Showing 15001 words to 18000 words out of 157517 words
min baya haka ina ganin babu amfanin cigaba da rayuwa ta, kar ka manta kai ɗaya ne bayan Alhaji Baba Ka kasance garkuwa gare Ni, kada ka yi min haka, idan wani abun nayi maka we need to talk, ba wai ka sauya min ba.” dafe kansa yayi yana gama faɗar hakan tare da lumshe idanunsa.
A sanyaye Yaya Khalil ya juyo yana fuskantar ɗan'uwansa cike da so da kulawa tare da tausayawa rayuwarsa, sai kuma ya ji a ransa cewa bai kyauta ba kan abunda ya aikata, he should haven't act in such a way, but it's not too late. Fuska sake ya riƙo hannun Yaya Sadauki tare da haɗe su wuri ɗaya da nasa.
“I'm sorry man!, I shouldn't have not done such, duk irin yadda muka kasance but I can't hold it more Shiyasa nayi fushi da kai, don Allah Man, ka sanyaya ranka, ka ƙara haƙuri da jajircewa, ƙungiyarku na shirin durƙushewa saboda yadda ka raunana, don Allah ka koma Sadaukin da Abatcha Family ke alfahari da shi, kada ka bari maƙiya suyi dariya, ka koma kan aikinka Sannan ka koma ga Ahalinka, a cikinsu akwai waɗanda suke cikin ƙunci da rashin ka, be linient with them please, Ka koma don Allah, na maka alƙawrin kasancewa by your side.”
Shiru ne ya wanzu tsawon wani lokaci kowa da abunda yake saƙawa cikin ransa, Yaya Khalil na addu'ar ubangiji ya bashi sa'ar kwantar da wannan raunananniyar zuciya shi kuma Yaya Sadauki na addu'ar Allah ya sauƙaƙa masa al'amarin.
Lumshe idanuwansa yayi tare da buɗe su lokaci guda sai kuma ya kalli Ya Khalil, kamar ba zai yi magana ba sai kuma ya ce “Ok”
Da sauri Yaya Khalil ya ɗago ya dube shi jin amsar da ya bashi wondering if amsan da ya bashi yaji da kyau. Tunaninsa ya koma kwacakom ga bai ji da kyau bane. Ganin dai ba ƙara magana Yaya Sadauki zai yi ba yasa yaya Khalil faɗin “Man ka haƙura zamu koma Naija??” kamar ba zai kula shi ba sai ya ɗaga kansa alamar eh. Da sauri yaya Khalil ya miƙe ya rungume Yaya Sadauki, bai yi ƙoƙarin dakatar da shi ba coz he need it, he need someone to hug him ko zai sa damuwoyinsa raguwa. Cike da Farin ciki Yaya Khalil yake faɗin “Masha Allah, thank you so much, Allah ya ƙara maka lafiya.”
Cikin ransa ya amsa da “Amin” sai kuma ya janye Yaya Khalil ɗin da ke jikinsa zuwa gefe.
Lokaci guda kuma suka shirya, ko da Dr. Ya zo yayi discharging nasu ba su tsaya ba suka wuce bayan shawarwarin da Dr ɗin ya bawa yaya Khalil game da rashin lafiyar yaya Sadaukin.
******************
Ganin duk ƴan matan sun tafi yasa Hajjaty ƙwalla ƙiran Zahrah da ke kwance kan sofa. Da sauri ta miƙe tsaya tana faɗin “Ina zuwa Hajjaty ” a gefen Hajjatyn ta zauna, nan Hajjaty ta fara jan ta da taɗi, sosai suka sha hirarsu Hajjaty na ƙara kula da yanayin Zahrah tana mai ƙara fahimtar ta. Lokacin sallah da yayi Hajjaty ta saka Zahrah gaba suka gabatar da sallar su wanda su biyun suka daɗe a sujjada suna masu faɗawa Ubangiji damuwarsu wacce kusan duk kusan abu ɗaya ne suke roka wurin Ubangiji.
Bayan sun yi sallah suka yi lunch ɗin su, ko tashi daga dining area basu yi ba sai ga Nasreen ta shigo ɓangaren Hajjatyn.
Cike da son tsokalo Hajjatyn ta ce “Zahrah samu kiyi wanka tunda kin shirya mu tafi part ɗin mu.” Hajjaty da ke shirin miƙewa ta ce “Kya yi ki gama ai, ko uwarki Ruƙayya bata isa ta zo tace Zahrau tabi ta ba.” dariya Nasreen tayi ta ce “Mai da wuƙar Hajjatyn mu, ba da faɗa min ga na zo ba, na zo ne na ɗauki ƴar'uwa ta mu ɗan huta.”
A ɗan fusace Hajjaty ta ce “To ai sai ki ɗauakd ta ko! Ke Nasreen wallahi ki kiyaye Ni, har Ni zaki faɗawa yan'uwan taka? To ki ɗauke ta ku je maza.”
Ganin dai da gaske Hajjaty fushi tayi yasa Nasreen kwantar da murya hanmayenta biyu haɗe ta ce “Yi haƙuri masoyiyar kakata wacce babu kamarta, wasa nake kawai na zo na ɗebewa Zahrah kewa ne.”
Kamar ba Hajjaty ke masifa ba sai ta saki fuska yana washe baki “Kai amma naji daɗi sosai Nasreen, Shiyasa kullum nake ƙara yabon ƴaƴan Ruƙayya , Allah dai yayi Miki albarka. ”
Sai ta kalli Zahrah da ta miƙe itama tana kallonsu tace “Zahrau kuje bedroom ɗin ki ke da ɗiyar Albarka ko?”
Kai kawai Zahrah ta gyada tana mai sakin fuakarta tare da nufar yadda Nasreen ɗin ke kallonta tana murmushi ita ma.
Tare suka ƙare yinin nan sai wuraren 5:25 Nasreen ta ce zata wuce, “Zahrah kiyi wanka kafin na dawo”, “Ok” Zahrah ta bata amsa, daga nan Nasreen ta wuce zuwa part ɗinsu. A hanzarce tayi wanka ta saka kaya, ko kwalliya bata yi ba duk da kasancewar ta gwanar hakan. Wasu EXTRA Kaya ta kwaso ta fito, tana zuwa parlour suka yi kiciɓus da Hajiya Babba. “Eh an Damah Hajiya Zan kaiwa Zahrah ne Yaya Auwab zai raka ta tayi shopping ” kamar zata ce wani abu sai kuma kawai ta yi mata alama da hannunta da ta wuce. Sai da ta sauƙe ajiyar zuciya kafin ta fito da sauri. Ganin Zahrah ta yi wankan ya sa Nasreen miƙa mata kayan. “Ki saka wannan kafin gobe ki yo shopping,”baki Zahra ta buɗe zata yi godiya, kamar Nasreen ɗin ta san me zata ce ta dakatar da ita tana ɗaira index finger nata a kan baki “Dont say thanks, u deserve more.”
Haka Zahrah ta sanya kayan da suka matuƙar amsar jikinta, abun ba'a cewa komai tayi kyau sosai. Nasreen ce ta kalle ta tace “Wow! Kinga yadda kayan suka yi Miki kyau kuwa Zahrah? Abun ba'a magana fah!”
Murmushi Zahrah tayi tama faɗin “Lallai kam, babu wani kyau fah, you are just kidding ”
In a serious tone Nasreen ta ce “For sure Zaharah I'm telling the fact, kin yi kyau, kina da kyau ma zance” “Ok thank you dear, kema kin yi kyau ai”. Zahrah ta bata amsa cike da son kawar da zancen.
“Kin ga Zahrah, let's get going” Nasreen ta faɗa tana riƙe hannun Zahrah
“Ina ne zamu je haka Nasreen?” Zahrah ta tambaya. “Lallai ma Zahrah ” Nasreen ta bata amsa tana harararta. “Ba Hajjaty ta ce zan raka ki ki gaida mutanen gidan ba kuma na nuna Miki gidan ba” “Oh” Zahrah ta faɗa “Wallahi na shafa'a, mu wuce ko” daga haka suka fice har lokacin hannunsu riƙe da na juna suna tafe suna taɗinsu har suka fito daga part ɗin Hajjatyn.
Da Ya Aufa suka ci karo yana ƙoƙarin shiga ɓangaren Hajjaty, da sauri suka gyara masa hanya tare da gaida shi. Tsayawa yayi yana kallon su kamar wasu sababbin halittu, ganin irin kallon da yake yiwa Zahrah yasa duk ta ɗan rikice, gyaran murya Nasreen tayi tana faɗin “Ehm Yaya Aufa mun wuce ko” sai ta ja hannun zahrah suka yi gaba. A ɓangaren ya Aufa sosai ya yaba da kyau da kuma tsarin halitta irin na Zahrah, sai ya tsinci kansa da jin ƙaunarta,zuciyarsa ta ƙara masa ƙarfin guiwa da faɗin “Ƴaruwarka ce ai!” da haka ya ahige part ɗin Hajjatyn cikin sanyin jiki.
Su Zahra na wucewa suka nufi part ɗin Alhaji Babba wanda ya kasance haɗaɗɗe tun daga wajensa, yana da girma da kuma faɗin gaske, kai tsaye Nasreen ta ja hannun ta zuwa cikin part ɗin da ke ɗauke da sassa uku manya manya. A hankali Nasreen ta furta “Nan shine sashen mu Zahrah, ɓangaren Alhaji Babba kenan ai kin gano shi?” kai ta gyaɗa mata daga nan suka tunkari sashen Hajiya Babba, wato sashen sun Nasreen ɗin.
A parlourn suka tarar da Hajiya Babba kwance kan sofa ga kuma Fruits a ɗan basket ɗin da ke table ɗin gabanta. Sunkuyar da kai ƙasa Zahrah tayi ganin matar ita kuwa bata ma san ta shigo ba coz hankalinta na ga labaran da take kallo.
Ko da suka isa dai-dai tsakiyar parlourn sai Zahrah ta zauna ƙasan carpet ɗin, Nasreen ce tayi gyaran murya tace “Hajiya Babba!” a lokacin ta ɗago ido tana duban Nasreen ɗin, bata kai ga ɗauke idonta daga gare ta ba taji wata sassanyar murya mai taushin gaske na faɗin “Ina yini”.
A lokacin Hajiya Babba ta mayar da dubanta ga sashen da sautin ya fito, duk da cewa kanta a ƙasa ya ke amma hakan bai hana zuciyarta bugawa ba. Fuakarta babu yabo babu fallasa ta amsa da “Lafiya ƙalau ƴan mata, ya kwanan baƙunta.” Zahrah da kanta ke ƙasa ta fara magana yayin da zuciyar ta ke gudu da sauri da sauri wanda bata san dalilin hakan ba. “Alhamdulillah Mama”
Ɗan sakin fuska kaɗan Hajiya Babba tayi tace “Kar ki saka damuwa a ranki, ki ɗauke Ni tamkar Uwar da ta haife ki,ga Nasreen nan zata kasance a tare da ke, amma ki kula sosai!” daga haka tayi shiru. Zahrah ta ce “Na gode sosai, Allah ya ƙara girma” bata ji amsar Hajiya Babban ba amma cikin ranta tana ayyana wasu abubuwa, why take ta haɗe mata fuska ko bata farin ciki da zuwanta ne?, abu na gaba haka ta jinjina mulki irin na Hajiya Babbar har take tunanin anya ita ta haifi Nasreen?.
Muryar Nasreen ce ta dakatar mata da tunanin ta “Mu je gaba kada Maghrib tayi bamu gama zaga gidan ba.” miƙewa tayi ta kai dubanta ga Nasreen ɗin kafin su yi waje tare, Hajiya Babba dai da ido ta bisu har suka ɓace.
Ɓangaren Hajiya Karima suka yi, a nan kam Zaharah ta samu kyakkyawar tarba daga Hajiyar tsakiya. Sosai ta nuna farin cikinta da ganin Zahrah, haka mutanen da ta tarar ma a parlourn, Hibba, da Samha su ma suka yi ta zolayanta sai taji kamar kada su tafi.
Daga nan suka wuce part ɗin Ƙaramar Hajiya, babu laifi nan ma Zahrah ta samu Garba musamman daga Aunty Meerah dake tare da ƙaramar Hajiyar.
Sosai Nasreen taji daɗi ganin yadda suke nuna mata ƙauna, can dama su part ɗin su ba'a faɗa in fact duk kansu haɗe yake Shiyasa ko da ta shiga bata fuskanci wani kallo ko hali na nuna cewa su ɗin abokan zama ne ga mahaifiyarta ba. Hakan yayiwa Zahrah daɗi duk da cewa ta saka Ayar tambaya akan hali irin na Hajiya Babba ɗin.
Daga nan sai da suka yi tafiya mai ɗan tsayi har suka wuce wani ɗan cool down mai ɗauke da flowers masu Kyan gaske, though Zahrah bata tambaya ba amma Nasreen told her that cikin estate ɗin nan akwai kwatankwacin irin wannan wuri kusan guda Ashirin, and its all meant for refreshing minds. Sai dai ta faɗa mata cewa “Wannan kuma da kika gani ba kowa ke zuwa ba saboda na Yaya Sadauki ne! Ko baya gari babu mai gigin zuwa wurin saboda wurin zamansa ne.”
Sai da zuciyar Zahrah ta buga da jin sunan though this is the first time da ta ji sunan. Amma sai ta samu ƙarfin halin faɗin “Who is he?”
Nasreen ta bata amsa da faɗin “In mun koma I'll let you know who is Yaya Sadauki, zan faɗa Miki!”
_Masn son magana da ni kai tsaye ko suke buƙatar littafin daga farko, ga number na +2347061707238._
_React please, a taya Ni isar da saƙon ta hanyar sharing don Allah, ina ƙaunarku my. esteem fans, Allah ya bar mu tare. Diamond Bhatool taku ce 🤗_
*TALLA! TALLA!! TALLAH!!!*
Ina mata ƴan ƙwalisa! Ina uwar gida sarautar mata!!! Amarya kema ban barki baya ba, Naji da yawa na complain akan yadda fatarsu ta koma saboda rashin samun ingantattun kayan gyaran jiki, fuskarsu ƙuraje da sauran skin infections.
Hohoho! Nesa ta zo kusa fah! Kuyi maza ku garzayo don samun naku kayayyakin gyaran jikin waɗanda basu da wani side effects a jikin mai amfani da su.
*Kayayyakin su haɗa da:*
1. Supplement gummies waɗanda zasu gyara Miki fuskar ki tayi luwai tamkar fatar jariri, ta yadda ko ina kika shiga sai an tambaye ki ina kika samu wadannan kayayyaki masu inganci.
2. Breast enlargement cream Wanda bashi da wata illa ga mai amfani da shi, cikin kwanaki ƙalilan zaki ga yadda yake aiki.
3. Akwai sauran kayayyakin gyaran jiki masu matuƙar inganci wanda babu Algus cikinsu.
*Ƴar'uwa matso kusa ki mallaki naki kan farashi mai sauƙin gaske.*
*Kai tsaye ki tuntuɓi wannan number +2347062283256 Kada ku bari ayi babu ku ƴan ƙwalisa.*
[12/7, 9:03 AM] Diamond Bhatool:
*🏡A BABBAN GIDA🏡*
*TAKUN ƘARSHE*
*©Diamond Bhatool*
*💎💍ELITE DIAMOND WRITERS💍💎*
_Where diamonds shine, words ignite_
_Wattpad: @diamond_bhatool_
_Arewabooks: @diamondbhatool3_
*PAGE* 0️⃣8️⃣
﷽
Daga nan suka wuce part ɗin Daddy, kamar koyaushe Mamie, Mommah da Ammie ne ke zaune a katafaren parlourn da ya gaji da haɗuwa wanda shigar su tayi dai-dai da fitowar Nainarh daga bedroom nata.
Da gudu ta karaso tare da hugging Zahrah tana faɗin “Irin wannan suprise haka!” sai kuma ta sake ta tare da kama hannunta.
“Ina kuma zaki da ita?”Nasreen ta faɗa tana ƴar hararar Nainarh.
“Im sorry sis Nasreen wallahi ni ban ma lura da ke ba”
“Ina kuwa zaki lura dani tunda Zahrah na rako, silly girl!” ta ƙarasa tana hararar Nainarh wacce ke dariya. Hayaniyarsu ce ta sa mutanen da ke cikin parlourn suka farga da wanzuwar su, Mommah da ta sa idonta kan Nasreen sai ta haɗe rai thinking why is that girl there? Me ta zo yi part ɗin ta. Su ma sauran duk sai suka mika kallon su ga wurin da Mommah ke kalla. Caraf idonsu ya sauƙa kan baƙuwar fuskar da basu sani ba. Da sauri Nainarh ta ja hannunsu tana faɗin “Lets get in” a sanyaye suka bi bayanta har suka kai tsakiyar parlourn yayinda suka lura da kallon banza da ake aika musu wanda hakan ke da nasaba da zuwan Nasreen ɓangaren.
A ƙasa Zahrah ta zube kan guiwowin ta, cikin sassanyar muryarta tafara gaida su, nan suka amsa zukatansu fal da alhinin son sanin wace ce ita, Nasreen ma ta gaida su, sai dai babu wacce ta amsa ciki sai ma kallon Banza da Ammie ta cilla mata.
Ganin za'a iya samun matsala yasa Nainarh faɗin “Mommah ga nan jikanyar Hajjatyn da nace miki ta dawo gida, sunan ta Zahrah.”
Ɗan murmushi kaɗan Mommah ta saki saying “You are welcome Zahrah” Suma Ammie da Mimie suka faɗi hakan kamar yadda Mommah ta yi.
Nasreen da ke gefe ne ta ɗan taɓo Zahrah, saboda haka suka miƙe, Zahrah na faɗin “Nagode sai anjima”. Daga nan Nainarh tabiyo bayansu suka fice Ita dai Zahrah an cika ta da tunani, ta rasa kan wanne ma zata yi yanzu. Irin yadda taga an yi ma Nasreen ko kuma dai kallon da Ammie ke binta dashi ta ƙasan ido?, Bata san wanne ɗaya ya kamata ta tattauna ba ita da zuriyarta. A haka suka zaga sauran parts ɗin, jiki gajiye suka dawo part ɗin Hajjatyn lokacin ana kiran Sallah a masallacin estate ɗin.
Ko da suka yi sallah nan suka baje babin hirarsu, har kusan Isha Nainarh ta ce zata wuce ɓangaren su. Daga nan suka yi sallama. Ita dai Zahrah dama jira take Nainarh ta fita ta fara baje kolin tambayoyin ta ga Nasreen wacce duk cikin ƴan'uwan nata tafi jin nutsuwa tare da ita.
“Yauwah Nasreen what about that Yaya Sadauki da kika ce zaki yi gisting na about him?”
“Ai dama na san ba zaki manta ba” Nasreen tabata amsa tana ɗaura hannayenta kan na Zahrah. “Kaɗe kunnuwanki ki ji labarin Sadaukin Abatcha” hararar wasa Zahrah tayi mata saying “See you girl, har wani kaɗe kunne zan, kinga muje don yau inaga anan zaki kwana coz I've so many questions for you.”
“Dan ma dai na san the story will be so boring to you, amma lemme start.”
Murmushi Zahrah tayi tana mai gyara zamanta kafin ta ce “All ears.”
“Toh Zahrah kamar yadda kika ji nace Yaya Sadauki haka mu muke ƙiransa, amma Aliyu shine ainihin sunansa. Ya samu wannan take ne daga yarintarsa daga wurin Alhaji Baba kamar yadda Hajjaty ta taɓa bamu labari. Yaya Sadauki mutum ne irin masu tsattsauran ra'ayin nan ne da suke rayuwa irin ta kaɗaici kuma basu buƙatar wani ya kutsa cikin rayuwarsu, wanda hakan kuma na da nasaba da tarin damuwoyi da suka masa yawa. Yaya Sadauki miskili ne ajin farko, don zan iya ce miki a rana zaki iya ƙirga words ɗinshi.”
“Idan har kinji maganarsa to shi da Yaya Khalil ne, ko kuma Hajjaty da Alhaji Baba, shima kaso 90 na maganar a hannun su yake.” ta dakata tare da jan wani dogon numfashi alamar tana buƙatar faɗar wata gaɓar da ke da muhimmanci.
“ Zahrah, Duk Cikin estate ɗin nan kai duk faɗinsa babu wani mahaluki da ke da kwarjini irin nasa, babba da yaro kowa shakkar sa yake. Ba wannan ba ma, kin san irin tarin dukiyar da ya mallaka tasa kuwa?, Wallahi Zahrah zan iya ce miki duk estate din nan babu wanda ya kai shi tarin dukiya, shiyasa most yan matan family suka maƙale masa Though shi bai ma san suna yi ba don ana yawan samun fadace fadace cikin gidan nan, ke dai Zahrah zaki ga abubuwa iri-iri, kiyi taka tsantsan wajen mu'amala da kowa, Domin akwai abubuwan da ba sai na miki bayani ba lokaci kaɗai zai nuna miki su.”
Gauron ajiyar zuciya Zahrah ta saki lokaci guda kuma maganganun Nasreen na yawo cikin ranta, and she needs time to think more about them. Shirunta yasa Nasreen murmusawa tana faɗin
“Watz wrong Zahrah?”
Numfashi Zahrah ta ja tare da fesar da wata zazzafar fuska kafin tace
“Nasreen amma ban taɓa kallonsa cikin gidan nan ba.”
Cike da kulawa Nasreen din tace
“Zahrah In na miki bayani ma ba Lallai ki gane ba, yanzu haka maganar da nake miki baya ƙasar shi da yaya Khalil duk da cewa dama can ba ma'abocin zama bane amma wannan tafiyar ta sha bamban da wacce yake yi”
Cike da ƙaguwa Zahrah tace “gist me please, haka kawai nake jin kamar shi ɗin wani sashe na jikina ne duk da cewa hakan take