Showing 126001 words to 129000 words out of 177840 words

Chapter 43 - FITAR TSIRO COMPLETE HAUSA NOVEL BY RUFAIDA UMAR

11 Jul 2024

79130

sannan uwa uba ma za ta hana Maama aure gaba daya. Ta ƙara da cewa ai Maama ita ta yi mata asirin da har gobe take zaune a gida ba ta yi aure ba. Wannan abu ya ƙara rura wutar tsanar Maama a zuciyar Mabruka. Dama ta jima ai tana zargin hakan, kuma an taɓa faɗamata a wurin biye biyen malamanta, yanzun da ta ƙara samun tabbaci daga bakin Bokanya, sai ta ƙara yarda ɗari bisa ɗari hakan ne. Ita ma haka ta yi mata ɓarin kuɗaɗe har ma da alƙawarin ƙara mata fiye da hakan matuƙar auren ya tabbata da ita ba da Maama ba. Daga nan ta tashi ta bar wajen.

***
Daji ne ba gida gaba babu a baya, kamar yanda take gudu da iyakar ƙarfinta tana tsallake itatuwa da duwatsu, haka ita ma ƙatuwar baƙar magen ta ke tsalle da gudu don ta cimmata. A ƙarshe ta ji ta kife tana juyawa ta ga magen nan ta yi tsalle ta dira a kanta, ƙoƙarin kai mata cafka a fuskarta kawai ta ke yi amma iyakar ƙafinta take sanyawa ta na riƙe ta tana karanto addu'o'i. Sai magen ta yi wani ihu ya jiya ta kai mta yakushi a ƙafafunta, ita kuwa ta ƙara buɗa murya ta hau karanto ayatul kursiyyu da ƙarfi kawai ta nemi magen ta rasa. Daidai nan ta farka a gigice tana mai ambaton sunayen Allah, gumi ta ko'ina ya wanke ta. Ta yi zaton abin iyakar mafarkin ne kawai, sai ɗaga ƙafa ta yi ta ga duk karta na faratunan magen nan. Ta waiga ta kalli Haulatu wacce ta yi nisa a bacci ba ta san ma inda kanta yake ba kafin ta miƙe ta faɗa banɗaki. Umma ta jima saman darduma tana addu'o'i sannan ta koma bacci tunda a lokacin ko huɗu ba ta yi ba. Abin da yake wuya ka ga ta yi, wato makara sallar asuba, shi ta yi a yau, sai da Haulatu ta tashe ta kafin ta miƙe ta faɗa banɗaki.

Koda wayewar gari babu wanda ta sanar da batun mafarkinta, ta san dai abu ne mai matuƙar ban al'ajabi, amma kuma ba ta ga amfanin furtawar ba balle ta ɗagawa jama'a hankali.

Ranar kuma ta kasance Haulatu za su fara zuwa jami'a. Wannan ma na daga cikin manyan dalilan da suka hana ta makara sallar Asubahi, kusan kullum ma Umman ke tashinta. Ta yi wankanta fes an sha hoda da kwalli, doguwar riga mai haɗe da mayafi ta saka sai ko jakarta da ta rataya. Komai sai da ta tabbatar ya yi tsaf kafin ta ɗauki facemask ta zura a gefen aljihun ƙaramar jakarta da zummar sai ta isa za ta saka. Kai tsaye ta sauko falon ƙasa inda su Umma ke karyawa tare da Hajja, Hajjar ce ma ba ta jin dadi za su je asibiti. Bayan an gaisa take ƙara yiwa Hajja sannu da jiki sannan ta yi zaman kari. Baba Saude sai tsokanarta take yi wai duka wannan kwalliyar na zuwa jami'a ne? Ta yi dariya kawai, tana kula da Ummanta sam ba ta da walwala sai murmushin yaƙe, sai da ta kasa haƙuri ta ce.

"Umma, kema ba ki da lafiya ne?"

Umman ta girgiza kai, ba ta kuma ji wani mamakin tambayar da Haulatun ta yi ba, kaf duniya babu mai iya karantarta kamar ita.

"Lafiyata kalau, maza dai ki yi ki ƙarasa kar ki bari ƴan uwanki su yi ta jira."

Ta amsa da toh ba don ta gamsu ba, a ganinta ai yanzun duk damuwar da mahaifiyarta za ta shiga yanzu mai sauƙi ne tunda dai sun rabu da Ɗan Mutuwa. Miƙewa ta yi ta yi musu sallama gami da kallon Hajja.

"Toh Hajjaju, sai a dawo cin gumba ko?"

Hajja ta yi mata daƙuwa murya a ƙasa ta amsa.

"Nan da kike gani sai na kai uwarki kema na kai ki ɗakin miji."

Haulatu ta yamutse fuska.

"Taɓ, ashe kuwa za ki yi mutuwar zaune da jiran tsammani."

Daga haka ta yi gaba ta bar Hajja na mitar za ta dawo ta same ta yayinda Umma ta kalli Hajja kawai ba ta ce komai ba. Ita ina ta ga wani aure yanzu? Ai sam ita tsoron ma ƙara auren ta ke yi, amma ta kula sosai mahaifiyarta ke son nan gaba idan hankalinta ya ƙara nutsuwa ta cika watan da ya yi mata saura na idda toh ta samu miji ta yi aure.

***
A ɓangaren Baba Alhaji suka haɗu da Radiya, ita ma Safina ta ke jira ta kammala su taho. Ganin Safina ko kaya ba ta gama sanyawa ba ne ya ɓata ran Haulatu, ta dubi lokaci, ƙarfe tara saura ƴan mintuna.

"Kai please Feenah, ya ci ace yanzu muna skul fa."

Yanayin murya na yanga da ƙasa ƙasa da ta yi amfani da shi ne ya sanya suka sanya dariya baki daya.

"Inye, ka jimin yarinya da iyayi. Toh an ƙi a yi saurin, ni ji nake ma kamar na fasa zuwa fa. Duk tsoro nake ji." Cewar Safina. Radiya ta karɓe.

"To yi zamanki, kinga sai mu cewa Baba Alhaji kawai aure kike so."

Ta kai mata duka da ɗankwalinta, sua yi dariya kafin a gaggauce ta kammala shiri, sun sani lokutan karatunsu sosai zai iya bambanta tunda kowacce da ɓangarenta. Yau ma kamar yanda Najeeb ya faɗamusu, ba lallai ne su samu darasi ko guda ba tunda a cewarsa har lokacin wasu na ta registration. Dayake can yake kuma yana ajin ƙarshe inda yake karantar business admin, lokutan da ba shi da makaranta ne suke zuwa kamfani wurin Yaya Sadauki shi da Haidar. Shi ma Haidar can yake sai dai shi ɓangaren Accounting yake.

Aikuwa dai koda suka je ɗin, ba wani karatun aka yi ba, amma sun ɗan ƙara wayewa kan abin da kuma sanin makarantar tunda Najeeb ne ya zagaya da su da kuma yi musu bayanan abubuwa da dama gudun kar su sami matsala.

A hanyarsu ta komawa gida ne wayar Haulatu ta yi ƙarar kira. Ganin Hindatu ya sa ta ɗagawa, suka gaisa, jin muryarta da yanayin damuwa ne ya sanya ta ba ta uzurin tana kan hanyar gida ta bari za su yi magana idan ta nutsu. A dole suka yi sallama ita kuwa Haulatu ta san ai dama Hindatu zai wahala ta rabu da matsala tunda shi ta aura. Zama da irin Ɗan Mutuwa ai sai wacce ta shirya. Ta kan ji baƙin cikin tuna shi ne mahaifinta. Sai dai ta yi imani da ƙaddara komai ma da zai faru mai kyau ne tunda haka Allah ya tsara.

"Ke Haulatu, nikam dama ina ta so na tambayeki, Anti Zaituna kuwa tana da labarin abin da ke faruwa?"

Maganar Radiya kenan wacce ta katse tunanin Haulatun. Ta yamutse fuska don ba ta ma son a yi mata tunin Yaya Zaid. Tun da ta samu labarin tijarar da ya yi a gaban Hajja ta ji ya ƙara ba ta haushi.

"Ta sani mana, toh me ta ce? Kin san ai tana da fahimta, ita koda ta kira ni ta yimin zancen cewa ta yi na dage da addu'a duk abin da yake alheri ne, Allah ya tabbatarmin a rayuwata. Amma bayan haka ba ta ƙara zancen ba."

"Allah Sarki, ai fa kin san Anti Zaituna babu ruwanta. Za'a iya cewa soyayyar Yaya Zaid ma kawai ƙaddararta ce." Faɗin Safina kenan.

Jinjina kai Haulatu ta yi don ba ta cikin yanayi na son magana. Daga haka har suka isa babu wanda ya ƙara tankawa. Koda suka dawo gida sai wuraren yamma ta tuna da Hindatu ta kira ta a waya.

"Kashe zan kiraki kar na ƙarar maki da ɗan katin naki." Cewar Hindatun. Ba musu kuwa ta katse kiran tana murmushi, a ranta tana faɗin Allah Sarki, da ace Hindatu za ta ga yanda take gudanar da rayuwa maikyau a nan da ta sha mamaki. Sai ta ji kamar ba ta kyauta mata ba bisa duhun da ta bar ta a ciki, duk kuwa da yanda suka kai ga aminci. Amma kuma ai ta yi ne saboda tsaro. Ba ta kai ga ƙarasa tunaninta ba, Hindatun ta kira. Suka gaisa nan ta soma magana.

"Haulatu ina fa cikin damuwa babba, na rasa ya zan yi wallahi."

Sai da Haulatu ta ji faɗuwar gaba, ta dai daure ta ce.

"Mene ne ya faru kuma Big Mama?"

"Um, ba za ki gane ba. Don Allah ya za'a yi ka dinga rayuwa da miji wanda ba ya son sallah? Wai fa gaba daya Ibrahim bai damu da ibadarsa ba. Kinga ba ya sallah kwata kwata sannan ko karatun Alkur'ani ya shigo ya tarar na kunna a gidan zai hau ni da faɗa yana nunamin shi gidansa a tsarkake ya ke, ya sanya an zo an yi sauka sama da goma don haka na bar kunnawa idan ma zan ji wai na saka earpiece. Ki ji fa don Allah? Sai abu na biyu, ba shi da wasu shaƙiƙan ƴan uwa a nan kusa, nayi nayi ya kai ni na ga koda wasu a danginsa ne ya nunamin shi da kowa, ga wata Hajiya Adama ya ce nan duniya idan ina neman yar uwarsa ta jini na same ta na gama. Toh ni gaba daya hankalina ya kasa nutsuwa. Kuma kin ga da cikin dare...."

Ƙit, ta ji an katse kiran, gaba ɗaya hankalin Haulatu ya tashi, duk da dai abubuwa ne da ba baƙonta ba ne a rayuwarsu tare da Ɗan Mutuwa, ta sani sarai sai ya ga dama ya ke sallar asubahi, shi ma a cikin gida ba ya taɓa zuwa masallaci, sauran sallolin ko ba za ta yi hukunci ba tunda a waje yake wuninsa. Amma abin ya ba ta tsoro, babu ma kamar Hindatu da tausayinta ya lulluɓe ta. Kamar ta bi bayan kiran sai ta fasa tunda ba ta san dalilin katse kiran da Hindatun ta yi ba. Kar ta haifar mata da matsala. Kwanciyarta ta gyara saman kujerar tana mai zurfafa tunani na wannan irin Uba nata a ƙarshe daƙyar ta watsar.

***

Kano...

Hindatu wacce ta shagala tana waya da Haulatu, sam ba ta ji tsayuwar motar Ɗan Mutuwa ba sai ganinsa ta yi ya shigo falon, babu shiri da sauri ta yanke kiran a matukar tsorace. Idanunsa na kanta fuskar nan a murtuƙe ya ƙaraso ciki sosai. Sai da ya bi wayar da kallo sannan ya maida dubansa gareta.

"Sannu da zuwa." Ta yi ƙarfin halin furtawa. Ya gyaɗa kai gami da cire babbar rigar dake jikinsa sannan ya nemi wuri ya zauna.

"Hala da saurayinki kike waya ganina ya sa ki tsorata?"

Yanayin da ya yi maganar cikin nuna halin ko in kula balle kishi sai ya ba ta mamaki musamman ganin ya saki har da murmushi.

"Saurayi kuma? Ina da aurena? Ka na mijina kana min wannan magana?"

Ya taɓe baki.

"Toh mene ne don kin ajiye mai ɗebemaki kewa idan ba na kusa? Ni sam kar ki damu ba ni da matsala dangane da haka. Rayuwarki ce, kamar yanda nake gudanar da tawa rayuwar ba na son a sanya min idanu, haka ba zan tauyeki ba kema."

Daga haka ya miƙe yana buga uban hamma don dama jiya ba gidan ya kwana ba shigowarsa kenan da yammacin wai yana da baƙi daga ƙasar waje zasu yi meeting a Hotel, kamar dai yanda ya faɗamata.

Ta kasa magana gaba daya tamkar wacce ta haɗiyi dutse. Ƙirjinta har wani bugu yake da sauri.

"Oh, ki sa Favour su shirya abincin mutum uku, wasu amintattun yarana na wurin aiki za su kawo min ziyara anjima da ƙarfe takwas. Sannan kar ki sake ki tashe ni a bacci don na sanki."

Daga nan ya wuce ya nufi ɓangaren ɗakinsa. Ita kuwa Hindatu hawaye ta shiga fitarwa cike da al'ajabin wannan irin watsewar. Mijin aurenta ke ba ta lasisin kula wasu samarin a waje da sunan soyayya? Wannan wane irin masifa ce ta aura? Ta yi kuka sosai kafin kuma ta tuna da saƙonsa ta ja waya ta kira Favour. Nan ta sanar da ita saƙon Maigidan kafin ta tattara kuma ta shige ɗakinta don har wani jiri take ji ga mararta da ke faman ɗaurewa ta ƙasa. Dama kwana biyun nan haka yake mata, likita ta ce ta rage sanya damuwa a ranta zuwan ƙarshe da ta yi, amma abubuwan ne sun fara shallake tunaninta.

***
Katsina...

Washegari kuwa koda suka je, su duka babu wacce ba ta fara karatu ba, sai dai Radiya ce ma suka yi har darussa biyu. Su kuwa haka suka cinye sauran lokacin ba a ƙara musu komai ba.

Ruwa kawai Haulatu ta watsa ta sauya kaya sannan ta fito don cin abinci. Tana ji Hajja da ta ɗan samu ƙarfin jikinta ba kamar jiyan ba tana ba Umma labarin rikicin da Maimuna ke ciki yanzu da mijinta akan dukanta da yake. Faɗi take.

"Idan na dauki mataki na ce ba za ta koma ɗakinta ba sai cibi ya zama ƙari a wurin su Yaya Dakta, su bi su ce na ɗaurewa yarinya gaba ta ƙi zaman aure alhalin su ba su san irin wahalar da ta ke ci ba. Shi kuma ubanta (Mijin Haj Hadiza) tunda ɗan ƙaninsa ne sai ya rufe idanu ya ci mutuncin ɗiyarsa a kansa, tsabar tsoron uban ma da suke yi ba sa iya buɗe masa cikinsu sosai. Toh wannan karon idan Salahu ya yarda na taka na dauko Maimuna, ta bar auren kenan har abada tun da ba shi da mutunci."

Umma dai haƙuri ta ke ba Hajja tana nunamata ya fi kyau a kira a yi mishi nasiha da kuma gargaɗi akan dukan, tunda dai ai babu mai son mutuwar aure sai dole. Haulatu kuwa dake gefe tana cin abinci tana sauraronsu duk sai ta ji ta tsani mijin Maimunar da aka kira Salahu, a duniyarta duk wani azzalumin miji mai dukan matarsa ba zai taɓa burgeta ba. Kamar ta tsoma musu baki a hirar sai kuma ta tuna hakan ba daidai ba ne, a baya dai ta sha yi, kuma ta sha ɓatawa Umma rai akan hakan. Yanzu kam ta nutsu ta bari.

***
Bayan Kwana biyu...


Tana kwance a gado tana duba abin da aka yi musu a aji yau, gaba daya ita ba ta ma fahimci darasin ba balle ta iya aikin da malamar ta ba su, ta yanke tashi zuwa ga Fu'ad ƙanin Sadauki wanda shi ma fannin da yake karanta kenan amma yanzun shi yana aji na biyu, ta san dai za ta sha wulakanci tunda ba shiri suke ba, amma fa a kan karatun nan ta gwammace da dai ace ta ba kanta da ma Yaya Sadauki kunya, gwara ta jure cin kashin Fu'ad din muddin zai koyar da ita.

Wayarta ta yi ƙarar shigowar saƙo ta whatsapp, kamar ta share sai dai hango sunan Sister Zaituna da ta yi ne ya sanya ta buɗe.

"Yayana ya yi min zancenki, ya ce na yi hakuri na yafe masa laifukan da ya yi min a baya, kuma na taya shi yaƙi don ya same ki tunda wai a yanda yace na san yanda soyayya take."

Wannan saƙon mai ban haushi da mamaki da bayyana rashin tsoron Allah da kunya irin na Yaya Zaid, shi Anti Zaituna ta aikomata.

"Na fara yarda Yaya Zaid ba shi da hankali wallahi." Ta furta a fili don ta ma kasa amsawa Anti Zaituna don haka kawai ta ja guntun tsaki ta kashe datar ta kwashi kayan karatunta bayan ta zura hijabi ta fito kai tsaye ta nufi ɓangaren su Momi Nuratu bayan ta nemi iznin Ummanta.
Cike da tunanin rashin kai na Yaya Zaid ta ƙarasa ɓangaren Momi Nuratu. Ta kuwa iske ta a falo cikin kwalliyarta na zuwa turakar miji. Ganin Haulatun sai ta ɗan faɗaɗa fara'arta gami da amsa gaisuwarta.

"Lafiya lau Haulatun Hajja, ya Umman taki?"

Tana murmushi ta ba ta amsa da lafiya lau.

"Wani abu ki ke so ne?" Faɗin Momi Nuratu, sai ta ɗan kalli inda Fu'ad da Zuhra suke kowannensu da waya a hannu amma tambayar Momi Nuratun ce ta sa su duban Haulatun wacce ita din ma aka yi sa'a ta kai duba ga Fu'ad din.

"Dama wajen Fu'ad na zo ya koyamin wani Assignment da ban gane ba."

Nan da nan ya haɗe rai gami da zaro ido.

"Wa? Wai ni? Tab! Ai kuwa...zan koya maki."

Ya ƙarashe da abin da ba hakan ya yi niyyar faɗi ba dalilin kaifin idanun Yayan nasu Sadauki wanda ya zuba masa su, shigowarsa falon Momi Nuratun kenan daga na Mahaifinsa. Momi Nuratu ta harari Fu'ad.

"Oh, da ya ke ka ga dodon naka ai ka iya lauyance magana. Je ki ya koyamaki Haulatu."

Ta amsa da toh kafin ta juya ta gaida Yaya Sadauki wanda kwana biyu ba su haɗu ba. Koyaushe kamar ana ƙara masa kyau haka ta ke gani. Ya amsa mata sannan ya ƙaraso ga Momi Nuratu ita kuwa Haulatu ta yi wurin Fu'ad da ya ke harararta a faƙaice. Sai ta bi shi da murmushin ta ci galaba. Shi kuwa babban burinsa Yayan nasu ya bar falon ya gwabza mata rashin mutunci amma ina, su na gama magana da Momi Nuratu, ita ta yi falon Daddy shi kuwa ya ƙaraso cikin falon ya zauna. Ba shiri Zuhra mai danna waya ta ajiye ta jawo jakarta na makaranta, dama ita ma Assignment za ta yi ta ɓige da chatting da ƙawayenta, ita a sannan tana SS2.

Ganin Yaya Sadauki a zaune ya na ta amsa waya yana zuba uban turanci da abokin cinikayyarsa dake a garin Abuja, ya sa Fu'ad a dole soma yi wa Haulatu bayani dalla-dalla, dama Allah ya ba shi baiwa na karatu, duk kuma daƙiƙancinka idan ya iya tafiyar da mai koyo yanda zai fahimta ƙwarai. Sai kuma aka yi sa'a ita ma Haulatun nan da nan ta ke ɗauka musamman idan ta samu mai yi mata filla-filla. Tun tana ɗan ɗari-ɗari saboda Sadauki da ke zaune yana kallonsu jifa-jifa, har ta saki jiki. Sai shi ma Fu'ad ya ji daɗin karatun nasu saboda shi ya na son ya ga yana karantarwa ana masa tambayoyi masu ma'ana, hakan na ƙara sanyawa ya ƙaunaci koyarwar. Ko bayan tashin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login