Showing 66001 words to 69000 words out of 157517 words

Chapter 23 - A BABBAN GIDA 2

10 May 2025

5155

ko ka'dan a halin yanzu ba ya so ya 'kara sanya iyayensa a damuwa duk.da cewa they were behind the issue, da ba dan selfishness nasu ba da ba tabbacin zai rasa Zahrah, ga shi yanzu ya rasa ta rashi na har Abada in dai ba suna da rabon ganawa ba.


Haka yinin ranar ya shu'de ba tare da kowa yaji daga Yaya Sadauki ba, sosai hankalinsu ya tashi musamman Hajjaty da Alhaji Baba wana su ka'dai suka san ya bar Abuja, to babban abun da ya gama 'daure kanunsu bai wuce rashin samun wayarsa ba, hakan ba ta ta'ba faruwa ba, bai ta'ba aikata wani abu kwatankwacin hakan ba domin duk tafiyar da zai yi in ya kai masau'ki yakan 'kira ya sanar da su. Sai a lokacin suka fara tunanin me ma yaje yi a Bauchi? Rashin mai ba su amsa yasa suka fauwalawa ubangiji al'amarin don ganin ya zai 'kare tare da addu'ar Allah ya sa jikan nasu yana cikin aminci.

Ko da Zahrah ta fahimci halin da ake ciki sosai ta shiga wata matsananciyar damuwa har kanta ya fara ciwo, fatanta da addu'arta Allah yasa a wani mugun abu bane ya faru da shi duba da yadda gabanta ke tsananta fa'duwa tunda ta shi daga bacci. A haka ta sa su Hajjaty a gaba tana kwantar musu da hankali that Yaya Sadauki na lafiya may be yanayin aiki yasa bai 'kira ba, su masa uzuri ko yaya ne zuwa safiya in sha Allah zai 'kira, Allah sarki tsofi, da haka hankalinsu ya 'dan kwanta ka'dan.

*AUNTY MABRUKA*

Sosai kanta ya fara sarawa saboda damuwar da ta ma'kalawa kanta na rashin samun wayar mijin nata. Bayan ta yi sallar Maghrib ta samu ta 'dan kwanta kan praying mat 'din cikin ranta tana nema masa kariyar ubangiji a kowanne hali yake. Kamar an zabure ta ta mi'ke ta fito parlour ta kwanta tsawon wasu da'ki'ku kafin daga bisani kamar mai shafin iskoki ta kunna TV, da yake jiya shi yayi kallon 'karshe a NTA, hakan yasa tana kunnawa ta yo baya ba tare da sanin takamaimai dalilin jin son ganin tashar ba kasancewarta mace maras son hayaniya da wargi, sam ba ta damu da kutsa kanta rayuwar kowa ba hakan yasa ba ta tashi da son kallon labarai ba.

Kwacakom hankalinta na ga TVn har sadda suka tafi talle, bayan wasu mintoci kuma suka dawo, kamar an ce ta gyara kwanciyarta kuwa ta 'dan zunku'da, maimacin labaran rana aka fara, tana gani zuciyarta na tsananta bugu kamar za ta faso 'kirjinta ta fice, ba ta ankara ba haka ta ga abun da yayi sanadiyyar tashin hankalinta, idan har ba ta manta ba to babu shakka Bauchi mijim nata ya tafi. A matu'kar firgice ta tashi tsaye tana dafe saitin zuciyarta, kafin ka ce me wani irin jiri ya kwashe ta, nan ta fa'di 'kasa sumammiya.

*YAYA KHALIL*

Tashin hankali, wai ba a sa masa date, tunda ya shiga facebook nasa ya fara cin karo da wasu irin post wanda kusan dukkansu are relevant to each other, a lokaci 'daya zuciyarsa ta 'kara tsananin bugu haka kuma 'kwa'kwalwarsa ta tsaya cak da aiki, ba abunda yake fahimta tsawon wani lokaci, abun kamar tsafi 'kwa'kwalwarsa ta dawo aiki. A matu'kar razane yace
"What!" Sai kuma ya mi'ke tsaye yana 'kara zuba idanuwansa ga screen 'din wayarsa don 'karyata abun da idanuwansa suka hango masa. Bai kai ga cimma matsaya ba sai ga 'kira daga Alhaji Babba.

A matu'kar ru'de ya 'daga yana fatansa dai Allah yasa Alhaji Babba zai 'karya masa abunda ya gani ne.
"Assalamu Alaikum, an yini lafiya Alhajinmu?"
Sallamar kawai ya amsa masa, tun daga yanayin muryarsa Yaya Khalil ya rasa gaba'daya hope 'dinsa. Ba tare da ya bi takan gaisuwar da Yaya khalil ya masa ba yace.
"Kai Khalil, ina 'dan uwanka ne?"
kamar zai yi kuka yace
"Alhaji ai Sadauki ya tafi Bauchi 'dazun nan ma jirginsu ya tashi, sai dai kuma...."
ba tare da ya bar Yaya Khalil ya kai ga aya ba ya fara doka salati.
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'una..innalillahi wa'inna ilaihi raji'una.."
haka Alhaji ke ta doka salati ba tare da ya katse kiran ba, a matu'kar firgice Yaya Khalil ya katse kiran don zuwa yanzu ya yadda da abubuwan da ya gani. Tsabar yadda zuciyarsa ta gama raunana ta kuma bushe 'kayau hawayen ma kasa zubo masa suka yi, tunani ya fara me ya kamata yayi yanzu? Tunawa da 'yar'uwarsa yayi hakan yasa ya figi motarsa sai gidan Yaya Sadaukin.

Sallama yake kwa'dawa but shiru, hakan yasa ya shige da sauri yana addu'ar Allah dai yasa news bai kai gareta ba, bulb ya kunna sai dai abun da idonsa ya gani yasa zuciyarsa bugawa tare da 'kara raunana. Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un kawai yake furtawa, a hanzarce ya nufi Aunty Mabruka da ke kwance 'kasa a halin rayuwa ko mutuwa. Ya ma rasa mai ya kamata yayi sai da ya hangi glass cup 'din da ke kan centre table yayi hanzarin 'daukowa ya shafa mata a fuska, wani irin gauron numfashi ta sau'ke tare da fa'din
"Shikenan..." ba ta kai ga 'karasawa ba jikinta ya 'kara saki.

A matu'kar tsorace ya 'kara 'daga hannunta, ganin ya sake yasa ya 'daga ta da sauri ya nufi mota da ita, ko da maigadi ya g haka tuni ya wangale get yana fatan Allaj yasa lafiya...musamman da ya san Yaya Khalil mutum mai barkwanci amma yau ko kallonsa bai ba, uwa uba kuma Hajiyar da yaga an fito da ita a hannu.

Da matsanancin gudu ya figi motar, bai tsaya ko'ina ba sai asibitin estate nasu, a matu'kar 'dimauce ya fito da ita a hannunsa, nan ya ma rasa ina ne mashiga sai dube-dube yake.
Dr. Mubarak da ya fito don wucewa gida ya ga Yaya khalil ri'ke da maras lafiya yasa ya kwa'da masa 'kira, a matu'kar 'dimauce ya waiwayo, da sauri Dr. Yayi wa nurses magana, kan kace me sai gasu sun turo stretcher har zuwa wurin da yake. Babu 'bata lokaci suka shige ciki da ita don bata taimakon gaggawa. Yaya khalil bai tsaya ba ya kira Numbern Humaira yace tayi maza ta taho asibiti za ta kula da mai jinya, idan ba ta same shi ba tayi wa Dr. Muba magana zai kaita. Da haka ya katse kiran yana bin wayarsa da kallo, sai a lokacin ya ga missed calls ba adadi, Daddy, Papa, da sauran uncles nasa duk sun 'kira ba adadi, sauran cousins nasa da su Aunty Madina duk sun 'kira bai ma sani ba, haka friends nasu ma 'kira babu adadi.

Ta riga ta tabbata, hakan yasa ya nufi cikin estate 'din don ganin halin da suke ciki. Abun mamaki har lokacin su Hajjaty da alama labari bai kai musu ba sai dai suna cikin matsanancin tashin hankali. Ajiyar zuciya ya sau'ke daga nan ya juya ba tare da ya ida shiga ba, karo suka ci da Ya Qasim wanda fuskarsa tayi ja alamar dai kuka yayi ga kuma tashin hankali 'karara a fuskarsa.
Rungume shi Yaya Qasim yayi tare da sakin wani irin kuka wanda duk wani mai sauraro ko mai gani yaji ko ya gani dole zuciyarsa ta raunana more especially da ya kasance namiji ne ke kukan, namijin ma irin Yaya Qasim da ya kasance mutum mai juriya da tawakkali.

Har lokacin Yaya khalil bai samu damar zubar da 'kwalla ba ko da kuwa 'digo 'daya ce, bai hana Yaya Qasim 'din kukan ba saboda shima kansa zuciyarsa ta gama raunana har hawayensa sun 'kafe, tsawon mintuna goma suka kwashe suna rungume da juna tukun Yata Qasim ya saki Yaya Khalil yana aika masa wani irin kallo da ke nuna bu'katar 'karin bayani.
"Da gaske shikenan mun rasa shi?, kace min ba haka bane Khalil!" Ya fa'da a matu'kar raunane.
Rasa wace irin amsa zai bashi yayi hakan yasa ya ke'be shi zai wuce. A matu'kar zafafe Yaya Qasim ya cakumo Yaya Khalil 'din.

"Ya za ka wuce ba ka bani amsa ba, ka fa'da min meye gaskiyar batun!" Ya fa'da cikin zafin rai "I can't afford to lose suck brother Khalil, ka ce abun da na gani ba haka bane!" Ya fada cikin raunin murya.
Ganin yana shirin tara jama'a shi kuma ba ya so a ji mutuwar sarki a bakinsa yasa ya bu'de baki murya 'kasa-'kasa yace
"It's all true Akhy, Yaya mun rasa 'dan'uwanmu da gaske....."
Ba tare da ya 'karasa ba ya zame jikinsa zai koma mota sai dai me? Ganin su Hajjaty da wasu daga family members 'din yasa ya 'dan tsaya yana kallonsu.

Muryar Hajjaty ce ta doki kunnensa
"Ban gane me kuke magana a kai ba Halilu,waye aka rasa kuma meyasa Qasim ke kuka? Me ya faru ku bani amsa!" Ta fa'da cikin sigar tsorata don ba shakka da za a gwada bugun zuciyarta a lokacin to tabbas ya tsananta.

Ajiyar zuciya Yaya Khalil ya sau'ke ganin convoy na motocin iyayensu sun shigo. Juyawa yayi ba tare da ya motsa daga yadda yake ba yayin da su kuma gabansu ya yanke da juyawarsa ba tare da ya amsa tambayar Hajjaty ba. A tsanake suka fito fuskarsu kame kamar ba abunda ke damunsu, sai dai fuskar Papa da Alhaji Babba ba ta iya 'boye yanayin da suke ciki. Haka suka tunkaro part 'din Hajjatyn a jere, abun da ya 'daurewa Hajjaty kai shine babu wanda yayi magana, ganin hakan yasa Alhaji Baba da ya kasa furta komai bayan bugun zuciyarsa da yake saurara ya ce
"Mu shiga ciki"

Babu musu suka bi bayansa kowa ya koma, a matu'kar tsorace kowa yake ta yadda za ka fahimci hakan parlourn ya koma kamar wani graveyard ko sautin numfarfashinsu ba a ji yayin da kowa idanuwansa ke 'kasa.

Cike da dakiya Daddy ya yi sallama, bayan sun amsa ya fara jawabi.
"Kamar yadda muka sani duk abunda ya faru da bawa mu'kaddari ne daga mahaliccinsa, ita 'kaddara kan zowa kowa ta fuskoki mabanbanta, kada mu mance duk abunda ya faru da bawa to a rubuce yake cikin zanen rayuwarsa, babu yadda kuma bawa zai yi ya tsallake abunda ubangiji ya gindaya a kansa."

Shiru yayi yayin da zuciyarsa ke wani irin bugu, cike da danne emotions nasa ya bu'de baki zi ci gaba, ku kiyasta cewa ku ne a wannan mataki kuke jiran jin me Daddy zai fa'da, kamar haka su ma mutanen da ke zaune a parlourn suka shiga hali irin na ru'du musamman wa'danda ba su san me yake faruwa ba.

"Ubaniji shi ke da ikon busa mana numfashi haka kuma yana da damar ya tsayar da shi a lokacin da yaso saboda cikar wa'adin numfashin da ya rubuta za mu yi tsawon rayuwarmu! Ubangiji kan 'dauki ran wani daga cikin mutane ba don ba ya son sa ba, kamar yadda ya 'dauke ran habibinsa kuma shugabanmu Annabi muhammad, zai iya 'daukar kowa duk kuwa yadda mutane ke tsananin sonsa, ko da kuwa duk duniya za su sadaukar da numfashin su saboda wannan rai 'daya, ubangiji ba zai dakatar da 'kudurinsa ba."

Shiru ya kuma yi, i zuwa wannan lokaci hankalin duk wani mazaunin parlourn ya kai ga 'kololuwar tashi yayin da masu raunin cikinsu suke share hawaye saboda zukatansu ba za su iya 'daukar wannan al'amari ba.

*React and share please*


[1/22, 4:40 PM] Diamond Bhatool:











*🏡A BABBAN GIDA🏡*
*TAKUN ƘARSHE*
*©Diamond Bhatool*

















*💎💍ELITE DIAMOND WRITERS💍💎*
_Where diamonds shine, words ignite_





_Wattpad: @diamond_bhatool_
_Arewabooks: @diamondbhatool3_
Please follow





*PAGE* 3️⃣1️⃣




Shi kansa Daddy a wannan ga'bar jarumtarsa ta kusa gushewa, muryarsa na rawa ya ci gaba da magana.

"Na san kun 'kosa ku ji meyasa nake wannan dogon sharhi, ina so ku dubi maganganu na ku musu kyakkyawar fahimta, ku yi imani da 'kaddara mai kyau ko akasin haka, ku amshe ta hannu biyu kada ku yiwa ubangiji butulci."

Hajjaty da zuwa yanzu jikinta ke karkarwa ga yadda zuciyarta ta yanke tace
"Muna sauraronka Umar, ka fa'da mana me yake faruwa."

Murmushin da na kasa fahimtar na meye Daddy yayi, shi ka'dai yasan yadda zuciyarsa ke yi. Daurewa yayi yace.
"Tabbas mun yi babban rashi cikin wannan family, mun tafka rashi wanda in mun kar'ba da hannu biyu hala ubangiji ya kawo mana kwatankwanci."
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'una" gaba'daya parlourn ya 'dau salallami, wa'danda ba sa kuka ma tuni sun fara saboda yadda sa'kon rashi ya bugi zuciyarsutun kafin su ji wanene ma ya Rasu.

Shima Daddy sai da ya faki idanuwansu ya share 'kwallar da ta zubo masa.
"Ubangijin da ya ba mu Sadauki yau ya 'dauki abunsa sakamakon ha'darin jirgin sama da ya afku, a halin yanzu babu abunda yake bu'kata daga gare mu matsayin masoyansa face addu'a, babu shakka kowanne mai rai mamaci ne."
Yana gama rufe bakinsa Hajjaty ta sulale 'kasa sumammiya, Alhaji Baba kam hawaye ne kawai ke sintiri daga idanuwansa. Shikenan! Shikenan ya rasa jikansa mafi soyuwa gare shi?
Zahrah kuwa tun lokacin da kalaman Daddy na 'karshe suka doki kunnenta ta daina fahimtar komai, nan duniyar tafara juya mata, kafin kace me ita ma ta sulale 'kasa sumammiya.

Wa'danda suka zubda 'kwalla su godewa Allah atleast sun rage wani kashi na tarin damuwarsu, har wannan lokaci ko 'digon 'kwalla ba ta zubo daga idanuwansa ba, ra'da'din da yake ji ba zai misaltu ba saboda duk duniya babu wanda ya sha'ku da shi sama da shi, tun ba su da hankali suke tare har zuwa wannan lokaci amma mutuwa ta yi musu yankan 'kauna, a rikice ya nufi Hajjaty da idonsa ya fara kaiwa gare ta kafin ya juyo 'daya 'bangaren da Zahrah da kuma Nainarh ke yashe 'kasa, Ransu na shirin barin gangar jikinsu.

Alhaji Babba da kuma Papa wannan mutuwa ta kaf 'daya ta bugi zukatansu haka nan Abba da saura kawunnan mamacin, ba 'karamar dauriya Daddy yayi ba saboda ya kwantar musu da hankali don ba lallai a samu wanda ya kai shi jin ra'da'din rasa nagartaccen 'dan nasa ba. Ganin yadda wasu suka fara fita hayyacinsu yasa ya 'daga waya ya 'kira aka turo ambulance don tafiya da Hajjaty, Nainarh da kuma Zahrah wa'danda suke sume, bayan an wuce da su asibiti ne kowannensu ya koma 'bangarensa don gobe da sassafe suke sa ran wucewa takamaimai wurin da za a samu pieces na jirgin la'alla ko za a samu gawarsa, in ba a samu ba kuma sai a yi masa salatul ga'ib.

Tabbas wannan rana ta shiga tarihin wannan ahali musamman da suka tafka babban rashi wanda kai tsaye za mu iya 'kiransa da 'kaddararsu, shikenan fa ya tafi, babu wanda zai kuma kallonsa a wannan gida na duniya, Allah sarki rayuwa. Amma duk da haka ana sa masa ran dacewa ne saboda shaidar da ya samu. Mutuwarsa in sha Allah hutu ce, ba ya shiga ha'k'kin kowa, ba ya zaluntar kowa kuma tsakaninsa da mahallincinsa ma ana kyautata zaton kyakkyawar mu'amala ce, ya gama aikin alkhairi, da azumi a bakinsa wannan abu ya afka masa.

Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, ubangiji ya ji'kan Yaya Sadauki yasa aljanna ce makomarsa. Tabbas kowanne mai rai sai ya 'dan'dana mutuwa, ina wa'danda suka shagala da duniya? Kuna ganin irin wannan mutuwa bagtatan kuwa?, ga dai Yaya Sadaukin nan da safiyar Allah kakanninsa sun gana da shi, haka kuma Zahrah da take da rabo, ya yi wa matarsa sallama lafiya lau yanzu ga shi ana labarin mutuwarsa, ya zama tarihi kuma.

Ya kamata mu 'kara kyautata ala'karmu da mahalicci haka nan kuma da mutane, muna tuna mutuwa, muke sanya ta a agenda namu, mu sa a ranmu in mun wayi gari lafiya ba lallai mu yammace da ran mu ba, haka nan in mun kai yammaci mu sa a ranmu ba lallai mu kasance raye ba safiya ta gaba. Wannan zai 'kara sa mu 'kara kusantuwa ga mahaliccinmu. Allah yasa mu dace, wa'danda suka riga mu gidan gaskiya tun daga kan al'ummar farko zuwa yanzu muna ro'kom ubangiji ya musu rahama, idan tamu mutuwar ta zo ubangiji ya sa mu cika da imani.

Kafin 9:00pm tuni mutuwar ta zaga kowanne sa'ko na ahalin kama daga na cikin gida da wa'danda ke nesa da gidan, mutuwar da ta ratsa zukatan mutane da dama yayin da ta zama sulhu ga wasu, ta kuma zama abun farin ciki a zukatan wasu sai dai su ma kada su manta ba tabbata za su yi a doron duniyar ba.

Sosai ABATCHA ESTATE ya zama tamkar ma'kabarta, kowanne sashe shiru yake kowa na 'kara jimamin mutuwar yana hawaye irin na yankan 'kauna, ba iya ahalin gidan ba hatta ma'aikatan gidan sun matu'kar razana da mutuwar Yaya Sadauki, sun yi kuka tamkar wa'danda suka rasa wane sashe na jikinsu, kai dole ma su yi kukan don kuwa ba lallai Marigayi ya mu'amalance ka ba ka ji 'kaunarsa cikin ranka ba, yana da salon mutuntawa da iya mu'amala. Saboda yanayin Alhaji Baba yasa Daddy ya zauna a tare da shi, Yaya Khalil da kuma Hajiya Babba suka wuce asibitin don zama kusa da marasa lafiyan, sai a lokacin ne Humairah ta koma, a nan kuma Hajiya Babba ta san da cewa Mabrukan ma ashe tana nan.

Duk wanda ya farfa'do cikinsu da zarar ya tuna da event 'din da ya faru sai ya koma, haka dai wannan dare ya kasance ga wa'dannan mutane uku, sai dai kuma wa'danda ke jinyar sosai zukatansu suka fi raunana, gwanda Hajiya Babba ta zubarda hawaye, Yaya Khalil kam ba a magana illa iyaka dai idanuwansa sun sauya daga wa'dannan fararen zuwa jajaye kamar gauta ga kuma yadda suke masa zafi kamar ana hura wuta a ciki, zafin da suke masa kuma in za a kwatanta shi da wadda zuciyarsa ke yi ba a magana, jijiyoyin kansa sun fito ru'du-ru'du. A hakan idan Hajiya ta gama kukanta sai kuma ta hau masa nasiha. Addu'a kuwa daren ranar ya sha ta daga masoyansa.

Wannan dare dai ya yawaita tsayi tamkar an dakatar da tafiyar lokaci haka suke gani ko dan saboda kashi 98% nasu ba su rintsa bane,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login