Showing 84001 words to 87000 words out of 177840 words
Duka iri ɗaya da su Safina, su kuwa Maman Safina ce ta siyamusu.
Tare suka fito daga ɗakin su Zaitunan. Da Matar Uncle Abba suka soma kiciɓus, ita dama kullum fuskarta a tamke haka yanayinta yake, da kallo kawai ta bi su amma babu ko yabawa. Ita ma ta ci nata gayun cikin leshinta kore.
"Ita dai wannan matar kamar tana shan yis, kullum fuska a kumbure." Faɗin Haulatu da murya ƙasa-ƙasa, suka yi dariya har ta tsargu ta juyo amma ganin ba kallonta suke ba sai ta yi gaba. Baba Saude kuwa har da su guɗa tana yi musu kirari da manyan mata, jikoki ga Hajja. Farin wata masu haskaka duhu. Su dai murmushi suka yi, su Umma tuni sun tsufa a wurin taro, babu kowa a falon sai sa'annin Hajja, su ma sun cakare daidai nasu suna jiran mota.
"Haule, Zaitun, ku ne kuwa? Ikon Allah, kamar daga wata duniya ku ka ziyarce mu? Irin wannan kyau haka?"
Aka yi dariya, idan ka ɗauke Haulatun da Zaituna masu ɓata ran sunan da Hajja ta yi kiransu da shi.
Safina da Radiya ne suka shigo, a kusan tare suka ce Wow! Gami da ƙarasawa su ɗan rungumi ƴar uwarsu.
"Kai kun yi kyau wallahi, shegiya kin ganki kuwa?"
"Kul! Ke Radiya ki fita idona, ban hanaku sheganta kanku ba?" Cewar Hajja daga zaune don fes ta ji su. Suka yi waje suna ƙunshe dariya, Radiya na kira Sorry Hajja. Don dai yanzun albarkacin Haulatun ba kunya su ma takan ja su da wasa kai ka ce ba Hajjar da suka sani mai zafi da tsauri ba.
Suna isa farfajiyar gidan inda da yawa sun wuce wasu kuwa na tsaye ana jiran mota, Zaituna dai ta bar su a nan ta wuce tawagar ƙawayen Amarya su Jannat. Haulatu na tambayar to su yanzu wace motar za su biɗa, tambaya take ko dai ta gwada kira musu Yaya Mu'az ya kai su? Amma kallon da ta ga Safinar da Radiya na bin ta da shi ya sa ta dakata da maganar gami da watsa musu harara.
"Ban ciki da iskanci. Wannan kallon fa sai ka ce yau ku ka taɓa gani na?"
"Ai ba su ba, ni ma haskakamin fuskata ki ka yi na bar taron waɗancan manyan na yo wajenki." Ta ɗaga idanu ganin Haidar ta kai masa duka da purse dinta, ya kauce yana dariya.
"Kai! Ai ni da nasan kin fi Bebina kyau da ke na lallaɓa ma ki yarda ki jira na kammala jami'a mu yi aure. To mene don na ba ki shekaru uku kacal a duniya?"
Suka yi dariya idan ka cire Haulatu da ta ja guntun tsaki.
"Yaya Haidar mu dai don Allah mota muke nema." Faɗin Radiya kenan tana marairaice masa. Ya jinjina kai
"Hum um, an gaisheku kun ji. Ni kaina neman wanda zai kwashe ni nake, idan ban samu ba sai na lallaɓa na ja Lifan ɗina ya kai ni. Amma yanda na ci wanka ai ba girma na hau Lifan."
Haka ya yi ta zuba musu hira, kowa ya zo wucewa sai ya tanka Haulatu kafin a yi jam'u a haɗa su duka ukun a tanka. A hankali fadi suka masha Allah tubarakAllah.
Ya yi daidai da shigowar motar Yaya Sadauki gidan, a bayansa kuma motar Mu'az.
"Ke Safina ga mutuminki nan Yaya Mu'az, na tafi, ku roƙe shi ya kai ku. Kun san dai shi Boss ko giyar wake ku ka sha, ba zai ɗauki manyanku su Jannat ba ballantana ku karan kaɗa..."
Bai kai ƙarashe ba sakamakon hon ɗin da suka ji da ya ɗauki hankalin jama'ar dake wajen, ƙirjin Jannat hsr ɗan bugu ya yi da ta waiga ta ga motar Sadaukinta ne ake zuba wannan hon ɗin. Sai kuma can shiru ya biyo baya, kowa dai ya zuba idanu ba kamar Jannat da take jin kamar idanunta za su faɗo ƙasa don kallo, jira take ta ga da ya tsaya a filin farfajiyar gidan bai karasa wurin parking ba, wa ya zo ɗauka, shi kuwa Mu'az tuni ya fito ya nufi inda Mominsa ke tsaye tana jiransa da tawagarta. Farko sam ba ita ya yi niyyar ɗauka ba face Haulatu, so yake a yau kafin Sadauki ya riga shi cewa komai, ya kasance shi ya riga isar da saƙon zuciyarsa wanda bai gama tantance shi ba sai a daren jiya da ya gama sauraron ɗan hatsaniyar da aka yi akan Sadaukin. Ya na tsoron ya tabbata Sadauki na son Haulatu. Idan har ya riga shi furtawa to zai iya ji har a zuciya ya haƙura. Amma muddin ya samu yaƙinin cewa babu komai tsakani daga ita Haulatun, anan ne zai bajakolin soyayyarsa a wurinta, har ransa yana ji haƙansa zai cimma ruwa.
Wayar Haulatu da ta ɗauki kara ta duba. Sunan Yaya Sadauki ta gani ɓaro-ɓaro. Ƙirjinta ya ɗan buga, ta dubi motar kafin ta ɗaga. Bai ba ta damar magana ba ya tari numfashinta.
"Da ke da sauran aljanun da ku ke tare, ku zo."
Daga haka ya katse kiran. Ta dube su, dama kunnuwansu na ga wayar da take yi, shi ma Haidar ya saki baki da hanci da kunne yana son jin me za ta ce. Ta kama hannun Radiya dake tsaye daga damanta.
"Yaya Sadauki na kiranmu."
Jin haka suka ruɗe, Safina kira take yi mun shiga uku. Haidar kuwa cewa ya ke yi, ai fa shikenan, bye bye, ku je zan baku labarin yanda ta kaya a gidan bikin. Babu ku babu cin Meena's Bites."
Ko kallonsa basu yi ba don ba wannan nutsuwar suka ɗunguma ga motar Yaya Sadauki wacce gaba ɗayanta tinted glass ne a jiki sai gaban kawai da babu. Suna isa ya bude gidan gaba, ya dubi Haulatu.
"Get in."
Ba musu ta shiga, su Safina kuwa ya ba su umarnin shigewa baya. Nan ma duk suka zauna ya rufe ya yi ribas da motar ya fice daga gidan. Fuskarsa babu ɗigon fara'a, ga shi nan dai ya sha gayunsa cikin wani tsadaddan yadi baƙi da ya fiddo da hasken fatarsa muraran. Hularsa na ajiye daga saman wurin sitiyari, tuƙi kawai yake yi da hannu ɗaya.
Fitarsu ya sa Jannat jin zuciyarta kamar za ta buga, ta yi baya sakamakon jirin da ke ɗibarta Allah ya taimaka Zaituna da wata ƙawar Jannat ɗin dake tsaye a baya suka ɗan tare ta. Nan fa wuri kuma aka hau ƙus-ƙus din Yaya Sadauki, wato dai ya yi abin da ba ya daga halayyarsa, ɗaukar ƴan biki. Shi karƙari iyaye, sam ba ya bari ƴanmatan ƙannensa su hau mishi mota. Kowa faɗi yake anya ba son Haulatu yake ba, tunda dai sun san kafin zuwanta ai bai kalli inda su Safinar suke ba kuma banda haka ma ita ce a gidan gaba. Zaituna kuwa ta ji wani sanyi a ranta, tunawa da abin da ya faru jiyan tsakanin ƙanwarta da Jannat ɗin, ko babu komai duniya sun shaida wanda ake so da wanda ke son.
Mu'az da ke ƙokarin tayar da motarsa bayan matsowar su Mominsa, sai da ya ji wani abu ya daki ƙirjinsa, ransa idan ya yi dubu ya ɓaci. Me Sadaukin ke nufi? Dagasken wai yana son Haulatu ko kuwa dai ganin damar ɗaukarsu ya yi?
Babban burinsa Mominsa da ƙawayenta su hau ya bi bayan Sadaukin amma sai ya ga sun tsaya su na maida maganar ko me Sadaukin ya gani a jikin Haulatun da ya soma bin ta kamar jela?
***
Shi kuwa can ya furzar da huci, ita ma Haulatu ta ɗan yi ajiyar zuciya, ta juya da nufin satar kallonsa, aka yi katari a sannan shi ma ya ɗan karya wuya kaɗan ya dube ta. Ta yi saurin kauda kanta. Yamutse fuska ya yi.
"Ku yanzu don rashin ta ido sai ku je gidan biki a haka mayafi kamar abin tatar koko kun saƙale shi a kafaɗa ko? To wa za ku burge? Saurayi za ku je nema?"
Suka yi shiru babu wanda ya ce uffan don tsoron maganar ma suke, ita kuwa Haulatu kirjinta ke bugu da ba ta san dalili ba, duk dai a yanzu sadda za ta haɗu da shi wuri guda sai ta ji wannan bugun. A gefe guda ta tuno Jannat da ta yi ido huɗu da ita sadda take ƙokarin shiga gaban motar Yaya Sadauki kawai ba ta san sadda murmushi mai dan sauri ya suɓuce mata ba. Safina da Radiya suka waro idanu, Safina dake zaune daga bayanta ta ɗan ja rigarta ta gefen ƙofa. Nan da nan ta shiga taitayinta, duk suka dube shi jin bai ce komai ba, sai ma murmushin da suka ga ya ɗan yi.
Har suka ƙarasa wajen bikin bai ƙara magana ba, koda ya yi parking ya dubi Haulatu.
"Oya, maza ku gyara zaman mayafan idan kuwa ba haka ba yanzu zan juya na maida ku gida."
Ai kan ma ya ƙarasa suka hau gyara. Haulatu duk ta kusan susucewa don har ta kammala bai kauda kai daga kallonta ba. Ya zura hannu a aljihunsa ya fiddo chanji ƴan hamsin hamsin yana fadin.
"Na sani, ba ku da ko sisi sai efizzy."
Su dai ba su saba ba don haka suka yi shiru, ya miƙawa Haulatu.
"Ku riƙe."
"Yaya mun gode." Faɗin su Radiya suna fita daga motar, Haulatu ta ji ta wajenta a rufe don haka ta juyo ta dube shi da idanunta masu ƙara tsuma shi yana ɓoye yanayinsa.
"Ya ƙi buɗuwa." Ya ɗan matse fatar leɓɓansa wuri guda yana mai jinjina kai.
"Ok. Please ban da rawa da rawar kai. My eyes on you."
Ba ta da nutsuwar fassara zancen kawai ta bishi da toh. Sadda ya bude ta zura ƙafa guda za ta fita ya ce.
"Kin yi kyau."
Sai da ta juyo ta dube shi don ta tabbatar shi ya fadi, kalmar ta tafi da ita sosai don baki da idanu ta ware. Ba ta san sadda ta bishi da irin murmushin da ta ga ya jefa ta da shi ba. Ajiyar zuciya ta sauke, hakanan ta ji ta kamar a cikin ƙanƙara don sanyin jiki da kuma annashuwa.
"Nagode."
Daga haka ta fice da sauri ta rufe mishi ƙofar, Safina da Radiya burinsu kawai ta fito su shiga yanda za su samu damar gulmar abinda duk ya faru a hanya da ma yanzun.
Shi kuwa gyara parking ya yi yana yiwa kansa faɗa, ya kamata ya koyi haƙuri da danne zuciyarsa. Ya bi komai a hankali din. Can kuma ya ɗan wurga hannu ɗaya.
"To me na yi ma?" Ya yiwa kansa tambayar a fili.
Zaid da ke tsaye a farfajiyar wajen tsaf ya kula da abinda ke faruwa, wani irin huci ya shiga furzarwa. Haulatunsa ce a motar mutumin da ba sa ga maciji? Me wai ma hakan ke nufi? Sadaukin sonta yake ko kuwa soyayya suke yi? Ya ji ransa na tuƙuƙi yana mai cin alwashin ko shi ko shi. Ba zai taɓa haƙura da Haulatu ba, su zuba su gani.
***
*Littafin nan na kudi ne. Ki siya ki karanta hankalinki kwance gudun shiga haƙƙin marubuciyar.* *Ibrahim Rufaida Umar, *9034973645 Opaybank.* *₦500* *Idan kin biya ki aiko shaidar biya ta 09034973645*
*****************
Ba ma iyakar rawa ba, motsin arziki Haulatu kasa yi ta yi, su Safina kuwa shiru suka yi don tun shigowarsu suke jifan Haulatu da tambayar ko dagaske Yaya Sadauki na sonta amma kamar kurma. Munira wacce ta riga su zuwa sai tambayarsu meyafaru take yi? Radiya ta labarta mata. Murmushi ta yi.
"Dama ai na faɗamaku zai wahala idan ba sonta yake yi ba. Ita ma ga dukkan alamu tana sonsa."
Sai a nan Haulatu ta dube ta gami ɗan harara.
"Ni na faɗamaki? Ko shi ne ya sanar da ke?"
Suka yi dariya, a hankali ita kuma ta sauke ajiyar zuciya, kalmar ta yi kyai da ya furta ta tuna bata san sadda ta saki wani lallausan murmushi ba. Wayarta ta yi ƙarar shigowar saƙo. Kasancewar an ɗan kashe sautin kiɗa MC na sanar da isowar Amare wajen.
_"Duk wanda zai maki so ba zai kai wanda nake maki ba._ Na shirya bayyana maki kaina a kowane lokaci daga gobe."_
Ta ja guntun tsaki, mutum ne da ba ta san ko waye ba, koyaushe saƙon safe daban da na dare, idan kuma ta kira layin sai kiran ya ƙi shiga tun sau ɗaya da ta kira aka ɗaga kuma aka yi shiru ba'a ce komai ba. Ta dinga raba idanu ko za ta ga Yaya Sadauki ya shigo amma har aka kammala aka watse babu ƙeyarsa. Koda suka fito ma babu motarsa a wajen, Mu'az ne ya zo inda take a tsaye don a lokacin su Safina na can ana ta hotuna kamar wanda aka yi a ciki bai ishe su ba. Ta waigo ta dube shi kafin ta sauke ajiyar zuciya.
"Au, ashe kai ne."
Ya ɗan ɗagamata gira kaɗan.
"Ki na expecting wani ne?"
Ta girgiza kai. Shi kuwa ya jinjina na shi kan.
"Ok. Wai ke kin ma san matsayinki a zuciyata kuwa? Rashin sanin hakan ne yasa ki ke aikata abin da zai ƙonan raina ko?"
Kanta ya ɗan ɗaure, me yake son ya ce toh?
"Ban fahimci inda ka dosa ba Ɗan birni?"
Ya girgiza kai.
"No, ba za ki fahimta ba ai, zan fahimtar da ke sosai. Gobe mu haɗu mu yi maganar. Idan ma bai samu ba sai na kira ki a waya."
Yana kai wa nan ya yi gaba ganin su Safina sun tunkaro inda ta ke. Haulatu kuwa ba abin da ya faɗomata a rai face saƙon da aka turo mata ɗazun. Gobe? Mu'az ya ce za su yi magana gobe? To ko dai shi ne mutumin dake turo mata saƙonnin soyayya a ɓoye? Idan shi ne da wane idanun za ta dubi Safina? Ranta ya ɓaci ainun, ta shiryawa duk abin da zai faru a goben, za ta ba shi mamaki fiye da zatonsa, ita zai yiwa wasa kwakwalwa? A tunaninsa za ta so shi ne? To ai ko babu Safina cikin alaƙarsu ba ta taɓa yi mishi wannan kallon ba. Ta yi ƙwafa da ya sanya Safina dubanta.
"Lafiya kuwa? Wani abun ya faru? Dama na ga Yaya Mu'az ya bar wajenki yana cin magani. Ko faɗan da ku ka saba yi ce ta motsa?"
Sai ta ɗan ja guntun tsaki gami da wayancewa.
"Rabu da shi, ai shi ba ya son zaman lafiya. Ɗan rikici ne kamar Mominsa."
"Abin har da cin fuska? To ba na son haka." Fadin Safina tana ɗan harararta. Ita kuwa sai ta ɗan yi murmushin yaƙe.
***
Washegari aka ɗaura auren Raudha da Batulu. Raudha anan garin Katsina za ta zauna ita kuwa Batulu ɗan Kano ta kwaso. Kowa fuskarsa cike da walwala. Abokan angwaye sun shigo an gaisa da iyaye, yayyunsu sun sha shadda kowanne da kalarsa sai dai masu fari sun fi yawa. Haulatu leshi kalar silver, ta sanya suka yi anko da Zaituna, Maman Zaituna ce ta ɗinka musu, ta yi adonta cikin sarƙar da Sadauki ya kawomata tsaraba sadda ya yi tafiya. Sam ranar ta tashi ne babu wani kuzari, da damuwar wai Mu'az ke turomata saƙo a waya ta kwana ta tashi, tun jiya ta ke kwaɓar kanta cewa kar ta sake ta ba shi amsa har sai sun haɗu ido da ido. Shiyasa ana ta hotuna a falon Hajja da Amare amma ita ko shiga ba ta yi ba, tana tsaye kawai daga ƙafar bene ta ɗan riƙe ƙarfen tana kallon jama'a wanda kaf cikinsu babu Sadauki babu Mu'az hakanan ba ta ga Khaleefa da Zaid ba, ba ta sani ba ko don su ne manyan yayyun, girman suke son kamawa. Jifa-jifa kuma tana kallon wayarta jiran shigowar saƙon mutumin da ta ba kanta cewa Mu'az ne. Ai kuwa ko mintuna uku ba ta yi daga ɗauke kanta daga saman wayar ta ji saƙon ya faɗo.
"Ki same ni a wajen rumfa."
Ta sauke ajiyar zuciya har tana ɗan hura hanci. Ji take yi ta shiryawa komai. Daidai ta ke da Mu'az, ita ba ta son halin yaudara, hatta da saƙonnin da ya dinga aikomata da wata lambar a ɓoye ta saka a rai cewa yaudara ce zallarta.
Ficewa ta yi ta ƙofar kicin ɗinsu don ta fi saurin zuwa lambun. Babu mutane sai yara dake ɗan tsalle-tsallensu. Tun kan ta ƙarasa ta hango shi ya juyamata baya yana zaune daga saman dakalin da ya zagaye rumfar ta farko, farar shadda ce jikinsa babu babbar riga, sai ko hula da ya ɗora a ka. Sam ba ta gane waye ba, kawai idanunta ya rufe da tunanin Mu'az ne. Yana daga zaune ba don haka ba da ta kula wannan ɗin ya fi shi tsayi da ma.
Tun sadda ta hango fuskarsa kafin ta kai ga ƙarasa shiga rumfar, sai ta yi saurin ja baya.
"Yaya Zaid ina wuni." Ta gaishe shi kuma ba ta jira me zai ce ba ta juya da nufin tafiya don ita bilhaƙƙi ba ta kawo shi ba ne amma ta ji ƙirjinta na dukan tara-tara cike da fargabar kar dai ace shi ne mai aikamata saƙonnin ba Mu'az ba?
Gani ta yi ya sha gabanta. Idanunsa gaba ɗaya ya shigar cikin nata a ƙoƙarinsa na aikata da saƙonnin da suka jima a ƙoƙon ransa. Ya ɗan narkar da murya.
"Please yau ki ba ni dama mu yi magana ido na ganin ido."
Haulatu ta waiga hagu da damanta, kafin cike da tsantsar mamaki ta ɗago mishi fuskar wayarta duk da babu abin da ta buɗo, baki na rawa ta ce.
"Kai....kai...ne?"
Ya ɗan lumshe idanu ya buɗe su a cikin nata. Kamar mai raɗa ya amsa.
"Yes, ni ne. Duk saƙon da kike receiving ni ke turowa. Na fara sonki tun ganin farko da na yi maki a rayuwata. Na rasa ta hanyar da zan bi na ɓullo maki, dalilin kenan da na zaɓi ragewa kaina damuwa ta hanyar turo maki saƙonnin da ke nuni da bayyana zuciyata gareki. Sai dai na ga hakan kamar ba zai haifarmin da ɗa mai idanu ba, wannan dalilin ya sa na yanke shawarar tunkararki kai tsaye na sanar da ke ina sonki, ina kaunarki. Ba na jin rayuwata za ta cika idan babu ke a cikinta."
Ita dai kamar an shuka ta, kallonsa kawai ta ke