Showing 156001 words to 159000 words out of 177840 words

Chapter 53 - FITAR TSIRO COMPLETE HAUSA NOVEL BY RUFAIDA UMAR

11 Jul 2024

79176

yi sallama da Malama wacce a farko kallonsa ma ba ta yarda ta yi ba. Sai da ya dinga magiya da neman gafara tare da alƙawarin daga ranar yau ba za ta ƙara jin makamancin haka a kansa ba. Ya haƙura da Haulatu, a nan ne ta iya dubansa har ramar da ya yi ta ba ta tausayi.

"Na yafemaka, Allah ya yi albarka. Ka yi ta addu'a sannan ka ji tsoron Allah gun sauke haƙƙoƙin da ya rataya a wuyanka na matarka. Allah ya tsare ya kai ka lafiya."

Har wata ajiyar zuciya ya saki na samun sa'ida. Ya jinjina kai.

"Ameen Umma, in sha Allahu na maki alƙawarin kiyayewa. Allah ya ƙaramaki lafiya."

Da haka ya miƙe ta bi shi da kallo har sai da kwalla suka cicciko mata. Addu'ar neman sauƙi da rangwame daga Allah ta ɗaga hannu ta shiga yi wa ɗan nata.

***
Garin Kano an wayi gari da saukar ruwan samu, misalin ƙarfe goma da mintoci Khaleefa ta ƙarasa shiga cikin garin da motarsa Land Cruiser baƙa wuluƙ mai gilasai masu duhu sai sheƙi take yi sakamakon wankin da ta sha, ga kuma ruwa da ya ƙara wanke ta tas.
Da kansa yake tuƙin, kai tsaye bai zarce ko'ina ba sai Bristol Hotel inda ya yi amfani da google map har ya ƙarasa. Nan Ango El-Mu'az Ƙaraye ya fito tarbarsa shi da wani abokinsa sun sha babbar riga. A lokacin ruwa ya tsaya sai dai har a sannan garin bai washe ba, ga kuma ni'imantaccen sanyi. Ya fito suka yi musabaha da raha da komai, Khaleefa ba ma'abocin yawan magana ba ne da hira, El-Mu'az ya fi shi wannan sakewar, koda kuwa bai yi niyya ba, idan an haɗu sai an sanya shi magana da darawa. Bai wani jima ba suka ɗunguma zuwa masallacin Umar Ibn Khattab inda anan ne za'a ɗaura auren. Koda aka kammala kai tsaye reception aka tafi aka yi ƙaramar liyafa sannan aka wuce gidan Amarya.

Nan ma hotuna ne aka yi ta ɗauka bayan gaisawa da iyaye. 

Sai da Khaleefa ya huta sosai a masaukin Otal ɗin har ƙarfe huɗu da kusan rabi ya buga, kiran Hajja ne ya fargar da shi tunawa da aikin da aka rataya a wuyansa.

"Ya Salam." Ya furta gami da juya akalar motar ta koma hanyar da za ta sada shi da filin jirgin na Malam Aminu Kano.

"Khaleefa, ka ɗauko ƙanwar taka?"

Ya runtse idanu.

"Afuwan Hajja, saura kaɗan na ƙarasa shiga Airport ɗin. Abu ne ya ɗan riƙe ni."

"To ba damuwa. Na maka uzuri tunda kai ne, da Mu'azu ne cewa zan yi da biyu ya yi."

Murmushi kawai ya yi sannan suka yi sallama. Can kuma ya ji shigowar saƙo, Umma ce ta turo lambar Zaitunar. Kafin ya ajiye ta kira shi.

"Ɗana, ga lambar ƙanwartaka na nan, da shi ta yi kiranmu yanzu ba jimawa."

Ya amsa da toh gami da godiya suka yi sallama. Bai gwada ko kiranta ba sai da ya ƙarasa ya nemi wuri ya yi parking. Daidai sadda ya rufe motar ne ya ji ta ɗaga wayar da sallama cikin harshenta da ya haɗu da larabci da yaren Malay ga kuma Hausa.  Sai sallamar ta fita daban da irin na cikakken Bahaushe, ta yi dadi. Ya amsa mata.

"Khaleefa Dawud ke magana, ki fito ina waje."

Ta amsa da toh, ba jimawa ba, yana tsaye yana kallon ƙofar sai ya hango tana fitowa, wani ɗan matashi yana jan trolley ɗinta.

Khaleefa daga nesa ya ƙare mata kallo tas. Riga ce ta yadin Abaya kalar ruwan ƙasa mai V shape a jikinta, tsawonta har ya zarce gwuiwa sosai, ta ɗan kama ta kaɗan daga ƙirji daga ƙasan kuwa ta buɗe, sai dogon wanda baƙi da ta sanya sai ko high heel baƙi da ke a ƙafarta. Baƙin mayafinta ƙarami sai ta zagaye fuskarta da shi. Sai ko baƙin sunglasses da ta rufe idanunta da shi. Ta sha hoda da jan bakinta da ya fiddo tsantsar kyawunta. Komai na Zaituna cike yake da burgewa ga uwa uba yarinya ce mai aji da iya gayu. Hannunta babu komai sai wayarta da ƙaramar baƙar jaka da ta riƙe.

Khaleefa ya kauda kai bayan kallon da ya ƙare mata. Ɗan bakinsa ya taɓe. Ba laifi ta iya kwalliya. Sai kuma ta ba shi haushi ganin kamar kowa a wurin kallonta ya ke yi. Har ta ƙaraso bai kalle ta ba, sai ma ya juya ya nufi motarsa ya buɗe boot, matashin ya sanya jakar a ciki bayan ya tambayi Zaituna ko shi ya zo ɗaukarta ta amsa da gyaɗa kai cike da jin babu dadi na yanda ko gaisuwarta Khaleefa bai amsa ba. Shi kuwa sallamar matashin ya yi ya tafi sannan ya buɗe motar ya shiga, da hannu ya buɗe mata gidan gaba ganin ta kai hannu za ta shiga buɗe ƙofar baya ta shiga. Sai da ya ɗauke farar babbar rigarsa da ke jikin kujerar ya maida baya sannan ta shiga ta zauna da bismillah a bakinta ta rufe ta ɗaura seatbelt. Kafin ta ƙara dubansa tana fidda gilashin ta mayar saman goshinta.

"Yaya Khaleefa, barka da yamma."

Kallonta ya yi fuskar ba yabo ba fallasa.

"Yauwa, daga yau kar ki ƙara kwalliya idan za ki biyo hanya. Babu amfanin kina mace ki yi ta abubuwan da za ki ɗauki hankulan maza."

Zaituna ranta ya sosu, nan da nan sai ga ƙwalla sun cicciko mata, Khaleefa da tuni ya maida kansa ga tuƙi yana ƙoƙarin yin ribas bai ƙara kallonta ba.

"Abu Affan, wallahi ban yi kwalliyar da wannan manufar ba. Bari na goge."

Ya nanata sunan da ta ambace sa da shi, ɗan kallonta ya yi ganin ta zuge jaka ta fiddo tissue wanda ke zuwa  a ƴar ƙaramar leda da nufin goge bakin. A sace ya kalli leɓɓan ya kauda kai.

"Ni ban ce ki goge ba. Bar kayanki."

Kallonsa ta yi sai ta sauke ajiyar zuciya ta maida tissuen cikin jaka. Katafaren wurin abinci da kayan maƙulashe na Albaik dake kan titin Kurna ya yi parking ɗin motarsa. Ta dubi gidan abincin, eh tana jin yunwa don ba ta iya cin komai a jirgi amma fa ta fi ɗokin ta gan ta a gida. Ba dai ta ce komai ba, ya ce ta jira shi sannan ya fita. Ta bi bayansa da kallo, dogo cikakken namiji, babu macen da ba za ta yi fatan Khaleefa a matsayin mijinta ba sai dai marar sa'a da rabo. Ita tunda take da shi ma ba ta wani tsayawa ƙare mishi kallo, yau ɗin ma don yana nesa da ita ne kuma babu damar da zai gan ta tunda ta waje duhu ne.

Ajiyar zuciya ta saki sannan ta ciro wayarta tana dannawa. Murmushi ta yi ganin saƙon murya daga Haulatu ta whatsapp, buɗewa ta yi ta kunna.

"Ƴar uwata kun taho kuwa? Allah ya kawo min ke lafiya, na matsu ki ƙaraso."

Ta maida mata da saƙon muryar ita ma.

"Ni kaina haka my sister, amma fa na ji ance ki na gidan Maama ai."

Koda ta amsa ganin bai shiga baki ɗaya ba ne yasa ta fahimci datar a kashe sai kawai ta sauka ita ma. Ta ɗan ci mintuna kusan biyar kafin Khaleefa ya fito hannunsa ɗauke da ledoji.

Yana shiga ya miƙa mata, karɓa ta yi gami da furta Thank you. Daga haka ya sanya seatbelt ya yi ribas ya hau titi. Ita kuwa gudun kar ya ji babu dadi ya sanya ta buɗe ledar, shinkafa ce da ta ji kayan haɗi sai kaza, ɗayar kuwa lemu ne da ruwa sai youghurt.

"Abu Affan, ba za ka ci abincin ba kai?"

Yana so ya ce mata ba ya son sunan da ta ke ambatonsa da shi, amma kuma ya kasa, haka kawai tana wani maida shi tsohon ƙarfi da yaji, eh ya haifi Affan, amma meyasa ba za ta kira shi da Yayan ba kamar yadda sauran ƙannen ke faɗi? Bai kalle ta ba a can ƙasa ya amsa.

"Alhamdulillah. Ki ci."

"Toh."

A nutse ta ke cin abincin kamar yanda shi ma ke tuƙin a nutse. Yana yi ne gudun kar ya yi takun da zai sa ta kasa cin abincin. A hankali ya ke satar kallonta, komai cikin nutsuwa ta ke yi. Ta ci sosai sannan ta rufe ta maida leda, ta yi amfani da tissue ta goge hannun wanda garin cin kazar ta ɓata, ta kora ruwa kaɗan saboda ba ta son ta fitsari ya kama ta a tsakar daji.

Jingina kai ta yi jikin kujerar a hankali kuma tun tana bin hanya da kallo bacci ya sure ta don a kwanakin sam ba ta samu ta runtsa sosai ba tsabar zumuɗi da kuma yawon shiga kasuwa siyayya.

Khaleefa jin shirun ya yi yawa ne ya sanya shi ɗan waigo kansa. Fuskarta na kallon saitinsa, bacci take yi cikin kwanciyar hankali abinta. Ta cire gilashin ta ɗora bisa cinya, ya maida kai ga kallon titi sannan ya ƙara juyowa ya dube ta. Ya maimaita hakan har bai san adadi ba, shi kansa bai san me ke ɗaukar hankalinsa ga kallon ba, amma kuma duk sadda ya dubi fuskarta yakan ji ba ya kaunar ya daina kallo. Sallar Magriba ce ta sanya shi tsayawa a wani masallacin gefen hanya cikin wani ƙauye. Jin tsayuwar motar ya sanya Zaituna farkawa, dubanta ya yi.

"Ina zuwa, zan yi sallah ne."

Ta gyaɗa kai sannan ya fice. Wurin akwai jama'a sosai, kamar ma kasuwa ce, kowa dai harkokinsa yake. Wayarta ta fiddo a jaka ganin tana ta ringing. Hajja ce. Tambayarta take ko sun ƙaraso, ta ce mata sun dai kusa kawai don ba ta ma san ina ne nan ba. Suka yi sallama bayan ta musu fatan isowa lafiya. Ba ta koma baccin ba har Khaleefa ya dawo. Sai bayan ya cigaba da tuƙin, wani baccin ya ƙara kwashe ta.

Suna isa cikin garin Katsina, nan ma ba ta farka ba har sai da ya shiga cikin gidan nasu ya tsaida motar, ya kula dagasken gaske bacci ne a kanta. Farfajiyar gidan babu kowa an tafi masallaci gabatar da sallar isha'i. Zaituna kuwa jin kamar a tsaye suke ya sanya ta farkawa bakinta ɗauke da sunan Allah. Idanuwanta cikin na Khaleefa suka faɗa, ta yi saurin miƙewa zaune tana rarraba idanu, ba ta son yin doguwar magana saboda ta san zai wahala bakinta idan ba ya ɗan tashi sakamakon bacci da ta yi don haka ta kauda kai.

"Ashe mun iso? Abu Affan ba ka tashe ni ba."

Madadin ya ba ta amsa sai kawai ya buɗe motar ya fita, ganin haka ita ma ta fito. Shi kuwa akwatin kayanta ya ciro. Har a sannan sallah ake suna ji daga masallaci ba a idar ba, zagayowa ta yi riƙe da ledojin abincin da ya siya mata da zummar karɓar akwatin, don a ganinta ba girmansa ba ne ya riƙe akwatinta. Fuska a ɗaure ya ce.

"Ki je ciki, zan taho da shi."

Ta ɗan kalle shi tana murmushin da har gefen kumatunta na lotsawa, Khaleefa ya sauke ajiyar zuciya. A zuciyarsa ya furta masha Allah.

"Nagode sosai Abu Affan."

Daga nan ta juya ta yi gaba ta bar shi da bin ta da kallo kafin ya numfasa ya rufe motar shi ma ya shiga ciki. Ya kula ma kamar da gayya take faɗin sunan da bai wani yi mishi armashi ba.

Umma da Hajja baki ya ƙi rufuwa suka tarbi Zaituna da murnarsu. Khaleefa kuwa ko zama bai yi ba bayan ya kawo akwatin ya yi musu sallama ya wuce. Zaituna sai da ta yi wanka ta sauya audugar mata dake jikinta kafin ta sauko ƙasan tana yin video call da Haulatu inda take yaba kyawun da ta ga ta yi, fadi take.

"Sis kin sauya baki daya, har wasu kumatu na ga kin yi."

Ɗan farr da idanu Haulatun ta yi mata.

"Ka ga Mrs Abeed Ridwan Malumfashi."

"Yes, ita ce."

Suka yi dariya, Zaituna cikin sauri ta maida fuskar wayar ga Umma da Hajja da ke zaune, ai tuni Haulatu katse kiran baki ɗaya. Umma murmushi kawai ta yi gami da girgiza kai. Hajja ko cewa take.

"Ja'ira, wato kam Sadaukin Alhaji ya sauya min ita ko?"

Umma ba ta amsa ba sai Zaituna dake kare ƴar uwarta.

***
Momi Nuratu ta zubawa takardar idanu tana karancewa ganin babu wani abin tashin hankali a saksmakin gwajin ya sanya ta murmushi gami da sauke ajiyar zuciya lokaci guda tana mai godiya ga Allah.

"Alhamdulillah. Na ji daɗin hakan. Ni dama ba ni da kokwanto, sai dai ka sani, tunda har Rahma ta soma haka, gwara a yi abin da zai toshe bakinta da ƙananun magana. Koda dai, nasan ko hakan ma ba a tsira ba."

Sadauki ya yi murmushi yana mai amsawa da hakane.  Ita kuwa Momi Nuratu ta saka a rai duk radda Mamain Khaleefa ta ƙara zuwa da wani batun to fa ba za ta ƙyale ta ba. Tunda ba ta san kara ba.

***
Washegari tun da wuri Zaituna na kammala shiri ta shiga ɓangaren kowa a gidan aka gaisa, kowa ya gan ta dai ya hau murna da washe haƙora. Yarinya ce mai shiga rai tun a baya, ba ta da girman kai ko kaɗan. Sai da ta yi dagaske kafin ta samu kanta a ɓangaren Momi Nuratu don ita ma gwanar son hira ce. Ɓangaren Baban Kowa nan ne ƙarshen inda ta shiga, sun gaisa, Radiya ma ta fito ta hau ihun murnar ganinta suka rungume juna. Ranar ba zata shiga makaranta ba hakan yasa Zaituna roƙon alfarmar ta yi mata rakiya gidan Maama.

***
Khaleefa ya tamke fuska sosai yana kallon Jannat da ke kwance tana wani nishi kamar mai naƙuda ya yin da Mami ke tsaye a kanta gaba daya ta ruɗe, faɗi take.

"Ka tsaya kallonta kamar ba jininka ba, matsayinka na likita ba za ka yi kokari ka auna ta a san matsalarta ba?"

Bai ko kalli Mamin ba, idanunsa a kan Jannat wacce Nos ke tsaye a kanta tana ɗan tattaɓa hannu da goshinta.

"Ku je waje Mami, bari na duba ta."

Ba musu Mamin ta fita, Nos ta bi bayanta.

"Tashi zaune ko na karairayaki." Ya faɗi murya a kausashe.

Jannat duk da irin ruɗewar da ta yi, sai da ta daure gudun kar a gano ƙarya take yi, ta ƙara wani juyi da riƙe kai.

"Wash!"

"Za ki tashi ko sai na wanka maki mari?"

Ai bai kai ga ƙarasa zancen ba ta yi zumbur ta miƙe zaune tana ƙunƙuni.

"Don ba ki da mutunci akan ɗa namiji ki ke tayarwa da tsohuwarmu hankali? Toh na rantse maki matuƙar ba ki bar waɗannan shirme da shiriritar ba sai kin koma gidana da zama na maki hukuncin da ba ki taɓa zato ba. Banza kawai da ba ta san ciwon kanta ba. Ni na sani babu uwar abin da ke damunki, tsabar kin raina mutane ne ki ke wannan ƙananan iskance-iskancen. Daga yau kika ƙara bari na ganki a asibitin nan saboda mutumin da ba ya ta taki sai na maki allurar mutuwa kowa ya huta."

Ai fa nan ta hau rarraba idanu, hawayen suka wanke fuskar. Dagaske yake babu ciwon komai tattare da ita, ta yi ne don Mamin ta gane ba za ta iya rayuwa babu Sadauki ba. Hakanan Abbanta wanda sam ya ƙi goyamata baya.

Ganin hawayen sai kuma ya ɗan ji tausayinta, zama ya yi a gefe ya shiga yi mata nasiha da nuna mata illar auren wanda ba ya sonka. Jikinta ya yi sanyi, har wani ɗaci ɗaci take ji a maƙogwaronta, dagaske dai ta rasa Sadauki?

"Yaya, Allah ya ban wanda ya fi Yaya Sadauki." Ta na kaiwa nan ta fashe da kuka sosai, ya ɗan rungume kafaɗarta yana rarrashinta. Son maso wani ciwo ne babba, ta kuma ji har a ranta ta haƙura da shi ɗin. Khaleefa ya fi kowa a gidan kusanci da Sadauki, tunda har ya rantse mata akan cewa Sadauki ba zai aure ta ba, ta ji ta yarda kuma za ta haƙura da shi. Amma fa ko bikin ba za ta iya zuwa ba ko don su Fa'iza da za su yi mata dariya. Har abada kuma ba ta ga zumuncin da za ta yi da Haulatu ba, a cewarta.

Ya dai cewa Mami ciwon kai ne kawai sai damuwa, ya rubuta magunguna suka fito tare tana lallaɓa ɗiyarta har tana mata raɗa a kunne kan cewa kar ta wani damu, ta san idan an yi gwajin nan Momi Nuratu ba za ta amince ɗanta ya auri Haulatu ba don tana ji a jikinta yarinyar na da cutar ƙanjamau. Ita dai Jannat ba ta ce uffan ba, ba za ta ƙara biyewa Mamin ta dinga kwaɗaita mata abin da har abada ya fi ƙarfinta ba don haka ta yi gaba zuwa mota ta bar Mami tare da Khaleefa.

***
Zaituna sakin baki ta yi bayan sun gama murna da farin cikin ganin juna da Haulatu, ta yi wani kyau, fatar nan sai sheƙi take yi, ga wani ƙamshi dake tashi a jikinta duk inda ta gifta koda kuwa ba ta shafa turare ba. Ko'ina ya ƙara cika dam dam. Duban Maama ta yi murya a shagwaɓe ta ce.

"Ni ma Maama ke zan sa ki kira a yi min gyaran jiki idan aurena ya zo."

Maama ta yi dariya, idan da sabo ya ci ta saba da rashin ta idon Zaituna, sam ba ta mata kallon uwa sai wata abokiyar kuka da dariya.

"Magana ta ƙare ƴata, yanda ki ka ce haka za'a yi. Amma har yanzu dai gafara Sa ake, ban ga ƙaho ba."

Murmushi Zaituna ta yi don dagaske yanzu ba wani da take kulawa, Zaid din ma da ƙarfin addu'a ta cire shi a ranta ta haƙura.

"A taya mu addu'a Maama."

Maama ta jinjina kai.

"Sosai muke yi sai dai mu ƙara. Su ma ƙawayen nata ba don abin ya zo gab da gab ba, ai babu abin da zai sa a ƙi haɗe bukukuwan wuri guda."

Radiya ta sunkuyar da kai tana murmushi, Haulatu ta ɗan bugi kafaɗarta tana mata raɗa, aikuwa ta kai mata duka a kafaɗa suka yi dariya. Zaituna ta harare su.

"Munafukai, ni Maama ai dama an sani an haɗa, na kula son auren suke yi. Safinar ma kusan kullum whatsapp status dinta kalamai da waƙoƙin soyayya ne."

"Laaah." Haulatu da Radiya suka firta a tare

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login