Showing 105001 words to 108000 words out of 177840 words
nan gidan ya shigo ya furta sakin ƙwarara har uku rak!"
Mamaki sosai wannan karon Haulatu ta ji, kafin ta ƙara wata tambayar Hajja ta shiga warware mata zare da abawa, hawayen farin ciki suka sulmiyo daga idanun Haulatu, ta rungume mahaifiyarta. Baƙin ciki ko damuwar da suke tunanin za ta yi sai suka ga ko alamarsa babu duk da dai ta danne ainahin damuwar a ƙasan ranta. Kowace ɗiya za ta so yau a nuna mata mahaifinta a mutumin kirki, ta yi mishi kyakkyawan zato da tunanin zai shiryu koda ba sa tare, sai dai da ƙaryar da ya zo har ma da kudaden da ya mallaka a yanzu wanda ko shekara ba'a rufa ba ya tabbatar mata nata Uban ba zai fasa halinsa ba duk muninsa kuwa. Murnar rabuwar Umma da mutum irinsa ya shafe wannan damuwar nata. Tana kuma da yaƙinin yanda a baya bai ci galaba a kansu ba, gaba ma babu abin da zai taɓuka.
"Umma shi ne ki ka yi kuka har fuskarki ta sauya? Don Allah kar ki ƙara zubarmasa da hawayenki. Kansa ya yiwa ai."
Faɗin Haulatu kafin ta miƙe zuciyarta wasai don ji take kamar an raba ta da wani nannauyan dutse. Hajja ta bi ta da kallo tana fadin "Yauwa ƴar albarka, ke dai ki nusar da mahaifiyarki. Duk ta bi ta saka ranta a damuwa."
Haulatu ta yi murmushi tunano da kalaman da Yaya Sadauki ya yi mata wanda a lokacin ta yi musu kallon marar dalili.
Umma kallonsu kawai take yi. Ita ta san Hajja ta fahimci damuwarta saboda ga duk mai hankali ya san mutum irin Ɗan Mutuwa ba mugu ne kuma babu tsoron Allahn da zai yi sanadin dakatar da shi ga aikata wani mummunan abin, shi ne babban dalilin Hajja na tausarta da ƙara yi mata nuni da babu abin da zai faru. Tabbas ta sani, yanzun ma addu'a ce ta yi nasara a kansa har ya zo ya yanke igiyar aurenta uku dake kanta, ta kuma sani a gaba ma addu'ar ce za ta yi tasirin da in sha Allahu ba zai cutar da ita da ɗiyarta ba. Damuwarta me zai yi? Wane matakin zai ɗauka? Ta san shi a zaman shekara da shekarun da suka yi da juna, mutum mai kafiya da shegen taurin kai wanda babu gurbi na yafiya a zuciyarsa kwata-kwata. Ai shi ba ma ya yafe laifi sai ya yi ramuwa a kai. Ga kuma mamaki na wannan uban kudin da ya tara da take da tabbacin ba halaliyarsa ba ce, ko ta wace hanya ya bi ya tara? Gefe ɗaya kuma tausayin aminiyar ƴarta ta ji, haƙiƙa ta jefa kanta a hannun baragurbi wanda nan gaba za ta yi dana sani.
"Ke Na'imatu, ki fita idona na rufe. Wato duk ɓaɓatun da nake yi ashe ya tashi a banza? Ina nunamaki gabas kina tafiya yamma? Tunanin uban me ki ke yi da nake ta magana ki ka yi shiru?"
Maganar Hajja ta maido Umma duniyar da ta bari na lokaci, Haulatu wacce ta fito daga banɗaki tana gyara zaman hannun rigarta da ta naɗe don yin alwala ta dubi Umma a raunane ta ce.
"Don Allah Umma ki cire komai a ranki, abin fa mu godewa Allah ne. Hajja kusan kullum ina yawan kama ta cikin dare tana addu'a tana kuka. Ni na san kuma addu'arki ce Allah ya amsa ya kawo mana waraka har gida."
Daga nan ta saka hijabi ta shimfiɗa darduma ta bar Hajja na ɗorawa daga inda ta tsaya.
***
BAYAN KWANA BIYU...
KANO...
A yau ce ranar zuwa taronsu na ƙungiya wannan ya sa ya kasa yin wani baccin kirki ba don komai ba sai don ɗoki da ya ke yi da ma ƙaguwa da ya yi ya je su yi magana da Uban Dodo don a san matakin ɗauka game da Na'imatu. Ya rantse ba zai bar rayuwarta ta zauna cikin aminci ba har sai ya salwantar da ita, ya kuma aika mugun abu wanda zai hana ta sakat a duniyar da ta zaɓa madadinsa. Har garin saurin ya fice taro ya mance bai fesawa Hindatu hodar da ya saba shaƙa mata ba mai sa bacci. Ita kuwa ƙarfe biyu da mintoci na dare ta farka daga bacci don yin fitsari. Ganin ba ya gefenta ta yi tunanin ko banɗaki ya shiga don haka ta ɗan zauna tana aikin murza idanu gami da jiran ya fito ta shiga, gajiya da zaman ya sa ta fice zuwa banɗakin dake falo ta yi ta dawo, har ta kwanta na ta ji alamun fitowa daga banɗaki ba sai hakan ya sauya tunaninta, to ko dai ba ya ciki ba? Ta miƙe da sauri ta hau buga ƙofar, jin shiru ta bude, babu alamun mutum, ta fito ta rufe gami da fita zuwa sashinsa. Nan ma wayam, ga dai kayansa na bacci da ya saka ɗazun ya cire su ya bar su a saman gadon, bandakinsa ma ta leƙa ba ya nan. Kamar mahaukaciya haka ta shiga duba dukkan ɗakunan gidan sai dai ba ta sauka ƙasa ba saboda tsoro. A ƙarshe ta dawo ɗakinta ta fiddo wayarsa ta kira nan ma a kashe. Ta yi saurin buɗe labule ta leƙa farfajiyar gidan, motarsa da ya fita da ita ɗazun, ba ta nan.
"Na shiga uku." Ita ce kalmar da ya fito daga bakin Hindatu yayinda wani tsoro da firgici suka mamaye zuciyarta lokaci guda. Ina Alhaji Ibrahim ya tafi toh? Ita ce tambayar da ba ta da amsarta.
Wani wawan ƙara Uban Dodo ya saki kafin ya zaro ido ya dakawa Ɗan Mutuwa dake durƙushe a gabansa tsawa mai firgitarwa.
"Kai! Ai mu ba'a zuwar mana nan da wasa! Me na ce maka? Ban ce ka bi komai a hankali ba?! Ka san irin ranar da Na'imatu za ta yi maka a gaba?! Shi ke nan, yanzu ka sake ta! Har abada kuma ba za ta dawo gidanka ba! Dama na faɗamaka! Idan ba ka bi a sannu ba za ka yi nadama."
Gumi ya tsirfowa Ɗan Mutuwa, ya sani ba nadamar rabuwa da Na'imatun ake nufi ba don yana sonta, sai don wani babban muƙami da girma da Uban Dodo ya hango masa samun shi nan gaba muddin bai rabu da ita ba. Uban Dodon bai sanar da shi wannan labarin ba sai a haɗuwar da suka ƙara yi a wannan daren.
"Tuba nake Jagorana, a yafemin. A taimake ni a haskamin wata mafitar."
"Ƙarya kake yi! Ni Uban Dodo ba na magana biyu. Tun da har ka rabu da ita, wannan rabo wuce ka. Abu na gaba, ina maka albishir da cewa matarka na ɗauke da juna biyu, wanda ya kasance mallakinmu ne. Ranar da abin da aka haifa ya fito duniya, ko wanka bamu yarda a yi mishi ba, ka kawo mana shi har mabiyarsa. Wannan alƙawari ne da ya zame maka dole ka cika mana."
Da girmamawa ya amsa da toh ya yi godiya kafin ya bar gaban Uban Dodon wani ya maye gurbinsa da na sa kalar buƙatar.
Koda suka fito a hanya Ɗan Mutuwa sai huci yake furzarwa na takaici ya ma kasa magana duk da irin ruwan masifar da Hajiya Adama ke surfawa wai meyasa bai ji shawararta ba ya kwantar da kai har ya samu ya ƙara shawo kan Na'imatun? Ta ƙara da faɗin.
"Ni jikina ya ban tunda har ka ji Uban Dodo ya ce ka bi komai a sannu, toh dama akwai abin da ya hango. Yanzu shikenan, watakila ma rashin sa'a da baƙin jini za ka yi kiciɓus da shi a harkokin siyasar da ka ke son tsunduma saboda rashin Na'imatun."
Ran Ɗan Mutuwa ya ƙara ɓaci, ya dube ta a fusace.
"Au, kin san da hakan shi ne ba ki ankarar da ni ba sai bayan ta faru ta ƙare? Ina zan san cewa wani abin ya hangar min tunda ba saninsa na yi ba sai yanzun?"
Haj Adama ta ja tsaki.
"Aikin gama ya riga ya gama, yanzu dai ka yi kokarin cika alƙawari da zarar lokacin haihuwar Hindatun ya yi kar ka kusa ka bari kowa ya raɓe ta, kuma ka zuba idanu a kanta."
Sunan Hindatun da ta ambata ya tunatar da shi bai fesa mata hoda ba. Ya ɗan bugi sitiyari.
"Kash, kin sa na tuna fa. Yau garin sauri na fitowa mu haɗu ban sumar da ita ba. Ina da tabbacin za ta iya farkawa koyaushe cikin daren nan ta bincika ko'ina da zummar nemana."
Ta ƙara jan tsaki karo na biyu.
"Wannan kuma matsalarka ce. Sai ka san me za ka yi. Tun farko ai sai da na shawarceka da koyamata ɗan korawar nan, da tana yi ko yaya ai da wataƙila yanzun ta kai Habasha."
Ya jinjina kai.
"Ni ma ina son ta iya harkar nan, sanadinta mu samu customers. Kin ga idan ta koyawa wasu matan musamman wadanda suke cikin damuwa da tabon ɗa namiji, za su dinga sadaukar da kuɗaɗensu wajen siya. Ba ma su kaɗai ba, ina son har matasan ƴan mata su tsunduma wajen siya, yanzu samarin sun fi ba da haɗin kai yanda ya kamata. Waɗannan duk ƙananun matsaloli ne, yanzu babban takaicina shi ne damar da ta suɓucemin sanadin wautana. Amma ba kya tunanin idan na saka wani ya aure ta kuma ya sakarmin ita ni kuma na ka na aure ta, damar ba za ta dawo min ba?"
Haj Adama ta yi dariya sosai kafin ta girgiza kai.
"Ni ban san wace irin kwakwalwa gareka ba wani sa'in, ban da wauta irin taka, waye zai ƙara kallonka a mutum a cikin zuri'ar su Na'imatu har a ƙara yarjemaka da batun aurenku karo na biyu? Kai Ɗan Mutuwa, ba fa a bariki ake wannan soki-burutsun ba."
Ya ji zafin maganganunta sai kawai ya share bai ƙara tayarwa ba, har suka isa gidanta, ita ɗin ma tun a motar ta buɗe kwalaben codein har biyu ta shanye, waɗannan sam ba su yi mata aiki a jiki yanda ya dace yanzu, zai wahala su bugar da ita ba ta dauke su komai ba sai ta haɗa da ƙwaya. Ba su yi wani sallamar arziki da Ɗan Mutuwa ba ta shige, shi kuwa ya damƙawa Maigadinta muƙullin motar sannan ya shige tasa ya fice.
Hindatu kuwa a ɓangarenta gaba ɗaya hankalinta ya tashi, daƙyar ta jure aka yi sallar Asubahi sannan ta fito wajen masu gadi da tambayar inda mijinta ya je? Nan suka ce ba su da masaniya, haka ta koma ciki duk ta ruɗe sai kuka, ganin abin zai mata yawa ne ta soma kokarin kiran Mominta kenan ta ji ƙarar hon ɗin motarsa. Ai da sauri ta yi wurgi da wayar ta fito a guje, yana shigowa ya wuce ta fuskarnan a murtuke ya nufi ciki. Jikinta a sanyaye ta bi bayansa har ɗakinsa da ya shiga ya hau fidda kaya.
Ganin babu fuskar yin wata tambayar yasa ta ja jiki ta fice ta koma na ta ɗakin tana hawaye. Koda gari ya yi haske tarr bai fito ba, da ta leƙa ma ta ga ya bararraje yana baccinsa har da munshari don haka ta ja masa ƙofar kawai.
Sai wuraren ƙarfe huɗu na yamma ya tashi, tana ta son ta tayar da shi domin yin sallar Azahar amma tana shakkar kada ya rufe ta da faɗa.
Tana zaune bayan ta kammala cin jellof rice din da Bayarabiyar ƴar aikinta mai kula da ɓangaren girki ta yi. Ta hango shi ya sauko daga bene, ya yi wanka, kai tsaye inda take wajen cin abinci ya ƙarasa, madadin ɗazu da fuskarsa ke a kacame, wannan karon ya saki har da sumbatarta a goshi kafin ya ja kujera ya zauna yana fadin.
"Madam, sannu."
Ta yi murmushin yaƙe.
"Yauwa. Fatan ka tashi lafiya?"
Hankalinsa na ga duba wayarsa don ganin waɗanda suka kira shi tun safe, ya amsa mata kafin ta miƙe ta jawo faranti ta shiga zuba masa abinci.
Sai da ta ga ya maida hankali wajen ci ta ɗan yi gyaran murya ta ce.
"Jiya na tsorata da ban ganka ba. Na ma yi zaton ko wani mummunan abu ne ya faru."
Ya ɗan taɓe baki yana fadin.
"Uhm uhm, ko kusa. Dama na san za ki damu. Wani cikin abokaina ne ya kira ni a waya ba lafiya gidansa shi ne fa na je. Uwargidansa ce don ya sanar mata batun zai ƙara aure ta nemi kai shi lahira. Toh yanzu dai case din yana hannun jami'an tsaro. Shi kuma mun kai shi asibiti don ta yanke shi a gefen ciki amma an ci sa'a wuƙar ba ta shiga ciki ba. Sam na mance da na kashe wayata, da ɓacin ran wannan jahilcin na wasu matan na dawo gidan ɗazu. Ki yi hakuri na san na tada maki hankali."
Har zuciyarta ta yarda da tatsuniyarsa, sai a lokacin ne kuma ta ji wannan tsoro da fargabar da ta shiga ma tunanin inda ya je ta kau, sosai ta saki ranta har da taya shi jimamin wannan abu. Daga nan dai komai ya wuce kamar bai faru ba. Shi kuwa Ɗan Mutuwa har wani murmushin cin galaba ya yi, abin da ke sosa ransa yanzu bai wuce na fansar da ya ke son dauka a kan Na'imatu da ɗiyarta ba. Nan da nan zancen Sadauki na ƙarshe ya faɗomasa a rai, Hindatu aminiyar Haulatu ce? Ai kuwa nan ne hanya mafi sauƙi ta samun lambobinsu. Don haka ya umarce ta da ɗauko masa robar tsinken fitar da nama ko wani abin a tsakanin haƙora idan ya maƙale (toothpick) a saman teburin tsakiyar falon sama. Ta kuwa miƙe ta bar wayarta wanda tuni ya san mabuɗin tun zamansu a Dubai. Ya shiga laluba sunan Haulatu sai dai bai gani ba, ya koma na Na'imatu nan ma ya rasa, ya kasa gane wane sunan ta saka, ga shi dai ba ƙwarewa a waya sosai ya yi ba. Jin za ta sauko sai ya wayance da buɗe ma'adanar hotuna ya shiga kallo. Koda ta ga wayar a hannunsa sam ba ta ji wani abu, ba ta da abin ɓoyo tunda ya san tana tiktok da su instagram. Bai kuma taɓa hana ta ɗora hotuna da bidiyo ba. Mominta kuwa sun fi yi waya akan magana ta whatsapp.
Ya miƙa mata wayar yana karɓar robar ya zari tsinke ɗaya ya dube ta.
"Ke km kamar ba ki da ƙawaye ko? Ban taɓa jin wata ta ce za ta zo maki ba sai dai makwafta masu shigowa."
Hindatu ta yi dariya lokacin da take tattara farantan.
"Ni kuwa ke da ƙawaye, sai dai gaskiya aminiyata ɗaya ce. Haulatu, amma ta bar garin ita da mahaifiyarta da jimawa."
"Meyasa?" Ya ƙara tambayar yana dubanta a tsanake ba tare da ya maida hankali ga wayarsa dake ƙara ba, ƙarshe ma ya katse kiran.
Hindatu sai ta ji ba za ta iya fitowa ta ba shi labarin rayuwar ƙawarta ba, ta zaɓi ta ɓoye aibunsu don haka ta ce.
"Uwar ce suka rabu da baban shi ne ta koma wajen ƴan uwanta."
Ta zaɓi ta yi mishi ƙaryar da ba ta da masaniyar gaskiya ce a yanzun. Shi kuwa ɗan murmushi ya yi, wato yana yiwa Yarinyar kallon sokuwa ashe tana da wayo? Lallai ya yarda ba ta san shi ɗin waye ba.
"Kuna waya?"
Ta jinjina kai.
"Muna waya har lambar Ummanta gare ni."
Fuska a sake ya ce.
"Amma kuwa watarana ya kamata ki kai mata ziyara. Ni na san za ki so hakan."
Ai kuwa ta washe haƙora ta dube shi.
"Dagaske?"
Ya jinjina kai yana ƴar dariya.
"Eh mana. Ai kin ce aminiyarki ce, duk abin da kike so kuma ni ma ina sonsa."
Ta kuwa rungume shi cike da jin dadi, ya yi dariya. Ta sake shi.
"Na kuwa gode sosai, ni na san Umma da Haulatu za su yi murna da gani na."
"Hakane, sai dai ban taɓa ji kun yi waya ba. Faɗamin gaskiya Bebi, ko ba ki da lambobinsu ma."
Ta ɗan turo baki a shagwaɓe ganin yanda ya ƙarashe zance cike da zolaya.
"Allah dagaske nake fa muna waya da su, kalli fa ko sati bamu yi da magana da Umma ba."
Ta fadi tana bude wayarta gami da lalubo lambar Umma wanda ta yi saving da My 2nd Mom ta nunamasa. Har wata ajiyar zuciya ya sauke na jin dadi, ya mike yana dariya da fadin.
"Yanzu kam na yarda kuna waya. Bebi bari na je na dawo, maza ɗaukomin turare na ƙara fesawa, saman ne bana son komawa." Da murmushi ta amsa da toh sannan ta juya tana wani rangaji ta nufi matattakala. Tana bada baya kuwa ya dauki wayar ya shigar da lambar Na'imatun don yanzun shi ya fi buƙata ba na Haulatu ba.
***
Katsina...
Da tsantsar mamaki dauke a fuskar Malama Safiyya take duban ɗan nata dake tsugunne a gabanta yana russunar da kai.
"Ka ce me? Haulatun Hajja ka ke so? Zaidu ka san me kake faɗa kuwa?"
Zaid ya kasa ɗago kai ya dubi mahaifiyartasa, zuwa lokacin soyayyar Haulatu ta na neman illata shi, sanadin yawan tunani ya soma samun matsala a harkokinsa na aiki da ma zamantakewarsa da matarsa Jalilah. Ya kai munzalin ko a mutu ko a yi rai, komai ta fanjama fanjam, ya ji ya gani zai juri dukkan wani abu da zai biyo baya. Zai shanye zagi da ma maganganun da zasu biyo bayan fitowar zancen nan. Don haka ya zaɓi yin shiru madadin ƙara jaddada abin da ya fadi, hakan zai sa Mahaifiyarsa ta ƙara fahimtar iyakar gaskiyar abin da ya faɗamata, kamar yanda ta saba fahimta a shirunsa.
"Ba zai yiwu ba, ka gaggauta fidda ta a ranka. Ko daga yanayinka kaɗai, na fahimci irin zurfin da ka yi a kan haka, sai dai ka sani cewa, ni dai Safiyya ba ni da idanun da zan dubi ƴan uwana ko iyayena na isar da saƙon ka garesu. Ai idan da kunya ma, ba ka fara ba Zaidu. Duka ba ma wannan ba, ita yarinyar ta san da wannan zance?"
Zaid wanda kalaman Malama suka jefa shi cikin firgici da tashin hankali wanda nan da nan ya haɗa gumi ya girgiza kai.
"Ta sani sai dai ba ta ba ni goyon baya ba."
"Ai dama ba za ta bayar ba, ko an fadamaka za ta kasa