Showing 102001 words to 105000 words out of 177840 words
zama na lumana da amana, lokaci guda kawai na ji kira daga Ramatu tana kuka take nunamin na zo inda take tana cike da fargaba da tashin hankali sakamakon barazanar kisa da wani tsohon bazawarinta ke mata. Na nuna mata babu abin da zai ƙara haɗa ni da ita muddin ina raye, yanda ta dinga roƙona sai na ji ta ban tausayi, haka a ranar da su Na'imatu suka fice biki nima na wuce gurin Ramatu ba tare da saninta ba. Zuwana ni dai nasan ina daga zaune muna magana da Ramatu a falonta, bayan na sha wani lemo da ta ajiye a gabana ban ƙara sanin inda kaina yake ba. Sai da na yi kwanaki uku a kwance, koda na farka na gan ni ƙulle a wani ɗaki. Hankalina ya tashi amma koda ta shigo ɗakin tare da wasu ƙatti uku, sai ta gargaɗe ni da ba ta haɗin kai ta hanyar yin shiru da bakina mu tattauna magana mai muhimmanci idan ko na ƙi ta rantse kashe ni za ta saka a yi tunda har na yi sanadin da asirin da ta yi a kaina ya lalace baki daya. Anan ne to duk ta labartamin yanda ta yi iya kokarinta na shiga rayuwata da Na'imatu ta hana mu zaman lafiya. Kaina ya daure matuƙa."
"Ita Ramatun wace ce?" Tambayar da Umma ta jefomasa kenan tana murmushi na zallar takaici da baƙin cikin yanda ƙaddarar aure ta haɗo ta da munafukin mutum marar tsoron Allah irinsa. Ya ji gumi ya ɗan tsirfo masa sai ya wayance ya ce.
"Idan ki ka ji ina waya ina cewa Bebi, to ba kowa ba ce sai ita. Na san ba za ki iya tuna ta ba, amma tabbas kun taɓa haɗuwa a baya. Ta fiki shekaru ma."
Umma ta ɗan yi murmushi kaɗan ta girgiza kai. Ya ci gaba da zancensa.
"Ni dai a taƙaice ba ni da masaniyar an kawo muku hari, bayan na fito daga hannun Ramatu wacce ta tabbatarmin ita ce ta saka a kawo mata Haulatu don ta nemi kuɗi da ita, kuma ta tabbatarmin lallai sai na aure ta muddin ina son cigaba da rayuwa a doron ƙasa, kai tsaye ban nufi gidana ba sakamakon labarin da na ji daga wani yarona cewa an zuba jami'an tsaro su na nemana. Babban tashin hankalina bai wuce inda iyalina su ke ba. Da taimakon Maigidana Alhaji Nazifi, na samu damar komawa Lagos da zama. Nan kuma na samu wani Ubangida mai amana da ya damƙamin amanar kasuwancinsa. A hankali kuma bayan na ɗan tara na dawo Kaduna, ta sanadin wani babban ɗan siyasa na samu jari mai ƙarfi da har ya yi silar samun arziƙina."
"A iya ƴan watannin nan?"
Sadauki ya furta yana zubamasa idanu. Ɗan Mutuwa bai ko kalle shi ba ganin yana neman ƙure shi ya maida duba ga Alhaji.
"Na rantse maka Baba, ni dai na yi nadamar komai, ina son Na'imatu ina kuma ƙaunarta. Ku taimake ni, ku yafemin kuma ku roƙamin gafararta ita ma."
Umma ce ta ƙara tankawa cikin zubar da hawaye.
"Ƙarya kake yi Ibrahim, ƙarya ka ke yi. Duk labaranka na ƙanzon kurege ne, idan ba ka sani ba, bari na tunasar da kai wani abu, da kunnuwana na ji kana ba da kwatancen inda za'a sami Haulatu a kama ta. Idan ba ka san cewa na ji wannan waya ta ƙarshe da ka yi ba, to yau ga shi na faɗamaka. Babu abu guda da ka faɗi wanda ya kasance gaskiya. Kuma ni dai idan har ni ce matarka, ina da ikon faɗin ra'ayina, toh har abada na haramta gareka. Har abada.."
Ta kasa ƙarasawa sanadin kukan da ya sarƙe ta, Hajja ta hau bubbuga cinyarta.
"Yi shirunki Na'imatu, yi shiru abinki."
Baba Alhaji ya yi gyaran murya.
"Ya isa hakanan. To Ibrahim, mun ji duk bayanan da ka yi mana. Idan kuma batu na yafiya ne, to ka sani, mu zuri'armu muna da saurin karɓar tuban wanda ya gane kurensa kuma ya nemi mu yafemasa. Don haka Allah ya gafarce mu baki ɗaya."
Cikin jin dadi Sanata ya dubi Ɗan Mutuwa suka amsa da amin don duk a zatonsu magana mai dadi ce ta sulhu za ta fito daga bakin Baba Alhaji. Su Hajja da Baba Dakta kuwa sun fi kowa sanin waye Alhaji Usman shiyasa ba su katse shi ba. Ya ɗora zancensa.
"Abu na biyu kuma, dama yanzun ko babu komai, ai zumunci ya riga da ya haɗu tunda dai kun haihu da Na'imatu. Sai dai ka riga da ka sani, shi aure ana yin sa ne bisa yarjejeniyar mutum biyu da kuma amincewarsu sun ji sun gani za su rayu wuri guda ba tare da ɗaya ya cutar da ɗaya ba. Haƙiƙanin gaskiya ɗiyarmu ba za ta koma gidanka ba, aure dai an yi shi, an kuma zauna kun rayu ba tare da mun san ya yanayin zaman ya kasance ba, sannan koda wata ce ba Na'imatu ba, a yau ta furta ta gaji ba kuma za ta koma gidanka ba, tabbas ita ta san abin da ta ƙunsa, mai ɗaki shi ya san inda yake masa yoyo. Kamar yanda ka zo a ka yi komai a mutunce, to ina neman ka rubutamin takardar sakin Na'imatu ka ba ni."
Ran Ɗan Mutuwa ya ɓaci, nan da na fuskarsa ta ɗan sauya, wannan zafin ran na nema ya taso mishi, Sanata ya kula don haka nan da nan ya ɗan mishi raɗa sai kuma ya saita fuskarsa kaɗan.
"Baba a yi hakuri, don Allah tunda kun ce komai ya wuce, a yi hakuri kar a raba auren sunnah."
Fadin Sanata kenan, Baba Alhaji ya yi ɗan murmushi.
"Yaro ba na magana biyu, tunda har ka ji na nemi ya ba ta takardarta, toh ya bayar kawai. Yarinya kuwa yanzu haka karatu za ta fara, mun kuma dauke maka dukkan nauyinta mun yafe, sai dai matsayinka na Uba a wurinta, idan abu ya tashi dole nan gaba za'a iya tuntuɓarka. Ba zan hana ka zumunci da ɗiyarka ba."
Duk yanda Ɗan Mutuwa ya so ya yi magana dole ya haƙura sakamakon dannarsa da Sanata Hashim ke yi. Wannan tsohon mai dattin goro a baki ya yi mugun raina hankalinsa. Shi da matarsa har ake wani ba shi umarni don an ga ya biyo ta lallami? Toh wace ce Na'imatun, matar da zai samu fiye da ita har da ƙwarƙwara idan ya so. Ya kasa haƙuri ya shanye ɓacin ransa kamar yanda Uban Dodo ya gargaɗeshi a kai, don yace zai haifar masa da dana sani a gaba, kawai ya dubi Baba Alhaji.
"Shi ke nan Baba, tun da haka ku ke so, ni Alhaji Ibrahim na sauwakewa Na'imatu igiya uku dake kanta na aurena. Kuma ita Haulatun ku je na bar maku ita har abada. Zan iya auren sama da mace daya a rana guda a yanzu kuma duk su hayayyafa. Don haka ba ni buƙatarsu baki daya." Yana kai wa nan ya miƙe zai nufi ƙofa, da sauri Sadauki ya sha gabansa gami da cin kwalarsa har ya soma kakari.
"Kai a wa? How dare you! Ka shigo har gidanmu ka ci mutuncin iyayena ka ce za ka fita lafiya? Uban wa ya tsayamaka? Aminiyar ɗiyarka Hindatu da kake aure yanzu fa?!"
"Yauwa Sadaukin Alhaji! Nuna masa kurensa don ubansa!". Hajja ke wannan kalamin tana daga zaune, shi kuwa Sanata na kokarin ƙwatar abokinsa, sai da Alh Ridwan ya dakawa Sadauki tsawa kafin ya saki Ɗan Mutuwa ya tura shi ya fada jikin Sanata, kawai sai ya juya ya fice daga falon ransa na tsananin zafi.
Ɗan Mutuwa ya gyara kwalarsa yana ɗan tari, ya dubi Na'imatu duban wulakanci.
Daga haka ya sa kai ya fice ya na ji Hajja na fadin Kurwar diyarta kurr tana fadin wannan kallon daga gani da wata manufa ya yi ta. kuma ta Allah ba ta shi ba mugu baƙin azzalumi.
Umma kuka kawai ta ke yi na wannan lamari, ga dai Allah ya kawo mata komai da sauki, tana zaune a inda ta ke, Ɗan Mutuwa ya zo har ya raba ta da nauyinsa dake kanta na aure. Ta sha mamakin jin da ta yi Sadauki ya ce wai Hindatu yake aure yanzu. To ya aka yi ya sani? Kamar Baba Alhaji ya san me take tunani, ya shiga rarrashinta da tunasar da ita muhimmancin yarda da ƙaddara a matsayinta na musulma mai hankali. Nan ya hau ba su labarin cewa ai tun kan ya zo sun san da maganarsa daga bakin Haulatu. Ya fadamusu duk yanda aka yi ya ƙara da fadin.
"To Allah ne ya kawo mana komai cikin sauƙi sai ga shi ya kawo kansa kafin mu kai ga nemansa. Ki godewa Allah sosai Na'imatu da al'amarin ya zo a yanda ba mu yi zato ba. Shi kuma ya je, idan kuna da haƙƙi ai ko kun yafe zai gani a ƙoƙonsa."
Umma ta jinjina kai tana share hawayenta gami da ɗan jan majina. Wato Haulatu ta san da maganar ta yi shiru ta ɓoyemata gudun jefa ta cikin hali na damuwa? Sai ta ƙara jin kaunar ɗiyarta a rai.
***
Ya yi wurgi da hularsa a bayan motar ya na jijjiga yatsarsa manuniya.
"Na rantse maka ba zan bar Na'imatu haka ba, daga ita har ɗiyarta sai sun san ni ba sa'an yin su ba ne. Ko zan rasa dukkan abin da na mallaka sai na yi maganinsu. Sai na wulaƙanta ta."
Sanata ya jinjina kai.
"Ban ga laifinka ba Alhaji Ibrahim domin ƙarshen tozarci sun mana shi a yau, duk kuwa da irin kwantar da kai da labaran ƙanzon kurege da muka shirya don neman sulhu amma suka watsamana ƙasa a ido. Tabbas na ba ka goyon baya ka dauki kowane irin mataki a kansu"
Ɗan Mutuwa ya jinjina kai kafin ya fashe da wani mahaukacin dariya wanda hatta da direban Sanata Hashim dake jin su sai da ya ɗan kalle shi ta madubi a tsorace kafin ya maida hankali ga tuƙi.
"Da ni suke zancen."
***
Ƙarfe ɗaya daidai Malama Ruƙayya ta tashe su, kowa ya fito har da Haulatu dake ɗan hira da wata mace tana mata ƴar tambaya game da karatun baya. Har suka iso bakin ƙofar fita suna hirarsu, matar ma da motarta ta zo. Take cewa Haulatu ita ɗin daga Nijar mijinta ya auro ta, babban lauya ne. A can ta yi karatu da harshen faransanci. Mijinta ke son ta koyi turancin shi ne dalili da ya sanya ta a makarantar. Jinjina kai Haulatu ta yi tana murmushi, ita ko sunanta ba ta tambaya ba amma dai kasancewar ita ta gabatar da kai a yau, duk sun san sunanta. Motar Sadauki da ta gani a fake a wurin sai mamaki da kuma wani dadi ya kama zuciyarta lokaci ɗaya. To shi da ya ce Gali ne zai zo ɗaukarta, ya aka yi kuma ya dawo? Ganin ya sauke gilashin motar sun hada idanu ya sa ta saurin yi wa matar sallama ta nufi motarsa. Ita ma matar ta nufi nata motar.
A hanya shiru babu wanda ya ce uffan sai can ya dube ta.
"Kina jin yunwa?"
Ta gyaɗa kai don dagaske yunwar take ji, rabon ta da abinci tun ƙarfe tara na safe. Aikuwa ta ga kai tsaye madadin ya yi gida, ya zarce da ita wani haɗaɗɗen restaurant, kamar ta yi magana sai kuma ta fasa. Sadauki ya yi musu order na abinci, su biyu kawai a teburin. Sai ta ji wani irin nauyi da kunyarsa ya kama ta. Ta ɗaga cokalin za ta kai baki, sai ta ga kawai ita ya zubawa idanu da wani irin kallo ga murmushi saman fuskarsa. A ransa babu abin da yake ayyanawa sai dadi da farin cikin da za ta shiga idan ta ji batun rabuwar Umma da Ɗan Mutuwa. Ya san babu wanda zai kira balle ya neme su a waya tunda ya sanar da Umma da Hajja kar su damu zai je ya ɗauko ta suna tare.
A hankali ta maida cokalin ta ajiye tana ɗan gyaran murya. Ya sauke ajiyar zuciya.
"Sorry, na hana ki cin abinci ko?"
Ta girgiza kai.
"Bismillah, daure ki ci mu tafi."
Daga nan ya yi bismillah ya soma cin nasa. Ganin ya maida hankali sai ta fara ci ita ma sai dai ba ta wani ci sosai ba don duk a takure take ga rashin sabo da hakan tsakaninsu.
"Kin ƙoshi?"
Da sauri ta gyaɗa kai.
"Ba abin da kika ci Haulat."
Ta ɗan yi narai-narai da fuska.
"Allah kuwa na ci Yaya, na ƙoshi kuma."
Ya girgiza kai.
"No, ban yarda ba. Ki ƙara sai mu tafi."
Wayarsa da ta yi ƙara ne ya sanya shi fadin Ina Zuwa sannan ya miƙe.
Ita kuwa ta ƙara abincin don dama zamansa a wurin ne ya hana ta cin, kafin ya dawo ta ci ya fi loma biyar don ba laifi ya ɗan jima. Shi kuwa a ɓangarensa har ya kammala zai shigo ya ga ta maida hankali tana ci sai ya gane nauyinsa ne ya hana ta ɗazun wannan dalilin yasa shi komawa baya ya ɗan tsaya don ba ta dama. Can da ya ga alamun ta kammala ya ƙaraso bai ko zauna ba ya ce su tafi. Ta dauki robar lemunta ta yi gaba tana jira ya ƙaraso. Can ya fito, ta saci kallonsa, kai Yaya Sadauki ya haɗu ba ƙarya, sam ba ta ga laifin su Jannat masu bori a kansa ba. Tunowa da Jannat din ta ji wani abu mai ɗan ɗaci a maƙogwaronta sai ta yi tunanin ƙila saboda sun taɓa samun saɓani yasa ta jin haushinta. Amma ba don komai ba.
'Da ace ki ga Jannat tare da Yaya Sadauki ba za ki ji komai ba?' Wani ɓangare na zuciyarta ta jefamata tambayar daidai sadda ta buɗe gaban motar ta shiga, haɗaɗɗen turarensa ya bugi hancinta, ta saci kallonsa lokacin da ta rufo motar. Hankalinsa na ga ribas ɗin da yake yi da motar yana kallon side-mirrow, ta bi kwantaccen sumar kansa da ido kafin ta kai duba ga cikar halittar da Allah ya ba shi wanda ya amsa sunan namiji kasancewar tshirt ce jikinsa a yanzu kalar ja da wandon jeans blue. Allah ya kyautata halittarsa, hakanan kuma ta soma kula da yana da ɗabi'u masu burgewa. Ganin zai juyo da sauri ta kauda kai ta maida ga kallon gefen windon tana ji kirjinta na dukan tara-tara. Kai! Ai ba su ma dace da Jannat ba, ita ɗin ma ta san ya fi ƙarfinta. Haka tunaninta ya ba ta. Sai kuma ta koma jin haushin kanta, to me ma ya kai ta wannan duka lissafe-lissafen alhalin babu gurbi na soyayya a rayuwarta?
"Thinking of me?"
Abin da ya fito daga bakinsa ne ya sanya ta dubansa da sauri, ya kuma yi murmushi ya kanne mata ido guda sannan ya maida kallonsa kan titi.
"Just joking."
Ya ƙara furtawa, ta sauke ajiyar zuciya duk sai ta bi ta tsargu don haka ta kama kanta daga barin tunanin da ta ba shi matsayin na wofi marar amfani. Sadauki kuwa tunaninsa na ga maganar da za ta tarar a gidan, ya so ƙwarai ya yi mata batun kafin ma su ƙarasa gudun kar a faɗamata a lokaci guda ta tashi hankalinta, sai kuma ya yi tunani ya ga kamar zai fi kyau ta ji daga Ummanta hankalinta zai fi kwanciya ta kuma fi samun nutsuwa idan tana da tabbacin dagaske babu inda Umman ta tafi ta bar ta.
Ya ɗan ja ta da hirar yanayin karatun don ya ji ko tana fahimta, ta amsa mishi, sai dai ya kula ta kasa sakin jiki da shi har a sannan wannan ya sa bai takura mata ba ya ƙyale. Har suka isa ba su ƙara wata magana ba sai ma kiransa da aka yi yana ta magana a waya game da harkar kasuwancinsu har suka iso gida ta yi lamo ta ma kasa fiddo wayarta balle ta ji wane ne ke kiranta har sau uku.
Bayan sun iso za ta fita a motar ta yi mishi godiya har ta zura ƙafa ya kira sunanta da sigar da ya haifar mata da jin wani sanyi da kuma nutsuwa a zuciya da kwakwalwarta.
"Na'am." Ta amsa tana mai dubansa.
"Take care please. Babu bawan da Allah ba ya jarabta, babu jarrabawar da addu'a ba ya maganinta. Kin ji ko?"
Ta kasa gane dalilin wannan zance, sai dai kalaman sun shige ta ainun, don haka ta sauke ajiyar zuciya.
"Toh Yaya, nagode."
Ya girgiza kai.
"Ba godiya tsakaninmu."
Ta ɗan dube shi, ya yi murmushi sai ta mayar masa da martanin murmushin kafin ta fita ta rufe motar tana jin wani dadi da annashuwa a zuciya, duk da ranar da ake tsulawa a garin da kuma zafin da ya ziyarce ta lokaci guda sakamakon ta fito daga raɓar AC na mota, hakan sam bai katse mata nishaɗin da take ji a rai ba. Daƙyar ta kwaɓi zuciyarta ba ta juya don sake duban Yaya Sadauki ba.
***
Babu kowa a falon ƙasa, Baba Saude ma tana daga kicin tana aiki don haka kai tsaye ta haye saman fuskarta dauke da wani murmushi da annashuwa na musamman, a falon saman ma ba su nan, ta san watakila saboda lokacin sallah ne, kowannensu ya shige daki ya yi duk da wasu lokutan ma a falon suke yi. Sai dai tana shiga ɗakinsu da sallama ta hango Hajja zaune gefen gado kamar tana yiwa Umma nasiha da tausarta, ita kuwa tana daga gefe zaune fuskarnan ta yi ja. Koda suka haɗa idanu da Umma sai da Haulatu ta ji ƙirjinta ya buga. Da sauri ta ƙarasa har jakarta na zamewa ta faɗi ta dafa hannun Umma.
"Lafiya Umma? Hajja wani abu ya faru?"
Umma ta girgiza kai tana ɗan murmushin yaƙe. Hajja kuwa tuni ta soma magana.
"Ba abin da ya faru sai alheri Haule, yau addu'ar da muke ba dare ba rana Allah ya karɓa. Ya kawo karshen auren wancan azzalumin da mahaifiyarki."
Sai ta yi saranda don ita ta mance wane ma azzulumin da kuma wani batun auren Umma sai kuma lokaci guda ta tuna.
"Wai Mijin Umma? Ya mutu ne?"
"Uhum, ina fa, Ɗan Mutuwa bai mutun ba, kwanan bai ƙare ba. Har