Showing 141001 words to 144000 words out of 177840 words

Chapter 48 - FITAR TSIRO COMPLETE HAUSA NOVEL BY RUFAIDA UMAR

11 Jul 2024

79173

kuma faɗar ba shi da ma'ana tunda ba lallai a wasu su yarda ba musamman mahaifiyar Fahima Haj Hadiza wacce ta dage ai shegen iyayin Haulatun ne ya sa ta fadi, har da cewa wataƙila ma danna waya take yi. Ita dai ba ta ce uffan ba, Umma ma dake zaune ko miƙewa ba ta yi ba ballantana a ce ta yi wani abin. Maimuna wacce ta samu zuwa bikin bisa iznin mijinta, sai sannu take jero mata. Tsabar baƙin ciki tana wanke bakin amma hawayen bai bar zuba ba, daƙyar jinin dake fita a leɓan ya tsaya amma bakin nan ya kumbura. Ranta ta ji yana zafi, ta rantse Fahima sai ta yi kuka fiye da wanda ta sanya ta.

Abincin ma fasa shiga ta ɗiba ta yi, Hajja sai sannu ta ke jerowa, har da yiwa Baba Saude faɗa akan ta yi sauri ta kammala gugan, ba ta bi ta kan wayarta ba ta wuce ta koma sama. A falon sama ta iske Fahimar zaune tana danna waya. Suka haɗa idanu Fahima ta ƙyaƙyace da dariya sai ta wayance kamar mai yin voicenote a whatsapp ta ce.

"Ke, wani abu na gani ya tunamin da Shrek. Hum, ina ganin salo a gidanmu, ai ina faɗamaki Yaya Sadauki dai ya fi ƙarfin mutum, kuma duk yanda aka ƙwallafa rai a kansa ake mishi tallar ciki da waje ba'a ishe shi kallo ba."

Tsaf ta gane inda maganar ta dosa, rufe ƙofar ɗakinsu ta yi bayan ta shiga, tabbas akwai ranar ba ta amsa, akwai babbar ramuwa tana zuwa. Ba kuma a yau ba.

Ba ta jima ba sai ga Maimuna ta shigo da sallama, ta amsa mata, abinci ne a faranti ta kawo.

"Ga abinci Hajja tace a kawomaki."

Kamar ta ce ta ƙoshi amma sai ta ji ba za ta iya ba don dagaske yunwar dai take ji, godiya ta yi mata. Maimuna ta zauna tana miƙa mata wayarta gami da furta.


"Wannan ta ci screen."

Ta karɓa ta ga wani far far yake yi, sai kawai ta ajiye a gefe. Duban Maimuna ta yi.

"A nan za ku kwana?"

"Aa fa, yana hanya ma yanzu zai ƙaraso mu tafi."

Ta jinjina kai, daƙyar ta ke sa abincin a baka da cokali saboda raɗaɗin da leɓan ke mata.

"Ki yi hakuri, na san Fahima ce da wannan aikin."

Maganar Maimuna ya sa ta dubanta da mamaki. Ta jinjina kai.

"Na gan ta, zan shiga kicin ajiye kofi, na ga sadda ta saka maki ƙafa ta gudu. Don Allah kiyi hakuri."

Ɗan murmushi Haulatu ta yi, kamar ta tambaye ta dalilin da ya hana ta faɗi amma sai ta share.

"Bakomai, kar ki damu. Kanta ta yiwa."

"Hakane, ban faɗa ba ne saboda ba na so ya jawo abin magana, kin san yadda Hajiyar tawa take."

Wato Haj Hadiza mahaifiyarsu, Haulatu dai ba ta tanka ba ban da wani murmushin. Wayar Maimuna da ya yi ƙara ne ya sanya ta miƙewa.

"Kin ga har ya zo ma, bari mu wuce sai da safe. Allah ya ƙara sauki."

"Amin, sai da safe nagode."

Ta na ba ta amsa ma kafin ta kai aya ma Maimuna ta wuce, ga dukkan alamu daga yanayinta mugun shakkar mijin nata take yi. Ta maida hankali ta ci abincin ba wani sosai ba, ko wayar ba ta son kallo tsabar baƙin ciki don wani baƙi ta yi daga tsakiya har ba ka iya ganin fuskarta sosai. Fita da abincin ta yi ta maida ƙasa ta rufe a kicin sannan ta dawo ta yi kwanciyarta bayan ta kashe wayar gaba ɗaya ta jefa a dirowar gefen gadon. Nan kuma ta tsunduma tunanin Sadauki, ta manta da dukkan wata damuwa, kalamansa suka shiga dawowa tiryan-tiryan a kwakwalwarta yayinda ƙaunarsa ke ƙaruwa a birnin zuciyarta. Sai ta ji tana kewar muryarsa da ganinsa, kamar ma sam a yau ba su ga juna ba haka ta ke ji don soyayya da shauƙi. Daƙyar ta samu dai ta yi addu'ar kwanciya bacci ta kwanta, kafin Umma ta shigo tuni ta yi nisa a baccinta.

***
Kano....
Mummunan labarin da ya risƙi Haj Adama na tashin gobara a makeken store ɗinta dake a keɓantaccen wuri a daji wanda ba kowa ya sani ba, ya jefa ta cikin kaɗuwa da tashin hankali marar iyaka don har suma ta yi saboda tsabar firgici. Nan da nan ta baza tare da muƙarrabanta don zuwa ganewa idonta. Sai dai babu wani kayanta da ya tsira, wuri ya shafe ya zama toka. Ai sai ga Haj Adama na maganganu kamar zararriya. Fadi take.

"Allah ya tsinewa Ɗan Mutuwa, Allah ya isa! Sai na ga bayansa! Na rantse sai na zama ajalinsa! Da ni Adama ya ke zancen! Ni na san babu wanda zai min wannan aikin sai shi! Dama ya ci alwashin ramuwa! Ashe ta nan ya ɓullo!"

Sai kawai ta shiga kururuwa da ihu ana riƙe ta. Daƙyar ta iya shiga mota tana kuka wiwi da majina suka bar wurin. Babbar asara ce na kayyakin da ba nata ita ɗaya ba. Ta sani idan kowa ya mata uzuri ya ba ta damar haɗa wasu kayayyakin, to fa ban da Major Musbahu, ba shi da mutunci ko kaɗan. Ko yau wuraren hudu na safe sai da ya dokamata kira akan a fito da kayansa a biyo hanyar Lagos, har ta ji haushi ta rufe shi da faɗan na fa tsoronsa take ba, har da cewa ita daga wannan ma ba za ta ƙara haɗa harka da shi ba. Suka yi zage-zage, ya kuma ci alwashin muddin ba ta aikomasa kaya ba zai yi maganinta. Ashe kuwa kayan da ba za su aiku ba kenan. Sai ta ƙara fashewa da wani gunjin kukan. Wayarta dake ruri ta duba, gabanta ya yi mugun faɗuwa ganin sunan Major Musbahu na yawo saman screen. Hannu na rawa ta miƙawa ƴar amanarta Yakura.

"Kashemin wayar gaba ɗaya."

Abin da ta ce kenan, ba musu Yakura wacce ta sha man bilitin fiskarnan kamar ɗanyen nama ga hudan hanci da bai mata kyau ba, ta cika umarnin Uwar ɗakinta.

Haka suka koma cikin gari Haj Adama na saƙe-saƙen matakin ɗauka.

***
Hindatu ta zubawa Mominta dake rawar jikin haɗa kaya idanu. Ba na komai ba ne sai na tafiyar da Momin za ta yi Dubai a satin don yo mata siyayyar haihuwa wanda Ɗan Mutuwa shi yake shiryamata komai na tafiya. Duka hakan kuma don ya ƙara wanke kansa a wurin Hindatun ne don a tunaninsa rashin ta idon da ya yiwa Mahaifiyarta ne ya sanya ya chanza.

"Momi." Kiran sunanta da Hindatun ta yi ne ya sa ta ɗagowa ta dube ta fuskarnan cike da annashuwa ta amsa.

"Na'am ƴar Mominta. Shalele mai goshin arziƙi, ta Alhaji Ib..."

"Momi don Allah mana, ni bana son duka wadannan abin, ba na son dukiyarsa hatta shi ɗin ma ya ficemin a rai. Ni ki maida masa komai a raba aurenmu."

Ai ba ta san sadda ta saki ɗan ƙaramin akwatin ɗan kunnen da sarƙa da take ƙoƙarin jefawa a jakar tafiyar da ɗoki ya sanya ya fara shiri tun wuri ba.

"Eh?? Me ki ke cewa? A raba aurenki da Alhaji Ibrahim? A'a ina jin ban fahimci zancen ba. Hindatu, auren nan ki ke fatan a raba?"

Cikin zubar hawaye Hindatu ta gyaɗa kai tana kallonta.

"Eh Momi, ba na son auren nan."

A harzuƙe Momin ta amsa tana nuna ta da yatsa.

"Kin yi kaɗan, ke ban ma yarda ke ce ba, na rantse ture aka yi maki. Ni dai na shiga uku na lalace! Yanzu ɗiyartawa ma ta yi aure maƙiya da mahassada shi ne suka sako min ita a gaba? Burinsu a yi ta ƙirga maki aure? To ba zai yiwu ba! Lallai ɗaukar mataki ya zame min dole. Ina na jefa wayata?"

Daga haka ta shiga laluben waya, Hindatu ta yi shiru sai hawayen dake fita, cike da baƙin cikin jin wacce Momin ta kira, wato sabuwar aminiyarta Hajiya Tani, ta sani bai wuce batun zuwa wajen ƴan tsibbu ba don haka ta fice daga ɗakin. A kujerar falo ta zube ta hau kuka sosai, wannan ne karo na farko da ta ji kewar mahaifinta da ƴan uwanta, da ace yau tana hannunsa, tana da tabbacin abubuwa da dama ba za su faru gareta ba. Aurenta tun daga na farko har na biyu babu wanda aka nema a dangin mahaifinta, Mominta ita ta yi kiɗa da rawarta tare da wasu tsirarun ƴan uwanta maza waɗanda suke da hali irin nata na zalama da haɗamar abin duniya, da babu hakan a gabansu, ko kallonsu bai kamata su yi ba tunda Momin ba ta nemansu idan ba kasuwar buƙatarta ce ta tashi ba.

Ganin kukan ba zai mata magani ba sai ta share hawayenta, ba ta da wata aminiya sama da Haulatu, za ta yi shawara da ita don jin abin da za ta ce, sai dai ko giyar wake ta sha, ba za ta iya fitowa ta faɗamata abin da ta ji da kunnuwanta mijinta ke faɗi ba. Wayarta ta jawo ta kira ya fi sau uku sai dai duka amsar guda ce, a kashe. Haka ta gaji ta koma kiran ta Umma, ta ci sa'a kuwa ta shiga. Suka gaisa da Umma cikin mutunta juna, ita dama ta na ganin dattakon Umma, wasu lokutan har ma ta kan ji inama Mominta ke da nutsuwa irin nata, ga iya kalamai.

"Hindatu, hala ƙawarki kike nema? Wayarta ta samu matsala ne. Ba ta nan ma ta je makaranta."

Abin da Umman ta ce kenan. Da ɗan damuwa ga rawar murya ta amsa.

"Toh Umma. Don Allah idan ta zo ta kira ni."

"In sha Allahu zan faɗamata, amma ina fatan komai lafiya?"

Kafin Hindatu ta amsa ta ji an warce wayar. Da sauri ta duba, Mominta ce.

"Da uwar wa ki ke waya Hindatu? Da wanda ke zuga ki ko? Hello, waye a kan layi?"

Momi ta ƙarashe da saka wayar a kunne gami da tambaya har wani huci take fitarwa tana yi tana hararar Hindatu wacce gaba daya ta rame a ɗan tsakankanin nan.

"Hajiya Shatu, ni ce Hajiya Na'imatu. Ya gida?"

Tsaki Momi ta ja.

"Oh, Na'imatu? Sannunki toh. Ni dama na san ba banza ba yarinyarnan ta.."

"Kwace wayar Hindatu ta yi.

"Momi! Mene ne haka kike yi?! Na ce maki wani ne ya zuga ni?! A karon kaina na yanke hukuncin rabuwa da Alhaji Ibrahim don ba zan iya cigaba da zama da ɗan ƙungiyar asiri ba!"

Shaf ta mance ma ba ta katse wayar ba, ta yi wurgi da wayar gefe ta fice ta ƙyale Momin a tsaye baki sakaka. Madadin ta tsinci abin dubawa matsayinta na Uwa a kalaman ɗiyarta, sai ta ƙara shiga tsoro da firgicin wai an shiga tsakanin ƴarta da mijinta. Ta saki huci ta furzar. Ta rantse matuƙar ta ziyarci malaminta aka tabbatar da sa hannun Na'imatu sai ta kassara rayuwarta. Haka ta yi ƙwafa ta shanye ɓacin ranta ta koma ciki don rarrasarta, tunawa da ta yi da Ɗan Mutuwa wanda ya ce kar a sake a yi abinda zai jefa matarsa cikin ƙunci.

***
Katsina...

Umma kuwa turus ta yi da waya a hannunta, a daidai lokacin da muryar Hindatu ya karaɗe kunnuwanta tana tabbatarwa da Momi cewa mijinta Alhaji Ibrahim Ɗan Mutuwa ɗan kungiyar asiri ne, a sannan Umma na zaune ne a falo ita da Baba Saude suna aikin tsinkar zogale na yin dambu. Duka-duka sannan ƙarfe ɗta da mintoci na rana. Wayar ce ta sanya Umma fidda hannunta a tiren ganyen zogalen. Labarin da ta tsinta na tabbatuwar Ɗan Mutuwa ɗan kungiyar asiri daga bakin matarsa ta yanzu Hindatu, sai ya girgiza zuciyarta fiye da kalaman da Momi ta soma a farko.

"Hajiya lafiya?" Faɗin Baba Saude kenan ganin sauyin yanayi daga Umman. Murmushin yaƙe ta yi.

"Babu komai. Bari na kama ruwa na dawo."

"Toh, ai wannan ma zai isa, mun tsinke da yawa."

Umma ba ta iya amsawa ba ta haye sama kai tsaye ta shige ɗaki. A gefen gado ta zauna tana ambaton sunayen Allah, ita kuwa ta taɓa cin karo da mutum irin Ɗan Mutuwa a duniyarta? Ace duk inda hanya ta shiriya da alheri suke ba ya nufarsu? Tausayin Haulatu har ma da na Hindatun duka ya kama ta. Ga nan ɗiyarsa jininsa, da ba ta san daɗin Uba mahaifi ba balle kuma tsawatarwarsa akan mai kyau da marar kyau. Hawayen da ba ta san da su ba ta ji ɗuminsu a saman leɓɓanta sai ta share su. Ita kaɗai ta san damuwar da kalaman Hindatun suka jefa ta ciki, sai da ta yi fatan ina ma ace ba su shiga kunnuwanta ba. A ƙarshe ta tattara tunaninsa ta watsar gami da bin sa da addu'ar shiriya da kuma roƙawa Hindatu kuɓuta daga sharrinsa.

***
Ta fito tare da Radiya don tafiya gida, Safina ba ta kammala ba sai ta yi lakca na 4-5pm. Facemask ne ya taimaka wajen ɓoyuwar kumburin leɓanta don ba ta yarda ta cire shi ba sai a aji wanda ya zama dole babu yanda ta iya da wani Malami guda mai tsauri ya ce sai ta cire hakanan masu niƙaf. A dole ta cire tana rufe bakin da hannu. Suna cikin napep Radiya ta numfasa ta ce.

"Safina fa ta dage gidansu za ta koma. Har ta kammala haɗa shirginta."

Haulatu wacce ta lula tunanin Yaya Sadauki da kuma damuwar kar rashin jin ta a waya ya sanya shi tunanin ko saboda shi ne ta katse wayar, maganar Radiya ta maido ta hayyacinta.

"Uhum, rabu da ita, sai ka ce sauran jama'ar gidan ba mutane ba ne. Amma fa idan har a ɓangaren Baba Alhaji ne na yarda da shawararta, don ko ni ba zan iya jurar zama da mutum irin Anti Mabruka ba. Kuma ta ƙi yarda ta dawo wajenmu."

Murmushi Radiya ta yi.

"Ai fa, nima dai zan fi so ta koma gidansu koda ace za ta bar mu da kewa, kinga dai nan gaba kaɗan aure za ta yi, ko yaya ta ɗan ƙara jin ɗumin Mamanta kafin nan."

Jinjina kai ita ma Haulatu ta yi tana murmushin.

"Akwai abinda nake son faɗamaku yau, amma ina tsoron shaƙiyancinku."

Da zumuɗi Radiya ta kalle ta.

"Ah haba kin san ai ba komai ne muke zolayar junanmu a kai ba. Don Allah mene ne?"

Dariya Haulatu ta yi.

"Ba zan fadamaki ke kaɗai ba, duk mai son jin labari ya zo ya same ni da zarar an yi sallar Magriba."

"Ai kuwa za ki gan mu. Fatanmu dai ya kasance alheri."

Ta lumshe idanu ta na murmusawa ta amsa da in sha Allahu.

***
Sadauki tun daren da ya yi magana da Haulatu ya kasa sukuni, abin da ya ƙara jefa shi cikin damuwa bai wuce wayar da ya kira ya fi a ƙirga amma bai same ta ba. Tunaninsa har ya soma ba shi tsoro, ko don shi ta kashe wayar? Daƙyar ya iya jarumtar zuwa ofis washegari, ko tashi ba'a yi ba, karfe biyar saura ya taho gida. Madadin ya bi ta gate ɗin gidansu, sai ya zagayo ta babban gida, shi dai kawai ya sanya ta a idanuwansa.

Koda ya yi parking kai tsaye ya fito ya yi ɓangaren Hajja. Su Najeeb da ya yi karo da su suka gaishe shi da girmamawa ya gyaɗa kai yana amsawa ta hanyar motsa leɓɓa. Sam dauriya yake yi wurin ɓoye haƙiƙanin abin da ke ransa, wato damuwa.

Sallamarsa a falon Hajja ya sa Umma dubansa tana amsawa, ita kaɗai ce a falon, Hajja har a sannan ba ta dawo daga ɓangaren Baba Alhaji ba, yau hirarsu suke sha har Baba Dakta ko kuwa ace maganarsu na abinda ya shafe su matsayin ƴan uwan juna. Sallar la'asar ma can ta yi, Haulatu kuwa tun dawowarta da ta haye sama ba ta sauko ba. Da murmushi sosai a fuskar Umma ta tarbe shi.

"Bismillah, shiga ciki mana Abeed."

Ya shiga ya zauna ba musu, madadin ta je su gaisa sai ta koma ta ɗaukomasa ruwa ta dawo falon, sai da ta zauna ya gaida ta. Ta amsa da yanayin fuskarta na koyaushe, wato murmushi.

"Ya wajen su Hajiya? Ya kuma gajiyar biki?"

"Alhamdulillah Umma, su ma duk suna lafiya. Hajja ba ta nan ne? Ban ji ta ba."

"Yau Hajjah an je sada zumunci, tana can sashen Baba Alhaji."

Ya amsa da ok yana mai buɗe ruwan ya sha. Alamun gajiya har ma da yunwa da Umman ta gani tattare da shi ne ya sanya ta miƙewa, dambun da tuni ya sauka saman wuta ta zubo masa ta jera komai saman faranti ta kawo. Shi kuwa hankalinsa ya yi hanyar hawa benen, yana son tambayar Haulatu amma nauyin Umman ya sanya shi kasa yi. Ƙamshin ne ya soma bugar hancinsa, dambu ne da ya ji gyaɗa da mai ga kuma ganye, sai ko sauce ɗin hanta da aka yi aka zuba a gefe. Aikuwa tuni ya yi bismillah ya soma ci. Umma na ɗan taya shi hira nan da nan kuwa ya shiga amsawa, kan kace me ya kusa tashi da filet ɗin dambu.

Daidai lokacin Haulatu ta sauko zuwa ƙasa, tun kafin ta kai ga ƙarasawa ta hango shi, shi ɗin ma ya ɗaga cokali zai kai baki ya ganta, har wata ajiyar zuciya ya sauke, Umma ta ɗan waiga don ganin abin da ya ɗauke hankalinsa har haka, ganin ba ta ga kowa ba sai ta juyo. A lokacin ita kuwa Haulatu kunya ya sanya ta yin baya da sauri, a karshe ma duk da yunwar da take ji bai hana ta sulalewa ta koma sama ba. Ba ta kaunar ya gan ta da wannan kumburin bakin da Fahima ta wuce gidansu yau ta bar ta da shi.

Shi kuwa sai ya ƙara jin ma wani kuzari na cin abincin. Yana kammalawa ya kora da ruwa.

"Bari a ƙaro maka."

Faɗin Umma tana ƙoƙarin miƙewa da sauri ya ce.

"Umma a'a, Alhamdulillah na ƙoshi. Nagode."

Ta yi murmushi ta koma ta zauna.

Baba Saude ce ta fito daga kicin din suka gaisa sannan Umma ke fadin.

"Wai nikam ɗiyartaki ta sauko ta ci abincin? Me ta ke yi haka?"

Baba Saude ta yi dariya.

"Ai yau dai babu wayar latsawa balle in ce shi ya dauke hankalinta, ga dukkan alamu mulkin ne ya motsa. Bari na bi ta da shi."

"Aa Baba, rabu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login