayi da martaba a rayuwarki, Allah da kansa ya girmamaki matsayinki na ɗiya mace. Wasu abubuwan da suka faru a rayuwarki duka har da rashin ilimi. Koda ace ba a hannuna za ki yi karatu ba kamar yanda nake kwaɗayi, to ko anan ɗin ma ki maida hankalinki kin ji ko? Nasan ba za ki ba ni kunya ba."
Suka yi wa juna murmushi. Umma ce ta shigo ɗakin don hayaniyar ƙasan ya ishe ta, anan Maman Zaituna ta labarta mata yanda komai ya faru ita dai Umma murmushi kawai ta ɗan yi. Ta ce Allah ya kyauta daga nan ba ta ce uffan ba ta shiga banɗaki, ita kaɗai ta san ciwon da ƙirjinta ke yi ga kuma kanta dake sarawa. Taron sai ya ƙara haifar da gutsuri tsoma akanta da ɗiyarta.
***
Sadauki ba shi da labarin komai don bayan fitar Haulatun shi ma ta ƙofar baya ya bi ya fice daga gidan. Masallaci ya nufa koda aka idar da sallah sai bai dawo ciki ba suka zauna a nan ƙofar gidan suna hira da Khaleefa da wani abokin Khaleefan da ya tarar da su a tsaye. Wayarsa kuma tana silent don haka al'adarsa take muddin zai shiga masallaci to fa ba ya barin ko vibration ne ballantana ringing. Wannan ya saka har wayewar gari bai samu labarin abin da ake ciki a gidan ba. Sadda ta koma ɗakinsa ya tarar da missedcalls din Momi Nuratu da ma na Mamin Khaleefa dare ya yi.
Washegari da safe kuwa, Momi Nuratu sam ba ta ce masa komai ba don ita haka Allah ya yi zuciyarta, ba ta iya kwana da abu a rai ba. Sai ma da ya ce mata ya ga kiranta kuma dare ya riga ya yi sannan ta tuna dalilin kiran. An tashi da shirye-shiryen kamu yasa kawai ta ce mishi babu komai ya je za'a kawo masa abin kari.
Sadauki dai bai ji komai ba sai a bakin Mu'az da suka haɗu a hanyar zuwa ɓangaren Alhaji. Mamaki sosai ya yi.
"Shi wannan hayaniyar duka dai a kaina a ka yi shi?"
Mu'az ya taɓe baki. Babu abin da ya ɗan sosa ransa sai na zargin soyayyar da aka ce Sadaukin na yi da Haulatu.
"Haka dai abin ya kasance. A iyaka sanina kuma babu komai tsakaninka da ita. Hakane?"
Sadauki bai ba shi amsa ba face cigaba da tafiyarsa da ya yi fuskarsa ba yabo ba fallasa. Nan ma wurin Maama ya ji ƙarin bayani tiryan-tiryan na yanda Jannat ta danganta Haulatu da bariki. Sai ya ji zuciyarsa ta ƙara zafafa.
"My son, dagaske ne kana sonta?"
Tambayar Maama ya sa shi ɗago idanunsa da suka kaɗa don ɓacin rai ya dube ta.
"Ka yi shiru." Maama ta ƙara furtawa tana dubansa a nutse. Ya kauda kai daga duban Maama kafin ya ce.
"Maama karatunta fa?"
Murmushi ta ɗan yi.
"Tambayar da na yi mala, ka na sonta?"
Ya ɗan ciji leɓɓansa na ƙasa kaɗan kafin ya soma magana a tausashe.
"Duk son da zan yi mata, ina kaunar ta nemi ilimi. Wannan ne dalilin da yasa na fi buƙatar na nemi yardarta yanda mu'amalarmu zai zama ba wani ne ya yi mata dole a kaina ba. Ba na mata so irin na ko ta mutu ko ta yi rai lallai sai ta zauna da ni. Na fi muradin ta ƙaunace ni domin kanta ba wani ya tilasta mata ba. A taƙaice dai, ina sonta Maama."
Ya ƙarashe yana mai ɗan sunkuyar da kai. Maama tun da ya fara aman abin da ke binne a zuciyarsa murmushi kawai ta ke yi tana kallonsa. Koda ya kai aya sai ta furta hamdala a fili. Ta ƙara da faɗin.
"Na jima ina maka kwaɗayin auren Haulatu. A yanzun da na ji hanzarinka da ya sa ka zaɓi jan bakinka ka yi shiru, sai na ƙara jin kwaɗayin lamarin. To Allah ya shige mana gaba, ya sa rabonka ce ta alheri."
Sadauki ya yi murmushi yana mai motsa leɓɓansa da furucin amin. Daga nan suka yi sallama. Maama ta miƙe ta fito waje zuciyarta cike da walwala, haƙiƙa ta ji daɗi kwarai na amsar Sadauki tana kuma fatan alheri gare su.
Sadauki kuwa can wajen Baba Alhaji suka haɗu da Mu'az don dama sun rabu ne akan zai je ya yi magana da Maama.
***
Gidan gaba ɗaya ana ta shirin fita kamu da yini a babban ɗakin taron biki da aka kama mai suna Paramount Event Centre. Haulatu gaba ɗaya ta sake don Maman Zaituna sam ba ta yarda ta bar ta hakanan ba walwala ba, tun a jiya take nan nan da ita ga ita kanta Zaitunar da kuam su Safina waɗanda ke nunamata ta watsar da lamarin Jannat.
Shiri sosai kowa ke yi, ankon sisters daban domin iyaye fasa ankon aka yi kowa ya saka na shi. Hakanan na ƙawayen Amare ya fita daban. Sai dai kowa ya fi ganin kyawun na sisters ɗin, atamfa ce mai adon ja da ruwan madara.
Ɗinkin Haulatu da su Safina iri guda ne, riga doguwa mai ado a wuya da hannuwa sai kuwa daga can ƙasa. Ta dubi kanta a madubi, ita kanta ta san ta yi kyau ga makeup da Zaituna ta yi mata a fuska don sosai ta iya kwalliya. Sai dai ba sana'a ta ɗauke shi ba don a yanda ta nunawa Haulatun ma, sanadin Zaid ta koya tun tana Katsina da ta ji ya taɓa cewa shi ire-iren kwalliyar na burge shi. Haulatu ta jinjina abin a rai, zuwa lokacin ta rage mamakin irin son da Zaituna ke yiwa mutumin da a ganinta sam bai cancanta ba. Ita kanta Zaitunar ta yi kyau ainun, riga da siket ta yi na ƙawaye don ta rantse ita cikin ƙawaye take tunda dai Batulu ƙanwar Mu'az ƙawarta ce sosai. Ta su atamfar ruwan madara ce da baƙi. Amma sai kushewa take yi tana cewa ita da ace ma ta san tun farko na Sisters aka siyamata. Ta ci alwashin kafin Allah ya ƙaddara komawarta Malaysia sai ta siya don ta burge ta.
"TubarakAllah Masha Allah."
Ta faɗi tana ƙara duban Haulatu bayan ta gama yi mata ɗaurin kallabi. Ita kuwa ta hau farr da idanu tana ɗan jujjuyawa suka yi dariya. Mayafin ma kalar ja, a kafaɗa aka ɗan naɗe shi aka ɗora. Ƙaramar purse ɗinta ja hakanan takalmin.