Showing 138001 words to 141000 words out of 177840 words
Safina sam ba ta da daukar magana asalima cewa Haj Hadiza ta yi, ai babu wani abu, idan kishiya irin masu halin Umma ce a kawomata. Ba irin wadanda ba su san mutuncin mutane ba. Amsar ta yiwa Umma dadi kuma tana gani yanda Haj Hadiza ta haɗe rai wai an faɗamata baƙa, silar dawowar Umman ɗaki kenan.
"Don Allah Umma mene ne ya faru? Na ganki wani iri."
Tambayar Haulatun ya sanya Umman dubanta ta yi murmushi.
"Babu komai, jiki da jini, kaina ke ɗan ciwo, saka kayan ki ɗaukomin magani na sha."
Jin haka kawai ta mike ta zura hijabi tana fadin.
"Bari na karɓo maki a wajen Hajja." Daga haka ta fita da sauri zuwa dakin Hajja don ta san inda take ajiyar magunguna. Suka yi kiciɓus da Maman Safina, bayan sun gaisa take tambayarta inda Umma take, nan ta nuna mata daki ita kuwa ta wuce. Ba jimawa ta dawo, ta iske Maman Safina na ba Umma haƙuri akan abin da ya faru.
"Kya biyewa Hadiza ki ɓata ranki a banza? Waye bai dan halinta ba na shegen ɓakar magana da yada habaici? Don Allah ki saki ranki."
"Babu komai ya wuce. Nima kaina ke ɗan ciwo shi ne fa zan sha magani. Haulatu ina yake?"
Da haka Maman Safina ta ankara da Haulatun sai ta miƙe da kulawa tana mata fatan samun sauƙi, ita kuwa Haulatu da ta tsinci abin da ya faru, ranta ya ɓaci. Dama ta sani ga dukkan alamu wani abin a ka yiwa Umma, ba mace ce mai saurin nuna abu ba, amma idan ya yi mata ciwo da yawa, to fa ba ta iya ɓoyewa sai na kusa da ita ya fahimta. Ba don darajar Hajja ba ai da ta kai ƙara Haj Hadiza wurin Baba Alhaji amma ta sani har Umman ba dadi za ta ji ba. Tana kallo Umma ta sha maganin sai dai madadin ta kwanta kawai ta fice tana cewa Haulatu ta ƙulle ƙofar shiga saman idan ta kammala tunda babu kowa. Ta amsa da toh.
Kwalliya ta yi sosai wanda ya amsa sunan kwalliya sannan ta fiddo ankon da suka yi su uku abinsu babu wanda suka sa a ciki. Tana cikin shiri sai ga Radiya ta faɗo, kusan a tare suka furta
"Wow! Masha Allah." Kowacce na santin kyan da ƴar uwarta ta yi, ita Haulatu na kwalliya da ma yanda ɗinkin ya fiddo Radiya, ita kuwa na kwalliyar Haulatun da yanda ya karɓi fuskarta kai ka ce makeup artist ce ta rangaɗa mata.
"Malama ki sauri ki shirya, ana can ana ta raye-raye. Bikin Maamarmu gida. Kin ga yanda ake bin mu da kallo ni da Safina? Fa'iza da Fahima sai da suka kasa haƙuri suka yi ƙorafin wai meyasa za'a ce babu anko kuma mu yi? Humm, ni nasan dai mun ja magana."
Radiya ke maganar, Haulatu kuwa dariya ta yi lokacin da ta zura riga ta juya baya don Radiya ta taimaka mata da zuge zif ta amsa.
"Ni nasan a rina, ai sai da na ce maku kar mu yi kar ya zama abin magana. Amma Feenah ta dage. Amma ke gwara da aka yi hakan, tunda dai ai kinsan idan mun nuna musu iyayi za su yi su ce bai yi ba."
Haka dai a gaggauce ta yi daurinta mai kyau, ta fesa turare sannan ta dauki mayafinta ƙarami don a farko cewa suka yi ba ma zasu saka mayafi ba tunda cikin gida ne, amma ustaziyarsu Radiya ta ce ita sam a'a. Dole aka nemi mayafin da ya hau da kalar atamfar. Haulatu ta sanya takalminta baƙi mai tudu mai igiyoyi daga sama, duk ta malƙwaye igiyar daga saman ƙafafun, farar fatarnan ta ƙara wa takalmin kyau don ko yaya tsagar ɗinkinta na gefe da gefe ya fito, sai ka hango. Ga lalle an sha.
A hanya ma suna tafe ba su tsira da kallo ba, ƴanmatan sai habaici da kauda kai. Har suka isa ɓangaren Daddy Ridwan haka ake bin su da kallo, su gaida manyan dake wurin su wuce, kowa na yaba kyan da suka yi ban da waɗanda suka shaƙa. Suna isa wurin kuwa wanda ya ƙawatu, sai ka yi tunanin ma hall ne tsabar haɗuwar da ya yi, su na soma bi ta kan red carpet din da aka shimfiɗe har zuwa inda Maama za ta zauna, MC ta sa aka saki kiɗa na sabuwar waƙar Gwanja mai suna Sauti. Idanu duka a kan su Haulatu, Jannat da tawagarta a gefe har wata ashariya ta yi na tsabar hassada da kishi. Nan da nan idanunta suka kada fadi take.
"A gidan uban wa aka ce a yi anko? Wato yan iskan yaran nan anko suka yi ba su sanar ba? Shegu, an fadamusu sun fi mu son Maamar ne?"
Nan dai ta dinga ɓaɓatu wanda rabinsa ma wadanda ta ke yiwa ba ji suke ba saboda ƙarar kiɗa. Safina dake gefe tana ganinsu kuwa ta taso suka haɗe a tsakiya suna rawa, nan fa Mc ta soma koɗa su. Wai ga wasu ƴanmata kamar wasu taurari. Ba su jima ba suka fice, rawa ce ba ta wani murguɗa jiki ba, ta hankali suka yi. Ba jimawa sai ga Maama ta fito bisa rakiyar samarin yaranta huɗu, Khaleefa, Mu'az, Sadauki da Zaid wanda ke faman cin magani, yana daga gefen Khaleefa, shi kuwa Mu'az suna daga dama tare da Sadauki. Abin sai ya burge sosai, Maama ta sha ado har ta gaji da kyau cikin jan leshi, su kuwa sun fito cikin fararen shadda sai dai kowa da kalar tasa, ba anko ba. Nan aka hau sowa da hotuna, Mc na faman roƙon a yi hakuri a zauna amma kamar ba a jin ta. Har Maama ta zauna sannan suka koma mazauninsu, an ci an sha an kuma yi nishaɗantu, kowa a wajen na murna idan ka ɗauke Anti Mabruka dake ƙume a ɗaka ita da ƙawarta.
Kamar yanda idanun Sadauki suka kasa ɗaukewa a kan Haulatu duk motsin da za ta yi a wajen, haka Zaid shi ma don ji ya yi kamar babu gurbin haƙuri a zuciyarsa a kanta. Sam ba zai iya ba. Yau zai tunkare ta, ko me su Baba Alhaji zasu ce yana ji sai dai fa su faɗi.
Haulatu ko hanya ba kama zuwa ɓangaren Hajja don cire takalmin da a sannan tuni ya dame ta. Su ma wurin an tashi domin haramar sallah. Tana isa ɓangaren Hajja saƙo na shigowa wayarta .
"Mu haɗu a garden ɗin Daddy, after magrib. Abeed."
Yaya Sadauki ne. Sai ta yi wani murmushi duk kuwa da cewa ta ji faɗuwar gaba, fatanta Allah yasa abinda take ji a kansa shi ma ya na ji. A yau sai ta ji kamar an ƙaramata sonsa. Ta kuma kasa ɗauke idanu a kansa a wurin, sun sha haɗa idanu sai ta yi maza ta ɗauke kai. Ai kuwa da sauri ta faɗa banɗaki ta yi tsarki da alwala ta kuwa goge kwalliyar tas tukunna kafin alwalar sannan ta fito ta yi sallah.
***
Zaid kuwa a ɓangaren Sadauki suka yi alwala, koda suka dawo daga masallaci shigowa gidan ya yi da zummar neman Haulatu ya yin da Sadauki ya nufi garden zaman jiran hasken idaniyarsa. Mutane duk an tafi shirin yi wa Maama rakiya gidanta.
Sadda Haulatu ta shiga garden din gidan Daddy Ridwan, akan idanun Zaid dake biye da ita, sai kawai ya bi sahu.
***
Mu hadu gobe idan Allah ya nufa.
Tun kafin ta ƙarasa ciki sosai ta hango shi zaune saman kujera mai lilo ya kwantar da kai yana kallon sararin samananiya. Lokacin ya cire babbar rigar hakanan kansa babu hula. A hankali ta ke takawa har ta ƙarasa inda ya ke, kasancewar ta sauya takalmi zuwa flat, ya sanya bai ji tahowarta ba sai sallamarta da ya cika dodon kunnensa. Ya buɗe idanu ya kalle ta yana mai amsawa da yi mata nuni da gefensa.
"Bismillah." Ta zauna jikinta a sanyaye, ƙamshin turarensa mai haifar da nutsuwa ya na bugar hancinta. Ya zauna sosai gami da ɗan dafa gefen kujerar yana kallon fuskar da ba ya taɓa gajiyawa da kalla. Ita kuwa dake duban ɗan adon da aka yi a tsakiyar wurin ta sani ita ya ke kallo don haka duk sai ta kasa sukuni kaɗan. So ta ke kawai ta ji meke tafe da shi.
Zaid wanda ke bin Haulatu a baya, ya yi matuƙar fusata ganinta zaune tare da Sadauki, ya ji kishinta na neman kashe shi da ransa. Kamar ya ƙarasa sai kuma ya juya kawai ransa na suya, ya yi alƙawarin ba zai rasa ta, Sadauki ya samu ba. Wannan ba mai yiwuwa ba ne.
"Kin yi kyau fiye da kullum."
Maganar Sadauki ya katse tunani da fargabar da ta tsunduma ciki. Sai ta ma kasa haɗa kalmar godiya ta furta don mamaki, abin ta ji shi banbarakwai, sai da ta ɗan yi gyaran murya kafin ta amsa.
"Nagode."
"Haulat."
Yanayin da ya kira sunan ta ji shi har ranta, ta kalle shi, amma kuma ta kasa jure kallon da ya ke jifanta da shi hakan ya sa ta sauke kai tana wasa da gefen mayafinta.
"Uhm, ba ki amsa ba?" Ya yi tambayar cikin kwantar da murya. Ta lumshe idanu sannan ta bude.
"Na'am."
"Ke ta musamman ce a wurina, kin samu matsayi irin wanda ban taɓa hangowa zan ba kowace ɗiya mace shi ba. Tun ina ganin kaina a cikin madubi, har ta kai idan na kalla sai dai na ga fuskarki tana min gizo. A taƙaice, ki na cikin manyan burikana ma rayuwa a yanzu."
Wai Allah! Haulatu sai ta ji kamar ta nitse a inda ta ke don dadi da kuma kunya. Ta ma nemi fassarar abin da ya ce ta rasa a kwakwalwarta. Ba ta gama farfaɗowa ba ya ƙara jefa zuciyarta a shauƙi da kalamansa.
"Haulat, na yi iyakar ƙoƙarin na ga na haƙura da komai har zuwa sadda koda ace ba ki kammala karatunki ba, to ya kasance kin cimma tsakiyarsa. Ni mutum ne da ba na son tauye ra'ayin abin sona koda kuwa zan cutu, dalili kenan da na zaɓi ƙarfafa maki gwuiwar cika muradinki. Sai dai nikam na gaza, haƙurin ya kasa tasiri a kan soyayyarki."
Ya ɗan numfasa, shiru ya biyo baya na sakanni, wayarsa na ƙara amma bai ko damu da dubawa ba. Haulatu babu ita sai gangar jikinta, amma ruhi da tunaninta kacokam sun lula wata sabuwar duniya wacce a baya mafarkinta kawai take yi, a yanzu kuwa ga ta nan a zahiri a gabanta, ga Abeed Sadauki da kansa shalelan Baba Alhaji, ya na amayar mata da abin da ya ke ji a kanta. Ta kasa kallonsa duk kuwa da yanda take ji zuciyarta na ingiza ta da son ta kalle shi ɗin don ta ƙara samun tabbaci wai wadannan kalaman daga bakinsa suke fita, sai dai tana jin nauyin su haɗa idanu.
"Ba zan tauyeki ba, zan ba ki wadataccen lokaci daga nan har zuwa jibi, duk abin da ki ka yanke a kaina, ina roƙon ki kar ki ki nauyina, koda ta saƙon waya ne, ki sanar da ni. Koda ace ni Abeed ba na daga cikin jerin irin mazajen da ki ke fatan ɗayansu ya kasance matsayin miji a gareki. Feel free ki faɗamin. Na maki alƙawarin zan fahimceki daidai gwargwado in sha Allah."
Ya ƙarashe zancen da wani sanyin murya da na jiki, sai a lokacin ya kai hannu ya ɗauki wayarsa, Khaleefa ne, tambayarsa inda ya shiga ya yi don ana ta shirin tafiya kai Maama gidanta, ya amsa da yana tafe. Ita kuwa yana amsa wayar ne ta dube shi, kalamansa sun haifar mata da daɗin ƙauna da kuma wani tausayinsa a rai. Ta ya ya za ta ce ba ta son namiji irin Yaya Sadauki? Ganin ya ajiye wayar ta yi saurin kauda kai. Ya yi murmushi.
"Oh, kin ga za'a tafi rakiyar Maama a bar mu ko? Tashi mu je."
Kamar jira ta ke kuwa ta miƙe, saurin da ta yi har sai ta ya ɗan kalle ta ya ƙara murmusawa. Suka jera kowa da tunanin da ya ke. A ɓangaren Sadauki, wani ɓangare na zuciyarsa na son tabbatar masa cewa Haulatu fa tana son shi, yayinda gefe guda ke kashe masa wannan ƙarfin gwuiwar cewa ba haka bane, karatu ne a ranta, watakila ma girmansa ya zube a idanunta. Ko kuma tana shawarar kai sunansa gaban Baba Alhaji shi ma. Bai damu da mutanen da ke bin su da kallo tun daga farfajiyar gidan Daddy Ridwan ba har suka fita zuwa can filin parking na babban gidan baki ɗaya inda tuni motocin tafiya sun hallara jama'a na ta shiga. Mamin Khaleefa dake tsaye tana magana da Jannat akan inda ta kai mata ƴar jakarta, ta hango su. Sai da ta ji gabanta ya fadi, Jannat ma idanunta da ya kai kansu sai da ta ji wani jiri na neman kwasarta. Safina da Radiya baki suka saki suna dubansu, wai dama duk wannan uban neman da suke yiwa Haulatun, tana tare da Yaya Sadauki? Ai hatta Momin Mu'az sai da ta ganewa idanunta, balle kuma Zaid wanda ya ji kamar ya ƙarasa ya shaƙe wuyan Sadauki saboda tsananin kishin dake cin zuciyarsa.
Haulatu ta dubi Sadauki kamar ta yi kuka ta ce.
"Bari na je na dauko wayata."
Murmushi ya yi gami da kashe ta da wani kallo wanda ya sanya ba shiri ta kauda kai ta juya ta nufi ɓangaren Hajja. Aikuwa Safina da Radiya kamar jira suke suka mara mata baya. Shi kuwa Sadauki kai tsaye ya nufi motar Khaleefa wanda shi ma tun zuwansa idanunsa ke kansu yana murmushi mai ma'ana biyu, a gefe na taya ɗan uwansa murnar samun cikar buri, a wani ɓangare kuwa taya kansa jimamin rasa wata zarah mai haskaka duhun dare.
"Na shiga uku! Wayyo Allahna! Mami zan mutu." Cewar Jannat tana kokarin kifewa a wurin tsabar baƙin ciki da zafin da ƙirjinta ke yi.
Mamin Khaleefa da sauri ta tare ta gami da yi mata raɗa a kunne.
"Ke nutsu don Allah, mene ne haka za ki bar mana abin magana? Ba kya ganin da mutane a wurin?"
Sai a sannan Jannat da idanunta suka kaɗa ta kalli gefensu, Amarya ce kishiyar Momin Mu'az tsaye a gefe ita da Maman Safina suna taɓa hira. Can gefe ɗaya su Fa'iza ne da su a Nusaiba ƙanwar Mu'az. Dole ta hadiye kuka da tashin hankalinta amma fa jikinta ma rawa yake yi. Sai wanda ya raɓe ta zai fahimci haka.
Haulatu kuwa koda suka haɗu da Umma ba ta tambaye ta daga inda take ba tunda su Safina sun zo har nan nemanta, sai dai tambayar na ranta, yanzun hayaniyar jama'a da shirin tafiya rakiyar Maama.
Tana shiga ɗaki ta ji tashin muryoyin Safina da Radiya a bayanta da sauri ta waigo.
"To Laila ta Majnun!" Cewar Safina. Ita kuwa Radiya kira take.
"Rabu da ita, wato ta samu Yaya Sadauki ta mance da mu ko hotunan kirki yau ba mu ɗauka ba ko?"
Ajiyar zuciya ta sauke babu wanda ta ba amsa sai ma ta juya da borin kunya tana jan guntun tsaki da bude sif ta ciro wayarta lokaci guda tana ƙoƙarin ɓoye murmushinta.
"Ni ba zan biyemaku ba. Mu je kar a tafi a bar mu."
Radiya da Safina suka dara gami da cafkewa.
"Ko an tafi za'a dawo, mu da muke da mota a hannu? Ko ya kika ce ƴar uwa?" Faɗin Safina. Radiya ta amsa da kwarai kuwa tana dariya.
Ita dai harararsu kawai ta yi sannan ta soma tafiya.
"Idan kun fito kwa rufe ƙofar ku ba Hajja muƙulli."
"Aa jira mu." Sai ta tsaya daga falon ta ba su baya tana ta murmusawa, yau jin ta take yi kamar a wata duniyar ta daban. Wai haka soyayyar take da daɗi dama? Tambaya da babu mai ba ta amsa. Har suka rufe suka zo gefenta ba ta sauya daga yanayin murmusin da take ba. Hakan ya sa suka yi murmushin su ma ba su ce mata komai ba, sun san dai za ta ba su labari idan dai Haulatu ce.
Motar Yaya Sadauki, Maama ce ta shiga, don haka suka shige motar siena ta gidan. Gidan Maama ya haɗu iyakar haɗuwa, kayayyaki masu tsada da kyau su Khaleefa suka zuba mata. Su hudun musamman ma Khaleefa, Zaid da Sadauki wadanda suka fi Mu'az samu sosai, sun yi iyakar ƙoƙarinsu wajen yi wa Maama kaya na gani na faɗa wanda jama'ar wurin suka ce ko gidan budurwa ƴar gata sai haka. Ba a wani jima ba duka aka watse, Safina an sha kukan rabuwa da Maama, dama ko bayan ɗaura auren ta yi kukanta ta ƙoshi, ita yanzu kam ta san zaman gidan ba dadi zai mata ba tare da Anti Mabruka, zama ne na haƙuri, da kuma ace ta yi wannan zaman ta gwammace ta tattara ta koma gidansu. Dama tuni ta yanke hakan, Mamanta dai ba ta ce mata uffan ba, shi ko Abbanta ya ce babu takura duk yanda ta ke so hakan za'a yi.
Koda suka dawo kowa ɓangarensu ya yi, Haulatu ta shiga dakinsu ta watsa ruwa ta yi alwala ta sa kayan baccinta, sallar isha'i ta gabatar da nafila kafin ta miƙe ta nufi ƙasa sanye da hijabinta, ita sai a lokacin ma ta tuna da yunwar cikinta. A hanyar sauka ne ta ci karo da Fahima wacce ita ma tuni labarin ganin Sadauki da Haulatu ya je mata, a bakin su Fa'iza. Za ta gifta ta, kusan tana sani ta sanya mata ƙafa aikuwa ta yi wata irin kifawa ta tafi tun daga tsakiyar benen har ƙasa, nan da nan bakinta ya fashe, wayar hannunta kuwa wata irin faduwa ta yi da screen din ya tsage. Mutanen dake zaune a falon suka yo kanta suna salati, Fahima tuni ta hayewarta sama da gudu-gudu, gudun kada a zarge ta.
"Sannu, garin yaya haka?" Faɗin wata dattijuwa cikin baƙin Malumfashi.
Ita kuwa miƙewa ta yi. Hawaye ta soma, ba na komai ba sai na baƙin cikin wannan abu da Fahima ta yi mata, ita ta sani da gayya ne, amma