Showing 90001 words to 93000 words out of 177840 words

Chapter 31 - FITAR TSIRO COMPLETE HAUSA NOVEL BY RUFAIDA UMAR

11 Jul 2024

79139

suka yi da ita duk a kan Sadaukin babu abin da bai ji ba. Idan har kuwa tana son Sadauki, bai ga dalilin takurawa a kan sai ta ƙaunace shi ba, shi mai mata ma kenan. Ba ya tunanin za ta so shi. Wannan dalilin ya sanya shi zaɓar barin komai da manta komai. Ya kuma zaɓi ya kauda kai daga gareta, sai dai ganinta na yau ɗin ya so warware dukkan shawarar da ya yankewa kansa a kwanakin da suka wuce, shawarar na kallonta matsayin ƙanwarsa tamkar sauran ƴan uwannasa. Bai san kuma sadda abin ya ɗarsu a rai ba da har ya yi wannan zurfin ciki ba. Yana ji ba girkin da ya ji Hajja na mata gori ba ta iya ba, ko tsaftar ce ba ta da ita, zai iya haƙurin zama da ita a kowane yanayi, fiye da haƙurin da yake yi a rayuwarsa da Hafsat.

'Ina za ta so ka? Alhalin tana da Sadauki? Shi ta ke so?'

Wata zuciyar ta yi mishi tuni sai ya ji wani zafi a rai, don haka ya buɗe idanunsa da suka kaɗa. Ya miƙe ya shiga banɗaki ya wanke fuskarsa ya goge da farin tawul kafin ya fito. Hand Sanitizer ya matsa a hannunsa, daga nan ya fita ya rufe ofis din zuwa inda su Umma suke.

Can ya tarar ana ta fama da Haulatu wajen neman jijiya za'a sanya mata drip amma ta ƙi tsayawa sai kuka take yi tana riƙe Umma. Babu irin tsawar da jan ido wanda Umma ba ta yi mata ba amma abu ya gagara.

"Lafiya?" Jin muryarsa tuni ta yi ɗif da ihun, ta dubi yanda ya ɗaure fuska, ya maida kallonsa ga ma'aikatan jinyar biyu da ke kokarin ganin ta ba su haɗin kai.

"Yauwa ai gwara da ka zo da kanka, ɗazun ma ganin idonka ne ya sa ta tsayawa aka ɗibi jinin."

Faɗin Umman kenan. Tana ƙara cewa a baya sam ta san ba ta da wannan iya shegen na tsoron sirinji sai yanzun ta rasa me ya hau kanta.

Ita dai Haulatu shiru ta yi tana kukan zuci gami da runtse idanu sa'ilin da Khaleefa ya karɓi kayan aikin ya ba su Nos din umarnin fita. Daga shi sai Umman da ita. Wayar Umma ta yi ƙara ta ɗaga ganin Hajja ce, nan ta shaida mata jikin da sauƙi ruwa kawai za'a ƙara su taho gida. Daga nan ta shiga tambayarta ko su Haj Nafisa sun isa. Anan Hajja ke cewa ai sun jima da sauka a Kano. Ajiye wayar Umma ya yi daidai da kammalawarsa. Ya dube ta.

"Umma ko akwai abin da ku ke buƙata?"

Ta yi ɗan murmushi.

"Babu komai sai ruwan sha."

Ya maida mata martanin murmushin gami da amsawa da toh ya fice. Ta dubi Haulatun.

"Sannu." A hankali ta ɗaga kai. Can kuma bacci ya ɗauke ta.

***
Abuja...

"Wai Zaid lafiya? Tun da muka dawo na rasa gane kanka. Ko girkina ka daina ci, don Allah akwai wani abu ne da na aikata gareka ban sani ba?" Faɗin Jalilah kenan hawaye na kwaranyowa a fuskarta. Tun dawowarsu daga Katsina ya sauya mata, hatta a shimfiɗa ba ya nemanta. Wannan shi ne sanadin shigarta damuwa da rashin sukuni. Lokacin an yi sallar isha'i, duk da laulayin da ta ke ɗan fama da shi, bai hana ta cin ado ba kamar yanda ta saba domin tarbarsa. Yau ɗin ma ya shigo babu walwala, koda ya yi wanka ɗaki ya shige don abincin ma ya ce ba zai ci shi ba. A ɗakin ta ƙarasa ta iske shi da tambayoyinta.

Idanunsa a rufe kamar bai ji ta ba amma a zahiri babu harafi ɗaya nata wanda bai shiga kunnensa ba. To me zai ce mata? Soyayyar Haulatu ce ta yi mishi mummunan kamun da ke neman kassara shi ko kuwa ƙiyayyar da take mishi gami da furucin ba za ta taɓa sonsa ba ne ke ƙona ransa har yake jin komai ba ya burge shi a rayuwar?

"Babu abin da za ka ce? Ko dai gajiya ka yi da ni ne? Ko girkin nawa ba ya maka dadi?"

Sai a sannan ya buɗe idanunsa ya dube ta, ita ɗin ma shi take duba da nazarin ramar da ya yi a kwanakin nan. Zaid sai ya ji ta ba shi tausayi matuƙa, ta riga da saba da tarairaiyarsa bai kyautu ace sanadin abin da zuciyarsa ta makance a kai ba, ya yi mata irin wannan sakayyar ba. Ya tuna tana da haƙƙoƙi a kansa wanda bai kamata ya tauye mata ba. Zaune ya miƙe ya ja hannunta ita ma ta miƙe daga durƙuson da ta yi ba musu ta koma gefensa. Hawayen ya share mata da tafukan hannayensa.

"I am so sorry. Akwai wata ƴar damuwar da nake ciki amma in sha Allahu zan yi iyaka kokarin ganin ban ƙara shiga haƙƙinki ba. Kin ji?"

Ta gyaɗa kai tana ɗan tura baki da ɗan shagwaɓa ta ce.

"Toh meke damunka? Na yi zaton mun zama ɗaya, abin da ya shafeka ni ma ya shafe ni."

Ya yi mata murmushinsa mai kara jefa ta kogin so da ƙaunarsa. Lokaci guda ya sumbaci bayan hannunta.

"Ya shafe ki, amma Allah ya kiyaye abin da zai dame ni kema na jefa maki damuwarsa. Na fi buƙatar na tattara naki damuwar na haɗa da nawa, su dagula lissafina ni kaɗai."

Wani murmushi ta yi tana mai jin daɗi kalamansa, a duniyarta tana son Zaid ya yi magana. Ya ƙware da kalamai masu daɗi masu sanyaya ruhi.

"Toh abincin fa?"

Ya ɗan yamutsa fuska.

"Ban tare da yunwa."

"Please ko kaɗan ne ka ci."

Ganin kamar za ta yi kuka a dole ya miƙe.

"Ok, muje na ci."

Wannan yasa ta miƙe zuciyarta fari ƙal suka fita falon.

***
Katsina...

Sai wuraren takwas da mintoci na dare Umma suka shigo gidan. Hajja ta tarbe su tana zuba wa Haulatu ruwan sannu. Mu'az dake falon tare da Hajja, bai jima da shigowa ba ya ji Haulatun ba lafiya, yana kokarin bin su zuwa asibitin ne kuma ya ji Hajja ta ƙara kira sun ce suna hanya, wannan yasa shi zaman jira. Shi ɗin ma gaba ɗaya ya ɗan yi rama, bai taɓa zaton maganganun Haulatun zai dame shi har haka ba. Sai dai ya mishi ciwo, madadin ya ji ta fice a ransa sai ma saɓanin hakan. Ya kwana biyu ba ya ko shigowa sashin Hajja sai a ranar, nan ma kasa jurar rashin gani da jin ta ya yi, dolensa ya saɗaɗo ya shigo.

"Sannu Haule, Allah ya ƙara lafiya kin ji?"

Ta gyada kai, ta ɗan ji ƙwarin jikinta sanadin ƙarin ruwan, ganin Mu'az a falon yasa ta kama hanyar bene za ta nufi sama.

"Aa, dawo maza ki sa wani abu a cikinki sai ki sha magani ki yi sallah ko?"

Ta dubi Hajja sannan ta ce.

"Ni a sama zan ci, bandaƙi zan shiga yanzu."

Daga nan ta wuce, Umma kuwa zama ta yi tana ba Hajja bayanin cewa Malaria ce ba wani abu ba. Dama tuni ta yi sallarta a asibitin.

"Mu'azu, ina ka shiga kwana biyu. Ciwo ka yi ne? Na ganka wani iri."

Ya shafi ƙeyarsa jin abin da Umman ta ce, yana murmushin yaƙe, ya sani ba don komai ta ƙi zaman falon ba sai dominsa.

"Au, ke ma kin kula ashe? Ai faɗan da na gama yi mishi kenan. Gaba ɗaya ya fige kamar kazar mayu. Ka tashi maza kai ma ka je ɗan uwanka ya aunaka." Faɗin Hajja.

Ya ɗan ɓata rai.

"Ni fa zazzaɓin dare ne na ɗan yi amma yanzu na samu lafiya, na sha magunguna."

"Sannu, Allah ya ƙara lafiya." Umma ta furta, ya amsa da amin.

Hajja ce ta sanya Baba Saude miƙawa Haulatu abinci.

Ta iske tana sallah ta ajiye ta fita. Koda ta idar kwanciya ta yi saman gado jikin duka ba dadi, ba jimawa Umma ta shigo, nan ta hau faɗa kan abincin da ba ta sanya a ciki ba balle ta sha magunguna. Daƙyar ta iya loma biyar, ta sha magani ta bi lafiyar gado bayan ta fidda abayar da ke jikinta.

***
Washegari kusan sosai ta ji daɗin jikin, tun safe ƙawayenta suka shigo duba ta, suka hau hira don ɗebe mata kewa. Tana daga kwance a saman gado daga ita sai riga iyaka gwuiwa na shan iska, waƙar da Radiya ta kunna a wayarta tana sauraro na Chiza Dani shi ta maida hankali ga ji yayinda Safina hankalinta ke kan Instagram tana ta kallon hotunan wani aure da aka zuzuta shi ne aure mafi kyau da kashe kuɗaɗe da aka yi a garin Kano a shekarar, abin ma mamakin ganin mutumin ya girmi Amaryar nesa ba kusa ba. Sai dai inda Allah ya taimaka sam ba shi da muni. Ita ma Radiya tana ta leƙa wayar Safinan suna kalla yayinda Haulatu a kwancen hankalinta ke kan waƙoƙin, don tuni an kammala an faɗa wani waƙar na Hamisu Breaker. Lumshe idanu ta yi tana tunano dukkan abubuwan da suka faru a kanta lokacin bikin nan. Sauyawar alaƙarta da Sadauki, daga kallon mugu kuma marar tausayi da take yi masa zuwa na mutum mai sanyi da kuma sauƙin kai. Shi dai, da ake mishi caa da tunanin wai soyayya suke yi. Ta ji tausayin kanta ya kama ta da ta tuno Zaid sa Mu'az da suka furta da bakunansu wai suna sonta. Ita ko me ta mallaka har haka da mazan nan ke bibiyarta haka?

"Ke Haulatu wai ba za ki kalla ba? Don Allah dube su, wallahi ni dai ba zan iya auren babban mutum ba duk kuɗinsa." Faɗin Safina tana miƙawa Haulatu wayar, karɓa ta yi tana ɗan cije leɓɓanta na yanayin rashin lafiya ga damuwar da tunani ta jefa ta ciki. Kallon wayar ta yi sosai, hoton ta tsurawa idanu, ba haske na fata ko kuma ƙiba da ya ɗan yi ba, ko turai ya je aka sanya shi a inji ba ta tunanin fuskarsa za ta ɓace mata. Balle kuma Hindatun da ta gani. Ta yi masa ta karanta caption na hoton, Ibrahim&Hindatu. Shi ta ga an rubuta. Miƙewa zaune ta yi don kaɗuwa da mamaki.

"Lafiya? Kin san su ne?" Cewar Radiya da suke dubanta. Daidai nan Umma ta shigo ɗakin, ta yi saurin fita daga instagram din gami da cilla wayar ga Safina. Suka dube ta da alamar tambaya, ita kuwa kallon Umma ta yi.

"Au, ba ki shirya ba? Maza tashi ki shirya muje lokacin allurarki ya gabato, sha biyu ya ce."

Ta amsa da toh cike da ƙarfin hali sannan ta mike don kaucewa tambayoyin da take da tabbacin samun su daga garesu.

***
A hanya ma tunani kawai take yi tana share hawayenta a fakaice, tunaninta kar bayyanar wannan mutumin ya ƙara haifar da damuwa da tsoro a zuciyar Ummanta, sam ba ta kaunar Umma ta ga abin da zai tayar mata da hankali yanzu, sai dai tabbas za ta je ga Baba Alhaji ta yi musu zancen da kuma nuna musu hoton Ɗan Mutuwa ko don a ƙwatar Ummanta ƴanci. Ko kusa ba ta yi mamaki don ya yi ƙazamin kuɗi ba har haka, ta kawo a ranta harkar ƙwayoyin da yake ne ta samar mishi ko wani mugun abin. Damuwar da take ciki na hoton da ta gani yasa sam babu gardama ba komai ta tsaya aka yi mata allura, ba su haɗu da Khaleefa ba saboda ya shiga theatre.

Daƙyar ta bari aka yi la'asar rana ta yi sanyi, ta gwadawa Umma ai za ta ɗan tattaka ne don ta ji dadin jikinta, Allah ya taimaka su Radiya sun fice islamiyya. A hankali take tafiyar har ta ƙarasa sashin Baba Alhaji, shiga ta yi da sallama. Ranar ta kama Asabar. Ba ta yi tsammanin ganin Sadauki ba duk da weekend ne dama yakan zo su yi hira da Alhajin. Ba ta ji komai a ganinsa ba ta ƙarasa da sallama. Abin da ke tafe da ita ya ninka damuwa ko tsoron Sadauki a zuciyarta. Ta gaida Baba Alhaji, ya amsa yana mata sannu da jiki har yana jan ta da wasa wai ta biyo shi ba ta jira ya je ya kai kayan dubiya ba. Ita da murmushi ta yi mai kama da yaƙe. Ta maida idanunta ga Sadauki wanda ke nazarinta. Ya kula kamar da magana a bakinta.

"Ina yini Yaya."

"Lafiya, ya jikin?" Ya furta a tausashe. Ta amsa da lafiya Alhamdulillah. Daga nan ta yi shiru kuma ta ƙi tashi.

"Meke tafe da ke? An yi wani abun?" Sadauki ke tambayar ba Alhaji ba.

Ta ɗago ta dube shi karo na biyu, take wasu hawaye masu zafi suka zubo mata. Ta haɗiyi miyau tana jin bakin cikin kasancewarta ɗiyar mutum irin Ibrahim Ɗan Mutuwa.

Wayarta ta buɗe ta shiga instagram, nemo hotunan bikin ba su yi mata wuya ba don su ke tashe, ta miƙawa Sadaukin wayarta, ya kalla cike da rashin fahimta kafin ya miƙawa Baba Alhaji dake tambayar mene ne? Ya maida duba gareta.

"Mene haɗinki da su? Ko kin san su?"

"Wannan kuma waye?"

Sadauki ya fara tambayar kafin Baba Alhaji.

"Shi ne mijin Ummana da ku ke nema."

Abin da ta iya furtawa kenan.
*Garaɓasa!*

*Ƴar uwa kina zaune a gida babu sana'a, tunani da damuwar wace sana'a ya kamace ki da za ki juya sisi zuwa kobo ya addabe ki?* *To ki sha kuriminki, ga dama ta samu, ko yaya abin da za ki samu in sha Allahu zai amfanar da ke ya kuma taimaka makinda wasu cikin ƙananan buƙatunki da zai sa ki rage yi wa mijinki bani-bani.* *Esb enterprises, za su yi maku bonanza ranar juma'a akan naira 500 kacal, za ki koyi yanda ake haɗa graphics*
*Za su koyar da:*
*Flyer.*
*3d logo.*
*Invitation card.*
*Video invitation card.* *da kuma*
*Cartoon advert.*

*Ƴar uwa duka wannan abubuwan da na lissafo kan naira 500 za ki koya* *Bayan wannan ma tana koyar da yanda ake sana'ar siyar da data a kyauta, tana kuma siyarwa ita kanta.*

*Za ki koyi yanda ake sana'ar data a kyauta, kar ki bari a yi babu ke ƴar uwa.* *Ki tuntuɓe su ta wannan lamba kamar haka: 07045107521*

*******

"Kina nufin mahaifinki mijin Na'imatu?"

Cewar Baba Alhaji.

Ta runtse idanu jin an jinginata da shi wanda ta sani ya zama dole.

"Eh shi ne, ita kuma wacce ya aura aminiyata ce tare muka yi karatu."

Baba Alhaji ya yi salati kafin ya ce.

"Amma wannan ya cika shaiɗani, wato har ya samu damar fitowa idon duniya ya ci karensa babu babbaka, wane irin lokaci muke ciki haka da har mai laifi zai fito hukuma na kallonsa babu mai cewa don me? Kuma har ya auri aminiyarki? Ja'irin gaske kai."

"Ita aminiyar taki, ta san cewa mahaifinki ne?" Tambayar da Sadauki ya watso mata kenan.

Ta girgiza kai.

"A'a, ba su taɓa ko haɗuwa da shi ba, labarin yanayin zamanmu da shi kawai nake ba ta wasu lokutan."

Ta ƙarashe cike da dauriya sakamakon jin kamar zazzaɓinta ya dawo ga kanta da daman bai bar sarawa gaba ɗaya ba sai raguwa da ya yi, yanzun kuwa sai ya daɗu.
Sadauki da ya maida duba ga hoton yana ƙara kalle fuskar Ɗan Mutuwa cike da jin zafinsa, sosai ya shiga ya bincika shafukan a wayar Haulatu har ya ga ainahin sunan Alhaji Ibrahim. Sanadin harkokin kasuwanci ya san manyan mutane da dama a garin Kano. A take ya fiddo wayarsa ya dannawa wani babban ɗan kasuwa waya, mutumin suna harkar takalma da shi, yana sari sosai a kamfaninsu na nan Katsina, bayan sun gaisa da komai yake tambayarsa ko ya san da wani hamshaƙin mai kuɗi Alhaji Ibrahim wanda ya yi aure a satin da ya wuce? Nan take yace masa kwarai ya san shi. Ya nemi jin bayani game da shi. Ya ce ya ba shi nan zuwa dare duk abin da aka bincika masa zai sanar da shi. Daga nan suka yi sallama. Haulatu da tun soma wayar Sadauki take dubansa tana jin sanyi a rai ba don komai ba sai na yanda ya dauki abin da muhimmanci har a take ya nemi jin inda za'a sami Ɗan Mutuwa. Yana ajiye wayar ya dube ta, ba ta san lokacin da ta sakar masa murmushi ba lokaci guda hawaye na zuba a saman fuskarta. Ya ɗan kauda kai, sam ba ya son kukan mace.

"Goge fuskar taki, ki tashi ki je ki kuma yi ƙokarin ragewa kanki damuwarnan, damuwa ba shi je kawo ƙarshen matsaloli ba sai dai ya sanya maki wani ciwon."

Daga haka ya maida duba ga Baba Alhaji.

"Na yi magana da Alhaji Tasi'u Maiplaza, in sha Allah zuwa dare zai sanarmin abubuwa dangane da shi da ma inda za'a same shi. Ku kwantar da hankalinku."

"Alhamdulillah, na ji daɗi kwarai. Allah ya yi maka albarka. Ke Haulatu sai ki yi hakuri har mu ga abin da zai faru. Ki yi ta addu'a, kin ji? Komai zai wuce."

Ta amsa maganar Baba Alhaji da toh. Ta dubi Sadauki karo na uku.

"Na gode Yaya."

Ya yi murmushi kaɗan, wayarta ya miƙa mata ta karɓa, bisa kuskure har tana haɗowa da yatsunsa, da sauri ta kauda nata hannun, shi kuma ya yi saurin dubanta.

"Jikinki zafi, zazzaɓin ai bai sake ki ba."

Baba Alhaji ya dube ta.

"Assha, ka gani ko? Kin sha magungunanki?"

Za ta yi magana ma sai wayarta ta yi ƙara, tare da shi suka dubi fuskar wayar, sunan My Mom da ya gani yasa shi miƙamata.

"Ki ɗaga amma please kar ki yi abin da za ki jefa ta damuwa."

Ta gyada kai ta amsa wayar, Umma ke tambayar inda ta shiga sai fada take wai ba ta da lafiya ko magani ba ta sha ba amma ta fara fita.

Haƙuri ta ba Umman sannan tace ga ta nan zuwa, tana wurin Baba Alhaji. Sai a sannan Umma ta ɗan sauko tace to maza ta dawo ga Hajja ranta ya ɓaci. 

Bayan sun ajiye wayar ta miƙe tsaye kanta ya yi wani mugun sarawa sakamakon jimawar da ta yi zaune kuma ga ciwo da yake dama. Ta riƙe kan ta runtse idanu.

"Muje na raka ki. Baba ina zuwa."

Baba Alhaji yana murmushi ya gyara zaman gilashinsa yana dubansu. Ya amsa.

"Toh Sadaukina. Maza raka ta. Allah ya sa kaffara kin ji Haulatu."

Ta gyaɗa kai, ya bi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login