Showing 120001 words to 123000 words out of 177840 words
kaunar Haulatu, ki taya ni ba Baba Alhaji da Hajja hakuri, su bar ni na..."
"Zaidu!"
Yanayin ɗagawar muryar da ma kaushinta ya sanya shi dakatar da zancen gami da amsawa.
"Na'am."
"Idan har ni Safiyya na isa da kai, idan na isa na ba ka umarni kuma ka bi. Koda wasa ka ƙara shiga rayuwar Haulatu sai na saɓa maka. Har zuwa yaushe ne za ka daina jazamin abin magana? An ƙare da wancan yanzu kuma ka ke neman jawo min wani? To ni ban ma amince ka yi babbar sallah a nan ba, ka tattara iyalinka ku koma Abuja."
Tana kaiwa nan ta miƙe ta bar masa falon, shi kuwa ya ji kansa ya wani irin sarawa, dama kwanakin duka ba shi da sukuni. Batun ya bar Haulatu ma bai taso ba, ya san ba zai iya wannan ba zai dai nemi hanyar da zai lallaɓa Mahaifiyarsa da ma Hajja. Haulatu kam zai bi umarnin Malama da Baba Alhaji, ba zai ƙara nemanta a waya ba. Amma haka ba wai yana nufin ya haƙura ba.
'Za ka iya jurewa?' Wani ɓangare na zuciyarsa ya watsamasa tambayar wanda ba shi da amsarta. Haka ya miƙe jiki duk a sanyaye ya bar falon.
***
Ana saura kwana hudu babbar sallah, Uncle Abba autan Hajja ya zo da iyalinsa Katsina. Haulatu sam ta tsani matarsa don ba mace ce mai son mutane ba, shi kuwa Uncle Abba ba ruwansa mutum ne mai son jama'a don halinsa ɗaya da Maman Zaituna, Haj Nafisa. Daɗin daɗawa ma sai ga Fahima, wai ita ma a nan za ta yi babbar sallah. Sai gaba daya ma ɓangaren Hajja ya rage yiwa Haulatu dadi, ga shi sun yi hutun islamiyya. Lesson din da take zuwa ma sai bayan sallah za'a cigaba don haka wurin Maama ko Radiya ta ke tafiyarta. Ita ma Fahima ƙafar yawo ba zama take yi ba, sashin su Sadauki take gudu abin ta dab da shan ruwa za ta ci ado ta fice. Abin dai na ba Haulatu mamaki. Ana gobe sallah kuwa, suna zaune bayan kammala shan ruwa, yinin ranar dama kowa ibada ya shiga idan ka cire Fahima mai afkin kallo a waya, matar Uncle Abba, Anti Haseena da ƴan ukun yaranta ba sa nan sun je ziyarar wata yayarta.
Bayan gama shan ruwa Haulatu na zaune su na hira da Safina ta whatsapp, ita kuwa Fahima na gefe Hajja na jan ta da tambayar yanzu shikenan sai wata shekarar za ta sake jarrabawa amma tana amsa ciki-ciki don gaba daya ba ta so ma Hajja ke zancen nan gaban Haulatu ba, ta kula ma dariya Haulatu ke yi sai ta yi tunanin ai kawai ma da ita take. Wayar Haulatun ce ta yi ƙara, ta dan yi jim ganin sunan me kiran, Yaya Sadauki ne. Ba ya taɓa kira sai idan da kwakkwarar dalili don haka ta amsa gami da sallama, bayan ya amsa mata ta gaishe shi. Jin ta ambaci sunan Yaya Sadauki hankalin Fahima duka ya koma kanta.
"Idan bakya wani uzurin, ki fito ina nan parking space, ina son ganinki."
"Toh." Shi ne abin da ta ce kafin su yi sallama. Ta miƙe ta ja hijabinta da ta yi sallar magriba da shi, daga ita sai doguwar riga mai ƙaramin hannu. Ta dubi Hajja don Umma tuni ta haye sama.
"Hajja, bari na je Yaya Sadauki na kirana."
Ta fadi ba ta ko kalli gefen da Fahimar ta ke ba, Hajja ta amsa da toh sannan ta fice. Hankalin Fahima idan ya yi dubu to ya tashi. Yaya Sadauki har kiran wayar Haulatu yake yi? Abin da tunda take ko bisa kuskure ne bai taɓa kiran wayarta ba? To ai ba ita ba, ko yayyunta ma ba nemansu yake a waya ba, sai wanda ya kira don ya gaida shi, yakan ɗauka amma kuma amsar a ciki-ciki. Ita kuwa dama koda wasa ba ta gigin kiransa, ta sani ba ya son a dinga kiransa babu dalili.
"Ke ina magana kin lula wata duniyar, yanzu kenan shi ubannaki aure zai maki ko kuwa haka za ki zauna jiran shekara ta zagayo ki ƙara zana shi jam din."
Fahima ranta a ɓace ta miƙe tana turo baki.
"Ni ma ban sani ba." Daga haka ta fice, bayan Haulatu ta bi jikinta har rawa ya ke, gwara ko mene ne ta gane wa idanunta.
*LITTAFIN FITAR TSIRO NA KUDI NE. DUK WACCE TA FITAR MIN TA KWANA DA SANIN TA DAUKI HAƘƘINA. BIYA KI KARANTA HANKALINKI KWANCE. 9034973645 OPAY. IBRAHIM RUFAIDA UMAR.*
Sassanyar iskar da ke kaɗawa sakamakon wani haɗaɗɗen hadari har yana ƙugi, da ya kewaye sararin samaniya lokaci guda kuma a na zuba walƙiya, alamu ne na kowane lokaci ruwa kan iya sauka idan Allah ya ƙadarta. Hakan bai hana Haulatu takawa ba a sannu ga iskar dake ɗan kaɗawa tana ɗan manne hijabin a jikinta, wasu lokutan kuma ta yi kokarin ɗaga shi sama wannan ya sa ta zaɓi takawa cikin nutsuwa tana kare jikinta gudun kar wani sashin ya bayyana. Tun daga nesa ta hango shi zaune saman motarsa ya tanƙwashe ƙafa guda a gefe kuma wayoyinsa ne a a ajiye yana kurɓar lemun kwali na Chi Exotic a sannu-sannu. Sanye yake da tshirt ruwan ƙasa, ƙirarsa ta ƙarfi ta fito kasancewar ba dogon hannu ba ce, sam bai mishi muni ba sai ko baƙin wandonsa mai jikin cotton. Ƙafafunsa madadin ɗan silifas na zaman gida sneakers ya sanya, ga dukkan ma alamu shigowarsa gidan kenan don motar ko shigar da ita rumfar adana motoci bai yi ba, dama kuma ya fi adana motarsa can gidansu akan nan ɗin. Tana tafe ta gama ƙare mishi kallo tsaf, shigar sosai ta haskaka shi. Ganin ya maido hankalinsa kanta ya sanya ta sunkuyar da kai, har ta ƙaraso bai iya ɗauke ƙwayoyin idanunsa daga kanta ba. Ta yi mishi sallama, ya amsa. Saukowa ya yi daga saman motar ya kasance suna tsaye da kafafunsu su duka. Cikin yanayin lumshe idanu sakamakon iska da ke kaɗawa tana kwashe-kwashe ta dube shi.
"Yaya gani."
Ta furta tana ɗan murza idanu, ya kalli yanda hadarin ke haɗuwa, don haka ya kwashi wayoyinsa ya ce ta biyo shi. Ba musu kuwa ta bi bayansa zuwa cikin rumfar adana motoci, a nan sai suka samu sa'ida kadan daga iskar da ke kwaso musu ƙura.
Duk wannan budurin da suke yi, Fahima na daga can gefe jikin wata ƴar bishiyar dogon yaro tana hangensu, ga dai iska na barazanar raba ta da ɗan yalolon mayafin da ta yafa a kanta. Har wasu hawaye ta ga sun taho mata, babban baƙin cikinta yanda ta ga sun jera kamar wasu masoya sun nufi ƙasan rumfa. Me za su tattauna, me ya faru? Oho, duk babu ɗaya da ta sani.
Can kuwa Sadauki ya dubi Haulatu cikin nutsuwarsa ya soma magana.
"Hadari zai hana ni yin doguwar hirar da na yi niyyar yi."
Ya ɗan yi shiru ita kuwa Haulatu tunani ta shiga to wace kalar hira ya yi niyya din? Sai ta ƙara tsintar muryarsa. Na ji dukkan abin da ya faru a baya, don na daukesu matsayin past, ba na fatan a gaba na ji makamancinsu. Karatu shi ne babban burinki na yanzu, please ina so ki maida hankali ga abin da ki ke so domin cikar wannan muradin naki. Taya wanda kake so cikar burinsa muddin bai saɓawa shari'a ba, shi ne babban abin da ya fi kyautuwa. Da ace sun taya ki so da kwaɗayin cikar wannan buri naki fiye da son zuƙatansu, hakan zai yi min dadi. Kar ki ba ni kunya, ki nutsar da hankalinki wuri guda kuma kan abu guda. Ni dai na sani zai wahala idan kina soyayya. Ko kina da wanda ki ke so ne da ya sa ba ki ba waɗancan dama ba?"
Ya watso mata tambayar daga ƙarshe, ita kuwa cikin jin dadin yanda ya ƙarfafa mata gwuiwa da kuma fahimtar lallai su Yaya Mu'az sun fifita lamarinsu a kan nata, ta ɗago idanunta ta kalle shi, shi ma wani irin kallo ya ke mata mai wuyar fassara, a hankali ta sauke idanunta ƙirjinta na bugu da ɗan sauri-sauri. Girgiza kai ta yi.
"A'a."
"Ko wani mai suna Abeed?"
Ya furta yana miƙa mata lemun robar dake hannunsa, ta sa hannu ta karɓa shi kuwa ya samu damar kalle zanen baƙin lallen dake a hannunta, ga kuma ja da ta yi irin na salatif ɗin nan ya sha kyau. Ita kuwa fuskarsa kawai ta ke duba da tunanin waye Abeed don gaba ɗaya ma lissafinta ya kauce ta manta da waye mai ainahin wannan sunan don haka a raunane da sanyin murya ta amsa.
"Allah kuwa ni ban ma san waye Abeed din ba. A ina yake?"
Ya yi murmushi.
"Ƙunshin ki ya yimin kyau. Ki dinga yi kin ji?"
Ta gyaɗa kai tana ɗan maida hannunta cikin hijab.
"Yaya."
Ya ji sautin muryar har cikin kwanyarsa da ya haifar masa da wani yanayin da har sai da tsikar jikinsa ta tashi. Kallonta kawai yake yi bayan ya ɗan karya wuya kaɗan, ta kautar da nata idanun.
"Dama..um..tambaya zan yi. Waye Abeed?"
Murmushin da bai shirya yi ba ya suɓuce masa, ya ɗan shafi gefen wuyansa. Dama ya sani zai wahala idan ma ta fahimci manufarsa don haka ya dan jinjina kai.
"Ba lallai kin san shi ba, amma dai tambaya nake ko da shi ba kwa soyayya?"
"To ai Yaya ni ban ma san shi ba fa ballantana ma mu yi soyayyar bayan ma ni karatu ne a gabana yanzu."
Ta ƙarashe tana ɗan tura baki gami da sosa idonta na dama don tun ƙurar da ta shige mata a ɗazun ba ta fice duka ba. Ya ƙara samun damar bin ƙunshinta da kallo yana mai lumshe idanu da ambaton sunan Allah a ƙasan ransa kafin ya amsa mata.
"Na yarda. Please ki ƙara kiyayewa kin ji ko? Za ki samu wanda ya fi Mu'az da Zaid sonki, koda kuwa sunansa Abeed."
Ta gyada kai kawai tana murmushi gami da riƙe lemun gam a hannunta don ita ba ta gane ma manufarsa ba.
"Kin yi kitso?"
Da mamakin tambayar ta gyada masa kai. Sauke ajiyar zuciya ya yi da muryar da ta bambanta da na baya ya ce.
"Jeki kar ruwa ya taɓa ki na shiga uku wajen Hajja. Sai da safe ko?"
"Toh, Allah ya tashe mu lafiya."
Ya amsa da amin kafin ta soma tafiya tana tauna kalamansa na ƙarshe, kwakwalwarta ta shiga tunanin waye Abeed? A ina ma ta taɓa jin sunan?
'Kai, ai sunansa ne. Na tuna an ce sunansa na gaskiya Abeed.' Wani ɓangare na zuciyarta ya tunasar da ita.
Da sauri ta juyo ta dube shi, hasken fitilun da ya haska wurin tamkar rana ya haska mata kyakkyawan fuskarsa yana zubamata murmushi gami da kanne ido guda. Ta yi saurin kauda kai ta cigaba da tafiya kirjinta na faman bugu fat-fat. Wai sonta ya ke yi? Ko kuwa ba shi Abeed din ba? Madadin ta ji zafinsa a silar wannan hasashen sai ma ta ji wani irin dadi da sanyi, ta tsinci kanta da fatan inama ya kasance son nata ya ke yi? Tabbas da ta fi kowa sa'a a duniya.
Fahima dake tsaye tana kallonta sam ita Haulatun ba ta ma kula da ita ba saboda tuni ta fara ɗan gudu-gudu sakamakon ruwan da ya ɗan soma ƙarfi. Wannan saukar ruwan sam bai damu Fahima ba asalima hawaye take fitarwa sosai. Ta tabbata ko Jannat ba ta kai ta son Yaya Sadauki ba, amma ko irin wannan matsayin da Haulatu ta samu a wajensa har yake mata murmushi ita ba ta taɓa samu ba. Tana tsaye ruwa na ƙarfi yana jiƙa mata jiki har ya shige motarsa ya fice. Sai ta bi bayan Haulatu zuwa falon Hajja.
Hajja ko damar tambayar Haulatu kiran me Sadauki ya ke mata ba ta samu damar yi ba don tuni Haulatun ta tsallake su har Umma da ta sauko a falo ta haye sama, Hajja na kiranta tana ba ta uzurin kaya za ta sauya ruwa ya ɗan taɓa ta. Da wannan ta haye ta shige ɗakinsu ta rufe. Hijabin ta soma cirewa bayan ta ajiye robar lemun da ya ba ta, kafin ta dora saman kujera na gaban dress mirrow ta hau kallon kanta a madubi tana wani irin murmushi mai bayyana fararen haƙoranta a waje.
'Ke banza, idan kuma ba shi Abeed din ba? Ba kya tunanin wani yake nufi daban?'
Cewar wani ɓangare daga zuciyarta, to wai ma ita da ba ta ra'ayin soyayya, ta kasa gane dalilin da yasa sam ba ta jin zafi idan tana misalta Yaya Sadauki matsayin masoyi. Sauke ajiyar zuciya ta yi, ta sauya kayan jikinta kafin ta dauki lemun ta fito zuciyarta wasai. A falon Hajja ta yi kiciɓus da Fahima, ganinta a jiƙe ya ba ta mamaki. To ita kuwa wannan ina ta fita ta je? Wata uwar harara Fahima ta watsa mata kafin ta kauda kai tana jan tsaki ta nufi hanyar ɗakin da ta ke kwana. Taɓe baki Haulatu ta yi cikin nuna halin ko in kula don idan da sabo ta saba da wannan kallon banzan daga Fahima. Kusan ma yanda zuciyarta ta ke cike da annashuwa ba ta tunanin wata ƙaramar alhaki irin Fahima za ta yi nasarar ruguza mata.
Hajja da Umma babu wanda ya tambaye ta me suka tattauna da Sadauki, don gaba daya ma an duƙufa da aikace-aikace na tanadin gobe sallah. Umma za ta yi wainar masa da miyar taushe, ga kuma sinasir. Baba Saude har ma da ƙarin wata dattijuwa suna ta aikace-aikace na shirin suya na gobe sallah. Wannan ya dauke musu hankula, ita ma ta shiga taimaka musu da aikin. Sai dai duk wanda ya kalle ta sai dai ya ga tana faman zuba murmushi, yanda ma ta ke aikin babu nunawa gajiya ko jin bacci ya sanya ɗora mata ayar tambaya sai dai ba ta ce uffan ba.
***
Aka wayi gari da bikin babbar sallah, dakyar Haulatu ta tashi da asuba don jiya har kusan karfe ɗaya ba su yi bacci ba. Sai dai tana yin alwala ta ji baccin ya kau, Umma tuni ta sauka ƙasa don fara aiki. Wuraren ƙarfe takwas suka yi shirin zuwa masallaci. Bayan an sauko wannan karon ba a yi wasu hotuna sosai ba adalilin aikin yanka da za'a yi. Ƴan matan ne kawai da samarin gidan sai ko yara da suka zo hutu. Radiya ta dubi Haulatu ganin sai faman ɗaɗɗaga wuya take.
"Ke, wa kike ta nema ne wai?"
Ta sauke ajiyar zuciya gaminda yarfa hannu.
"Wa kuwa nake nema? Kawai kewar ƴar uwata nake."
Radiya ta ɗan ja guntun tsaki.
"Ke nima fa ina kewar Feenah, da yanzu muna nan tare ana kashe kala."
"Uhum." Amsar da ta bayar kenan. Jikinta ya yi sanyi ganin har aka watse ba ta ga ƙeyar Sadauki ba.
Ranar dai sun sha aiki ba laifi, don raguna biyu aka yanka a ɓangaren Hajja, ɗaya na Umma ne saƙo daga Daddy Ridwan, ɗayan kuwa na Hajja. Na Uncle Abba matarsa Anti Haseena ta tubure ita a gidan ƴar uwarta za ta yi nata aikin, Hajja sam ba ta ji zafi ba ta ba shi umarnin ya dauka ya kai mata can ɗin. Shi ne ma ransa ya yi babu dadi ga yaran ta kwashe su ta tafi da su can.
Tun sallar azhar ta kwanta bacci ba ita ta farka ba sai da Umma ta tayar da ita don yin sallar la'asar. Haka ta miƙe tana mutsistsika idanu kafin ta shiga hamma, sai dai nan da nan ta katse hammar dalilin wanda ta gani zaune a falon yana ɗan kallonta. Ai a ruɗe ta shiga neman hularta ta rufe ƙananun kitson da aka yi mata. Tuni dama ta sauya kaya zuwa doguwar riga irin mai zuwa da mayafin nan. Baƙa ce mai taushi da aka yi adonta da golden din zarurruka a wuya zuwa ƙirji da kuma bakin hannu rigar.
Ya kauda kai ya maida ga danna wayarsa, sai ta ga ashe ma ba shi ɗaya ba ne, ga Uncle Abba zaune suna hira ga Fahima dake gefe ta wani nutsu kamar gaske, sai ko Hajja. An jera faranti dauke da gashin nama sai ko na masa da miya sai lemuka, ita duk sai ta ji kunya ta gaishe su sannan ta yi sum sum ta fice zuwa sama. A guje ta nufi gaban madubin ɗakin ta na kallon fuskarta, ba ta yi wani muni ba, idanun dai sun kaɗa sun yi ja hakanan sun ƙara fitowa sai ko gefen inda ta jima kwance da ya yi shatin layi layi. Amma sam babu miyan bacci. Ajiyar zuciya ta sauke duk da haka dai ba ta so Yaya Sadauki ya gan ta a haka ba. Bakin ta wanke ta dauro alwala. Koda ta yi sallar ma kasa komawa ƙasan ta yi, duk sai ta ji ta takura ga wayarta na can. Sai wuraren biyar ta iya fitowa, nan ma sai da Umma ta shigo ganinta kwance ta hau faɗan kar ta sake ta yi mata baccin yamma kafin ta iya miƙewa ta sauka. Ta ga babu kowa ma sai Hajja kaɗai da gyangyaɗi ke ɗan kwasarta.
***
Washegari ɗaya ga sallah suka shirya fita yawonsu ita da Radiya, Umma har gidan Haj Rabi'atu (ƴar uwar Maman Bahijja ta Kano) ta aike su da ƙullin nama. Kowaccensu ta cakare abin ta, suna tsaye suna sallama da Umma da kuma Hajja dake zaune, sai ganin mutum suka yi ya shigo da sallama. Nan da nan Haulatu ta tamke fuska, shi kuwa Zaid ya ƙaraso ciki, suka gaishe shi suka yi gaba, yana ta bin Haulatu da idanu babu ko kunyar Hajja da Umma.
Ya gaishe da Umma, ta amsa fuska a sake tana fadin.
"Ashe ba ka koma Abujar ba?"
Ya ɗan shafe ƙeya da ya tuno daƙyar ya lallaɓa mahaifiyarsa ta haƙura ta yarje masa yin babbar sallah a garin tare da sharaɗin da yake da tabbacin har a rai ba zai iya cikawa ba. Ya gaishe da Hajja dake faman zuba masa ruwan harara tamkar idanunta za su faɗo. Kauda kai ta yi kamar ba ta