Showing 114001 words to 117000 words out of 177840 words

Chapter 39 - FITAR TSIRO COMPLETE HAUSA NOVEL BY RUFAIDA UMAR

11 Jul 2024

79178

cin gashin kaza ga wani sassanyan lemun kwakwa a gefenta. Ya yi murmushin yaƙe.

"No babu komai Bebi. Gama ci mu yi ƴar magana."

Ta amsa da toh kafin ta maida hankali tana yi tana tunanin ko me zai ce? Ita duk dadi ya cika ta kwanakin nan sakamakon samar mata admission da ya yi a jami'ar Bello Maitama za ta ɗora karatunta. Sai da ta kammala ta tattara komai sannan ta dawo ta zauna a gefensa.

"Na gama."

Ya numfasa.

"Dama batun uwargidata da na yi maki ne, ina son ce maki yanzu ba ma tare. Mun rabu."

Hindatu ta ɗan fiddo ido,

"Toh, lafiya kuwa? Me ya yi zafi haka? Kai amma ban ji dadin wannan zancen ba."

Har ga Allah kuwa ba ta ji din ba. Ɗan Mutuwa ya ɗan yamutse fuska.

"Kinsa halin kishi irin naku na mata. Da zarar kun ji miji ya ƙara aure shi ke nan sai cibi ya zama ƙari. Allah dai ya kyauta. Bari na ɗan fita akwai wanda zamu hadu da shi ne."

"Amma Yallaɓai ba za ka lallaɓa ta ba ko..."

Kallon da ya wurga mata ne yasa ta yin ɗif da bakinta. Kallo ne da bai taɓa yi mata ba. Ya haɗe fuska.

"Ba huruminki ba ne wannan. Na fadamaki abin da ya kyautu ki sani ne don kawai kar ki sanya min alamar tambaya."

Daga nan ya fice fuu yana zura takalminsa ya bar ta. Kamar ta tunasar da shi sallar Azahar da ba ta ga ya yi ba amma inaa tuni ya fice. Ta sauke ajiyar zuciya. Wayarta ta dauko ta dannawa Haulatu kira. Ta ci sa'a kuwa ta amsa.

"Ke dai kin yi wuya ƴar nan, ko ta whatsapp na maki magana sai ki dinga amsamin kamar ba kya so, wayar ma babu damar na kira na sameki a kusa. Ko wani laifin na maki?"

Ƴar guntuwar dariya Haulatu ta yi.

"Hajjaju Makkatu ki yi hakuri. Kin san ina ta shirin fara karatu, Alhajin da Umma ke aiki a wajensu ne ya biya min na ƙarasa makaranta, mutumin kirki ne sosai. Ya na daukar dawainiyar marayu da marasa karfi da dama."

Hindatu ta fiddo ido waje cike da mamaki da kuma farin ciki.

"Wai Allah! Wannan abun farin ciki da yawa yake. Nima fa ma fadamaki ko kwana biyar ba'a yi ba Yallaɓai ya samar min admission zan koma makaranta, amma fannin kasuwanci ya samar min. Ashe dai ke ma za ki koma? Amma na ji dadi ba kadan ba, gaskiya ko waye wannan Alhajin mutumin kirki da shi wallahi."

Haulatu ta yi murmushi mai sauti ta cikin wayar.

"Ke ma na maki murna sosai. Ai gwara maki karatun. Kin ga ko ba ki yi aiki ba, karatunki zai taimake ki nan gaba."

"In sha Allahu. Ke, ciki ne da ni fa."

Sai da ta ji shiru ta wayar don a zatonta ma ko kiran ya yanke tunda dai kati sama da na dubu biyar ta zuba a wayar. Ta fiddo daga kunnenta ta ga ba kiran ne ya yanke ba.

"Hello, na ji kin yi shiru? Kin ji abin da nace kuwa?"

"Eh na ji, afuwan hankalina ne ya ɗan ɗauke ina aiki ne. Kai na maki murna. Allah ya saukeki lafiya."

"Amin. Kin.." Hindatu za ta ƙara magana da shirin labarta mata da zancen sakin uwargidanta da ya yi sai ta ji Haulatu ta katse ta da fadin.

"Big Mama, please mu yi magana anjima ko ta whatsapp, an sanya ni aiki ne kar su ga na tsaya amsa waya. Kin san fa ana azumi."

Ta jinjina kai kamar su na ganin juna.

"Shikenan, ni ma dama shi ya hana ni azumin wai kar na wahalar masa da Bebi. Bari na ƙyale ki toh. A gaida Umma."

"Uhum, za ta ji."

Daga haka suka yi sallama, Hindatu ta miƙe, ta gaji da zaman shirun wannan ya sa dama ta ƙudirce za ta leƙa makwafta a gaisa da juna, ko babu komai ta samu ƴan uwa na zumunci.

***
Katsina...

A gefen Haulatu ko, sadda suka yi waya da Hindatu tana zaune tana ferar dankali a kusa da kicin daga ita sai tshirt da zani sakamakon yanayi na zafin da ake yi ga kuma hadari da ya hadu, ana saka ran samun ruwa kowane lokaci. Dama kwanakin nan zafin sai hamdala a garin.

Jikinta duk ya yi sanyi jin wai Hindatu na da ciki, sam ba ta cewa kowa wani abu a kai ba. Dakyar ta ture batun a ranta ta cigaba da aikinta.


***
Safina tana tare da Mahaifiyarta Haj Fatu da suke kira Yaya, hirarsu suke yi game da bikin da za'a yi na ɗiyar ƙanwar Yaya a can Abuja. Safina kira take ita dai za ta bi su, amma Yaya ta ce sam tunda dai karatu za su soma da zarar sallah ta wuce. A lokacin suka tsinci sallamar Jannat. Gaba daya suka amsa ta shigo falon riƙe da hannun ƙanin Safina, da fara'a Yaya ta ke fadin.

"Wa nake gani yau a gidan? Jannat? Sannu da zuwa."

Jannat kuwa ta shanye borin kunyar, dama gaskiya takan jima ba ta ɓullo ba, Safina kuwa tuni ta ji a jikinta ko mene ne ya kawo Anti Jannat gidan ba abin alheri ba ne tunda dai ba wani jituwa Maminta ke yi da Yaya ba. Bayan sun gaisa da Yaya, ita ma ta gaidata. Ta amsa fuska a sake. Sai da aka shiga hira, Yaya ta sakar mata kamar ba ranar ce ta soma zuwa gidan ba, a karshe ta mike ta bar su da Safina da zummar shiga kicin duba girki. Wannan damar ita Jannat ke jira don haka ta gyara zama da murmushi ta dubi Safina.
"Congratulations. Ashe dai ƙawarki Haulatu da Yaya Mu'az mun kusa shan shagalin bikinsu?"

Safina ta ji maganar tamkar saukar aradu, kirjinta sai da ya shiga bugun da ba ta yi zato ba. Har wani bibbiyu ta soma ganin Jannat din. Ta haɗiyi miyau mai ɗaci. Haulatu da Yaya Mu'az? Wannan tatsuniya ce kawai Anti Jannat ta shirya.

"Oh, na ji kin yi shiru. Ba ki da labari kenan? Uhm. Ai magana har ta je kunnen iyaye nima ta bakin nawa iyayen na ji shi, ashe wai tun zuwanta ba jimawa suka fara soyayyar, abu kamar wasa har Yaya Mu'az ne ya faɗamusu da amincewar Haulatun. Abin dai ni ya yimin dadi, ko babu komai can gasu gada, ba ita ba tunanin lashe kurwar Yaya Sadauki."

Wani murmushi mai kama da yaƙe Safina ta yi, idan ba wanda ya yi mata farin sani ba ma, ba za a kawo yaƙen ba ne. Ta dubi Jannat dakyau.

"Kema dai Anti Jannat, ki na tunanin magana za ta kai ga tsawo haka har ke da ba kusa da Haulatu ki ke ba ki ji, ni kuma na kasa ji? Uhum, to wannan zancen tun ma kafin abu ya yi nisa muke da labari ni da Radiya. Haulatu ta cancanci na sadaukar mata da komai, don na sani watakila labari ya riskeki cewa na taɓa son Yaya Mu'az ne a baya ki ke tunanin hakan da zan ji zai min zafi a zuciya ko?"

Ta na kaiwa nan ta yi ƴar dariya.

"Ko kusa, ai babu yanda za'a yi mu ɓoyewa junanmu sirri. Kuma ina yi musu murna da fatan alheri koyaushe. Ni tuni na rufe shafin Yaya Mu'az a raina tun ma kafin faruwar lamarin. Ke ma Allah ya sa ki gane."

Jannat tuni ta shaƙa, babu ma kamar furucinta na ƙarshe.

"Allah yasa na gane me? Me kike son fadi Safina?"

Safina ta yi murmushi.

"Kin san akwai ciwo son wanda ba ya sonka."

Ta kula dai abin da ta zo da shi bai samu matsuguni a zuciyar Safina ba, ta ma gane yarinyar muguwsr marar mutunci ce, wato ita za ta gasa mata magana ma? Don haka ta miƙe ranta na suya da zummar tafiya, ya kuma yi daidai da fitowar Yaya daga kicin.

"Ah, me nake gani? Ba dai tafiya za ki yi ba? Ki jira a sha ruwa mana."

Da yaƙe ta amsa.

"Lah, Yaya ki yi hakuri, Mami ta ce kar na kai dare. Dayake dama unguwarku na zo gidan wata ƙawata shi ne na biyo mu gaisa. Ni ba na ma azumin."

Yaya ta yi murmushi.

"Hakan ma ai kin sada zumunci. Jira ina zuwa."

Daga haka Yaya ta wuce zuwa ɗakinta, gidansu gini ne flat marar bene. Amma ya tsaru iyaka. Safina kuwa ta fake da daukar wayarta ta saka a flight mode a fakaice yanda Jannat ba za ta fahimta ba, daga nan ta kara a kunne ta ja mintuna kamar biyu sai ta soma magana.

"Amarsu ta Ango ba da kanki a sare."

Ta ɗan yi shiru tana ji a jikinta idanun Jannat na kanta. Can ta kara cewa.

"Na fiki murna rabin rai. Ai ranar akwai kallo, ke akwai fa magana."

Daga haka ta miƙe ta dan dubi Jannat wacce ke tsaye tana cika da batsewa, murmushi ta yi.

"Anti Jannat ki gaida su Mamin."

Daga haka ta wuce zuwa ɗakin da ya kasance na ta wanda har kullum idan ta zo gidan nan take sauka. Tana ba da baya kuwa sai ga Yaya da ƙatuwar leda. Ta miƙawa Jannat.

"Ga wannan ba yawa kya yi adon bayan sallah tunda yanzu kam sallah ta gabato." Ta ƙarashe da dariya, ita ma Jannat ta yi yaƙe, karɓa ta yi da godiya sannan ta fice.

A can ɗakin kuwa, Safina kawai gado ta fada ta shiga kuka mai sosa rai, dagaske ne abin da ta ke ji? Duk abin da Jannat ta fadi dagaske ta ke ba wasa ba? Ya za'a yi ta tabbatar? Ita sam ba zafin soyayyarsu ta ji ba kamar irin yanda Haulatun ta raina mata hankali. Ta rasa tunanin da ya dace ta yi don haka ta kunna wayarta ta kira layin dan uwanta Haidar. Yana ɗagawa bayan sun gaisa ta tambaye shi ko ya ji wata magana a gida dangane da Yaya Mu'az da Haulatu? Ya kasa magana sanin da ya yi tana son Mu'az din, sai da ta matsa sosai kafin ya amsa.

"Yes, dazu bayan Azhar na ji Maama na cewa wai Uncle Faisal ya zo wurin Baba Alhaji yake shaida masa batun soyayyarsu kamar dai yana nemawa ɗansa aurenta, ya ce sun jima wai suna son juna, Baba Alhaji dai ya ce a bar komai zuwa bayan sallah kuma sai ya ji ta bakin Haulatun. Ita ma dai Maama na ga ranta ya ɓaci sosai. Sai dai na fi ganin laifin ƙawarki, wannan wane irin cin amana ne? Duk zamanku tare ashe soyayya suke yi ta ɓoyemana? Bayan ta san irin son da kike mishi?"

Runtse idanu ta yi tana ji ƙirjinta na suya, ga kukanta da ya kasa tsayawa ƙarshe ma ta gaji da haƙurin da Haidar din ke ba ta, ta katse kiran.

"Meyasa haka Haulatu? Me na yi maki?"

Haka ta furta a fili cikin yanayi na kuka. A can ƙasan ranta tana kokarin yi mata uzuri amma kuma ji ta yi kawai ta kasa, so ba ƙarya ba ne, hakika tana son Yaya Mu'az tun ma ba ta san me ake kira da son ba, tun ba ta mallaki hankalin kanta ba. Wannan kauna ce tsaftatacciya. Da ace wata ce ma daban ba lallai ta ji wannan zafin ba. Hango murmushinta da kuma yanda ta ke yawan nunawa Haulatun irin matowar da ta yi akan Yaya Mu'az din kawai take, wato wannan ƙarfafa gwuiwar da take mata, wannan addu'ar da take ikrarin tana taya ta da shi, duk na bogi ne? Kanta ta ke yiwa? Kaunar da ta ke nunawa kamar tana yiwa Yaya Sadauki, duka ba gaske bane?

Ta sa a ranta har abada ba za ta cewa Haulatu komai ba, kuma za ta danne wannan ɓacin ran a rai, za kuma ta yi kokarin rage shiga sabgarta. Dakyar ta saita kanta ta shige bandaki ta gyara fuskarta ta fito zuwa falon inda ta tarar Yaya da mai mata hidima suna ta aikin jera kayan shan ruwa. Ita ma ta fada kicin din ta shiga taimaka musu, Yaya tsaf ta karanci damuwa a saman fuskar ɗiyarta, ta kuma ga sauyin da idanunta suka yi, shaidar ta ci kuka ta ƙoshi. Ba ta ce mata uffan ba har mahaifinta Dakta Hashim ya dawo suka sha ruwa. Tana ta kasa kunne ko za ta ji ya yiwa Yaya zancen auren Mu'az din da Haulatu tunda Jannat ta ce iyaye sun san da maganar, amma sai ta ji shiru. Da wannan ta gane mahaifinta bai kai ga ji ba.

"First Love, meke faruwa? Naga yanayin fuskarki kamar kin yi kuka ko?". Fadin Dakta Hashim yana kallon Safina cike da kulawa. Ta yi murmushin da bai ƙarasa zuci ba.

"Babu komai Dad. Kawai kaina ke ciwo."

"Kina gidan Dakta ki ke zama da ciwon kai ba ki nemi magani ba? To Sweetheart laifinki ne."

Sai ma ya ba ta dariya, shi dama ba ruwansa akwai son raha. Yaya tun tana jin nauyin ya dinga kiranta da wannan suna gaban yara har ta saba. Haka ya yi ta jan ta da hira har ta saki jiki, suka shiga magana game da karatunta, matsayinsa na Uba mai zurfin ilimin addini da na boko, ya yi mata nasiha sosai dangane da kama kai. Har da daukomata labarin aurensu da mahaifiyarta, ana zuwa gaɓar Yaya ta miƙe tana fadin.

"To wannan ba da ni ba. Ahyaan ku tashi mu je a watsa ruwa a sauya kayan nan."

Ahyaan na dariya ya mike, wato dai Yaya ba ta son su sha labarin. Daga Safina sai shi a wajen Yaya.

"No bar su na ba su labarin irin nutsuwa da kamalar da na gani tattare da ke mana har ki ka siye zuciyata."

Ita tuni ma ta yi gaba tana murmushi da girgiza kai. Hashim ba zai taɓa girma ba, kullum yana jin sa kamar wani matashin saurayi.

***
Duk wannan budurin da ke a babban gida, babu ɗaya da Haulatu ta ji. Hajja ita kanta zancen bai zo kunnenta ba. Sai bayan sallar isha'i suna zaune a na kallo, sai ga Najeeb ya shigo wai Baba Alhaji na kiran Haulatu. Kiran bai wani ba su mamaki ba tunda a wasu lokutan musamman idan ya kwana biyu bai ji gan ta ba, yakan turo a duba masa ko tana lafiya. Ta amsawa Najeeb kafin ta miƙe duk da tana jin dadin kallon film din hausan da suke haka ta hakura ta dora dogon hijabi saman riga da wandon da ba su matse ta ba, ta fita.

Tana shiga sashin Baba Alhaji, suka yi kiciɓus da Maama, kallonta ta yi bayan amsa gaisuwarta ta ce.

"Idan kun ƙare da Baba, ina son magana da ke kin ji ko?"

Ta amsa da toh, a nan ne ma ta ɗan sha mamaki, toh maganar me Maama za ta yi mata kuma? Ko yana da dangantaka da wacce Baba Alhajin zai mata? Ta hakura da canki-canka ta shiga falon Baba Alhaji da sallamarta. Ya amsa yana rage ƙarar rediyon da ya ke ji, ya dau gilashinsa ya saka.

"Baba ina wuni, an sha ruwa lafiya?"

"Lafiya kalau Haulatun Hajja, ya ku ke ya su Umman taki suka sha ruwa?"

Ta amsa da lafiya kalau. Ya jinjina kai gami da hamdala kafin gyaran murya ya biyo baya.

"Masha Allahu. To dama akwai wata magana da aka zo min da ita ɗazun, shi ne nake son na ji ta bakinki."

Ji ta yi gabanta ya ɗan fadi, ta hadiyi miyau, babu abin da ta kawo a kai face Yaya Zaid. Kenan don taurin kai da kafiya da naci irin nasa sai da ya samu Baba Alhaji da zancenta? A ranta ta yi ƙwafa gami da ƙara nutsuwa don jin me zai fito daga bakin Baba Alhaji.

"Babanki, Faisal. Ya same ni da batun nemawa ɗansa Mu'az aurenki, yace shi Mu'azun ya tabbatar masa kun fahimci juna kuma ku na son juna. Duk da cewa na nuna musu a bar zancen har mu sallaci idi in sha Allahu, amma na fi son na kara samun tabbaci daga bakinki. Kina son Mu'azu?"

Har wasu hawaye ta ga sun zubomata a fuska, kenan sharrin da Yaya Mu'az ya ƙulla mata kenan? Ta nan ya ɓullo? Sai ta ji ta tsane shi fiye da baya. Ta girgiza kai.

"Ni wallahi Baba Alhaji babu wata soyayya tsakaninmu. Kuma shi da Yaya Zaid ne suka ce su na sona, amma ni bana son dukkaninsu. Ban ma san Yaya Mu'az ya zo wajenku ba."

"Ikon Allah, shi Zaidun ne ke sonki?"

Ta gyaɗa kai cikin muryar kuka na zallar takaicin wannan magana ta amsa da eh. A ƙarshe ma sai da ta labartawa Baba Alhaji komai dangane da batun Zaid da Mu'az, ta ƙara da faɗin.

"Ni fa Baba na fadamaku ba aure nake son yi yanzu ba, ni karatu nake so. Ni sam ban shiryawa soyayya ba."

Murmushi Baba Alhaji ya yi irin nasu na manya.

"Shi ke nan Haulatu, ai magana kam an bar ta. Kar ki damu kin ji, in sha Allahu su ma babu wanda zai ƙara takura rayuwarki. Da kaina zan ja musu kunne. Ki kwantar da hankalinki, in sha Allahu burinki zai cika ko bayan raina. Aure kuma, sai wanda ke da kanki ki ka ji kina so, idan har mun yarda da nagartar wanda ki ka kawo, babu abin da zai hana aurenku."

Ta ji dadi sosai, ta kuma ƙara jin ƙaunar Baba Alhaji a ranta. Nan fa ta dinga godiya da addu'a kafin ya ce ta tashi ta je, kar ta ƙara sanya damuwarsu a ranta. Da haka ta fito ta nufi hanyar bene inda Maama ta yi. A dakinta ta iske ta, ta rage kayan jikinta daga ita sai daura ƙirji za ta shiga wanka. Maama ganinta sai ta zauna gefen gado, Haulatun ta zaune gefenta don sun yi sabon da suke mata kallon Uwa ga kuma shaƙuwa da ke tsakani. Ita ma Maama batun Mu'az din ta yi mata. Nan fa ta ƙara sanya wani kukan, ita Safina kawai ta ke tunanin ya za ta yi idan ta ji wannan zance. Ta zayyanewa Maama daga farko har karshe, hatta Zaid mai nacin nuna mata so ba ta ɓoyemata ba. Da yake Maama ta san da zaman Zaid, sai ta fi mamakin na Mu'az, ashe Haulatu ce yarinyar da yake cewa zai kawo ta gan ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login