Showing 66001 words to 69000 words out of 177840 words

Chapter 23 - FITAR TSIRO COMPLETE HAUSA NOVEL BY RUFAIDA UMAR

11 Jul 2024

79167

rayu ya siya gida ba, sai ya siya can cikin wata ɓoyayyar unguwa wadanda duka sabbin gidaje ne. Wani irin akwati ne wanda duk sadda ya buɗe bayan ya karanta wasu siddabarunsu, toh fa zai gan shi cike maƙil da sabbin kuɗaɗe ƴan dubunnai.
  Ɗan Mutuwa jin sa yake a sabuwar duniyar da bai taɓa hasko kansa ciki ba. Ashe haka kuɗi su ke da masifar daɗi? Tabbas ya yarda shiyasa Hajiya Adama ke mishi kallon baƙauye tunda bai san ya zai sarrafa aljihunsa ba ya zama abin burgewa a wurin jama'a. Yanzu kam suturu ya siye su kuma ya bada ɗinki, shi kansa ya sani idan sallah ta zo toh fa zai yi bushasha. Ga mota da ya yi odar ta daga Lagos za ta iso kafin sallah. Abu ɗaya zuwa biyu da ya yi mishi saura a yanzu, aure ne na farko. Sai ya zaɓa kuma ya darje. Yana dai sha'aninsa da matan waje. Yanzu kuma tunda akwai kuɗi, buƙatarsa ta biyu kuwa, nemo Na'imatu. Ko ba komai ta ga yanda rayuwa ta sauya mishi. Kuma zai bi duk wata hanya na ganin ya mantar da ita komai da ya faru a baya, su dawo da ɗiyarsa, har yanzu wannan mummunan ƙudurin da ya yi game da Haulatun yana ransa. Idan ma za ta kawo tangarɗa ai ga Uban Dodo nan, sai a tsaface mishi su ta yanda duk abin da ya ce to fa lallai hakan za su bi. Ko kara idan bai ce su tsallaka ba, ba za su tsallake din ba. Wannan ne mafarkinsa.

***
Katsina...

Malama ta dubi ɗanta a nutse, fuskokin kowa cike da murnar gobe za'a tashi da sallah sakamakon azumi da aka yi guda ashirin da tara cif kuma aka ga watan sallah. Tun safe suka iso Katsina daga Abuja shi da Jalilah don yin sallah a nan, ita kuwa sai bayan biki ma za ta koma.
Bayan falon ya rage daga Malama sai ɗan nata ta soma magana.

"Meke damunka ne haka? Gaba ɗaya ka rame sannan kallo ɗaya za'a yi maka a fahimci kana tattare da wata damuwa. Ko an yi wani abu ne?"

Zaid ya ɗan yi murmushin yaƙe.

"Babu komai Ummi, azumi ne kawai."

Ta ɗan yi shiru kamar ta ƙara magana sai kuma ta share.

"Ai shikenan."

"Bari na kai ta gida." Yana nufin Jalilah, Malama ta gyaɗa kai.

"Toh, Allah ya tsare. Ga saƙo ma ina ajiye da shi, yaran nan na dinga bi su kai min babban gida amma kowanne sai ya lafke wai azumi. Jikar wajen Hajja na siyawa sarƙar nan, Haulatu. Ka shiga da kanka ku gaisa da Hajja ka ba ta."

Nan da nan yanayin fuskarsa ta sauya. Hajja dai? Wai Allah, matar da ta faɗamasa magana a bainar jama'ar gidan gaban ƙannensa? Wannan shi ne ga samu ga rashi, abin da zuciyarsa ke kauna ta faɗo a muhallin da ya sani har abada ba zai samu ba. Yau kam daga ma yanayin fuskar mahaifiyarsa babu wasa a zancenta. Kafin ya yi magana ta tari numfashinsa.

"Har sai yaushe? Sai zuwa wane lokaci za ka cire komai a ranka ya zama tamkar ba'a taɓa yi ba? Kar fa ka manta kai ne babba a gidan nan, yau a dalilinka, daidai da Kamalu ba ruwansa da sashin Hajja saboda kai. Wane irin hali na banza na riƙo ku ke da shi? Ina ƙara tunasar da kai, kai din tamkar madubi ka ke a wajen ƙannenka, idan ka ce abu fari ne, toh su ma a wajensu hakan take babu sauyi. Duk kuwa abin da ka baƙanta shi, ka lura da kyau su ma a wajensu baƙi ne. Riƙo ba ya daga cikin halaye masu nagarta a rayuwar duk wani musulmi na ƙwarai. Ballantana wacce ka riƙe a rai, ba sa'ar yin ka ba ce. Uwa ce a wurina ni mahaifiyarku. Sai dai ka sani, gyaruwar mu'amala tsakaninka da Hajja ya zame maka wajibi muddin ina raye kuma na isa da kai koda kuwa ace silar gyaran a ɓangarenta shi ne aura maka Zaituna."

Duk a maganganun Malama babu wanda ya daki zuciyarsa ta kar furucinta na ƙarshe, wato tana nufin koda ace sulhunsa da Hajja shi ne ya auri jikarta Zaituna toh ya zama dole a wajensa? Ga dukkan alamu kuma umarni ne na kai tsaye, sai jikinsa ya yi sanyi. Bai taɓa ganin Malama cikin yanayi na damuwa da ɓacin rai mai yawa kamar na yau ɗin ba, kuma duk a silarsa. Ita kanta ta sani dole a ga kamar tun farko da laifinta, ya nuna ba ta isa da yaranta ba kuma babu mai iya tanƙwara shi tunda har su Baba Dakta sun mishi faɗa da nasiha akan rashin jituwarsa da Hajja sai dai ko gezau. Asalima ita kanta Hajjar fita ta yi sabgarsa don a cewarta tunda bai ji maganar yayyunta ba, to ita din wace ce? Ya kuma sha zagi sosai a wajenta sadda suka taɓa haɗuwa a ɓangaren Baba Alhaji, lokacin Alhajin bai jin dadin jikinsa. Ta ce idan har sai Zaidu ya gaishe ta za ta rayu toh ya riƙe gaisuwar, ta gwammace mutuwarta.

Runtse idanu ya ɗan yi tunano kalaman Hajja masu zafi.

"Ki yi haƙuri Umma, zan gyara. Zan je da kaina bisa umarninki."

"Idan ma ka ga dama kar ka je Zaidu, cigaba da nunawa duniya ɗan mace ne kai da ba ta isa ta sanyaka ka yi ba. Ka yi ta nunawa duniya ban yi iyakar yi na wajen ba ku tarbiyya ba. Wato kai ba ka san zuru ba ko? Hum."

Daga haka ta miƙe ta bar shi a falon shi ɗaya. Ya ɗan yi jim kafin ya dannawa Jalilah kira akan ta fito su wuce. Sai da ta shiga ta yiwa Malama sallama, Bebi na makale da hannunta ita wai ba ta son ta tafi, Juwairiyya kuwa da yake ta dawo daga Malumfashi cewa ta yi sai ta bita kawai kwana biyu ma sun huta. Ita dai Jalilah dariya kawai ta ke yi. Har waje suka raka ta inda Zaid tuni ya shiga mota ya kunna. Sai bayan ta shige suka yi sallama. Ta ɗan dubi mijinta kafin ta sauke ajiyar zuciya ta kauda kai, ta kula kamar ransa a ɓace yake don ko magana bai mata ba ita ma kuma sai ta ja baki ta yi shiru. Koda suka ƙarasa a zatonta zai shiga gidansu amma sai yace mata dai gobe. Sosai ta ji babu dadi, ko wane irin fushi yake ciki ai bai kyautu ya ƙi shiga gaida iyayenta ba tun da iyakarsu gaisawa a waya. Ya kalle ta.

"Akwai matsala?" Ta share ƙwallar da suka cicciko mata kafin ta girgiza kai.

"Buɗe boot na dauki jakar kayana."

Koda ya bude ta dauka ta soma tafiya sai kawai ya kashe motar ya fito. Ji ya yi bai kyauta ba a karon kansa. Ba ta san ya taho ba sai ji ta yi ya sa hannu ya karɓi jakar.

"I'm sorry." Ya furta a hankali. Ta dube shi kadan sai ta yi murmushi ranta ya ɗan yi fes, a duniyar mace tana son ta ga an mata laifi kuma an ba ta haƙuri akan wannan laifin, Zaid yana daga cikin masu iya tattali da kuma rarrashi. Shi dai kawai ka kula da harshenka domin ta lura yana da riko. Sai ka dauka ma ya mance abu kawai bayan kwana biyu ya tunasar da kai a matsayin laifi ne ka yi mishi. Ita har mamakin wannan halin ta ke don haka ta ke yawan takatsantsan gudun ɓata masa rai.

***
A can babban gida kuwa, an dinke da murnar dawowa Abba Ridwan da ma Baban Kowa. Kowa dai cike yake da murnar ma gobe sallah. Haulatu tare da Umma suka je har ɓangaren Abba Ridwan suka yi masa sannu da zuwa. Dama sam ba su da matsala da Hajiya Nuratu, mace ce mai fara'a da son mutane. Hakanan shi ɗin ma. Toh kusan a yaran nata ma guda goma cif, Sadauki ne Haulatu ke mishi kallon marar kirki sai ko wasu ƙannensa biyu Fu'ad da Zuhra. Amma hatta da Raudha wacce za'a yiwa aure bayan sallarnan ba ta da daukar kai.

"Su Haule an zo kunce jaka. Toh ko gumamar Makkah ba samu za ku yi ba."

Ta juya ta kalli Fu'ad, yaron da za su yi sa'anni da juna da shi, ya yi maganar ne ƙasa ƙasa cikin raɗa don gudun kar Maminsa ta ji. Wani dariya na rainin wayo ya yi, sai ba ta ce masa komai ba ta dauke kai ta rantse kuma sai ta rama ko ba yanzun ba. Hira Umma da Mamin ce ya sanya suka ɗan zaunu a ɗakin don har ƙuryar ɗakinta suka shiga, Mamin ke labartawa Umma labarin ƙasa mai tsarki, ita dai Haulatu duk ta ma matsu su tafi tun bayan da Fu'ad ya yi wannan furucin, wato ma sun zo don a basu tsaraba ne? Ai kuwa zai san ya yi da mai yi.

Sai da suka tashi da zummar tafiya ne suka tsinkayi sallamar Sadauki. Gaba daya suka amsa, Haulatu ta ɗan dube shi. A lokacin sai ta ƙara ganin kamanninsa da Mami Nuratu. Tsawon ne na mahaifinsa. Ƙananun kaya ne ya sanya farare ƙal, rigar ce a ka yiwa adon baƙi daga gaba. Ya russuna yana gaida Umma, ta amsa fuska a sake ita ma. Haulatu ta gaishe shi, ya amsa ba tare da ya maida hankali ga kallonta ba. Ta ɗan bi gefen fuskar da harara.

'Sarakin ƙarfi da yaji, sai girman kai.' Ta fadi a zuci. Tana kallon su Fu'ad duka suka fice daga ɗakin saboda dodonsu ya shigo. Miƙewa ta yi ita ma ganin Ummanta a tsaye. Suka yi musu sallama daga nan suka nufi ɓangaren Baban Kowa. Nan ma sun samu tarba daga Maman Radiya, dama ita mace ce mai hakuri ga zurfin ciki. Ita sam ba ta da magana ma. Duk irin taimakon da wasu za su yi maka, ko yaya idan kana halin na rashi sai an fahimta, kawai dai ba laifi akwai rufin asirin. Amma ko daga bambancin ɓangaren wasu da na su sai ka fahimta. A hakan ma Haulatu ta ji irin taimako da yan uwan ke yiwa Baban Kowa da iyalinsa daga bakin Safina, ta ce hatta da karatun yaran Alhaji Ridwan ya dauke. Abubuwa dai na alkhairai suna samu sosai. Suturu kuwa nan ma Safina ta ce Sadauki na yi musu sosai. Baban Kowa dai an ce yanzun shi ke riƙe da ƙatuwar gonarsu na gado, acewarsa ya fi zaman haka.

***
A hanya suna tafe suna hirar abin da ya shafi rayuwa da Umma. Haulatu ke tuna irin kalar rayuwar makarantar da ta gudanar a baya tana firamare wanda wasu lokutan ma hakanan za ta je makarantar babu abin da ta saka a cikinta, wani lokacin ma babu kudin dinka mata sabon kayan makarantar haka za ta dinga yawo da koɗaɗɗun kaya. Ta ƙara duban Umma tana ƙara damke hannunta kamar wasu ya da ƙanwa.

"Amma yau Umma kalli gidan da Allah ya jefo mu, cikin zuri'ar nagartattun mutane masu halayyar girma."

Murmushi ɗauke saman fuskar Umman ta kalli ɗiyarta da hasken fitilun da ya kewaye gidajen ya haske. Ga wani iska mai dadi da ke gudana a daren.

"Alhamdulillah, ɗiyata ta fara hankali."

Ta yi murmushin ita ma. Umma kuwa daga nan shiru kawai ta yi, mafarkan da ta ke yi kwanakin nan a kan Mijinnata yana matuƙar tsorata ta. Abubuwan dai na tashin hankali da hana sukuni. Sai dai duk sadda ta yi ba ta komawa bacci take tashi ta yi alwala da nafila, wani lokacin shi ke nan ta farka kenan har asubahi. Haka har aka shiga goma ƙarshe da ta hana kanta baccin dare. Babu wanda ta taɓa furtawa, ta dai dage da addu'o'inta ta kuma bar abun a rai.

A falon Hajja na ƙasa su na shiga suka ga mutum a tsaye daga gefe a kofa, shi bai ƙarasa shiga ba, kuma bai fita ba. Yana dai tsaye kamar an dasa shi.

Jin muryarta ya sa shi juyowa gaba daya. Zaid ta gani, shi ma kuma ita ya fara kallo har da sauke wani ajiyar zuciya kafin kuma ya gaida Umma.

Umma ta gane shi, Haulatun ma ba gane shin kaɗai ba, har da tuno labarin dalilinsa na rashin shiga ɓangaren Hajja wanda ta samu daga bakin Safina sai da ta yi, Umma kuwa a ɓangaren Baba Dakta sun haɗu har sau biyu sadda ya je wurin Maama. Ita din ma ta san da tarihin Zaid ba ya shiga wajen Hajja, daga bakin Hajjar. Har sai da ma a lokacin ta ji dama ba ta tambaya ba don Hajja sosai ranta ya yi zafi ta yi ta zagin Zaid har da Mahaifiyarsa don a cewarta har da nata laifin.

Haulatu dai shigewa ciki ta yi ta bar shi da Umma, kai tsaye sama ta nufa don ta je ta fesawa Hajja baƙonta na ranar. Umma ce ta ja shi zuwa falon suka zauna aka ƙara gaisawa duk sai wani ɗar-ɗari yake.

***
Hajja na zaune tare da Baba Saude suna kallon ƙasar Saudia su na hira, sai ganin Haulatu suka yi kamar wacce aka jefo.

"Ke Haule, lafiya? Wa ya biyo ki?" Faɗin Hajja a ɗan birkice.

"Uhum, Hajja wai kinsan waye baƙonki yau? Tab! Wallahi Yaya Zaidun gidan Malama ne su na falon ƙasa ma shi da Um.."

Ba ta kai aya ba sai ga sallamar Umma sun shigo Zaid din na bayanta. Hajja ta miƙe tsaye ranta a ɓaci.

"Zaidu? Idonka kenan a ɗakina? Yau kuma wace gulmar ce ta kawo ka? Ai na ɗauka bakar zuciyarka irin ta arnan farko ne. Na ce maka uban me ka zo yi min? Ko har soyayyar da ta hanaka kallon jikata ya ƙare?"

Zaid ya ji tsaf zai iya shanyewa, duk domin Haulatun da ya samu damar gani. Zuciyarsa ta yi sanyi. Ya na jin ya shirya durƙusawa gaban Hajja ya ba ta haƙuri. Ɓacin ran Mahaifiyarsa a kansa da ma kuma kaunar Haulatun da yake jin tamkar ba zai iya gudanar da rayuwarsa ba tare da ita ba ya sanya shi ƙarasawa ya ɗan russuna gaban Hajja.

"Ki yi hakuri. Ki yafe min."

Kalaman da suka fito daga bakinsa kenan, Hajja ta yi shiru sai huci take, ita kuwa Umma ta saka baki wurin ƙara ba Hajjar haƙuri gami da nunamata tunda har ya gane kurensa toh ta haƙura. Maimakon Hajja ta saduda sai ta fusata.

"Zaidu, ka tashi tun kafin raina ya fi haka ɓaci ka fitarmin daga gida tunda ka mance matsayina a wurin Mahaifin Uwarka, gaabar da ka ɗauka da ni, za ka iya yin ta da Kakanka Alhaji. Toh dakyau, ni Asma'u za ka sha mamakina Zaidu. Ka tashi tun kafin na cusa maka ashariya "

Umma ta kula dagasken ran Hajjar a ɓace yake, kusan ma kamar ta fi Haulatu zafin zuciya. Sai ta kama hannun Zaid ba musu ya miƙe suka sauka yana riƙe da ledar saƙon wurin Malama. Ita kuwa Haulatu sai ta ji ya ɗan ba ta tausayi duk kuwa da a farko ta ji zafinsa sosai na labarin abin da ya faru da ta ji. Amma yanda Hajjar ta rufe idanu har ya durƙusa ta ki kallonsa sai ta ji babu dadi.

"Kai Hajja, gaskiya kin dauki zafi da yawa."

"Ni sa'arki ce? Maza wuce ki bani wuri!"

Haulatu ba shiri ta yi dakinsu, ta yarda dagaske ran Hajja ya ɓaci, ba ta taɓa yi mata kallon banza ba tun zuwansu sai a yau da har ta haɗa tsawa. Ta bar Baba Saude da fadin a yi hakuri, ita kuwa Hajja sai bambamin faɗa take yi wai don me Umma za ta bi shi.

A falon ƙasa kuwa, Umma haƙuri da nasiha mai ratsa jiki ta yi wa Zaid. Ta kara nunamasa muhimmanci zuri'a a duniya, da kuma yanda ta ci wuya a baya a dalilin rasa su da ta yi. Jikinsa dai ya kara sanyi. Ya ce ta taya shi ƙara ba Hajja haƙuri. Daga haka kuma ya miƙa mata ledar da Malama ta aiko shi da ita a ba Haulatu. Ta karba ta yi godiya suka rabu. Ya na ta kallon benen ko za ta sauko amma ko ƙyallinta bai gani ba, haka ya haƙura ya fice.

***
Ranar Sallah...
Gaba daya yan matan dake babban gida da ma mazan aka yi shirin zuwa masallaci. Safina, Radiya da Haulatu sun yi ankon fararen hijabansu da Sadauki ya yi musu kyautarsa. Ba su yi kyalliya ba ta fuska, amma fa sun fito fes. Haulatu atamfarta mai ruwan hoda ta saka. Tun a hanya ta ke kallon wata mata mai kama da Maama amma ita ba ta kai Maamar shekaru ba. Ta ci wani uban gilashi tana tafe yana amsa waya.

"Wannan wace ce wai?" Ta furta a kunnen Radiya dake gefenta.

"Kin san ta mana, kawai ba ku taɓa ganin juna ba. Anti ce, Mabruka ƙanwar Maama autar Baba Dakta. Ita ce ba ta taɓa aure ba duk a yaransa. Watanta kusan uku  ba ta nan, tana Kaduna wurin Hajiyar Soja. Jiya da daddare ta dawo."

Haulatu ta ƙara bin ta da kallo.

"Ikon Allah. Ƴar gayu abin ta." Suka yi dariyar da har sai da ta kalle su kafin su yi saurin kauda kai.

Sai bayan an idar da sallah ne suka taho gidan, tun a hanya Safina ke son yi musu hoto amma Radiya ta hana ta, aikuwa su na shiga farfajiyar gidan suka soma hotuna. Su Haidar ma koda suka iso suka haɗu gaba ɗaya ana ta yi. A haka su Baba Dakta suka iske su tare da su Alhaji Ridwan. Nan fa aka kara gaggaisawa, kusan kowa na farfajiyar gidan har Umma don a sannan ne ake ta shigowa daga masallaci.

"Kai amma Yaya Sadauki da Yaya Khaleefa sun yi kyau wallahi." Jin abin da ya fito daga bakin Safina ne yasa Haulatu da Radiya kallon ɓangaren da ta ke duba. Sadauki da Khaleefa ne da ankon shadda coffee colour sai hular Tangaran. Tsayawa faɗin irin kyawun da suka yi ɓata baki ne. Haulatu ta dube su tana mai ɗora gwuiwar hannunta saman kafaɗar Radiya.

"Ba laifi." Ta furta hakan a fili, haƙiƙanin gaskiya tunda ta ke ba za

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login