Showing 63001 words to 66000 words out of 177840 words
ya yi masifar ɗaurewa.
"Umma, meke faruwa ne?" Ta yi tambayar tana duban mahaifiyarta. A nan ne ta ga hawaye ya zubo daga idanun Umman ta saka gefen hijabinta ta share su, dama tun bayan sallar azhar take zaune saman darduma tana tilawar Alƙur'ani. A haka Momi ta iske ta ta hau bambamin faɗa.
"Toh, gwanar na iya! Ke ma ina maki gargadi da babbar murya, kar ki ƙara shiga harkar ɗana. Can inda kuka je ku ka yi gadon barikancinku, ya ƙare a kanku amma ba ku isa ku zo ku gurɓata mana zuri'a ba. Ban da karuwanci irin na mace irinki, ke ma har kin san ki naniƙewa namiji ki liƙe masa kuna wasa da dariya irin wanda ko ƙannensa ba ya sakewa ya yi da su? To kuwa barikin ya ƙare a kanku. Amma wallahi na sha tabara na sha yasin, kuma ɗana zan ƙara tashi tsaye a kansa kafin ku raba ni da shi."
Haulatu ta mike tsaye saboda tsananin fusata jikinta har wani rawa ya ke yi. Ta ƙarasa har gaban Momi, ta dube ta da idanunta da suka hadu da bacci da ɓacin rai suka yi jazur. Umma ko kusa ba ta kula ma da ita ba saboda tsantsar zafin da kirjinta ke yi sai jin tashin muryarta ta yi cikin maidawa Momin Mu'az martani mai zafi.
"Momi kenan, ai kin ba kanki amsa da kanki. Kin ce mana ƴan bariki, toh ai duk wacce ta san bariki, ta san cewa babu boka ba malam, da murmushi ma kaɗai ya ci mu sace zuciyar ɗanki balle kuma ya..."
"Ke! Yimin shiru Haulatu, maza ɓacemin daga nan. Ko ba komai uwa take a wurin Mu'azu. Ba sa'ar yin ki ba ce."
Faɗin Umma da gaggawa bayan ta miƙe tsaye fuskarta a haɗe a ƙoƙarinta na son dakatar da ɗiyarta. Zuciyar ba dadi ga hawayen da suka zuba a saman fuskarta ta kalli Umma kafin ta juya ta kalli Momi dake faman zage-zage tana cewa idan Haulatu ba ta ƙarasa zancen da ta ɗauko ba toh ba ta haifu a gidan karuwai ba. Ta ciji leɓɓanta, idanunta tuni sun soma zubar hawaye, kawai sai ta juya, madadin ta yi sama sai ta nufi hanyar fita daga ita sai riga doguwa ƴan kanti sai ko hula da ta rufe kanta da shi. Wani kallo ta watsawa Nusaiba da ba shiri ta ba ta hanya ta wuce. A tsoron da Nusaiba ta ji, ta tabbatar idan ma duka ne, to fa Haulatun tsaf za ta kai ta ƙas ta jinga son ranta wannan ne babban dalilinta na ƙin musu. Umma kuwa ba ta damu da sanin inda Haulatun za ta je ba, ta san dai ba za ta je wani kewayen da ba na gidan ba.
Fitar Haulatun sai ita ma Momy ta juya suka fice daga gidan, Umma ta koma mazauninta ta yi shiru kawai, Baba Saude dake gefe tana fidda hawaye na tausayawa bayin Allahn ta matso tana rarrashin Umma gami da ban baki, murmushi mai ciwo Umman ta yi mata gami da nuna mata kar ta damu, komai zai wuce watarana.
***
Kai tsaye wani ɓangare ta je a zagayen gidan tsakanin wajen Hajja da na Baba Alhaji, ɗan ƙaramin garden ne wanda bai kai kyau da tsaruwar na Alh Ridwan ba, sai dai yana da rumfa har biyu da kuma kujeru a wajen. Sassanyan iska ke kaɗawa, wuri ne da mutanen gidan ba kamar mazan suka mayar wajen shan iska musamman ma a wannan wata mai alfarma da aka shiga. Yawan zuwansu wurin ne ma yasa su matan suka rage zuwa sai dai a ranar ta ci sa'a ma babu kowa, koda akwai din ma ba ta kula a dalilin ɓacin ran da take ciki. Shimfiɗewa ta yi ta soma kuka, a hankali sautin ke fita. Can kuma ta ɗan rage ƙarfin kukan sakamakon tashin ƙira'ar da ta ke ji yana fitowa daga rumfar kusa da ita. Murya mai taushi da daɗi, ana karatun tamkar wani balaraben ke yi, kai ba don tana jin muryar sosai ba za ta iya rantsewa ko a waya aka kunna sai dai wannan muryar a zahiri take. Lumshe idanunta ta yi tana bin surar a hankali cikin ranta. Sannu-sannu ta ji zuciyarta ta yi sanyi, damuwar da Momi ta haifar a cikinta gaba ɗaya ta shafe. Wani murmushi take bugawa na jin daɗin muryar mai karatun da ma ayoyin da yake karantowa. Tunani ta ke yi waye haka a gidan? Sai ta ji kwaɗayin son ganin ko waye ɗin, hakan yasa ta ɗan miƙe daga kwanciyar da ta yi a saman kafet ɗin dake wurin ta leƙa kanta kaɗan. Ba ta hango fuskarsa sai ƙeyarsa, ya juyamata baya. Sanye yake da jallabiya ruwan ƙasa, ya naɗa hirami a kansa. Ta dubi wayoyin dake ajiye a gefe ko za ta canki na waye, sai dai ba ma ta taɓa ganin kalarsu a hannun wani na gidan ba. Ba zato ta ga ya waigo, duk iyakar kokarinta na ganin ta saukar da kai kafin ya gan ta, ta makaro. Suka haɗa idanu bai ce mata komai ba ya juya kansa, sai da ya kai ayar da yake a karatun kafin ya juyo ya dubi rumfar.
Ita kuwa Haulatu shiru ta yi sai kirjinta dake bugu da sauri-sauri. Da ace ta san ma Sadauki ne a wurin ba za ta leƙa shi ba. Ta san ya riga da ya gan ta, idan ta ce za ta gudu a wajen zai mata kallon marar gaskiya ko kuma ya yi mata wata fassarar. Wato dalilin da yasa ma ba ta ga kowa a wajen ba kenan, tunda ita dai ta sani wurin ba ya rabo da mutane. Yau Asabar babu aiki, toh me ya hana shi yin karatun a ɗaki?
"Zo nan."
Ta ji sautin muryarsa daga sama, ta haɗiyi miyau kafin ta miƙe a hankali ta zagaye zuwa rumfar da yake. Kallo ɗaya ya yi mata ya mayar da kai saman ƙur'anin.
"Kina iya tafiya." Ta kasa gane manufar hakan, sai kuwa ta juya ta fice a rumfar ta zagaya, sai da ta ido saitinsa inda gini ne kawai ya raba tsakaninsu ya ce.
"Wani abu ya faru ne?"
Ya yi tambayar sakamakon tsaf ya ji kuka a ɗazun sai dai kuma bai san waye ba sai da ya ji shiru daga bisani jikinsa ya ba shi ana kallonsa ya juya suka haɗa idanu.
Ita kuwa Haulatu sai ta dube shi jin tambayar da ya watso mata. Ba don nasa dara-daran idanun irin nata suna dubanta ba za ta dauka ko da wani ya ke. Ta kauda nata idanun, kai ta girgiza masa.
"Aa."
Ta ɗan tsaya ta ji ko zai ƙara tambayar amma kawai sai sautin muryarsa ta ji ya cigaba da karatu bayan bismillah da ya yi. Ta kalleshi baki sake, wannan Yaya Sadaukin kawai kuma don ta ce a'a ba zai ƙara tambaya ba kamar yanda Mu'az ke mata naci da son jin meke faruwa idan ya ga ranta a ɓace? Kawai sai ta ɗaga ƙafa ta bar wurin tana jin dama ba ta haɗu da shi ba.
Shi kuwa sai kawai ya tsinci kansa da murmushin da ya bar wa kansa sanin dalili. Bai tashi a wurin ba sai da ya soma jin kiraye-kirayen sallar la'asar tukunna.
***
Hajja koda ta dawo sai da Haulatu ta zayyane mata komai bayan an sha ruwa, don su Baba Saude, Umma ta hana su faɗamata, ita kuwa Haulatu ba ta ga dalilin shiru ba tunda ita an hana ta yi magana balle kuma Umman da ko za'a yi abin da ya fi hakan ba za su ce musu uffan ba. Aikuwa sosai ta hau bambamin faɗa kamar ta ari baki. Ƙarshe ma hannu na rawa ta ciro waya ta sanya Haulatu lalubo mata lambar Mahaifin Mu'az, Injiniya Faisal. Nan ta hau zazzaga faɗa don ko amsa sannu da sha ruwan da yake mata ba ta tsaya yi ba.
"Lallai ka ja wa Matarka kunne idan kuwa ba haka ba zan nunamata ni ɗin koda ban haife ka ba toh ina da iko da isar da zan saka ka sauwaƙe mata. Da ni take zancen, ta ƙara gigin shigowa ta gwada cin zarafin ɗiyata da jikata ta gani."
Shi dai Injiniya hakuri sosai ya dinga ba Hajja ya kuma ce zai yi mata magana ba za'a ƙara ba.
Bayan sun ajiye wayar Haulatu ta kwashe da dariyar da ke cin ta a rai, Hajja sosai ta burge ta, Umma da tun dazu take zubawa Haulatu harara ta ce.
"Sai da ki ka faɗa ki ka ji dadi, burinki ya cika ai."
"Aa kin ga Na'imatu rabu da ita. Ke mene ne amfanin yin shirunki? Ita ma so ki ke ta zama kamar ke ta dinga yin gum tana shanye ɓacin rai da baƙin ciki har ya yi ajalinta ko? Toh ba ki isa ba, ke Haule daga yau duk wacce ta ƙara zuwa ko bana nan ki sanar da ni matuƙar ba alheri ne ya kawo ta ba. Idan ma na yi nisa ga Alhaji Babba can ko Yaya Dakta."
"Toh Hajja." Fadin Haulatu zuciyarta fes kwalliya ta biya kuɗin sabulu.
Umma girgiza kai kawai ta yi ba ta ƙara magana ba.
Sai bayan kammala shan ruwa Umma ta dubi Haulatu bayan barin Hajja daga falo.
"Kin kuwa kira Yayanki kin masa godiyar tsaraba?"
Sai ta ɗan waro idanu, ita shaf ta ma mance. Ta tuno haɗuwarsu da shi ɗazu da yamma, ina za ta iya yi mishi godiya a sannan alhalin ya zubamata waɗannan idanun masu kama da na mage.
"Kin yi shiru."
"Na manta." Ta fadi tana ɗan turo baki kaɗan. Ran Umma ya ɓaci.
"Amma ke dai an yi marar wayo. Wato ni kika bari da yin godiyar kenan ke ba ki bi umarnina kin kira shi kin masa ba? Ciro wayarki yanzu na ga kin kira shi."
Ta jawo wayar idanunta ya yi rau.
"To ai ban da lambarsa."
Girgiza kai Umma ta yi ta miƙa mata nata wayar.
"Duba za ki ga Sadauki a kai."
Ta karɓa ta ɗau lambar. Yanda Umma ta tsura mata idanu ya sa a dole ta danna kira.
"Assalamu alaikum."
Ta tsinkayi muryarsa a dodon kunnenta, wannan ai shi ta dubi Umma kafin ta haɗiyi miyau ta amsa.
"Waalaikumussalam. Barka da shan ruwa."
"Yauwa, go straight to the point, sallah zan shiga."
"Haulatu ce."
"Yes, na sani."
Ya fadi a hanzarce, ta shanye mamakin jin yana da lambarta don ta ji ya ce yana sauri ta ce.
"Dama godiya zan yi na tsaraba. Nago..."
"No, ba godiya. Ki gaida Umma."
Daga haka bai ƙara jira ba ya katse kiran. Ta bi wayar da kallo, ba don da kunnenta ta ji ana haramar tada sallah ba za ta ce da gayya ma ya yi mata hakan. Taɓe baki ta yi.
"Ya ku ka yi?"
"Cewa ya yi ba sai na gode masa ba. Kuma yana gaida ki."
"Ina amsawa." Daga nan ita ma Umman ta miƙe don ɗauro alwala. Ita kuwa Haulatu sai ta ƙurawa lambarsa idanu, 909090 har uku a ƙarshenta, lambar ta burge ta sosai. Ta adana akan waya da sunan Yaya Sadauki. A karshe kuma ta miƙe ita ma.
Washegari Mu'az ya zo ya sami Umma ya ba ta haƙurin cim mutuncin da Mominsa ta yi, Umma ta nuna babu komai kar ya damu. Haulatu kuwa ko kallonsa ba ta yi ba, tana tauna tsakuwa ne don aya ta ji tsoro ko yaya tana so ya fahimci ta san darajar kanta da na Ummanta ba wai hakanan daga Momi ta yi abu ta dinga sakin baki tana washe wa yaranta ba kamar wacce ba ta san ciwon kanta ba, amma ta rantse yanzu ma suka fara zumunci da shi sai dai baƙin ciki ya kashe Mominnasa.
***
A na jibi sallah bayan sun dawo daga gidan ƙunshi ita da Safina da Radiya, Allah ya taimake ta ba ta azumi saboda wani ciwon kai da ta ke fama da shi tun safe tsabar gajiya da kuma rana, ko ruwa ba ta sha a gidan ƙunshin ba ma ganin wajen a cike. Ta tarar an kawo kayanta daga wajen tela, Hajja ta yi mata kala biyu atamfa da leshi, sai ko Haj Hadiza wacce ta aiko Atamfa wai a ɗinkawa ɗiyarta. Umma koda ta gani a lokacin murmushi kawai ta yi, fatanta ƙaunar da take nunawa Haulatun a yanzu ya kasance har zuciyarta. Khaleefa ma sai da ya ba Umman turmin atamfa mai tsada ya kuma haɗa har Haulatu. Shi ma tun a azumi na da goma ya kawo, ba laifi koda ta masa godiya a take ya amsa.
Sosai ɗinkunan sun yi kyau sai dai ciwon kai ya sa ko iya gwadawa ba ta yi a sannan ba sai wajen takwas na dare bayan ta ci abinci ta sha magani har ta dan samu bacci ta farka.
"Kai Umma, wallahi wannan telan ya iya ɗinki. Kalli fa yanda kayan suka zauna a jikina?"
Murmushi kawai Umma ta yi, Hajja kuwa fadi take
"TubarakAllah Haule, sai kika koma kamar ni sadda ina budurwa."
Suka yi dariya har da cafkewa kamar wata sa'ar ta. Ta dinga juyi gaban madubin dake kusurwa daban a falon Hajja, kalar leshin ma ya hau da fatarta, silver mai adon baƙaƙen fulawa. Ya sha adon duwatsu. Jin sallama ba zato ya sa ta saurin waigowa, gaba daya suka dube shi. Khaleefa ne ya shigo, ita kuwa Haulatu ganin Khaleefan ba ta wani damu ba tunda dai sutura ne a jikinta, dama ƙawayenta ne ba ta son su shigo su iske ta cikin kayan, ta fi ƙaunar ta yi musu bazata a ranar sallah su ga yanda za ta ci ado.
Shi kuwa karasowa ya yi ya zauna yana gaida su Umma sai dai fa wani abu na jan sa ga kallon Haulatun. Ta gaida shi ta kwashe sauran kayan da aka kawo ta wuce ɗaki.
A ɗakin ma sai da ta ƙarewa kanta kallo a madubi kafin ta yi sauri ta sauya kaya, dama leshin kaɗai ya rage ta gwada, ta maida su ta ajiye cikin sif, tana da takalmi da jaka sabbi, hatta da mayafi wanda zai hau duka Hajja ta sa an siyo mata su tun daga Kano.
Shigowar su Safina da Radiya ne ya sa ta juyowa bayan ta rufe sif din.
"Inyee, masu ciwo an wartsake. Ai gwara ki miƙe haka kurum ba za ki kashe mana zumuɗin zuwa idi ba."
Faɗin Radiya dake riƙe da leda a hannunta. Ta harare ta tana dariya.
"Ai na rantse da ko fatalwa sai na maku na hana ku sakat, kuma ƙafata ƙafarku sai dai mu mutu tare. Hum um, na mutu kawai na bar ku kuna shanawa?"
Suka yi dariya gaba daya.
"Dallah can, kema ai a lahirar kina aljanna in sha Allahu." Fadin Safina.
"Eh na ji din, amma ba yanzu ba. Allah dai yasa mu cika da imani."
Suka amsa da amin.
"Ke kina ta wani rungume leda, ki ba wacce aka ce mu kawo wa mana."
Fadin Safina tana yarfa hannu. Haulatu ta bi ledar da Radiya ta miƙo mata da idanu.
"Ke hijabai ne fa, Yaya Sadauki ne ya kawomana kala bibbiyu. Fari da ruwan ƙasa. Kuma dukkanmu iri guda. Wallahi kamar ya auna tsawonmu. Amma na ji Maama ta ce a shagon wannan ƙawarta ta Anti Laila ya siya. Kin san hijabai da suturu ta ke siyarwa."
Ai kuwa ta zazzage ledar, hijaban an sanya su cikin farin leda an liƙe. Da zumuɗi ta ce.
"Bari na nunawa Umma, ina zuwa."
"Eh ki dawo ki nunamana tsarabarki ta China." Cewar Radiya.
A falon har lokacin Khaleefa yana nan, ta ga ya auna bp din Umma da abin gwaji, sai ta dan tsaya, bayan sun kammala ta ji yana cewa Umma komai yana tafiya daidai sai dai a ƙara kiyayewa.
"Ke kuma kin fito kin bar ƙawayen naki?"
Fadin Umma tana kallonta. Ta karasa tana murmushi gami da mikawa Umma hijaban.
"Umma kinga wai Yaya Sadauki ne ya siyo mana mu uku. Kowa kala bibbiyu."
Fara'ar Umma ta ƙaru, shi kuwa Khaleefa ya tsinci kansa da bin hijaban da kallo. Kyauta daga Sadauki? Saraki dai da ya sani? Eh yana da kyauta, amma meyasa Haulatu? Sai kuma ya kawar da tunanin don ya sani bai yi mata adalci ba idan ya fadi hakan. Ita din ma ai ƙanwarsa ce kamar yanda su Safina su ke a wajensa. Ya maida numfashi yana mai kallon Haulatun har ta miƙawa Hajja ledar hijaban ita ma ta a saka nata albarkar, can kuma ya yi saurin kauda kai. Yau me ke faruwa da shi ne haka? Kallo dai? Aa, wannan ba ya daga cikin ɗabi'arsa, don haka ya yiwa kansa faɗa ya shiga tattara kayayyakin gwajin ya ajiye gefe. A sannan ita har ta koma cikin yan uwanta.
***
Ɗan Mutuwa...
A ɓangaren Ɗan Mutuwa kuwa, dukkan wasu sharuɗɗan da Uban Dodo ya ba shi babu ɗaya da bai cika ba, ƙarshe aka mallaka mishi wani zobe mai sheƙi idan ka zura a yatsanka. Ranar farko da ya saka sai da ya ji shi kamar an yi mishi katanga tsakaninsa da imaninsa don a lokacin ji ya yi ba iyaka satar wani sassa a jikin gawa ba, saduwa idan aka ce ya aikata da gawar zai iya yi a sannan. (Wa'iyazubillah). Sharuɗɗan shi ne duk runtsi koda zai yi sallah to kar ya sake ya yi ta isha'i da Asubahi, kuma kar ma ya kara tunanin daukar azumi a duniya idan har yana son arzikinsa ya dauwama. Idan yana da aure ko kuma zai yi, toh ana so a yi shagali a yi ɓarin kudi na kata'i wanda haka zai sanyaya ran Uban dodo da aljanunsa, ba ma sai bikin aure ba, duk wani abu na sabga idan ya tashi toh fa a yi ɓarin kuɗi, wato dai a dinga almubazzaranci. Wannan zai ƙara haɓɓaka arzikin sosai. Uwa uba kuwa ga wani akwatim tsafi da aka ba shi yake ajiye a ɗakinsa don tuni ya dawo garin Kano da zama, koda sun haɗu da idon sani kawai sai dai su kalle shi amma babu wanda ke iya yi mishi tambaya kan abin da ya faru a baya. Sai ma ya bar wajen su ke tunawa ashe fa laifi ya yi. Sam ba a tsohuwar unguwar da suka