Showing 96001 words to 99000 words out of 177840 words
ji, shiru ya ɗan biyo baya kafin kuma cikin sanyin murya ya ce.
"Masha Allah, to ki daure ki bar damuwa da lamuran da za su toshe kwanyarki. Za ki yi farin ciki mai yawa a gaba in sha Allah."
"Toh." Ta amsa tana murmushi da lumshe idanu lokaci guda tana komawa ta zauna a gefen gado.
"Sai da safe?"
Yanda ya yi furucin kamar da alamun tambaya sai ta ji kamar ta ce masa a'a, ita kanta ba ta san dalili ba, sam ba ta gajiya da jin muryar Yaya Sadauki.
"Toh."
"Ok, Allah ya tashe mu lafiya."
Ta amsa da amin sai ta ji ya yanke kiran. Kan gadon ta yi baya kawai ta kwanta rigingine tana washe haƙora, sai kuma ta ware idanun da sauri ta miƙe zaune.
'Ke Haulatu ki raba kanki, ke da ba kya soyayya?'
Tambayar wani sashi daga zuciyarta, sai kuma a fili ta ba kanta amsa.
"Ai ba son sa nake yi ba, kawai yana burgeni. Tafiyarsa, ƙamshinsa, murmushinsa, maganarsa..."
Sai kuma ta yi shiru tana jin kirjinta na duka da sauri-sauri. Toh duk me ya kawo waɗannan zantukan idan ba so ba? Girgiza kai ta yi ta hau jan istigfari a fili don ji ta yi kamar ma saɓo ne ta aikata.
***
Bayan Sati Biyu...
Ɗan Mutuwa da Amaryarsa Hindatu sun dawo daga yawon more amarci, zuƙatansu cike taf da begen juna babu kamar ita Hindatun da ta haƙiƙance da ta yi dacen miji fiye da tsohon mijinta Alhaji Badamasi, bayan kuɗi har a fanni na tarairayar mace da nuna mata soyayya. Kwanansu biyu da dawowa garin ya soma shiri a safiyar wata Laraba, ta miƙe daga baccin da ya soma kwasarta tana mutsistsiƙa idanunta ta dube shi.
"Yallaɓai, ina za ka haka da sassafe?"
Ta madubin ya dube ta lokacin da yake gyara zaman hularsa yana murmushi.
"Ranki ya daɗe zan ɗan yi wata ƴar tafiya, nan nan Katsina zan je muna da meeting, amma kar ki damu ba ta kwana ba ce, yau ɗin nan zan dawo. Kin ji ko?"
Ta gyaɗa masa kai tana mai miƙewa ta shige banɗaki. Shi kuwa Ɗan Mutuwa duban kansa ya yi a madubin ya yi wani murmushi.
"Na'imatu ki shirya tarbar mijinki."
Abin da ya furta kenan kafin ya ɗauki wayoyinsa ya fice daga ɗakin bayan ya ajiyewa Hindatu rafar ƴan dubu a saman madubi. Koda ta fito tuni ya fice daga gidan gaba ɗaya, ta sauke ajiyar zuciya tana mishi fatan dawowa lafiya. Ta ƙara duban wawakeken ɗakin nata wanda zai ci gado uku ma ba biyu ba, ga hasken fitilu ta ko''ina ga kuma sanyin Ac na bugunta. Wani juyi ta dan yi da murmushi.
"Kai! Kuɗi sun yi." Ta furta a fili tana mai ɗaukar rafar da ya ajiye gaban madubi ta shinshina su. Sai ta ji aminiyarta Haulatu ta faɗomata a rai. Tabbas wannan ne lokacin da ya dace ta neme ta da zummar tallafawa rayuwarsu ita da Umma. Zuwa lokacin hankalinta ya kwanta dangane da dukiyar mijinta, ta sha jin yana amsa waya game da kasuwancinsa yana batun manyan motocin da suka taho da kayayyakinsa. Hakan yasa ta saki jiki ta kuma fahimci mutum ne mai gaskiya ba kamar mummunan fassarar da ta yi mishi a farko ba. Kai tsaye wayarta ta ɗauka daga ita sai rigar bacci iya gwuiwa ta fito falon tana ƙoƙarin kiran layin Haulatu.
*Littafin nan na kudi ne. Ki siya ki karanta hankalinki kwance gudun shiga haƙƙin marubuciyar.* *Ibrahim Rufaida Umar, *9034973645 Opaybank.* *₦500* *Idan kin biya ki aiko shaidar biya ta 09034973645*
******
Madadin ta ji muryar Haulatun sai ta ji ta Umma. Suka gaisa har Umma ta yi mata Allah ya sanya alheri, ta bi ta da ƴan nasiha kafin ta ce mata Haulatun ta shiga wanka ne. Daga nan suka yi sallama da zummar za ta ƙara kiranta. Kai tsaye ta shiga zagaye gidan nata cike da jin wani nishaɗi, ita dai Hindatu ita ce a wannan gida. Sai ta ji ma yunwar dake cin cikinta ya kau, da sauri ta koma ɗakinta don yin wanka ta haɗa bidiyon da za ta ɗora a duniyar Tiktok. Ko babu komai ita ma ta kai yanzu. Dama ta ɗora waɗanda ta yi a Dubai ta samu mabiya da yawa a kwanakin nan, hakanan masu sharhi a kai da nuna yabawa. A farko ta ɗauka mijinta zai yi ƙorafi sai kuma ta ga akasin hakan, bai yi faɗa ba sai ma cewa da ya yi shi dama yana son mace wayayyiya da ta san kanta.
***
A Katsina kuwa, da yamma Haulatu shiri take yi don zasu fita da Maama, za su yi mata rakiya gidan bikin ɗiyar ƙawarta. Ita ɗin ma zuciyarta fes sakamakon admission ɗinta da ya fito har an kammala biyamata kudin makaranta za ta karanci Political Science. Safina kuwa Accounting sai ko Radiya da za ta karanci Microbiology. Bayan babbar sallah za su fara karatun, wanda bai fi sati biyu ya yi saura ba a shiga watan sallar.
Babban albishirin da Sadauki ya yi mata shi ne na lesson da za ta dinga zuwa duk safiyar asabar da lahadi na koyon harshen turanci da ma karatu don kwakwalwarta ta ƙara gogewa. Wannan ya sa ta ji nan duniya ta ƙara ganin girman Yaya Sadauki duk da mahaifinsa ne ya dauki nauyin karatun nasu su duka. Sun je makarantar sun yi duk abin buƙata a jiya bayan da ya damƙa musu admission letter dinsu. Da wannan farin cikin ta wayi garin yau.
Ta kammala shiri ta sha kyau cikin atamfarta ruwan ganye da fari, sai ta yafa farin mayafi madaidaici. Hoda da kwalli kawai ta zizara a fuskarta. Ta yi sallama da su Umma da Hajja ta fice wajen Maama. Can ta iske Radiya da Safina zaune a falo, su ma sun yi tsaf Maama suke jira.
"Inye, ka ga ƴar jami'a." Faɗin Radiya cike da tsokana. Suka yi dariya.
"Kai, kun ji yanda nake wani farin ciki. Ji nake kamar na jawo lokacin da zamu fara karatu."
"Ban ga laifinki ba, amma ni ba karatun ba sai ka soma ka ji duk ya fice maka a rai. Ba kamar ni mai Microbiology, naji ance da wuya fa ko?" Fadin Radiya.
Safina ta harare ta.
"To wane karatun ne ba shi da wahala? Kawai maida hankali za mu ƙara mu zage damtse. Kun dai ji Yaya Sadauki ya ce idan ba mu yi karatu ba toh da kansa zai cire mu kuma aure za'a yi mana."
Dariya suka yi tunano maganar tasa.
"Tab, toh ina na ga ma lokacin soyayyar da har zan yi wasa da karatu? Sai ka na soyayya ka ke wasarere da karatunka ai. Ku dai zai yiwa kashedi. Ke mai Dr Yunus da kuma ke mai Yaya Mu'az."
Haulatu ta ƙarashe zancen nata da dariya. Shigowar Anti Mabruka falon yasa suka dube ta, kallonsu ta yi ta kauda kai gami da neman kujera ta zauna fuskarta ba walwala kamar koyaushe dai. Haulatu ta gaida ta don sai yanzu ita ta gan ta su kuwa tun ɗazun an gaisa.
"Lafiya." Ta amsa ba tare da ta kalle ta ba. Can kuma ta ce.
"Ina za ku je?"
"Maama za mu raka biki." Cewar Safina. Ba ta yi mamaki na yanda suna tare a wuri ɗaya amma ba ta sani ba, sam ba ta jituwa da Maama, yanzu za su yi daɗi, amma nan da lokaci kaɗan su hau sama.
Taɓe baki ta yi ba tare da ta ƙara tankawa ba. Haulatu ta ɗan harareta kadan, ita sam matar ba ta burgeta, kawai ta ɗorawa ranta tsana da bakin cikin Maama don Allah bai kawo mata mijin aure ba, kuma ikon Allah a haka Maama ta fi ta farin jinin samarin. Ta tabbata da ba ciki guda ta fito da Maama ba, abin da ma za ta yi mata zai fi haka.
Shigowar Maama falon tasa gaba ɗaya suka dube ta. Ta ci adonta har ta gaji da kyau, gaba daya suka dube ta, leshinta fari da golden wanda ya sha adon stones ya karɓe ta ƙwarai. Ta saka golden mayafi, idan ka kalle ta sai ka rantse ba daga jikinta su Najeeb suka fito ba saboda baiwa na kyan jiki da Allah ya ba ta. Mabruka kallo ɗaya ta yi mata ta kauda kai tsabar wani abu da ta ji ya tokare a maƙoshinta, ta hau waƙe-waƙenta na habaici.
"Don Allah a dinga tunani in an girma a san an girma."
Daga haka ta tashi ta nufi hanyar hayewa sama. Maama ko kallonta ba ta yi ba sai ƴanmatan yaranta da ta kalla tana murmushi ta ce.
"Oya, mu je ko?"
"Masha Allah, Maama kin yi kyau sosai wallahi. Allah ya kauda idanun maƙiya."
Fadin Haulatu tana ɗan buɗe murya don so take zancen ya shiga kunnen Anti Mabruka. Aikuwa karaf ya shiga don sai da ta juyo ta dube ta, ko kallon inda take Haulatun ba ta yi ba, sai su Safina da ke kula da irin kallon da Anti Mabruka ta watsamata. Maama kuwa ta girgiza kai kawai tana murmushi. Sam ba ta kawo ma da wata manufar Haulatun ta faɗi ba. Don haka ta dube su ta ce.
"Nagode ɗiyata. Ga muƙullin motar ku je ku jira ni. Bari na ga Inna."
Safina ta karɓa suka amsa da toh, Haulatu ta bi Maama ta gaida Innar dake lazimi, ta gane gaisuwa ce hakan yasa ta ɗan gyaɗa kai tana mata murmushi, daga haka ta fito ta bar Maama can. Mahaifiyar su Maama ce, matar Baba Dakta da suke kira da Inna, tana daga ɗakinta dake ƙasa, sam ba ta da hayaniya ta samu matsalar kunne ga matsalar ciwon ƙafa da take fama saboda shekaru da suka ɗan tura. Wannan yasa zai wahala a gan ta a falon idan an shigo kusan koyaushe tana ɗaki, Baba Dakta nan yake shigowa su sha hirarsu, wani lokacin kuma takan fito.
Safina tuni ta buɗe motar ta yi zaman dirshan a mazaunin Maama, Radiya a gefenta hakan yasa Haulatu ta shige gidan baya. Safina ta daki sitiyari.
"Kai! Mota fa ta yi a rayuwa, inama karatun nan da zamu fara kowaccenmu tana da motar kanta."
"Sai ki bari yayyunmu ma su mallaka tukunna." Faɗin Radiya.
Haulatu tana jinsu ta yi murmushi kawai. Radiya ta dube ta.
"Kai Haulatu ɗazu fa saura ƙiris ki jazamana. Ni nasan da biyu ki ka yiwa Maama addu'ar nan."
"Ashe kin kula kema? Kinga kallon da Anti ta watsamata? Ai wallahi ni dai na sani gaba ɗaya ta tsargu. Kuma ita ma dai ta ɓatan rai, ya za'a yi mutum ya girma amma bai san ya girma ba fisabilillahi. Jiya fa a gaban su Yaya Najeeb ta yiwa Maama rashin kunya wai don ta shigo falo ana kallo ta sauya tasha. Maama ta yi magana don me ba za ta yi kallon a falon sama ba ta bari a kalli abin da kowa ke so a ƙasa. Shi ne fa ta yi wurgi da remote din ta ce toh Uwata Maijidda zo ki dake ni. Maama ba ta ce mata komai ba, Yaya Najeeb kamar za su yi magana amma sun san Maama ba za ta so haka ba dole suka shanye. Yanzu fa wannan Justice din mai neman auren Maama, kar ku so ku ga yanda Anti ke kushe shi. Har zuwa ta yi ta samu Baba Dakta ta ce wai neman mata yake yi, ita ma ya taɓa yi mata zantukan banza a baya. Da Baba Dakta ya bincika ashe ƙarya take, ita fa kawai ta kasa sakawa zuciyarta dangana cewa aure lokaci ne kuma idan tana da rabon yi, za ta yi."
"Uhm, Allah dai ya kyauta. Amma ni dai ba zan juri ta yiwa Maama a gabana na ƙyaleta ba." Faɗin Haulatu ranta duk ba daɗi. Ta tsani ta ga ana wulaƙanta babban mutum, ko ya aka ce wane ya girmeka, to ita ta fi son ka ba shi girma musamman ma idan ya riƙe girman nasa. Suka bar zancen ganin Maama ta fito.
***
Bayan sallar magriba, Daddy Ridwan yana zaune a falonsa suna hira da Momi Nuratu. Wayarsa ta yi ƙara ya duba sunan mai kiran. Sanata Hashim ne, abokin karatunsa tun a can baya, an jima ba'a tare kafin su dawo su cigaba da zumunta.
Momi Nuratu ta ɗan dube shi kafin ta ɗauki remote ta rage sautin talabijin. Gaisawa suka yi sannan Sanata Hashim ya nemi jin ko yana da lokaci gobe zai shigo gidan su yi wata ƴar magana. Daddy ya ɗan yi mamaki amma sai bai kawo komai ba face alheri, ya ce masa ba damuwa. Nan suka tsaida lokaci kan zai shigo nan wajensa ƙarfe sha biyun rana. Koda suka yi sallama ya dubi Momi Nuratu.
"Sanata Hashim ne zai shigo gobe ya cemin. Ya na son mu yi magana ne."
"Toh, Allah ya sa mu ji alheri."
"Amin."
Ta ɗan sauke ajiyar zuciya.
"Ni ko daman ina ta son yi maka wata magana."
Ya dube ta a nutse.
"Na'am, ina sauraronki."
"Shi yaron nan, ba za ku yi mishi magana kan ya fiddo matar da zai aura ba?"
Ya yi murmushi, ya sani sarai Sadauki ta ke magana a kai, amma sai ya ce.
"Wane yaron ki ke magana?"
Ta ɗan harareshi da wasa. Ya yi dariya.
"Oh, wai ɗanki Abeed? Na yi wannan tunanin, abin da ya sa ban ce komai ba har yanzun, na fi so ya kammala ginin gidansa a nutse daga nan ko mene ne sai a yi. Kin ga hakan kamar zai fi. Ko kin masa zaɓi ne?" Ya ƙarashe fuska a sake.
Ta girgiza kai kawai . Dama ta sani ba zai ɗauki zancen da ƙarfi ba, ita kuwa ta gaji da wannan kiraye-kirayen wayar da iyayen ƴan uwa ke yi mata ana gwada cusa kai a wurinta don yin haɗin gida. Sam ba ta da ra'ayi ko buri akan Abeed da ya wuce ta ga yau ya samu macen kirki da ta san darajar kula da miji da girmama iyayensa.
Ji ta yi Daddy ya riƙo yatsun hannunta hakan ya maido da hankalinta gareshi.
"Kar fa ki damu kanki Nuratu, aure shi lokaci ne. Abeed namiji ne, ki bar shi ya bi komai a sannu. Yaro ne mai hankali ya kuma san me yake yi. Tunda ki ka ga iyayenmu ba su matsa ba, sun yarda akwai dalili ne. Ke dai matsayinki ta Uwa gareshi, kar ji taɓa gajiyawa da yi mishi addu'a. Na san dai kin matsu ne ki ga jikanki, toh in sha Allahu za ki gani."
Ta ƙwace hannunta za ta miƙe don jin nauyin zancensa na ƙarshe, ya kuwa riƙe ta ta dawo jikinsa yana dariya.
***
Ɗan Mutuwa ya dubi Sanata Hashim bayan ya cire wayar daga kunne suka yi dariya. Sanata ya ce.
"Shikenan fa, ai dama na ce maka komai ya zo da sauƙi, abokin karatuna ne shi kuma ko ba komai ana haɗuwa a wasu wuraren akan gaisa. Yanzu dai ka ga kenan dole kwanan ya kama ka a garin nan."
Ɗan Mutuwa ya nan ɗan girgiza ƙafa ya ce.
"Dole zan kwana kam, kuma daman da niyyar kwanan na taho duk da ba haka na nunawa Amary ba. So nake na kashe wannan wutar na maida Na'imatu ɗakinta, ni ta ɓangarena ba ni da matsalar komai don na tsara duk wani abu da ya dace da zan tunkari ƴan uwan nata da shi."
Sanata ya jinjina kai.
"Hakane, amma ina fatan ka sanar a gida?"
Idan suka ce gida ga junansu, suna nufin can ƙungiya wajen Uban Dodo, sukan yi amfani da kalmar gida a wasu lokutan don yin ɓadda kama da kuma sirrantawa tunda yanzun suna zaune ne a falon saukar baƙi dake gidan Sanata Hashim din.
"Tuni ma na sanar, an dai ce kar na yi da zafi-zafi, idan na yi da zafi to fa kwaɓa za ta yi ruwa. Zamu bi a sannun sai mu ga abin da ya turewa buzu naɗi."
Suka yi dariya. Sai da suka ci abinci, dama ba maganar sallah don sun shafe ta a babin rayuwarsu, daga nan suka yi sallama da juna inda Ɗan Mutuwa zai wuce hotel ya kwana washegari ya zo su je.
***
WASHEGARI....
***
KU YI HAKURI IN SHA ALLAHU GOBE ZAN MUKU POSTING...
Cikin dare misalin ƙarfe uku da mintoci, motsin Umma ya farkar da Haulatu daga bacci. Tana zaune saman darduma ta ɗaga hannuwa cikin yanayi na ƙasƙan da kai tana addu'a tana hawaye sosai. Sai ta ji ba dadi, ta ƙara yin lamo cikin lumtsetsiyar katifarsu, haƙiƙa ta san mahaifiyarta akwai abin da ke damunta kwanaki biyun nan, ko hira ake da ita sai ta cilla duniyar tunani har sai an taɓa ta ko an yi mata magana da ƙarfi. Hajja ta yi ta faɗa na don me za ta dinga jefa zuciyarta cikin damuwa, ta maida hankali ga islamiyyar da take zuwa zai fiye mata.
Ta yi ta juyi kafin ta ji ita ma baccin ya fice mata a rai don haka kawai sai ta tashi ta nufi banɗaki. Jin motsinta yasa Umma saurin ɗauke hawayen fuskarta, ita ma ɗin sai ta kauda kai tamkar ba ta gani ba. Alwalar ta yi ta shimfiɗa darduma ta yi raka'a biyu sannan ta yi addu'a ta shafa. Tana zaune tana salati, babu wanda ya cewa kowa komai a cikinsu, gyangyaɗin da Haulatu ta soma ne ya sa Umma tashinta da ba ta umarnin ta kwanta kafin a kira sallah. Ba musu kusa ta miƙe ta koma makwancinta.
***
Washegari tun safe ta ke jin jikinta a sanyaye, a ranar za ta soma zuwa lesson amma ji take kamar kada ta tafi. Sai da Umman ta yi ta magana kafin ta iya miƙewa daga inda ta yi karin kumallo ta koma ɗakinsu don kimtsawa tunda ƙarfe goma na safe ne zuwa karfe daya. Duka-duka awa uku ne, bayan ta yi shirinta cikin doguwar riga na yadi mai adon fulawoyi ruwan madara da ja, ta yafa jan mayafi. Ƴar ƙaramar jakarta da ta saka littafi da bironta ciki sai waya ta rataya a kafaɗarta na dama. Koda ta fito Hajja ta dube ta.
"Yauwa Haule, ko ke fa. Ke ce fa kika karaɗe kunnuwanmu da murnar soma zuwa karatun nan amma ɗan awannin da