Showing 111001 words to 114000 words out of 177840 words
neman zaɓin Allah."
"Hakan ya fi maki, Allah ya yi mana zaɓi na alkhairi." Faɗin Radiya karo na biyu, suka amsa da amin.
Wannan batun ne ya kore tambayar da suke jiran amsarta daga Haulatu, suka hau hirar saurayin Radiya wanda ya ce zai turo da zarar sallah ta wuce.
Sai wuraren tara na dare suka rabu da junansu, nan ma sai da Umma ta dokawa Haulatu kira akan ga dawo dare ya fara kafin su yi sallama da juna. Tare suka fito Radiya ta yi nasu ɓangaren ita ma ta nufi ɓangarensu.
Tana tafe tana tunanin maganar da Safina ta yi akan wai Mu'az ya sanar fa Maama yana da wacce ya ke so a cikin family. Kamar an ce ta ɗago daga kallon ƙasa da ta ke yi ta hango shi ya na nufo ta. Nan da nan ta tamke fuska ta ƙara sauri.
"Wannan gujemin da kike yi, ba shi zai sa na fasa niyyata na kai maganarmu gaban iyaye ba."
Cak ta ja ta tsaya, kenan ta tabbata ita Mu'az ke nufi zai gabatar matsayin wacce ya ke so? Ta juyo tana murmushin takaici gami da watsa mishi kallon ka yi kaɗan kafin ta soma magana.
"Ni dai ka ke nufi? Toh bismillah, ai ga fili ga mai doki. Ina ce a gidannan ba a auren dole ko? Kuma ba za'a fara a kaina ba Yaya Mu'az, ni na san wannan. Ka je ka tunkari duk wanda ka so tunkara da zancen aurena."
"Me na yi maki kika tsane ni wai Haula baby? Me ya yi zafi har haka? Mene ne laifina don na ce ina sonki please? Ba ki da tausayi wai?"
Ta harareshi da haushin kirata Haula Baby da ya yi.
"Haulatu ne sunana. Daga kai har Yaya Zaid na rantse ku fita idona in rufe. Na ce maku bana sonku, ai idan ma kai kana da tausayin Yaya Mu'az, ya ci ace ka tausayawa Safina tunda na san ko ba a fadi ba ka san tana sonka. Mace ce mai kunya da kauda kai, hakan ya sa ka zaɓi nunawa duniya ba ka fahimci tana son naka ba. Kuma ni yanzu ba na mata fatan ma ta aureka don ba ta dace da kai ba, zan fi kaunarta da wanda ya san tana sonsa kuma ya girmama wannan son."
"Wait, Safina ke sona? Dama saboda ita ce ki ka juyamin baya? Kuma ma wane Zaid din? Zaid ke sonki? Wow!"
Ya ƙarashe da jin mamaki da wani murmushi mai ciwo har yana ɗan tafa hannuwa.
"Wannan kuma matsalarka ce. Sannan ka sani da Safina da babu ba zan taɓa sonka ba."
Tana kai wa nan ta juya a fusace ta bar shi da bin ta da kallo. Ganin babu wani amfanin tsayuwar tasa ga su Najeeb a gefe da ke hira da musun ball daga can ƙofar gidan tare da abokansu, ga dukkan alamu ma sun hankalta da su a tsaye. Sai ya juya ya bar wurin gwuiwa a sake. Lallai dagaske ne a baya yana tunanin Haulatu ba ta sonsa, amma kuma a yanzu a wautarsa sai yake hangen ai tana sonsa kawai dai ta sadaukar da soyayyar ne ga aminiyarta da Yes! Ya sani ya jima dama yana zargin tana sonsa, kawai dai kunya da tsoro sun hana ta gwadawa. Ji ya yi yanzu ne zai fara yaƙin, tabbas idan har aure ya ƙullu tsakani zai yi duk iyakar yinsa ya shawo kanta ta karɓi soyayyarsa. Wannan duka mai sauƙi ne tunda dai kamar babu batun Sadauki. A ganinsa.
***
Washegari aka tashi da azumi, Umma na zaune bayan idar da sallar duha tana lazimi wayarta ta yi ƙarar kira. Ba ta ko duba fuskar ba domin sam ba ta kaunar duk wani abu da zai katse ta a ibada. Haulatu dake kwance jiki duk a mace ne ta miƙe ta dauki wayar, ganin lamba ce sai ta ɗaga kawai ta kara a kunne.
"Na'imatu."
Muryar da ta ji ya sa ta ji wani ɓacin rai da takaici.
"Me za ka yi mata? Kiran me ka yi? Kuma a ina ka samu lambarta?"
Wadannan tambayoyin da ta jero ne ya sa Umma dubanta da tunanin waye kenan?
Dariya ya yi wanda har sai da ta ɗan dauke wayar a saman kunnenta don ji ta yi kamar ya watsa mata garwashi kafin ta mayar.
"Ko ba a fadamin ba na san wannan ɗiyata ce guda ɗaya tilo mai..."
"Kar ka ƙara! Nace kar ka ƙara danganta ni da kai! Ni ba ƴarka ba ce!"
Ji ta yi Umma ta karɓe wayar a hannunta. Ita kuwa Haulatu don takaici sai kawai ta fice zuwa falo ta yi zamanta tana jijjiga jiki cike da ɓacin rai.
Umma kuwa daga daki ta soma magana.
"Kiran me ka yi min Ibrahim?"
Ya yi ƴar dariya karo na biyu.
"Ai bai kyautu ace kin yi min wannan tambayar ba Na'imatu. Ko babu komai kin sani akwai ƴa a tsakaninmu. Haƙƙina ne na dinga tuntuɓar lafiyarta da ma kula da rayuwarta. Sannan Na'imatu ki yarda sakin da nayi maki ba a son raina na yi shi ba. Ina sonki ina.."
"Ya isa Ibrahim, ba shi na ke son ji ba. Tambaya na yi kuma ka amsamin. Ban hana ka tuntuɓar komai na ƴarka ba duk da cewa ba ka da wannan damar don tuni ka yi watsi da ita. Sai dai tunda har da shi ka fake, ka nemi lambar Alhaji Ridwan kamar yanda ka nemi nawa ka dinga kira a can. Babu wata alaƙa da ta yi saura tsakaninmu Ibrahim. Koda wasa kar ka ƙara kirana."
Daga haka ba ta ko saurari abin da zai ce ba ta katse wayar, gaba daya ma sai ta kashe wayar. Ita ta sani ai, Ibrahim Ɗan Mutuwa magana ba ta wuce ba a wurinsa. Sai ya zo da wani rainin hankalin. Tana shirin fita falon don duba Haulatu sai ga Hajja ta fado dakin.
"Ke, wa Haule ke cewa ya kira? Maza ban wayar nan. Mu zai kawo wa iskancin banza da wofi?"
Yanda Hajja ta fusata sai Umma ta kwantar mata da hankali da nunamata ta yi maganin komai. Duk da haka Hajja sai da ta karɓe wayar Umman tana fadin daga yau ta bar amfani da layin.
***
Engr Faisal ya yi shiru can kuma ya dubi Mu'az wanda ke russuna kai cike da jin nauyin abin da ya fito a bakinsa.
"Ita Haulatun Hajjah ka ke so?"
Ya kasa furta eh sai shiru. Murmushi Engr Faisal ya yi.
"Toh masha Allah. Ai ƴar uwarka ce. Kun daidaita ne da ita?"
Da tsananin farin ciki ya girgiza kai.
"A'a Abba, ta nunamin karatu take son yi ne."
Engr Faisal ya ɗan yi jim kafin ya ce.
"Kana nufin ba ta amince da kai ba?"
Mu'az ya ɗan yi shiru, idan fa ya ce ba ta amince ba shikenan zai yiwa kansa ko? Ya sani dagaske a zuri'ar babu batun auren haɗi, sai idan kowane ɓangare ya ji ya gani yana so da kauna, idan kuwa ba haka ba, haƙura ake yi. Ya gwammace ya nunawa Abbansa ta amince hakan zai fi.
"Abba ta amince."
Murmushi Engr Faisal ya yi.
"Toh Alhamdulillah. Allah ya shigemaku gaba. Duk da haka ni ba zan ce komai a kai ba, ka je ka samu iyayenmu ka sanar da su. Allah ya tabbatar da alheri."
"Ba amin ba!" Suka juya jin muryar Momin Mu'az.
"Hajiyayye, kina cikin hayyacinki kuwa? Ki faɗomin babu sallama falo, kuma ki amsamin addu'a da salo na rashin ɗa'a?"
Engr Faisal ke zancen a matuƙar fusace ya na duban Momin Mu'az da ta ƙaraso tana hura hanci. Jin muryarta ne ma ya fito da Amarya daga ƙuryar ɗaki, ta ci adonta tsaf cikin leshinta mai farin da ruwan toka, irin dai na zuwa turakar miji. Wani banzan kallo Momin Mu'az ta watsamata jin tana tambayar ko lafiya tunda ita kam ba ta ji komai ba face muryar abokiyar zamanta tana magana a ɗage.
"Toh ke kuma gwana? Uban me ya fito da ke? Salo na munafunci? Mtsw, kai kuma wato duk jan kunne da kashedin da na yi maka game da fita harkar waccan karuwar yarinyar bai shiga kunnenka ba sai da ka saɗaɗo ka zo ka kawo wa babanka zancen? To idan dai ni Lubabatu ni na durƙusa na yi naƙudar Mu'azu, ban lamunce masa aurenta ba."
Injiniya Faisal ya ɗan sa hannu ya gyara zaman gilashin da ke fuskarsa.
"Ke a wa? Daga ke har shi ɗin a ƙarƙashin ikona ku ke. Kuma ki sani, aure babu fashi. Mu zuba ni da ke, zan nunamaki lallai ni Faisal na isa da gidana. Na kuma isa da ɗana. Tashi ka tafi Mu'az, ni da kaina zan nema maka auren Haulatu. In sha Allahu babu abin da zai hanaku aure muddin ku na son juna."
Nan fa Mominsa ta dinga zuba maganganu marasa dadi wanda ya ƙarawa Injiniya ɓacin rai da har ya yi mata tsawa wanda dole ta yi ɗif. Jiki na rawa ya miƙe tsaye tuni Mu'az ya bar falon don ya sani dole dama ya kirawo ruwa idan Mominsa ta ji wannan zance. Amarya dai na tsaye ta kasa magana don ita har mamakin abokiyar zamanta take a wasu lokutan.
"Na rantse maki ki ka sake ki ka ƙara magana a nan sai dai ki ƙarasa wunin yau a gidanku. Ki zauna don ba ki san mutuncin iyayena ba ki na faɗin maganganu a kansu? Ke wace irin marar tunani ce?! Don ina zubamaki idanu sai ki maida ni tamkar ban san me nake ba? Fice min daga falo tun ban saɓa maki ba!"
Ta shaƙa iya shaƙa, ta waiga ta ga Amarya dake tsaye, saboda tsabar takaici da haushinta da take ji sai ta ga kamar ma murmushi take. Kawai sai ta fice fuu har da banko ƙofar, wannan banka ƙofar Injiniya Faisal ya ji shi har a ƙasan ransa don haka ya yi ƙwafa kurum ya shige ɗaka. Amarya ba ta yi karambanin bin bayansa ba sai ta yi zamanta a falo, ta san hali, idan yana cikin ɓacin rai sam ba ya kaunar a ma gwada ba sa haƙuri, ya fi so don ka sa ya huce sannan ko maganar kar ka tayar, da kansa ya ke tayarwa idan ya matsu a ta yi din.
Ita kuwa Momin Mu'az a firgice ta shiga ɓangarenta, Nusaiba da ke taimakawa ƙannenta da yin homework ta bi ta da kallo. Ta sani akwai matsala don haka ta miƙe. Ita ce ta zamewa uwar kamar wata ƙawa, duk wani mugun hali irin nata babu ɗaya da Nusaiba ta bar shi.
"Momi lafiya?"
Ba ta ko kalle ta ba sai faman danna waya take amma ta kasa ma nutsuwa ta yi kiran wanda ta sa a gaba. Mamin Khaleefa ta ke son fesawa wannan mugun ƙulli da Umma suka shiryowa ɗanta. Ta miƙawa Nusaiba wayar tana zama a gefen gado kafafunta kamar za su fice daga ƙugunta tsabar yanda ta ke kaɗa su hakan ya ƙara mata zafin rai.
"Kiramin Hajiyar White House."
Sunan da suke kiran gidan su Khaleefa da shi kenan, saboda komai na fentin gidan daga waje fari ne gaba ɗayansa. Fentinsa ya sha bamban da na kowa. Yana kuma daga kan layin babban gida daga gefe.
Nusaiba ba shiri ta kira Mamin Khaleefa yana soma ƙara ta miƙawa Mominta cikin zuba kunne don ta ji me za'a ce. Ba tare da Momi ta damu da kerere din Nusaiba a kanta ba ta fara magana jin Mamin Khaleefa ta ɗaga da furta Hello.
"Hum, Hajiya Ƙarama, na shiga uku, Na'imatu ta shanye min ɗana."
Cikin nuna tashin hankali a murya, Mamin Khaleefa ke tambaya.
"Me ta yi maki kuma Hajiyayye?"
"Mu'azu ne ya haukace gaba daya shi nan duniya son Haulatu yake, duk irin barazanar da na yi mishi amma ko gezau har sai da ya sa ƙafa ya shure duk maganganuna. Yanzu shi Injiniya ya dage akan ko zan mutu aure babu fashi. Ni kuma na rantse muddin ina numfashi ko zan yi yawo tsirara ba zan haɗa jini da dangin karuwai ba. Yarinyar da ba a san salsalar haihuwarta ba."
"Kin min daidai Hajiyayye, ko ni ba zan taɓa aminta da haɗa jini da su ba. Ki tashi mu yi yaƙi, ni ma kuma zan taya ki daga nawa ɓangaren tabbas ba zai taɓa yiwuwa ba. Can ga su gada. Na fadamaki ai, ni dama tun ganin da na yiwa wannan ƴar banzar matar na san cewa ba hakanan ta zo ba. Haka kawai ta bi tana neman shanye mana yara fiye ma da Zakiyya (Maama)?"
"Uhm, ke dai bari kawai. Amma tabbas ban ga ta zama ba. Zan yi magana da Malam Shu'aibu, kinsan da zafi-zafi ake bugun ƙarfe."
"Tabbas, ki yi dukkan abin da ya dace, ni ma zan maki iyakar yi na ta ɓangarena. Amma fa sai kin iya takunki, ki danne ɓacin ranki kar ya haifar da kowace matsala."
Da haka suka yi sallama. Nusaiba da tun soma wayar ta fahimci inda zancen ya dosa ta yi kwafa ya fi a ƙirga, ita ma tauna zancen take, wai Yayanta na son rival ɗin ƙawarta kuma yar uwarta Jannat? Taɓ! Har abada ba mai yiwuwa ba ne. Hakan ta ayyana a rai.
***
A can White House kuwa, duk wayar da Mamin Khaleefa ke yi, yana zaune a gefe yana danna wayarsa, ya shigo ya tarar tana wayar kuma ba ta katse zancen ba. Bayan ta ajiye ta ƙara yin kwafa.
"Haka kawai, Na'imatu ta zo za ta shanye mana yara. Ku na neman fifita ta akan mu da muka haifeku? Wai ana zaune ƙalau yaron nan Mu'azu ya na neman janyo mana jafa'i a cikinmu. Ai har abada ba zamu amince masa haɗa iri da Haulatu jinin karuwai ba."
Maganar ta dake shi, dama ya ɗan ɗauki haske a wayar da ya tsinci Mamin tasa tana yi. Ya kuma gane a yanzu da Momin Mu'az suke zancen. Jikinsa ya yi sanyi haɗe da tausayin Umma da Haulatu. Wace irin tsana ce haka ne suka yi wa bayin Allahn da ba su ji ba su gani ba?
Jannat da ta shigo dauke da tray da ruwa da lemo a sama ta ajiye a gefen Khaleefa, tsaf ta ji abin da Maminta ke fadi tun tana waya don dama duka ita da kannenta uku ana zaune ne ana ta hira bayan sun kammala cin gashin kifi da aka yi don mahaifinsu Barrister Dawud wanda shi kadai ya yi azumi a gidan, su kaf sun ce sai na Arfah za su yi hakanan Mamin. Ba ta takurawa kowannensu akan sai ya yi ba kamar yanda ba ta yi ɗin ba ita ma tunda a cewarta ai ba na farillah ba ne.
Da rawar jiki ta bar falon ta koma ɗakinsu, ƙannenta duk ta ba su shekaru babu wanda zai ta ya ta hirar don haka kawai ta dauki waya ta kira Nusaiba suka yi ta zantawa suna masu jin haushin Haulatu. A gefen Jannat kuma ta ji dadi kadan, ita burinta ma abin ya tabbata ko ba komai ta huta da fargabar Haulatun za ta raba ta da Yaya Sadauki. Haka dai suka yi ta zantawarsu can jima Jannat ta yi caraf ta ce.
"Keee! Wai ma tsaya, ba na ji labarin an ce Safina ke son Yaya Mu'az ba?"
"Yes, na san da maganar. Kawai ita kin san ba kowa ya sani ba, ni ma tsintarsa na yi wani lokaci da na shiga wajensu, ina ji Najeeb na tsokanarta wai ga surukarki ta zo. Sai da na matsa ya ke fadamin, ita ba ta ma so na ji ba."
Wani murmushi Jannat ta yi.
"Ni na tabbata ba ta da labarin wannan soyayyar."
"Tsaya, ki na nufin za ki sanar da ita?"
Dariya Jannat ta yi, ita ma Nusaiba ta dara.
"Kai daɗina da ke akwai tunani a wasu lokutan. Kinga ko ba komai wannan alaƙar za ta rushe. Yanzu ai za ta gane me ake nufi da ƴar bariki."
Suka dara.
"Bar ni da su. Takanas zan shigo na samu Safina na ba ta wannan labarin."
"Ai ta zo gidan sauƙi, dazu ta shigo ta yiwa Momi sallama wai za ta je gidansu can za ta yi sallah. Ki bari kawai kya same ta a can."
Jinjina kai Jannat ta yi tana mai jin dadi. Daga nan suka yi sallama. Ita dai babban burinta ta ga Haulatu ta koma baya a kowane ɓangare. Ba Sadauki ba, ba ta fatan ta auri kowane mai hannu da shuni, ta fi son ta gan ta tayi aure a wuri ƙasƙantacce yanda za ta gane shayi ruwa ne.
***
Khaleefa ke tuƙi yana tunani, ya kuma gama fahimtar cewa haƙiƙa idan ya fito da abin da ke ransa game da Haulatu to fa zaluncin zai yi yawa. Shi kuma a kaunar da yake yi mata, ba irin wanda zai so kansa ba ne, kauna ce mai tsafta da zai so ta samu kwanciyar hankali daidai gwargwado wanda zai rinjayi rashinsa a gidan aurenta. Wannan dalili ya sa shi yankewa har a rai cewa ya haƙura da Haulatu. Zai kuma cigaba da bin ta da addu'ar Allah ya yi mata zaɓin miji nagari, shi ma kuma Allah ya kawo mishi wacce ta fi ta. Da wannan, ya rufe babin tunanin yana mai ji har ransa gwara da bai furta ba.
***
Washegari...
KANO...
Ɗan Mutuwa zaune a falon gidansa ya zurfafa cikin tunani. Wai shi Na'imatu ke gasawa maganganu har haka? Ganin ta samu ɗan ƴancin da bai taka kara ya karya ba? Ya yi ƙwafa. A ransa ya na jin eh ya ji ya yarda ya gama da babin Na'imatu, kuma ya rasa wannan damar da ya ke so na tsunduma harkar siyasa, amma fa ba zai bari ta ci bulus ba. Zai sa Uban Dodo ya yi mata turen aljanun da za su hana ta zaman lafiya da za su hana ta aure gaba ɗaya. Kai shi babban burinsa ma a ɗora mata cutar mutuwa, wacce ba ta da magani sai dai ta sadar da ita ga gushewarta.
"Da ni kike zancen Na'imatu."
"Me ka ce?"
Bai san da cewa zancen zucin da ya ke yi ya fito fili ba sai da ya ji muryar Hindatu sannan ya ankara, tana daga gefensa zaune saman kafet din dake malale a falon tana