Showing 24001 words to 27000 words out of 157517 words
faɗin “It's now the game will be started.”
Murmushi ya yi yana faɗin
“Alhamdulillah, na ji daɗin bayyanar gaskiya, Allah ya tsare gaba.”
“Sai dai Sadauki akwai wani hukunci da na yanke game da hakan, Dole za ka auri Mabruka in ba Haka ba ba zamu taɓa gano miyagun cikin familyn nan ba.”
“What? Alhaji Baba aure fa ka ce?”
“Eh Sadauki, aure dai na ce, auren Mabruka dai ƴar'uwarka, ko da Haka ba ta faru tsananin ku ba a tunani na in nace ka aure ta zaka yi babu jayayya but now da aka kawo wannan batun ko cikin family none of your brothers will marry her get my point Sadauki. Yanzu ba mu da wani evidence da za mu wanke ta da Kai kanka idon mutane, but I'm hoping that we'll get one soon.” ya ƙarasa a raunane.
His heart is beating faster to extent that yana ji kamar zata fasa chest ɗinsa ne ta for. He's speechless and soft, ko da was baya jin cewa zai iya ƙetare umarnin Alhaji Baba ba coz he's his everything, he's more than a Granny but someone qualified to be called a Father.
Abu na gaba kuma shi ne matsawar ya amince da wannan haɗin zai cutar da rayuwarsa da Kuma ta baiwar Allahr da Bata ji ba Bata gani ba, sannan shi a tsarin rayuwarsa ma babu saki bare ya ce in gaskiya ta bayyana zai sallame ta, hakan zai Zama babban cin fuska ga Hajiya Babba wacce ta ɗauke sa tamkar ɗanta Khalil.
Nooo ba zai ƙi amincewa da umarnin Alhaji Baba ba ko Dan samarwa Mabruka ƴancin ta Amma ya ɗau alwashi in ya binciko ko uban waye ke da sa hannu sai ya ɗanɗani kwatankwacin ɗacin da ya ji.
“Ka Yi shiru Sadauki, ya ka gani?”
Da ƙyar ya furta “Babu komai Allah yasa hakan shi ne mafi alkairi”
Murmushinsa irin na manyan mutane yayi sannan ya ce
“Allah yayi maka albarka Sadauki, Allah ya baka iyalan da za su Yi maka biyayya kamar yadda kake Yi Mana.”
Can ƙasan maƙoshi ya amsa da
“Amin”
Shiru ɗakin kamar babu kowa tsawon wasu daƙiƙu, cike da ƙarfin Hali tare da son ɓoye damuwarsa ya ce
“Alhaji about that girl ...ehm your granddaughter.” daga haka yayi shiru. Alhaji Baba yayi murmushi sannan yayi gyaran murya.
“Tun dawowar ta nake famar nemanka ba na samunka and it's about her issue....dama Ina son ka taimaka min ne after telling you how it happened.”
Nan ya bashi full labarin Madina tun tana a tare da su zuwa ɓacewarta.
Ransa ɓace ya ce
“Why Alhaji? Why ba za a ɗau mataki kan wannan mugun mutumin da ya cutar da Momy Madina ba? Wallahi sai ya San ya taɓo jinin Abatcha. Wallahi ba Dan ƙyale shi ba Kuma sai ya fito da ita ko ma Ina ya Kai ta!.”
“Halinku ɗaya da Mahaifinka, zafin nama da ɗaukar zafi, wannan ba maslaha bace, mu fara Nemo ta kafin mu koma Kansa.”
Wata zazzafar iska ya fesar.
“Ka je kun gaisa da mutanen gidan ne?”
Kamar ya tsala ihu ya ce
“Sai da safe tukun”
Nan fa Alhaji Baba ya fara mass faɗa Wai meyasa ba zai shiga ya gaida Mahaifiyarsa ba ko da ba zai duba kowa ba?
“Bana son irin Haka Sadauki, ba irin rainon da Rukayya tayi maka ba, yanzu ba sai gobe ba ka tabbatar ka shiga wurin Sughrah ka Kuma Bata haƙuri ka ji ko?”
Kai ya gyaɗa kamar zai Yi kuka ya ce
“To”
“Mu kwana Lafiya ni zan kwanta.”
“Allah ya Bamu alkairi”
Daga Haka ya fice zuciyarsa na ƙuna. Ba tare da ya je ɓangaren Mommah ba ya Wuce bedroom ɗinsa da ke part ɗin Hajiya Babba, ba Wai ya ƙi bin umarnin Alhaji Baba ba ne, sai dai baya son a Yi ba daidai ba musamman da yake sama, ya Kuma riga ya San halin birkitacciyar Mahaifiyarsa shiyasa kawai ya zaɓi ya huta Idan ya so da safe ya shiga.
Yana shiga yayi wanka sannan ya ɗauro alwala don yin shafa'i da witri kamar yadda yadda Saba coz yana jin yau ba lallai ya iya tashi don ya riga ya faka damuwar jama'a a gefe, in ya tashi daga baccin ya saɓa ko ya ɗuura ta a baya.
*Zahrah's POV*
Da sauri ta bar parlourn sai Kuma bedroom ɗinta. Kan bed ta faɗa tana maida numfashi
“Ya Allah! Allah dai yasa ya ci abincin kada ya kwana da yunwa.” she said so openly sai Kuma ta yamutsa fuska
“To Ina ruwa na da shi in ya ci in bai ci ba?”
“Kin manta kin ce Zaki taimaka wurin dawo da rayuwarsa daidai, it's part of your job.”
“Yea Haka ne! Amma meyasa nake jin sa mutum na musamman a rayuwata?”
“Saboda shi ɗin ɗan'uwanki ne.”
Kamar mahaukaciya Haka take ta surutu ita ɗaya. Kamar an ce ta nutsu sai ta tura bankinta gaba tare da cakumo blanket ɗin dake shimfiɗe kan bed ɗin saying
“Ke Zahrah relax! Relax! Relax please.”
Lokaci ɗaya ta kwashe da dariya
“Wallahi yau na Zama mahaukaciyar gaske, please lemme control myself!”
Sai Kuma ta Fara juyi kan bed ɗin. Tunawa da Bata Yi salla ba yasa ta diro da sauri ta nufi toilet, sai da tayi wanka tukun ta ɗauro alwala, bayan ta yi salla ta haye bed don ta fara tsara ta Ina zata Fara.
Ganin kamar an toshe brain ɗinta yasa ta yanke shawarar gobe sa zanta da Nasreen kawai. A Haka dai har bacci ya ɗauke ta.
*Devil Klans’ POV, 1:13 Midnight, in an unknown dark area full of long canopies and trees.*
Guguwa ce Mai ƙarfin gaske ta tashi kamar duniyar zata kife lokaci ɗaya Kuma ta ɗauke yayin da wani irin duhu ya mamaye farfajiyar wajen tsawon wani lokaci Kuma sai ga Haske yana bayyana kaɗan kaɗan har ya gama mamaye wurin.
Halittun Nan na kwanakin baya da za su Kai goma Sha biyar suka bayyana shugabansu kuma na zaune ƙafarsa ɗaya kan ɗaya. A yau dai Kam na gama tabbatarwa da Kai na waɗannam matsafa ne ko Kuma cultists waɗanda ke amfani da jinin mutane da wasu dabbobin Suna shayar da baƙaƙen shaiɗanu don Samar ma kanunsu da wani ƙarfin iko na sihiri, ɗaukaka ko Kuma dukiya.
A yau ma kamar ibada sai da suka gabatar da karatun dalasimansu da suke cewa addu'a kafin su Fara tattaunawa kan abun da ya Tara su.
“Kamar yadda na sanar da ku a taron mu da ya gabata, waɗannan Haske fa sun haɗe da juna Kuma Suna gab da Fara kawo Mana farmaki, yanzu lokacin aiki ya yi, kowa ya shirya don ba zamu bar kowanne mahaluki ba da zai kawo Mana cikas cikin tafiyar Devil Klans ba, babuai dakatar da mu har sai mun gama cimma ƙudirorin mu a doron ƙasa, har Sai mun tabbatar mun mulki duniya gabaɗaya tare da yin arziƙi na ban mamaki.”
Uwargijiya ta faɗa tana sauƙe numfashi kafin ta ci gaba.
“Saboda Haka nake roƙon kowanne a cikin ku yayi sadaukarwa ga dodon tsafi ta yadda ƙarfin mu zai ƙaru fiye da na da har ta Kai kowa na fargaban tunkarar mu. Zamu mulki duniya gabaɗaya tare da yaƙar duk wani maƙiyi.”
Ihu sauran su ke Suna faɗin wasu maganganu da babu su cikin harshen hausa Idan Kuma har akwai to zan iya danganta hakan da yaren tsafi ne.
“Dole kowa ya sadaukar da jinin makusancinsa domin dodon tsafi ya fi buƙatar irin waɗannam jini, sannan kowannen mu zai Yi sadaukarwccar baƙaƙen karnuka da aladai da Kuma jakkai, zai haɗa da ɓaƙaƙen kuliyu da jarirai da kuma samari goma-goma each.”
“Sai mun Yi! Sai mun Yi!!”
They said it in a chorus.
“Abu na gaba kuma shine kowa yayi kaffa-kaffa da na kusa da shi, ku Kula da sirrin warakarku don matuƙar wani ya gano shikenan taɓarɓarewa zata tabbata gare ka, zaka rasa ikon ku Kuma ku rasa nutsuwa cikin gamagarin mutane, hakan Kuma Jan iya jawo rauni ga Devil Klans Wanda ni ba zan jura ba, ku Yi yaka tsantsan don duk Wanda ya bari sirrinsa ya bayyana bayan rasa ikonsa za mu yi sadaukarwa ne da shi ga dodon tsafi.”
“Yea! Yea! Yea!!!”
“Jimjina ga Gutsirito Mai iko, kowa ya kiyaye ya Kuma Yi taka tsantsan. let's disappear!”
Kamar ƙiftawar ido suka ɓace wurin Kuma ya koma wani fili kamar dai football field ne ma.
_To jama'a yanzu mun fara wasan, yanzu ne ya Kamata ku kasance da ni don jin ya zata Kaya. Reactions da comments kawai nake buƙata daga gareku, thank you 🦋_
_I'm sorry for not updating my esteem fans matsalar caji ya sa hakan, Amma ga wannan a karanta._
*Don Allah a Yi reacting sannan a taya no sharing, wannan ita ce ƙaunar da zaku nuna min, Diamond Bhatool taku ce.*
[12/26, 9:59 PM] Diamond Bhatool:
*🏡A BABBAN GIDA🏡*
*TAKUN ƘARSHE*
*©Diamond Bhatool*
*💎💍ELITE DIAMOND WRITERS💍💎*
_Where diamonds shine, words ignite_
_Wattpad: @diamond_bhatool_
_Arewabooks: @diamondbhatool3_
Please follow
*PAGE* 1️⃣2️⃣
_Not edited_
﷽
*Sadauki's POV*
Ya so ya Samu isasshen bacci Amma hakan ya gagara sakamakon tarin damuwoyin da suka addabi zuciyarsa waɗanda with time yake hasashen matuƙar ba su bar shi ba ba lallai ya iya ci gaba da ɗaukar su ba. Wannan ma is part of his triumph and courage. Ganin baccin ba zuwa zai yi ba yasa ya miƙe tare da ɗauro alwala, Haka dai Daren Nan ya ƙare yana Kai kukansa ga Allah.
Fatan sa Allah ya bashi ikon ɗaukar komai da ya jarabce shi da shi.
Safiyar ranar bai samu zuwa breakfast part ɗin Hajjaty ba saboda baccin da ya ɗauke shi bayan ya dawo daga masjid.
Cikin baccin sa ya fara jin hayaniya sama-sama. Juyi kawai yayi ya ci gaba da baccinsa. Can kuma ya ji hayaniyar na ƙara ƙamari hakan ya sa ya buɗe idanuwansa yana mai karanta addu'ar tashi daga bacci. Tsaki ya ja tare da ziraro ƙafafunsa ƙasa sannan ya nufi toilet, wanka ya yi sannan ya shirya cikin wasu light Armani brand masu taushi sannan ya fesa turaren sa mai mugun daɗi.
Tsaki ya ƙara ja a karo na biyu don har ga Allah hayaniyar nan ta ishe shi, fuska ɗaure ya fito yana mai taka staircase ɗin a hankali. Sai da ya kusa sauƙowa ya hango fuskokin da yake gani as useless. “Ko me ya kawo su nan?” ya tambayi kansa.
Yana ƙarasa sauƙowa Mommah ta cillawa Hajiya Babba Harara tare da faɗin “Kuma ina dawowa.”
Da sauri ta nufi inda yake tsaye yana kallonsu cike da takaici while cikin ransa yana tunanin sai zuwa yaushe mutanen gidan nan zasu yi hankali ne. Bai ji zuwan ta ba sai da tayi hugging ɗin sa, cikin wata raunananniyar murya take faɗin
“Haba son! Sai zuwa yaushe ne za ka bar zuciya ta ta zauna cikin salama? Ka kwashe ka tafi and ka dawo ma sai dai naji a bakin jama'a? Haba son, ka rasa ma ina zaka tare sai nan, ɓangaren matar da ke shirin raba Ni da kai? Why son?”
Yes, ya san at times bai kyauta mata amma ita ma da gudunmawarta ga hakan ai, yanzu irin wannan zubda girman da tazo ta yi a nan ai bai dace ba, ta gefen ido ya kalle su fuskar su sake suna riƙe da ƙugu tuni ya ji ransa ya ƙara ɓaci hatta Mommahn ma haushin ta yake ji na mu'amala da wadannan mutanen da sam basu son zaman lafiya a rayuwarsu.
Jin ya yi nata mata shiru yasa ta ɗan ƙara kwantar da murya tare da sakin sa
“Mu je my son”
Har cikin ransa ya tausaya mata amma yayi alƙawarin dole ta fahimci kuskuren ta ta rabu da mutanen nan da take wa kallon masoya.
Dubansa ya kai ga Hajiya Babba wacce bata ce komai ba duk abunda ke faruwa sai ma karatunta da ta cigaba da yi. Bai ji daɗin abun da Mommah ta yi mata ba amma ya ji daɗin ganin yadda Hajiya Babban ta share su.
“Ka yi shiru son, mu je ko?”
“I'm going no where Mommah, sai zuwa yaushe ne zaki gane mutanen da ke tare da ke kai ji suke su baro ki?, Ahbeg Mommah, ki ja mutanen ki ku koma zan zo yanzu.” ya faɗa cikin ƙunar rai.
“Kin ji ko? Kin ji shi ko Rukayya? Na rantse da Allah ki sake min yaro na ya isa haka!”
Ta faɗa a fusace tana nuna Hajiya Babba da yatsa.
Abun nema ya samu, Ammie da Mami suka matso kusa da ita duk da cewa suna shakkar dizgawar Yaya Sadaukin.
“Ai tun ba yau ba nake faɗa miki Hajiya Sughrah, Rukayya ta riga ta mallake miki ɗa, ba iya shi ba kusan duka gidan ta mallaki kowa. Gaskiya dole ki tashi tsaye.”
Yaya Sadauki da ransa ke ɓace bai san lokacin da ya kalli Mami ba ya Wulla mata wani kallo da yasa ta shiga taitayin ta.
“Matar da kuke zagi duk ta girme ku amma gashi ta banzatar da ku, hakan kaɗai ya isa ya tabbatar muku da cewa ita ɗin ba tsararku ba ce, Mommah!”
Ya faɗa yana riƙe hannunta
“It's now time da ya kamata a ce kin gane masoyanki, na roƙe ki da Allah ki ja mutanen nan ku tafi zan zo na faɗa miki.”
“Ai gashi nan, kin ji me yake faɗi ko Hajiya Sughrah, to gaskiya dai Allah ya sa ka gane hanya, ina ga dai....”
“Gaskiyar ki Hajiya Saudatu, wallahi burin ta bai wuce ta samu tsohon can ya hana auren ɗan nan da ƴar ta Mabruka ba ganin ta yi kwantai kuma.....”
“Ya isa haka Baraka!”
A zabure suka juyo ganin Alhaji Baba ne da kansa kuma fuskarsa babu alamun sauƙi, nan kowacce ta shiga taitayinta suka sunkuyar da kanunsu ƙasa kamar wasu munafukai.
“Kun gama? Nace kun gama?”
“Haba Alhaji ya za a yi a daki mutum a hana shi kuka? Fisabilillah komai Hajiya Babba tayi cikin gidan nan bata da laifi?”
Hajiya Saudatu ta faɗa tana riƙe kunkumi kamar wata yarinya.
“Ban ce ki yi magana ba, Rukayya Allah yayi miki albarka, ki ci gaba da haƙuri da su har lokacin da za su yi hankali.”
Murmushi Hajiya Babba tayi wanda ake cewa ya fi kuka ciwo sannan ta amsa da Amin ba tare da ƙara cewa komai ba.
Alhaji Baba ne ya fuskance su sannan yayi murmushin takaici
“Kai Sadauki wuce ɗakin ka, ke kuma Bāraka ba wasa da gaske kuwa sadauki zai auri Mabruka sai dai ki mutu, me ma ya kawo ku nan..?”
Taran numfashinsa Mommah tayi kamar zata haɗiyi zuciya saboda baƙin ciki.
“Don Allah Alhaji Baba kada ka yi haka, wallahi sharri aka yi wa yaron nan ka san ba mutumin banza bane, ka taimaka kada ka masa auren dole, ga nan Kausar ta wajen Hajiya Baraka ina laifin a yi haɗin da ita?”
“Ba shawarar ki nake nema ba Sughrah, auren Sadauki da Mabruka babu fashi sai dai in bana numfashi. Ku kiyaye shiga sabgar Rukayya wallahi, duk ranar da na kuma ganin ku ɓangaren ta kun zo yi mata cin fuska wallahi sai na sa mazajen ku sun mayar da ku zawarawa tunda ku baku san mutunci ba.”
Daga haka Alhaji Baba ya nuna musu kofa da hannunsa.
Simi-simi kamar munafukai suka fice zuwa ɓangarensu, Alhaji Baba ya ƙara bawa Hajiya Babba haƙuri kana ya wuce abun sa.
A ɓangaren su Mommah ko da suka fita ɓangarenta suka wuce, nan suka fara zage-zage a kan rashin adalcin da ake yi musu a gidan (amma fa a nasu ganin.)
Nan suka ƙara zuga Mommah kan kada ta yadda a mata fin ƙarfi a kan ɗanta ko da kuwa hakan zai yi sanadiyyar barin ta gidan. Wannan shi ne abun ta hau kuma ta Zauna.
*Yaya Sadauki's POV*
Ko da ya shiga Bedroom ɗinsa ji yayi kamar ya sanya kuka saboda yadda abubuwan ke shirin dagula masa lissafi. Abun da ya faru ya sa ya ji ya ƙara aminta da auren Mabruka musamman da ya tuna irin tarbiyyar da Hajiya Babba ke bawa ƴaƴanta har da na mutane, shi kansa abubuwan da ya koya masu kyau daga gare ta Allah ya yi yawa da su.
Jin shiru yasa ya fito jiki sanyaye, har lokacin kuma Hajiya Babba na zaune yana karatunta. Jiki mace ya tsugunna ya ma rasa me zai ce mata. In a cool voice ya ce “I'm so sorry Hajiya, I don't mean it to happen, ban ji daɗin abubuwan da Mommah tayi miki ba, kullum ina ƙara nuna mata hanya amma ta kasa fahimta, don Allah ki yi haƙuri, sannan kada ki biye maganar Ammie da Mami ki ce zaki hana aure na da Mabruka, Allah meant it to happen, kada ki hana don Allah.”
Murmushin su na manya tayi kana ta shafi fuskarsa tace
“Kada ka damu son, ban isa na ja da hukuncin Alhaji Baba ba, sannan batun Sughrah ban taɓa ɗaukarsa da muhimmanci ba saboda na san ba yin kanta ba ne, fata na ka taya ta da addu'a Allah yasa ta gane da wuri.”
Dattaku irin na Hajiya Babba kullum ƙara burge shi yake, murmushi yayi sannan ya ce “Bari na je na duba ta, addu'a In Sha Allah muna kan taya ta.”
Daga haka ya wuce yana ƙara godewa Allah da ya sa abun da ya faru babu wani yaro duk suna school, Mabruka kuwa yana kyautata zaton ta wuce court abunta.
Abun da ya tarar a can ai ya dama wadda ya gabata, duk irin huɗubar da suke wa Mommah cikin kunnensa ne, duk shaiɗancin su bai taɓa zaton za su yi mata irin wannan huɗubar ba duba da yadda suke nuna cewa suna tare da ita, ya za a yi su ɗaura ta kan ta kashe aurenta akan abunda ta san ba Mai sauyuwa bane?.
Makewa yayi ya wuce tare da gyara murya, tuni suka miƙe suna yi wa Mommah sallama, shi dai da kallo ya bi su yana musu addu'ar shiriya cikin ransa kuma yana ayyana barin Mommah ta yanke ne ya dace da ita, In ta zaɓi kashe aurenta fine, zata koyi darasi ne ai.
Rungume shi tayi tana kuka kamar wata yarinya
“Son kana ganin irin cin mutuncin da aka min gaban idon ka ko? Ko tausayi na ma baka yi ko?”
Hankalinsa ne ya tashi don