Showing 174001 words to 177000 words out of 177840 words
kallonsu tana murmushi, hamdala take a ƙasan ranta na yanda su biyun suka haɗe kansu tun rasuwar mahaifiyarsu Inna, tsohuwa mai ran ƙarfe, ta sha jinya kafin lokaci ya yi. Tsirarta da Nene uwargidan Baba Dakta shekara ɗaya. Anti Mabruka ta yi aure har sau biyu, auren farko ta ci baƙar wuya a hannun mijin wanda ya zo mata da ƙarya ya nuna shi ɗin mai arziki ne, nan duniya ta ƙi amincewa da zaɓin da su Baba Alhaji suka yi mata ta ce ita wannan take so. Da yake ba sa yiwa kowa dole sai aka yarda aka aura mata shi. Tun daga gidan da aka kai ta ta ji hankalinta ya tashi, gida ne duk sumunti wanda aka ɗan yi ado da broken tiles a tsakar gidan. Kujerunta sun ƙi su ci falonta hakanan aka koma da wasu. Ciki da falo ne ɗaya sai fallen ɗaki guda. Sai wani banɗaki a tsakar gida sai ko kicin ɗinta. Kunyar duniya suka kama Anti Mabruka, ta buga tsalle kan ba za ta zauna ba. Baba Alhaji ya zuciya ya ce bata isa ba, haka ta soma rayuwa marar daɗi. Miji kuwa ta ki ba shi haɗin kai, faɗa suka yi kaca-kaca, karshe ko sati ba ta cika ba cikin dare aka shigo tana wani mugun bacci da ba ta san ya aka yi ya ɗauke ta ba, aka sace duka kayan lefenta da ma suturu da gwala-gwalan da ta taho da shi. Koda ta farka ta ga miji na bacci ta waiga ta ga alamar an shigo dakin ga shi nan a wangale yasa da sauri ta hau bincike, nan fa sabon rikici ya ɓalle inda ta rantse ta ƙara akan cewa mijinta na da hannu a wannan satar. A sannan ya kama ta ya yi mata lis da igiyar wuta, sai da ya ga ta daku sosai sannan ya rabu da ita. Tun daga nan ya ma hana ta fita don dama an kwace wayarta, kusan kullum sai ya jibgeta duk sadda ta masa rashin kunya. Kuma hakan bai hana ya kusance ta ba duk cizon da za ta yi da yakushi. Maama ta taimaka mata sosai don a ranar da ta kai mata ziyara ta ga halin da take ciki da yanda ta koma, ta ɗaura damarar kwatar mata haƙƙinta. A sanadin Maama ta kuɓuta daga azabar wannan bawan Allahn, don har ɓarin ciki ya sa ta yi sanadin duka amma bai faɗawa kowa ba, ita ma mugun halinta ya ja babu wani nata da ke kawo ziyara gidanta. Taimakon da Maama ta yi mata yasa ta ji kunya sosai ta kuma yi nadama tsantsa. Daƙyar Baba Alhaji ya iya yafemata. Koda ta kammala iddarta babu jimawa ta samu miji, tana zaune lafiya da shi, matansa biyu ita ta uku amma kowa da ɓangarensa. Ba shi da kudi sosai sai rufin asiri, amma suna zaman su lafiya. Yanzun hankalinta kwance.
Hawaye ya tahowa Haulatu ta yi azamar juyawa ta share su. Hamdala ta kara yi a zuciyarta na yanda komai yake sauyawa daga marar kyau zuwa mai kyau. Leɓɓanta ta ɗan ciza sakamakon mararta da ta ɗan ƙulle, can kuma yana saki ta miƙe.
"Ina za ki je? Ki dinga zama kina hutawa fa." Faɗin Maama tana kallonta. Ta yi murmushi.
"Maama wurin su Radiya zan je."
"Toh." Ta amsa. Suhail ne ya taho a guje yana ƙwala mata kira, Mami! Mami!! Ta juyo gami da dakatawa tana kallonsa da alamar gajiya.
"Ya aka yi Suhail?" Ya riƙo hannunta ya ɗan soma ja.
"Ki zo wani ne ke kiranki, wani gurgu a waje muna wasan keke da su Yaya Affan, Buzu Maigadi ya hana shi shigowa sai kuka yake yi."
"Haulatu, wai wani ne ya zo yana nemanki ke da Umma."
Ta ƙara jin muryar Radiya a gefenta, kafin ya farga ta ga Umma ta nufi bakin ƙaton ƙyauren gidan ita da su Malama da Momi Nuratu. Ga kuma su Safina a can, ƙirjinta ya shiga bugu da sauri-sauri, ta zare hannunta daga na Suhail ta nufi hanyar gate ɗin. Kar dai wanda ta ke yawan mafarki ne ya zo? Kai a'a, ya mutu, Hindatu ta ce mata ana zargin ya mutu. Don haka ba shi ba ne, amma kuma waye?
Ta kasa ba kanta amsa, a hanyar Radiya ke ce mata wai gurgu ne a saman keke sai wani ɗan matashi dake faman tura shi. Ita dai tuni ta ƙara sauri, kafin ma su karasa ƴan gayyar suna sun cika wajen. Daidai lokacin su Khaleefa da Sadauki suka taho, sun zo ne don yin hotuna kamar yanda Zaituna ta nema da magiya akan ita su zo a yi a ajiye tarihin sunan ƴan biyu. Suna hango cincirindo a ƙofa ya sa Muhsin mijin Safina fadin.
"Toh, lafiya kuwa?"
Babu wanda ya amsa sai ƙarasawa da suka yi wurin.
Umma ce ta soma tozali da shi kuma ta gane ko waye, a duk irin sauyin nan da ya yi na baƙi, rama da fita hayyaci, ga kuma yagalgalun kaya ba za ta kasa gane ko waye ba.
"Ibrahim? Kai ne haka?" Ta yi furucin cike da ɗumbin mamaki.
Jin sunan da Umma ta ambata ya sa Haulatu da ke kokarin ture jama'ar dake gabanta ta shiga ta ja baya tana ji kamar kafafunta na kasa ɗaukarta. Wato shi ne ya zo? Ɗan Mutuwa ne? Ji ta yi an riƙo ƙugunta sadda take shirin kai wa ƙasa sakamakon jiri da ciwon da take ji a mararta. Ido huɗu suka yi da mijinta.
Su Khaleefa ne suka buɗe hanyar suka ce kowa ya matsa gefe. Hakan ya ba Haulatu damar ganin mahaifin nata zaune a keken guragu, ga dai ƙafafun amma da alama sun samu wata matsalar. Ya yi wata iriyar rama sai karan hancin tamkar biro da suka ƙara fitowa tsabar babu tsoka a jikinsa. Cikin muryar kuka yake fadin.
"Ni ne Na'imatu, wallahi ni ne Ɗan Mutuwa ne. Kin ga yanda rayuwa ta maida ni ko?" Umma da hawaye suka wanke fuskarta ta juya da sauri ta ratsa mutane ta bar wurin duk kuwa da irin kiran da Ɗan Mutuwa ke mata yana furucin ta yafe masa amma ba ta ko juyo ba.
Haulatu wacce Sadauki ya tallafe yana kokarin barin wajen da ita, sai ta ji ba ta son tafiya. Tunda take a duniya ba ta taɓa ji har cikin ƙoƙon ranta ta tausayawa Babanta ma irin na yau. Ta ji zuciyarta ta yi wani irin karyewa ga ciwon marar dake ƙara gaba.
"Ba..ba." Ta furta da muryar da ya ratsa kunnen Sadauki tunda shi ke kusa da ita. Ya ɗan kalle ta, hawaye take yi, ta dafe mararta da hannunta na dama. Ita ma shi take kallo. Nan da nan ya dubi Mu'az.
"Ku shigar da shi ciki, ku kai shi wurin Baba Alhaji."
Mu'az zai yi magana, Sadauki ya tamke fuska, ba shiri kuwa ya juya don bin umarni.
Kowa ya koma ciki, baƙi na mamakin faruwar lamarin nan. Wato dai duk sharrin da ake yi da kananan magana akan Haulatu ba ta da Uba, ashe dai akwai? Kuma yana raye? Haka suke ta tattauna, a baya kam sanadin Momin Mu'az da Mamin Khaleefa wata gulma ta yaɗu wai Haulatu ba ta da Uba. Shegiya ce kawai Umma ta zo gidan da ita. Ta hanyarsu magana ta yaɗu na zargin kamar ma tana da cutar ƙanjamau, duk a dabararsu na cusawa mutan gari da yan uwa tsanarta. Sai dai haƙansu bai cimma ruwa ba a lokacin haka suka haƙura.
Ba wanda ya ƙara bi ta kan Ɗan Mutuwa, Sadauki dai ya ja matarsa ɓangaren Hajja zuwa ɗaki, so yake ta kwanta ta samu hutu amma ta ƙi, gaba ɗaya ita dai burinta ta je ta ji me ya maida mahaifinta haka. A baya ta tsane shi sosai, daga baya da kuma ta ji har a rai ta yafemasa komai, koyaushe addu'a da fatan shiriya take masa kafin mutuwa, wasu lokutan kuma idan tunaninta ya ba ta ko ya mutu ne, sai ta hau nema masa gafara da rahmar Allah.
"Please, ban son musu. Ki kwanta ki huta kin ji? Ko kina jin ciwo ne?"
Ta yi murmushin yaƙe don a sannan ciwon ya lafa.
"Aa, amma don Allah ka bar ni na je gurinsa."
Ta ƙarashe tana ƙara ɗora hannunta na hagu kan hannayensu da ya sarƙe wuri guda. Bai sha mamakin saukowarta ba don dama ya san tuni ta sauko daga dokin fushin da ta hau na mahaifinta. Ya sha kama ta tana zabga addu'o'i cikin dare.
"Shikenan. Amma ki bari zuwa anjima, yanzu kinga akwai baƙi a gidan."
Ta narkar da fuska za ta ƙara saka wai kukan. Da sauri ya sumbaci leɓɓanta kafin tace.
"Naji, na ji, tashi muje. Kinsan kuka na tsana ai."
Ba musu ya taimaka mata ta miƙe. Ba su kai ga fita ba suka yi karo da Ihsan ƴar Haj Hadiza da ta taho da sauri don kiranta zuwa falon Baba Alhaji kamar yanda Daddy Ridwan da su Barr Dawud suka buƙata. Kai tsaye suka ɗunguma can. A babban falon Baba Alhaji babu kowa sai zuri'arsu. Aka rufe ƙofar. Baba Alhaji na daga ɗaki, su Daddy Ridwan ke falon tare da Ɗan Mutuwa wanda aka ba ruwa ya sha, ga kuma abinci a gefe, ɗan matashin da ya rako shi, shi ya samu sararin ci, shi kuwa ba wannan ke gabansa ba, babban burinsa neman gafarar Bayin Allahn nan da ya baƙantawa a rayuwa ko zai ga haske can gaba.
Shigar Haulatu da sallama a bakinta, da Sadauki a gefe yana ɗan riƙo kafaɗunta tana takawa ahankali ta shiga ciki. Idanunta a kan Ɗan Mutuwa. Su Umma da su Haj Hadiza da Maman Zaituna suna daga gefe suna kallo. Umma hawayen itama take yi, ta ƙarasa ta zauna. Ɗan Mutuwa ya bi ta da kallo, yarinya ɗaya da ya mallaka a duniya. Ba shi da uwa balle uba, amma ya kasa nunamata soyayya. Karshe ma ya nemi jefa rayuwarta cikin uƙuba da kuma ɓata.
Bayan buɗe taro da addu'a ne Abba Ridwan ya nemi Ɗan Mutuwa ya faɗi abin da ke tafe da shi. Kamar jira yake ya soma magana da raunanniyar murya.
"Ba komai ya kawo ni ba sai na ba ku haƙuri na kuma nemi gafarar Na'imatu da Haulatu. Ku yafemin, sanadinku na ga ishara kala-kala a rayuwata. Ban kasance miji nagari gareki ba Na'imatu, na tabbata ba na daga cikin Uban da ɗiya za ta yi alfahari da samun sa."
Sai da ya ɗan tsaya ya ɗauke hawayen da suka zubo masa ya cigaba.
"Na haɗu da masifu iri-iri bayan kaucewa hanyar da Allah Ubangiji ya yi umarni a bi, na shiga ƙungiyar asiri, ni ne safarar yara mata kanana da manya zuwa ƙasar waje don su aikata alfasha su turomana kuɗi tare da Haj Adama. Ni ne siye da siyarwar miyagun ƙwayoyi. A ƙarshe da na rasa komai da na samu ta ɓatacciyar hanyar ƙungiyar asiri, na haɗu da ciwon shanyewar ɓarin jiki, inda komai nawa ya bar aiki. Mutanen da na riƙa matsayin yarana ƴan amana, su Duna da Ɗan Aljan, sun bar ni a asibiti yashe. Ƙarshe da kuɗin magani da aiki ya gagara aka sallame ni a asibiti. A sannan bakina ya buɗu ina iya magana kuma ina amfani da hannayena. Da magiya da kuka da komai, na samu wani mai tausayi cikin Alhazawan dake zuwa asibitin ya bani dubu goma ya kuma siyamin keken Ruwa, iska, sanyi, rana, haka nake yawo a titi neman abin sadaka da kuma abin da zan sa a cikina. Tun ina barar babu mai kallona, ko kuma na tara, ɓata gari su yimin wayo su karɓe. Da Allah ya so ni da shiriya, sai ya haɗa ni da dattijon kirki, kakan wannan yaron da muka zo tare. Su ma da bara suka soma kafin su samu jarin siyar da ruwa a bakin titi. Kakansa kuwa na siyar da goro a faranti. Mukan zauna mu yi hirar rayuwa, a hankali kuma aka saba, yasan ina da ƴa sai dai ban taɓa ba shi labarin komai nawa ba. Shi ya taimaka min da wajen kwana. Mukan je masallaci tare, mu yi sallah mu saurari tafsirin Alkur'ani Mai Girma sannan mu dawo. Daga nan na soma sha'awar daukar karatu. Dattijon ya ji dadi sosai, ya kai ni wurin Malaminsa na zaure. Na soma zuwa, ina ɗaukar karatu ina kuma kara nadamar abubuwan da na shuka. Ƙarshe ina kuka na zayyanewa Malamin komai. Bisa shawararsa da na dattijon na samu kwarin gwuiwar tunkararku don a duniya idan akwai wadanda na zalunta matsayina na marayan da bai riƙe maraicinsa ba ya biyewa abokai ɓata gari ya lalace, toh su biyo bayan Na'imatu da Haulatu. Ku dubi girma na Allah..."
Kuka ya hana shi ƙarasawa, falon kowa jikinsa ya yi sanyi. Daƙyar ya iya cewa.
"Ku yafe min. Na tuba, wallahi nayi tuban da ba zan ƙara waiwayar munanan aikin da na yi a baya ba."
"Na yafemaka Baba." Wannan furuci da ya fito daga bakin Haulatu sai da ya sa kowa kallonta da tsantsar mamaki musamman Umma, dama za ta iya yafe mishi lokaci guda haka? Shi kansa Ɗan Mutuwa sai da ya ɗago kai yana dubanta. Miƙewa ta yi da wani irin ƙarfin hali don bata bari Sadauki ya riƙe ta ba ta ƙarasa gareshi ta durƙusa ta riƙe hannunsa. Sai kawai ta fashe da sabon kuka wanda ya ba mutane tausayi.
"Na yafemaka Baba, ka ƙuntata min sau ba adadi, amma wallahi na yafemaka. Nima ina roƙon gafararka."
Wani sanyi da dadi ga kuma hawaye lokaci guda suka dirarwa Ɗan Mutuwa. Ya dafe kanta.
"Nagode Allah ya yi maki albarka, Allah yasa ki gama da duniya lafiya."
Ta amsa da amin, shi da ita kusan lokaci guda suka dubi Umma. Ta kauda kai ta maida duba ga Barr Dawud mijinta. Alama ya yi mata da idanu akan ta haƙura mana, sai ta sauke ajiyar zuciya.
"Na yafemasa. Allah ya yafe mu baki ɗaya."
"Toh Alhamdulillah, dama haka ake so, duk wanda ya yi maka ka manta ka yafemasa. Ya kamata ku mata ku koma ga taronku, kar ya kasance an samu ƙofar kananan magana duk da ba a raba ku da shi ko?"
Alh Yusuf baban kowa, mahaifin Radiya ya yi maganar yana karashewa da ƴar dariya. Nan kuwa duka aka miƙe har Umma, Haulatu na kokarin miƙewa ta ji mararta ta kulle.
"Ya Allah!" Ta firta da ƙarfi gani da komawa ta zauna. Nan da nan aka yi kanta, Sadauki ya tallofa ta a ruɗe.
"Haihuwa ce fa ina ji." Faɗin Khaleefa. Duk sai kowa hankalinsa ya tashi. Aka ɗauke ta zuwa mota. Dan Mutuwa ya ce zai bi aka ce ya yi hakuri ya zauna. Su Umma dai suka koma ciki ta yi kara saboda ganin kowa na son zuwa. Abba Ridwan ne yace Maman Zaituna da Momin Mu'az ne kaɗai za su bisu. Aikuwa haka kowa ya haƙura.
Suna zuwa babu jimawa ta haifi ɗiyarta mace. Labari na zuwa gidan aka hau sabon murna. Zaituna ji take kamar ta yi tsuntsuwa ta je asibitin. Ɗan Mutuwa kuwa yana ji ya shiga hamdala.
Washegari kuwa aka sallamota bayan an ga komai lafiya. Falon Hajja ya cika da mutan gidan zallah ana karɓar jaririya, shi kuwa Sadauki sai shan murr yake yi wai a dole ba a kyauta masa. Haka ya je inda Khaleefa da Mu'az har Zaid (wanda aikinsa ya dawo Katsina) suke tsaye, faɗi yake.
"Kai ni fa Allah zai min sakayya tsakanina da wacce ta fara kawo shawarar wankan gida a rayuwar Malam Bahaushe. Haka nan muna zaune da matata a wani raba ni da ita wai wankan gida. Toh na rantse wannan karon fa a gidana za ta yi jegon. Bari su ga yanda zan ɗaukemusu ita."
Su Khaleefa suka kwashe masa da dariya wanda ya ƙara shaƙar da shi.
Aikuwa kamar wasa da daddare ya shiga ɓangaren Hajja, nan ya ga Zaituna zaune da Khaleefa sun wani saka ƴan biyunsu a gaba suna kallo jikinsu a haɗe. Harararsu ya yi yana kiran shi ba zai yi abin kunya ba, ya haye saman ya bar su da yi mishi dariya. Ya iske Maman Zaituna zaune a ɗakin tana lallaɓa Haulatu kan ta daure ta ci abinci ko yaya ne. Bayan sun gaisa ya ɗan saci kallon Haulatu, ta kauda kai, ta san me ya kawo shi ba kuma ta so ya yi rashin ta idon a gabanta don haka ta ƙi kallonsa, da ace ma za ta iya miƙewa ta bar ɗakin da ta yi.
"Mama, amma dai ba anan za ta zauna ba ko?"
Maman Zaituna ta fiddo ido.
"Idan ba nan ba ina kake son ta je? Ai tana nan gidan sai ta gama wanka za ta tafi. Wa zai kularmin da ita a gidan naka?"
Wani abu ya soki zuciyarsa, kamar yace ni zan kula da abina, ai da kai da kayan duka mallakar wuya ne, sai kuma ya yi shiru ya haɗiye. Yana wani cin magani ya fice ya bar ɗakin Maman Zaituna na ka tsaya ka ga ɗiyarka amma ya ce sai gobe. Gaba ɗaya Haulatu ta ji wani iri, hakan ba ya daga cikin ɗabi'un Maman Zaituna, mace ce mai faram faram da komai, sai kawai ta ji ta saka dariya. Da sauri ta dube ta.
"My daughter, na iya acting ko? Kar ki damu kin ji ko? Kin zauna ne saboda surukarki kuma mamanki tace a bari ki yi wankan koda na sati ne sai ki koma gidanki. Ba don haka ba kin fi kowa sanin bana son harkar wankan gidan nan, ita ma waccan yayartaki don su Na'imatu sun goyamata baya ne. Amma tunda an yi suna dolenta su tattara su koma."
Murmushi kawai Haulatu ta yi. Koda Sadauki ya kira yana mita hakuri ta dinga ba shi, karshe ma har haushinta ya ji wai dama itama haka take so. Daƙyar ta lallaɓa shi. Ƙara shiga ranta yake yi koda yaushe, ga murnar ya dauki nauyin mahaifinta, ya kai shi asibiti mai kyau domin kula da lafiyarsa, Barr Dawud kuwa ya sallami yaron da ya rako Ɗan Mutuwa bayan ya bi shi da tarin alhairai.
Ranar sunan Baby Aidha, Hindatu ta zo har Katsina daga Sokoto inda take aure a yanzu. Wani ɗan