Showing 123001 words to 126000 words out of 177840 words
ji ba. Sai da ya ƙara maimaitawa har Umma ta karya bille ta yi magana.
"Hajja, yana gaidaki."
"Uhum, naji ina amsawa. Ko ba Zaidu ba ne? Mai ƙyamatar haɗa zuri'a da tsatsona?"
Umma ta sauke numfashi, kai, ita kam Hajja ba ta bari abu ya wuce ta yi ta dawo da shi baya kenan dama ta ce ba su hadu da Zaid ba tun faruwar lamarin, burinta su hadu ta yi mishi tas, a zaton Umma ai shikenan tunda an yiwa lamarin tufka, ashe dai akwia sauran rina a kaba. Shi kuwa Zaid ko a jikinsa sai murmushi da ya ɗan yi.
"Ki yi hakuri Hajja, ki yafemin bisa wannan furuci. Amma har ga Allah nake kaunar Haulatu. Ki taimaka ki yafemin abin da na yi a baya."
Wani irin guɗa Hajja ta yi kafin ta yi wani shewa da ya yi sanadin fitowar su Baba Saude daga zagayen da suke aiki, su a zatonsu ma ko wani abun ne na alheri ya samu. Ita ma Fahima da gudu har tana tsallake bene bibbiyu ta sauko tana fadin
"Hajja mene.."
Ba ta ƙarasa ba ganin Zaid a gefe zaune, ta gaishe shi amma ko kallonta bai yi ba. A shirye yake da dukkan wani abu da Hajja za ta yi mishi ko kuma tace muddin dai kwalliya za ta biya kuɗin sabulu. Ai buƙatar ma je hajji sallah. Komai mai sauƙi ne idan haƙansa ya cimma ruwa. Umma dai shiru ta yi tana salati a ƙasan ranta, idan Hajja na wani abun kawai Haulatunta take haskowa a fuskarta, shakka babu a jininsu yake. Rashin barin ta kwana da halin ramuwa. Wasu lokutan tijarar iri guda ce.
"Zaidu! Yau kai da bakinka ka ke cemin kana son tsatsona? Ah lallai! Kun ga ikon Allah ko? Ai ni dama na sani duk wannan cika baki da cin alwashin da ka ke, wai kai uban masu zuciya duk na banza ne. Kuma ka sani in sha Allahu soyayyar Haulatu yanzu ka fara, ita ɗin ce haramiyarka har abada. Kai muddin ma ina raye ko bayan raina ban yafe ba wani ya amince ka auri jikata. Alhakin Zaituna ne ka fara gani, wannan kaɗan ma kenan!"
Hajja ta ƙarashe tana mai sakin huci don ji take yi kamar ta kama Zaidu ta jibga son ranta, Khaleefa daya shigo ko sallamarsa ba wanda ya iya amsawa don hankalinsu na ga Hajja musamman Umma da ke kokarin ganin ta bar zancen. Ya tsinci duk abin da Hajjar ta ce, ya maida duba ga Zaid da ke gefe zaune kansa a ƙasa, ga dukkan alamu ko kalaman Hajjar ne suka sanyaya jikinsa. Ya ƙarasa ya zauna gefensa a saman kujerar yana gaida Hajja, ta amsa fuskarta ba wata fara'ar a zo a gani dalilin Zaid. Umma kuwa faran-faran ta amsa mishi tana tambayar Hafsat. Daga haka suka yi musabaha da Zaid da jikinsa duk ya yi laushi. Zaid bai haƙura ba ya ƙara duban Hajja.
"Hajja ki yi haƙuri, ki saka a rai ita ma Zaitunar Allah bai ƙaddaro sai na aure.."
"Uwarka Zaidu! Nace uwarka! Tashi ka bar min falo tun ban saɓa kamanninka ba!"
Da wannan Hajja ta hau sababi, ta inda ta ke shiga ba ta nan take fita ba, Khaleefa ya lallaɓa Zaid wanda tsabar gardama ya ƙi tashi sai faman ban haƙuri yake yi idanunsa har sun kaɗa saboda damuwa ga wani uban ciwon kai. Ya fa shiryawa duk wani cin fuska da zagi daga Hajja, shi dai fatansa ya cimma kyakkyawar manufarsa na auren Haulatu. Bayan sun fito waje shi da Khaleefa, ya dube shi da fuskar tausasawa da rarrashi.
"Cool down mana, kana ta tayar da jijiyoyin wuya kamar ba ka san ƙaddara ba? Idan fa yarinyar nan Allah ya nufa matarka ce, ko babu son rai na Hajja sai ka ga komai ya tafi daidai. Ni kam da za ka ji shawarata, da ka haƙura ka fawwalawa Ubangiji komai. Wannan hayaniyar duka ba shi zai sa ka samu cikar burinka ba. Matsayina na likita, ina ba ka shawarar ka ragewa kanka damuwa, babu abin da hakan zai haifar maka sai ciwo."
Zaid ya sauke ajiyar zuciya yana kallon Khaleefa da koɗaɗɗun idanunsa.
"Hajja ta kasa gane cewa ina son Haulatu. Na san na aikata mata laifi a baya, amma kuma hakan ba shi za ta riƙa a matsayin makamin da za ta azabtar da ni ba a yau. Ban san haka Zaituna ke ji ba sai da ya faru a kaina. Ban san ta hanyar da zan gwadawa duniya irin soyayyar da nake yiwa Haulatu ba. Na yi nadama, mene ne dalilin da ya sa ba za'a yi min uzuri ba?"
Ya ƙarashe kamar ya yi kuka yana duban Khaleefa wanda ke kallo da sauraronsa kawai. Ɗan murmushi ya yi yana mai ɗan buga kafaɗar Zaid.
"Ka nutsu, ka nemi biyan buƙata a wurin Allah. Let me tell you something, no matter how you love her, muddin ba ta sonka, zamanku ba zai taɓa daɗi ba. Ka kai zuciya nesa ka kuma koyi haƙuri. Ka rage zafafa al'amarin a ranka."
Zaid zai yi magana suka hango Sadauki tafe da Mu'az don haka ya yi shiru gami da tamke fuska. Ganinsa ya sa Sadaukin shi na ɗan sauyawa kaɗan. Dama Khaleefan da ya hango ne ya sanya ya ƙaraso. Mu'az kusan ma ba shi da matsala sosai da Khaleefa a yanzu tun sanadin Umma da ta yi musu nasiha sukan gaisa kuma sun bar jin wani abu a zuƙata game da junan, zumuncin ya daidaita ba kamar a baya ba. Bayan an yi musabaha da juna, Zaid na jin kishin Mu'az ya miƙa hannun aka gaisa, shi ma Sadaukin ba su wani sakewa juna ba gaisuwar dai kamar dole.
"Bari na wuce ni. Sai mun yi waya ko?"
Ya ce yana duban Khaleefa, shi ma ya maida hankali ga Zaid ɗin.
"Ok toh, please take care."
Ya yi ɗan murmushi ya fice zuwa wurin Baba Alhaji da Baba Dakta, don dama shigowarsa kenan bai je ko'ina ba ya fara isa ga Hajja. Mu'az shi ma ciki ya shige wurin Hajja. Aka bar Sadauki da Khaleefa na tattaunawa dangane da hidimar da suka shirya yi na auren Maama da Alhaji Nura Kankiya da zai turo a yi maganar aure a satin da za su shiga. Najeeb da Haidar sun nuna sam ba su son Maama ta yi aure yayinda Mubarak autanta ko a jikinsa. Haka suka tsaida kiransu su yi musu faɗa da nasiha. Maama dai ta ƙi a yi komai amma sun shirya haɗa mata walima koda kuwa a farfajiyar gidan ne. Maama ta yi musu komai a cewarsu, don haka farin cikinta nasu ne. Babu wanda ya yiwa ɗan uwansa batun Haulatu balle kuma na Zaid da Mu'az. Haka suke, idan suka haɗu, harkokin gabansu kawai suke gudanarwa.
***
Haulatu kuwa ba su ne suka dawo ba sai magriba don har gidan Haj Hadiza suka je, ta karɓe su kamar babu komai a ranta, can suka tarar da Ihsan sai cin magani ta ke yi, wai a gidan take aikin layyarta saboda miji ya yi tafiya. Hatta zancen hatsaniyar da samarin ke yi kan Haulatun sai da Ihsan ta gwaɓa mata magana. Wai ko dai tana zagayawa wurin na soro? Ita kuwa ba ta ji shakkar buɗe baki ta gwaɓa mata magana ba a gaban Haj Hadiza. Don kai tsaye ta amsa da cewa ai ita farin jinin a jininsu yake, koda ba boka ba malam a na bin su, idan ko za ta haɗa da tsibbun abun zai fi haka. Madadin Haj Hadiza ta ji zafinta, sai ta yi yaƙe ta nuna ai Ihsan wasa take, ita kuwa Ihsan ta cika ta yi fam. Kaifin idanun Haj Hadizar ce ya hana ta tankawa. Domin da idanu ta dinga mata nuni ta yi shiru kawai.
***
KANO...
Hindatu ta yi tsaye cak tana duban Mominta wacce ta zube uban layu da magunguna a saman kafet din ɗakinta. Cikin sanyin jiki ta ke fadin
"Wai Momi, wadannan tarkacen duka na mene ne?"
Momi ta watsa mata harara.
"Yanzu ke don ba ki da mutunci, na wuni babu ci babu sha ina tsallake kogi da hawa duwatsu don nemo maki abin da zai fissheki a gidan nan, shi ne za ki kira faɗi tashina da tarkace? Toh bari na fadamaki, muddin ki na wannan gidan sai kin miƙe tsaye don ba hakanan za ki baje ki zauna ba. Kin wani bari makwafta sun saba yi maki zarya da wasu garɗa-garɗan ƴanmata ko? Toh wallahi duk wacce cikinsu ta samu damar aure mijin nan naki ba bari za ta yi ki runtsa ba. Bare ma a na ganinki ke ɗaya mun yi nasara waccan ma mun kore ta ta fice, ai dole ki tara mahassada."
Ajiyar zuciya Hindatu ta sauke ta girgiza kai.
"Ni fa Momi yanzu duka ba wannan ne a gabana ba, Momi na kula fa Ibrahim ba ya sallah."
Momin ta ɗaure fuska.
"Ta ya ya ki ka san ba ya sallah?"
Da mamaki dauke a fuskar Hindatun ta amsa har tana wata dariya kadan.
"Momi, ya aka yi na sani? Muna rayuwa a gida ɗaya?"
"To na ji ya isa haka nan, ai ba ke zai yiwa sallar ba. Ni ba na son shaidar zurr."
"Momi wai..."
"Kin ga bar min maganar nan. Ba na son jin komai. Ni dai yanzu ki nutsu kowanne a nan akwai aikinsa. Ki buɗe kunnuwa ki saurare ni."
Nan ta shiga rattaba mata bayani yayin da ita Hindatu gaba ɗaya ma hankalinta ba ya kai, idanunta gaba daya sun cicciko da kwalla sanadiyyar wannan babbar matsalar da ta yiwa Momin ƙorafi a kai amma ta nuna ba shi ne a gabanta ba. Haka tana gani Momin ta tattara ta ɓoye su a dirowa har da cewa za ta yi mata saƙon murya ta whatsapp don ta kula za ta iya mance wasu a bayanan tunda a cewarta suna da yawa.
***
KATSINA...
Shirin tafiya makaranta ya kankama a wajen Haulatu da su Radiya. Safina ma ta dawo yayinda Fahima ta tattara ta koma gidansu cike da haushin sabon zumuncin da ta ga ya ƙullu tsakanin Sadauki da Haulatu.
Har zama suke yi su dinga gwada magana da yanayin tafiya su ƴan jami'a su yi ta dariya. Sati ɗaya da sallah aka zo aka yi zancen auren Maama, aka tsaida sati na zagayowa za'a ɗaura aure tunda ba wani taro za'a yi ba ma aure ne na biyu. Matansa biyu, Maama za ta je a ta uku.
Ranar da aka yi wannan kawo kudin, haka su Haulatu suka cika falon Innar su Maama da guɗa da kuma murna. Ko ƙeyar su Najeeb yaranta babu a wurin, Anti Mabruka kuwa tun safe ta fice a gidan. Maama ita dariya ma suke ba ta ganin sun maishe ta tamkar wata kakarsu don haka ta miƙe ta bar su da shirirtar yanka cake, Safina da guntun cake a hannunta ta shiga bin Haulatu a guje wai sai ta rama ta shafe mata a fuska, ita kuwa ta sa gudu tana dariya har ta na bangazar kafaɗar Jannat ba tare da ta kula ba, garin ta juyo ta ba da haƙuri ba ta ankara da mai shigowa ba ta ji ta yi karo da ƙirjin mutum. Ƙamshin turarensa ne ya sanya ta gane waye, garin ta ja baya da sauri ta kusa zubewa ai ko ya yi saurin taro ta ta hanyar riƙo hannunta ta tsaya sosai kan ƙafafunta da ya yi sanadin haɗuwar ƙwayoyin idanunsu. Ya bi ta da kallo har zuwa leɓɓanta kafin ya kauda kai da sauri ya kuma sake ta. Ita ma duk ta diririce, ɗakin tuni ya yi tsit an cire sauti an shiga gaida Yaya Sadauki. Ya maida hannuwa cikin aljihun wando ya na mai gyaɗa kai sannan ya ƙara duban Haulatu.
"Maama fa?" Ta ɗago kai ta kalle shi a kunyace tana mai nuna masa hanyar bene ta amsa.
"Ta hau sama."
Ga mamakinta wani murmushi ya sakar mata kafin ya juya ya nufi saman. Jannat kamar ta yi hauka, idanunta suka cicciko da hawaye. Wannan wane irin cin fuska ne? A gaban su Fa'iza (ɗiyar Aishatu mai aure a Kano, ƙanwar Barr Dawud mahaifin Khaleeefa) da take yiwa tutiya ita Sadauki na ta ne aka yi mata wannan wulakancin? Ta bi Haulatu da kallo wacce su Safina ke yiwa raɗa tana kai musu bugu. Ba zato ta ji hannun Fa'iza a kafaɗarta.
"Ah, paradise, ya haka? Me nake shirin gani ne? Yaya Sadauki naki ne ko na Haulatu ƴar bariki?"
Kalaman Fa'iza suka ƙara sanyawa ta harzuƙa sosai. Ta bangaje hannunta daga saman kafaɗarta ta na harararta.
"Aikin banza, ai gwara ni sau dubu an san ma ina son, ke kuwa da ke hauka akan Yaya Khaleefa a banza ki ke yi. Nonsense kawai!"
Daga haka ta kama hanyar ficewa, Fa'iza ta saka shewa ta na ba da umarnin a ware kiɗa. Ai kuwa Nusaiba da ke a lungu da ba ta san me suke ba dama da wayarta aka jona home theatres din dake falon, ta kunna kiɗan aka hau rawa, Haulatu kuwa sai ta ja gefe ɗaya ta zauna don kunyar buge Yaya Sadauki da ta yi take ji. Ba ta kaunar ya sauko ya ƙara ganinta tana tsalle-tsalle. Koda ya sauko kuwa bai ma yi kokarin hana su budurinsu ba sai ya sanya kai ya fice, daga yanayin fuskarsa shi ma yau ɗin cike yake da annashuwa.
***
Mamin Khaleefa da Momin Mu'az ne zaune a gaban wata bokanya ko a kira ta da ƴar bori. Ta sha adon ɗigo ɗigo a fuskarta tana zaune saman buzu da baƙaƙen kaya tana muzurai da idanu.
Momin Mu'az ce ta soma magana ganin Bokanyar ta zuba musu idanu ta kuma baza kunnuwa don jin me ke tafe da su.
"Ɗana wasu matsiyatan Uwa da ɗiya ƙadangarun bariki suka matsawa. Sun mallake shi sun hana shi sakat har yana tsallake maganata akan yarinyar. Taimakonki nake nema ki raba ta da ɗana."
Bokanya ta yi wata dariya ta bubbuga wata bulala mai gashi irin wanda yarbawa kan riƙe a hannu kafin ta soma wasu siddabarun maganganu ta yi tsit, su dai sun zuba mata idanu kafin can ta soma magana murya a ɗage.
"Ke Hajiyayye Lubabatu!"
Da mamaki Momin Mu'az ta dubi Mamin Khaleefa don su kam ba su sanar da ita sunayensu ba. Nan suka ƙara jin ƙwarin gwuiwa a kanta.
"Ki sa ranki a inuwa, zan raba ta da ɗanki rabuwa ta har abada, zai tsane ta, tsana mai tsananin gaske. Amma fa sai kin yi dagaske wajen ba da makaman aiki sosai, idan ko ba haka ba sai sun yi aure sun hayayyafa ma."
A farko albishirinta ya yiwa Momin Mu'az dadi, bayanan ƙarshe kuwa duk sai ta rikice farat ɗaya. Faɗi take.
"Mene ne makaman aikin? Na rantse maki ko mene ne shi zan aikata matuƙar Haulatu za ta fita hanyar ɗana Mu'az. A shirye nake na aikata komai."
Dariyar dai Bokanya ta ƙara yi.
"Ke ba ki san mene ne makaman aiki ba? Toh ga su nan."
Ta fiddo wata rafar ƴan goma goma ta ajiye a gabansu, Momin Mu'az ta ƙara duban Mamin Khaleefa karo na biyu suka yi murmushi, har wata ajiyar zuciya ta sauke.
"Af, wannan ai mai sauƙi ne. Dama ba mu tako mun zo ba sai da muka shirya, har alƙawarin ƙari nayi maki matuƙar hakan ya tabbata."
Daga haka ta buɗe jaka ta fiddo rafar ƴan ɗari biyar ta ajiye mata. Bokanya ta jinjina kai tana kallon rafar da aka ajiye mata tana ɗan washe haƙoranta da suka rine.
"Ki sa a ranki kamar an yi an gama kenan!"
Nan zuƙatansu suka cike da walwala. Mamin Khaleefa ita ma ta shigar da nata buƙatar akan Sadauki da ta ke son ya auri ɗiyarta Jannat. Bokanya ta gama buge bugenta da kiraye-kirayen wasu irin sunaye kafin ta tamke fuska.
"Sai kin yi dagaske don yaron ma aljanu ne da shi, zai wahala ya yi aure a duniya. Idan kuwa ma auren zai yi, toh ban hango masa auron kowa ba sai ita ɗiyar taki. Ke ma aikinki babba ne don sai na mishi turen nawa aljanun sun yi yaƙi da nasa. Wani satin sai ki dawo ku karɓi turare da garin magani wanda za ku tabbatar kun sanya masa a abinci ya ci, turaren kuwa ita ƴar taki za ta dinga shafewa a jikinta duk sadda za ta haɗu da shi. Muddin ya shaƙi ƙamshin a kofofin hancinsa ina mai tabbatar maku ya gama yawo!"
Cike da tsantsar farin ciki da jin dadi ita ma Mamin Khaleefa ta ajiye Bokanya kuɗaɗe masu tsoka kafin su tashi su tafi da zummar wani satin su dawo zuƙatansu fari tas.
Fitowarsu ne suka yi kiciɓus da Mabruka dake shirin shiga, sai aka tsaya kallon kallo, mamaki da firgici duka dauke a fuskokinsu.
"Mabruka? Me ya kawo ki nan?" Faɗin Mamin Khaleefa gaba ɗayanta a hargitse. Mabruka sai tambayar ma ta ba ta dariya ta yi murmushi.
"Hajiyar Khaleefa, ai abin da ya kawo ku shi ya kawo ni. Kya ce me ya kawo ni? Duk wanda ya zo nan ai ya san ba alheri ke tafe da shi ba face buƙatar son rai. Don haka idan ma ku na son kanku da lafiya tun wuri ku ja bakinku ku gimtse a kan ganin da ku ka yi min, idan kunne ya ji..."
Iyakar abin da ta ce kenan har da ɗan riƙe kunnenta alamar kashedi. Wurin malamin da take zuwa sam ba ta yarda da aikinsa na ci ba, dalili kenan da ta zo wurin Bokanyar nan ta hanyar wata ƙawarta. Ta wuce ta bar su da kallon juna. Sai da suka ɗan bar wurin jama'a kafin Momin Mu'az ya tanka.
"Ke ma dai, Mabruka ina ne ba za ki ganta ba tunda ta rasa miji kuma ga maƙiyiyarta za ta yi aure? Ai sai inda ta shiga ta fita. Tunda dai an riga an gamu, to babu wani abu da zai faru. Sai mu ja bakinmu mu yi shiru."
Mamin Khaleefa ta ɗan riƙe haɓa.
"Ah, dama wa zai ce wani abu? Kare ne ya cije mu?"
Suka yi ƴar dariya.
Ita ma Mabruka, albishir kala-kala ta samu daga wurin Bokanya akan za'a fasa auren da Maama a daura da ita