Showing 69001 words to 72000 words out of 177840 words

Chapter 24 - FITAR TSIRO COMPLETE HAUSA NOVEL BY RUFAIDA UMAR

11 Jul 2024

79154

ta ce ta taɓa yabon kyawun wani a cikin samarin gidan ba, yau kam ta yaba don dagaske kwalliyarsu ta burge matuƙa. Babu ma abin da ya kara ƙawata kwalliyar face da ya kasance dukkansu fuskokinsu a sake tamkar ba su ne masu yawan shan mur ba. Ta ƙarewa Khaleefa duba kafin ta maida kai ga Sadauki shi ma. Wannan sajen nasa nai sheƙi da duhu ya kwanta ya fita fes.

"Kee! Wai ko mafarki nake yi? Irin wannan kallo da kuma yabo? Dama kin iya shi ne duk sadda muke koɗa su kike wani raina mana hankali."

Maganar Radiyar da kuma tunkuɗe hannunta da ta yi saman kafaɗarta ya maido ta tunaninta. Ta sauke ajiyar zuciya. Kafin ta waske da hararar Radiya, amma ba ta kai ga magana ba aka dinga shelar a taho a haɗu a yi hoto a dole ta gimtse abin da take niyyar faɗi suka ƙarasa inda Alhaji da su Baba Dakta suka zauna saman wasu kujeru da aka ɗauko, yayin da matasan suka jeru daga baya sai ko su ɗin matan daga ƙasa. Ba ta ko kula da wanda ke a bayanta ba ta ja ta tsaya kusa da Safina, tsawonta bai kai na sa ba dalilin kenan da ba ta kare shi daga kallon camera ba. Sai da aka ɗauki hoton Haulatu na ta mamakin rashin ganin Mu'az, tana shirin barin wajen ta ji an ɗan riƙe hijabinta ta baya da sauri ta juyo har tana ɗan tunkuɗe shi da kafaɗarta tsabar kusancin da suka yi. Idanunsu ya tsarke a na juna kafin ta ɗan ja baya kaɗan.

"Ke da ƙawayenki, ku tsaya mu yi na tarihi."

Ba ita Haulatun da ya yi furucin ba, daidai da Safina dake a gefenta sai da ta saki baki tana kallonsa da tsantsar mamaki. Yaya Sadauki dai? Shi ke buƙatar a yi hoto? Safina har da ɗan murza idanunta kaɗan don a haƙiƙanin gaskiya ta yi tunanin mafarki ne take yi. Shi kuwa ya ja baya gami da miƙawa Najeeb wayarsa. Haulatu dai cike da sanyin jiki ta tsaya daga gefen damansa, Safina kuwa daga hagu yayinda ita kuwa Radiya ke daga gefen Safina. Kowa a wurin ya cika da mamakin wai Sadauki ne ke buƙatar a yi hoto. Maama dai kallonsa take amma ba ta ce komai ba sai ɗan murmushi. Khaleefa kuwa hannu ya tsarƙe a ƙirji yana nazarin ɗan uwa kuma abokin shawararsa. Bayan an kammala yi musu hoton ya sa hannu cikin aljihunsa ya fiddo sabbin ɗari biyar da bai san ko nawa bane ya miƙawa Safina.

"Your barka da sallah."

Daga nan ya shiga rabawa sauran mutanen gidan, shi ma Khaleefa ya ba su. Haulatu dai da yan uwanta kamar an shuka su a wurin.

"Wai ba wanda zai mintsile ni na dawo duniyar da na bari?"

Fadin Radiya, aikuwa ba zato ta ji an ba ta mintsili mai kyau a kafaɗa. Ta saki ƴar ƙara ta waiga, ganin Haidar ta kuwa maka mishi harara tana sosa wurin don sosai ta ji zafin mintsilin. Su Haulatu suka kwashe da dariya.

"Kaaii! Wallahi yau dai da alama kun fito a sa'a. Wai Boss ne ke ɗaukar hoto da ku? Tab! Ke ba ma wannan ba, nawa ya baku? Na ga kuɗinku sun fi na kowa kauri, ku yagarmin rabona."

Safina ta yi saurin damƙe hannunta.

"Ai wallahi ba ka isa ba. Mu aka ba, yanzu sai na kiramaka shi."

Dariya Haidar ya yi.

"Bismillah idan za ki iya. Ke da kike da shegen tsoro kamar farar kura. Ni wallahi Safina nasan ma wannan hoton da ku ka yi jinku ku ka yi kamar a ce muku arr ku arce da gudu. Ke kinga yanda kafafunki ke rawa daga tsaye ne?"

Suka kwashe da dariya idan ka ɗauke Haulatu da ta murmusa, dagaske wani irin yanayi ta tsinci kanta ciki amma kuma ta fi ba kanta da rashin sabo da shi. A sannan manya duka an ɗunguma babban falon Alhaji. Bisa al'adar gidan, duk sadda sallah ta zo ana haɗuwa ne a sashin Alhaji banda surukai mata, iya su kawai yara da jikokin a ci a sha ana raha da juna. Abin sosai ya burge Haulatu har ba ta san sadda ƙwalla ta cicciko mata ba, wai dama suna da wannan gatan? Kowa na cin abincin ita sai ta ji ma abincin ya fice mata a rai, murna da farin cikin ganinta cikin dangi haka mai yawa da alfarma ya fiye mata komai a lokacin. Don haka tsam ta miƙe ta cewa su Radiya tana zuwa amma kar su jira ta, ita ta ƙoshi, daga haka ta fice. Umma dama kunya bai bar ta ta je ba, tana can ɓangaren Hajja don har da su Daddy Ridwan da su Engr Faisal duka a wurin.

Tana tafe tana nazari kanta a ƙasa, karo ta kusan yi da Khaleefa wanda ya fito daga ɓangaren Hajja, ya je ne don su gaisa da Umman. Ta ɗago ta dube shi. Gaisuwa karo na biyu ta ƙara yi mishi ya amsa fuska a ɗan sake.

"Dakata." Ta ji ya furta a lokacin da ta gifta za ta wuce shi.

"Ga barka da sallahn ki, ɗazu kin karɓa da yawa shiyasa ban samu damar na ba ki nawa ba."

Ba ta fahimci me yake nufi ba, shi kuwa wani ɗan murmushi ya yi da ta kasa fassara shi. Lokaci guda yana miƙa mata ƴan dubu sabbi dal har guda biyar. Girgiza kai ta yi.

"Aa, ɗazu ai ka ba mu."

Ta faɗi ne don kar ya yi mata dole a karɓar sai dai nan take ya ɗaure fuska.

"Ni fa ba mahaukaci ba ne, ina sane da waɗanda na ba a ɗazun. Karɓa ki wuce tun kan raina ya ɓaci."

'Ikon Allah.' Ta furta a ƙasan ranta sannan ta sa hannu ta karɓa, ba ta kai ga ƙarashe godiyar da ta ɗauko hanyar yi ba ta ga ya yi gaba. Ta bishi da kallo kafin ta taɓe baki ta juya ta yi ciki. Ɗan shinshina kuɗin ta yi.

"Mayun turare, kowannensu da kalar turarensa."

Ta furta a fili, zuciyarta fes ta shiga wajen Ummanta. Ta iske ta a falon kasa tana cin abinci ga jikokin Hajja, ƙaramar yarinyar da suka fara gani farkon zuwansu gidan da kuma wasu yara su uku. Sai kuwa wani yaron ɗan wajen Ihsan. Ga dukkan alamu dai kawo su aka yi. Su din ma abinci suke ci Umma sai aikin gyara take yi musu da baki. Baba Saude ita ma tana daga gefe tana nata lomar.

"Har liyafar ta ƙare kenan?"

Faɗin Umma ganin Haulatun, ta ɗauke idanunta daga kan yaran da ba ta gama tantance ko su waye ba don ta san ba duka ne jikokin Hajja ba tunda mutum biyu kawai ta sani. Ta maida kallonta ga Umman. Lokaci guda ta cire hijabinta ta ajiye daga can gefen kujera gudun kar ya yi datti ta zube saman doguwar kujera.

"Wallahi na ƙoshi, ni bacci ma nake ji Umma."

"Ai fa, aikin kenan. Yanzu ke Haulen Hajja da sallar ma bacci za ki kwanta?"

Ta turo baki jin abin da Baba Saude ke faɗi.

"Eh naji. Toh me zan zauna na yi idan ba baccin ba? Yauwa Umma kun yi magana da Yaya Mu'az? Kwana biyu ba mu yi waya ba kuma ban gan shi ba."

"Mu'az ai a Kaduna ina ji ya yi sallarsa. Kuma ya shigo har nan mun yi sallama, lokacin kun je gidan kitso. Ba kwa waya yanzu ne?"

Ta ɗan yi shiru. Ita ai tun ma sadda Mommynsa ta yi musu wannan wulakancin ta rage shiga harkarsa, ya yi nacin ya ja ta da hirar amma ta watsar da shi ƙarshe shi ma ya yi fushi ya ƙyale ta. Wannan shi ne dalilin da ta san bai ko neme ta ba ballantana su yi sallama ba.

"Allah ya dawo da shi lafiya." Daga nan ba ta sake maganar ba sai ta maida hankali ga tambayar Umman ko su waye yaran.

"Waɗannan biyun ai kin gane su, da Husna mai sunan Hajja ɗiyar Maimuna, sai yaron wajen Ihsan. Saura ukun kuwa yaran kishiyar Ihsan ce suka yiwa Sultan rakiya nan."

Ta jinjina kai. Daga nan tun tana sauraron hirarrakinsu sama-sama har dai bacci ɓarawo ya yi awon gaba da ita.

Can cikin baccin ta ji wani ƙamshin turare mai daɗi, lokaci guda kuma ta ji ana bugun ƙafarta. Ta buɗe idanunta da suka ƙara girma suka yi ja saboda ba laifi ta jima a baccin har wajen sha biyun rana yanzun.

"Tashi ki koma ɗaki, nan ana ta baƙi kin kwanta kina bacci." Muryar Umma ta ji, ta miƙe ta na kallon wanda ke saitinta ya zubamata idanu kamar ya haɗiye. Zaid ne. Fararen kaya ne jikinsa da aka yiwa aiki da golden. Kansa sanye da hular da ta zauna ta yi mishi kyau. Sai da gabanta ya faɗi, ita tun farko ba ta son kallo, ta kuma tsani a dinga kallonta, shi kuma wannan ta lura mayen kallon ne. Ta ɗan taɓa fuskarta, Allah ya taimaka ba ta miyan bacci. Ɗankwalinta da ya zame ya fita a kanta ta ja ta rufe tana mai gyara zaman rigarta da ya buɗe ta sama. Da sauri ta ja hijabinta ba tare da ta tsaya jin ya amsa gaisuwarta ba ko aa, ta haye saman da sauri ko ta kan Bebi mai yi mata magana ba ta bi ba. Umma ta ɗan yi murmushi.

"Yayar taki magagin bacci ne, bari ta wartsake."

Bebi ta yi dariya. Shi kuwa Zaid ajiyar zuciya ya sauke yana ƙara ji kamar Haulatu na tafiya ne da dukkan tunaninsa. Dagaske ya ke ƙaunarta.

Barinta falon sai ya ji ya yi masa girma don haka ya yiwa Umma sallama ya fita zuwa can ɓangaren Alhaji. A lokacin ma tuni an watse sai ƙalilan, Sadauki ba ya nan, hakanan Khaleefa shi ma ya wuce gidansa.

***
KANO.

Yammacin ranar da aka yi sallah, ta fito daga gidan ƙunshi a lokacin ƙarfe biyar da mintoci, gaba daya ba ta samu damar yin ƙunshi ba da sai a ranar. Sa'ar da ta ci ma mai ƙunshin tsohuwar abokiyar karatunta ce a sakandire. Sanye take da doguwar riga na abaya kalar silver, ta yane fuskarta da gyalen abayar. Idan ka gan ta sai ka rantse budurwa ce ba bazawara ba. Ta yi tsaf duk kuwa da cewa ba kwalliya ta yi ba. Wannan ƙibar nata ya ɗan ragu sai hakan ya ba tsawonta damar fitowa. Ko'ina ta kalla a titin cunkoson mutane ne musamman ma da rana ta ɗan yi sanyi. Ba kamar ɗazun da ranar ta buɗe sosai ba. Yawanci ma duk abin hawan da zai zo wucewa to fa a cike yake da ƴan yawon barka da sallah.

Daidai lokacin babban mutumin ya taho zai wuce a motarsa kalar ruwan ƙasa mai matuƙar ɗaukar idanu, gilasanta duka tinted ba ka hango na ciki. Ta ɗan bi motar da ido, sai da ta sauke wata ajiyar zuciya a can ƙasan ranta tana ji inama ta samu arziƙin mallakar irin motar. Ba zato ta ji an yi ribas an tsaya daidai saitinta, sai da kirjinta ya shiga dukan tara-tara, ga wani ɗoki da fatan Allah yasa ba kwatance ne za'a tambaye ta ba, ita babban burinta ma ya kasance dominta aka yi tsayuwar, ta ji a hankali an sauke gilashin motar amma ta waske ba ta kalle shi ba.

"Sannunki ƴan mata." Jin haka ta ɗan ja numfashi sannan ta ɗan dube shi tana wani kashe idanu kaɗan.

Babban mutum ne da alama ba yaro ba, sai dai fa ya jiƙu da naira don wani ƙamshi da sanyi take ji su na bugo ta daga cikin motar. Shi kansa shaddar da ya saka abar kallo ce.

"Yauwa."

Shi kuwa ji ya yi kamar ya susuce da wannan kallon. Anya akwai abin da farat ɗaya ya taɓa shiga ransa kamar wannan baiwar Allahn?

"Idan ba damuwa ki shigo sai na kai ki inda za ki je mu samu damar magana a nutse. Ba girmanmu bane, daga ni har ke a gan mu a titi muna magana. Ina roƙon wannan alfarmar."

Ta ji kamar ta yi tsalle don murna, wayyo Allah. Wannan ai babban kamu ne ta yi, sai dai ta ɗan haɗe fuska kaɗan duk a ƙokarinta na ja masa aji.

"Ah haba dai, don ban san me nake yi ba. Ban sanka ba na shiga motarka? Gaskiya ina tsoro."

Ya yi ƴar dariya. Yana kashe idanu irin na tsoffin ƴan bariki.

"Haba Sarauniyar mata, ki kalle ni dakyau, ni ba kalar mayaudaran samarinku ba ne. Ki shigo na maki alƙawarin babu abin da zai faru da ke. Alheri ne ya kawo ni gurinki har na tsaya amma tunda nake ban taɓa tsayawa wata ɗiya mace a hanya ba. Ki shigo don Allah kinga idanu sun soma zarya a kanmu."

Ta ɗan waiga kadan ganin masu wucewa na kallonsu har da ɗan waige ya sanya ba musu ta bude gidan gaba ta shiga.

'Luntsumi.' Ta furta a can ƙasan ranta ganin yanda laushin kushin ɗin kujerar ya yi wani ƙasa da ita. Suka ɗan dubi juna suka murmusa kafin ya maida hankali ya hau kan titi ya soma tafiya.

"Ai ba irinku ake gani a ƙyale ba. Ga ki kyakkyawa ta ko'ina kalar hutu ce."

Murmushi ta yi kanta yana fasuwa.

"Aa fa, ni ba ƴar kowa a garin nan ba ina na ga hutu?"

Dariya ya yi.

"Ki saka a rai kin samu hutun kin gama. Wannan sallar ta zo maki da alheri kin ji? Mene ne sunan Sarauniyar?"

Cike da jin dadin wannan albishirin da ya yi mata ta ce.

"Hindatu."

Ya jinjina kai da murmushi.

"Ni kuma ana kirana Alhaji Ibrahim. Ina za mu nufa?"

Ta shiga yi mishi kwatance, sai da suka isa har ƙofar gidansu sannan ya dube ta a nutse.

"Hajiya Hindatu, gaskiya ba zan ɓoyemaki ba kin yimin ɗari bisa ɗari. Na fito maki ma a mutum, ni da aure nake sonki. Wallahi ko nan da sati ne idan za'a ba ni aurenki a shirye nake. Ina fatan ba wanda ya yimin shigar sauri don kyakkyawa irinki nasan kina da tarin masu rububin yin wuff da ke."

Ta yi dariya.

"Um um, ni babu wani yanzu da na ba fuskar neman aurena, amma zancen gaskiya na taɓa aure sai dai ko shekara ban rufa ba muka rabu. Ai ko watanni biyar ma ban yi su a gidansa ba."

Ya ɗan ɗaga kafaɗa.

"Wannan ba damuwa ba ce. Ko waye wannan akwai shi da farar ƙafa. Ta ya ya zai saki mace irinki? Ni ma ina da aure da yarinya ɗaya sai dai ba su nan sun yi tafiya mai ɗan nisa. Kusan ni da gauro ma duk ɗaya muke. Dama ina neman wacce za ta tausayamin ts rungume ni ta kuma ƙaunace ni. Kinsan abinka da maraya."

Suka yi dariya. Nan fa hira ta ɓarke a ƙarshe ya ba ta lambar wayarsa gami da ciro bandir na ƴan dubu ya miƙa mata. Sai da ta yi turus, kyautar ta yi matuƙar girgizata. Wane Alhaji Badamasi? Ina ma ya taɓa yi mata kyauta na bandir haka?

"Karɓi kin tsaya kallona kamar wani dodo."

Hindatu ta haɗiyi miyau.

"Wai duka nawa ne? Gaskiya ka rage ya yi..."

"Kul, kar na soma musu da ke tun a yanzu please. Ni mutum ne da ba wai alfahari ba, ina da kyauta. To wani ma ya yi rawa bare ɗan makaɗi? Wannan somin taɓi ne. Ki saurari babbar kyautar da za ki samu a zuwa na gaba da zan yi. Ki gaidamin da Momin tamu." Ya fadi haka ne saboda ta ce mishi babanta ya rasu a hannun uwarta take. Hindatu bakinta har ya na rawa ta yi mishi godiya sannan ta fita zuwa cikin gidan har tana waigen sadda ya ja mota ya bar unguwar. Mommy na zaune a tsakar gida sai ganinta ta yi ta faɗo ɓangaren nasu tamkar wacce aka jefo. Allah ya taimaka ma babu kowa a wurin.

"Ke kuma lafiyarki?" Ta furta tana miƙewa tsaye a tsorace har da kallon bayan Hindatun ta ga ko wani ne ya biyo ta. Hindatu ba magana sai hannun uwar da ta ja zuwa cikin ɗaki, suna shiga ta zube kudin a saman gado, Mommy ta zaro idanu.

"Na shiga uku! Ke Hindatu, duk lalacewata fa ban iya satar abin wani ba sai dai dabarun da zai dauka ya ba mu. Faɗamin gaskiya, a ina kika sato?"

Hindatu wacce ta nemi bakin gado ta zauna dalilin ƙafafunta da ke rawa ga wani irin duka da ƙirjinta ke yi ta haɗiyi miyau. Daƙyar ta iya tattaro nutsuwarta ta shiga ba Mommynta labarin duk yanda suka yi da Alhaji Ibrahim. Wani irin guɗa Mommy ta saka kafin ta tuna cewa gidan da mutane sai ta yi shiru, rafar kuɗin ta ɗauka tana kallo.

"Wai Allahna, kai Allah na godemaka. Babban arziƙi shi ne ka haifi ɗiya mace a duniya. Ta zame maka kadara kuma uwa uba ka samu alhairan da ba ka taɓa zato ba muddin kun iya taku kuwa, komai muninta kadara ce. Keee Hindatu Allah ya yi maki albarka. Ki ce nan kusa za mu ba marar ɗa kunya. Sannu goshi, ke kam kin yi goshi. Ai ba jira Hindatu, zaman me zamu yi? Tunda har dagaske yake, kar ki damu da kaina zan kai sunansa wurin Boka a yi mana dukkan ayyukan da suka dace a kansa."

Hindatu a sanyaye ta ce.

"Mommy wai bakya tunanin da nake yi? Ni fa na tsorata da shi, anya ba ɗan yankan ka.."

"Rufemin baki marar hankali wacce bakinta ba ya furta alheri. Ke don ubanki kawai kuɗi ne, kin ruɗe ne saboda ba ki taɓa haɗuwa da irinsu ba. To ni Allah na tuba sadda na ci ƙuruciyata ai ba kalar da ban gani ba, Allah ne dai ya yi zan auri ubanki mai farar ƙafa, ke dai a ban da tuna baya gyartai ya ci sarauta."

"Uhm." Shi ne kawai abin da Hindatu ta ce. Ga ƙoshi ga kwanan yunwa. Ga dai kalar rayuwar da take muradi na gidan arziƙi sai dai ta rasa dalilin da yasa zuciyarta ta kasa nutsuwa tun bayan wannan zunzurutun kyauta na Alhaji Ibrahim da suka shigo hannunta. Sam ta bayar zai mata kyautar da ba ta fi na dubu goma ko biyar ba amma sai ta ga saɓanin hakan. Ganin yanayin damuwarta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login