Showing 177001 words to 177840 words out of 177840 words
uwanta na ɓangaren mahaifinta ta aura. Haulatu ta ji dadin ganinta. Haka suka ƙulle a ɗaka da daddare ta ba ta kayayyaki masu kyau na musamman na ƴan Sokoto wanda take siyarwa da sunan shi ne tsarabarta. Har zuwa sannan Allah bai kawo wa Hindatu haihuwa ba sai ɓari da take yawan yi. Abin na damunta matuka, yanzun ma da ta ga jaririyar Haulatu sai ta kara kwaɗaituwa da son ganin na kanta. Ganin gaba ɗaya ta sauya ya sa Haulatu fahimtar inda zancen ya kwana don haka ta riko hannunta.
"Haba ƙawata, ki yi hakuri da abin da baki samu ba ki roƙi Allah mai bayarwa ya ba ki. Addu'a babu kaddarar da ba ta sauyawa. Don Allah bana son yanayin nishadin nan da muke ciki ya koma na kuka. Ko Mujahid ya soma ƙosawa da ke ne? Duka-duka shekarunku biyu da aure fa."
Hindatu ta girgiza kai.
"Ke babu ɗaya wallahi, shi tarairaiyata ma yake yi koyaushe. Ni ce dai, tun bayan rasuwar Momi nake son na ga na haifi wanda zai ƙara ɗebemin kewa. Har gobe yanayin da ta rasu ya kasa goguwa a kwakwalwata."
Jinjina kai Haulatu ta yi, tabbas hakane. Momin Hindatu ta yi wata irin mutuwa mai ban tsoro, a hanyarta na dawowa daga wurin Bokanta, ta karɓo magunguna da layu, haka motar ta faɗa rami suka fito babu rai. Bidiyonta ma da ƙunshin kayan har ma da wani rubutu jikin takarda da aka saka jikin wani ƙoƙon ƙwarangwal cewa 'Ni Shatu na raba Hindatu da Bashiru babanta har abada' sai da aka dauka. Zagi da cin mutunci babu irin wanda Momin ba ta sha ba da kuma la'ana. Hindatu hauka ne kawai ba ta yi ba, dakyar aka samu da roƙon Allah ta manta da kalar mutuwar mahaifiyarta ta kuma rungumi kaddararta da hannu bibbiyu.
"Allah ya ji ƙan Momi, ya gafarta mata." Faɗin Haulatu kenan. Ta amsa da amin a hankali.
***
Bayan cikar sati biyu aka tattara Haulatu aka mayar ɗakinta. Kowa ya kalli Sadauki a lokacin ya san yana cikin farin ciki. Jannat har da ita a ƴan rakiya don dama ta shiga gidan a ranar, ƙasa-ƙasa ta cewa Haulatu.
"Kinsan ki bi sannu, kin fi kowa sanin akwai sauran rina a kaba, kar ki biyewa wannan Yayan namu ki jangwalo jangwam."
Suka kwashe da dariya ita da Haulatun. Haka aka tattara aka bar ta daga ita dai Angon nata. Dole dai ya maida zalamarsa tunda ya sani ba ta samu tsarki ba.
"Dama kin sani, na ji ɗuminki ma a jikina ya fiye min komai. Da gangan kika biyewa su Mama aka wahalar da bawan Allah."
Tana wasa da sumar kansa ta amsa.
"Ka yi hakuri ka ji? Ka san duk yanayin da za ka tsinci kanka ciki, na fi ka azabtuwa. Daɗi ko rashin daɗi. Nima ba da son raina na nisanta da kai ba."
Jin haka ya ɗago kai ya shiga aikamata da saƙonni na musamman a duk birnin da fita a hayyaci ya lula shi.
***
Umma ta kai duba ga Haulatu da suke zaune tare da Jannat tana suna cin abinci a faranti guda. Murmushi take yi dake fitowa har zuci, a yau Haulatun ta kawomata ziyara ne da kuma maido Hasina ƴar aikin Umman wacce suke tafiya makaranta tare ta bata ajiyar Aidha idan za su shiga jarrabawa don suna shekararsu ta ƙarshe.
"Albishirinku?" Gaba ɗaya suka ɗago kai suna kallon Umma, lokacin sun ma kammala cin abinci sai ruwa da ke gabansu.
"Goro fari ƙal Ummanmu." Cewar Jannat.
"Toh in sha Allahu gobe Maminku za ta dawo gidannan, yau aka maida aurensu da..."
Ai ba ta kai ga rufe baki ba suka taso da murna aka rungumeta. Jannat ta shiga hawaye tana yiwa Umma godiya.
"Lallai Umma kin yi mana kyakkyawan albishir. Allah ya nunamana goben. Um, su Abba ashe shiyasa na ga yana ta fara'a yau." Jin abin da Haulatu ta ce ya sa Umma yi mata daƙuwa, ita kuwa suka sa dariya tare da Jannat. Mikewa Jannat ta yi don wanke hannu, ita ko Haulatu kasancewar da cokali ta ci sai ta ƙara gyara zama a kusa da Ummanta. Kwantar da kai ta yi saman kafaɗarta tana murmushi da hawaye lokaci guda.
"Umma, nagodewa Allah da ya sa komai ke sauyawa. Umma kamar ba Haulatunki ba mai kafiya da rashin tauna magana ba. Kinga komai namu ya sauya."
Umma ta ɗago ta, suka dubi juna da murmushi.
"Allah kenan Haulatu, ai duk abin da bawa zai roƙi Allah toh fa kada ya yi shakku akan tabbatuwarsa. Babu wani abu da yake dauwama a duniyar nan musamman idan ka yi haƙuri. Sadda zai wuce ya zama tarihi sai ka godewa Allah don babu mamaki a lamarinsa. Mu godewa Allah mu kara godewa."
Haulatu ya share hawayenta tana murmushi ta ce.
"Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulilla."
***
*Nima marubuciyarku mai ƙaunarku nace Alhamdulillahi da a yau na kawomuku ƙarshen littafina na Fitar Tsiro. Ina roƙon Allah ya sa mu amfana da darussan ciki, inda na kuskuro, ina neman a yi hakuri a kuma yi uzuri a gareni. Nagode, sai mun haɗu a littafina na gaba in sha Allahu.*
*Rufaida Umar.*