Showing 111001 words to 114000 words out of 157517 words

Chapter 38 - A BABBAN GIDA 2

10 May 2025

5148

abunda take da niyya tayi sakamakon wani dunƙulallen abu da ya maƙale mata a maƙoshi, da ƙyar ta iya haɗiye abunda ya tsaya mata sannan tace "Hajjaty Ya Ishaq ya ce ba zai aure Ni ba, ya ce ya fasa aurena! Me na aikata masa Hajjaty?" Kawai sai ta fashe da wani matsanancin kuka tare da ƙara lafewa jikin Hajjatyn, sai da tayi mai isarta kafin Hajjaty ta fara magana "Ya isa haka Zahrah, yi shiru maza, farin ciki ba zai taɓa gushewa daga inuwarki ba, ki kaddara duk abunda ya faru da bawa muƙaddari ne daga Allah....

*React and share*


Diamond 💎 Bhatool 🦋
*Follow my whatsapp channel fisabilillah:*

https://whatsapp.com/channel/0029VanUFkw5kg7G2ci16o2X











*🏡A BABBAN GIDA🏡*
*TAKUN ƘARSHE*
*©Diamond Bhatool*














_Wattpad: @diamond_bhatool_
_Arewabooks: @diamondbhatool3_
Please follow





*PAGE* 5⃣3️⃣




Gabaɗaya tsit parlourn kasancewar babu wanda ya san da faruwar wannan al'amari, ita manta Hajjaty ba ta samu lokacin magantuwa da Alhaji Baba ba, sai dai a tsattsaye ya ce mata ba da Ishaq ɗin aka ɗaura ba amma an ɗaura da wanda ya fi shi cancanta.

"Zahrah" Hajjaty ta ƙira sunanta "Kada ki sanya damuwarsa a ranki, ki sa a ranki cewa Allah ya musanya miki da mafificinsa, ki yi haƙuri kin ji?"
Ba tare da ta fahimci abunda Hajjatyn ke nufi ba ta gyaɗa kai sai dai tambayar da Mommah ta jefawa Hajjaty yasa Zahrah ɗagowa tana kallon Mommahn
"Amma dai wannan yaro Allah ya yi mutumin banza, to yanzu kenan ita ba a ɗaura nata auren ba."
Murmusawa Hajjaty tayi tare da faɗin "A'a Sughrah, kin san ai a ko'ina na Allah ba sa ƙarewa, wallahi yau da mun ji kunya sosai, to duk da dai ba komai suka faɗa min ba Alhaji yace an ɗaura da wanda yafi shi Ishaq ɗin cancanta."

Cike da tausayawa Mommah tace "To Allah rufa asiri, amma dai yaron bai kyauta ba, kina ji Zahrah, ki manta da shi kawai, ki gode Allah ma da ba a yi auren ba don ba a san me zai faru ba in da an yi, sai dai kuma Allah ya tsayar ya sa aka san halinsa."

"Haka ne kam Hajiya Sughrah, kin san Allah yaron nan a fuska kamar ba zai yi ba, amma ke ɗin Zahrah ta ina kika sani?" Hajiya Babba ta tambaye ta. Wani irin takaici ta haɗiye tare da faɗin "Saƙo ya tura min ta WhatsApp " daga haka ta kwanta tana tunano abubuwan da ya tura mata wanda ko giyar wake ta sha ba za ta baro wani nata ya kalla ba. Lumshe idanunta tayi tare da gyara kwanciyarta, ba a daɗe ba bacci ya ɗauke ta, su Mommah suka wuce ɓangarensu.

*THE BRIDES*

Ba sai na ce komai ba, duk da cewa suna cikin fargaban halin da ƴar'uwarsu ke ciki amma wannan dare ya kasance na musamman gare su, a wannan dare dukkansu suka zama cikakkun mata.

A cikin wannan daren ne kuma Nasreen tayi kwanan zaune musamman da ta tuna cewa ita kaɗai ce yanzu ba ta da aure cikin sa'anninta, ga kuma damuwar halin da Zahrah ke ciki wanda ba ta so aka ɗaura wannan auren nasu da ta fara hango ƙalubale a cikinsa, ta san dole dalilin wannan Ya Ishaq ɗin ne ƴar'uwarta ta shiga wannan hali, hakan ne ma yasa wata ƙiyayya da jin haushinsa suka ɗarsu a ranta.

Duk yadda taso ta runtsa hakan bai yiwu ba saboda tunaninsa da ya hana ta sakat, Ganin tunani babu inda zai kai ta yasa ta miƙe tana jera salloli har bacci ya ɗauke ta kan praying mat ɗin.

Haka zalika a wannan dare DEVILS KLANS 😈 suka gabatar da ganawa tsakaninsu. Tattaunawar da mafi akasari ta ta'allaƙa da hidimar bikin da aka yi a cikin dangin, Magajiyar uwargijiya da burinta ya gama cika ta sadaukar da baƙaƙen karnuka, bayan sun sha jininsu ta alƙawaranta musu cewa da zarar ta auri muradinta za ta ninka musu adadin karnukan tare da jinin bil'adama guda. A ƙarshen meeting ɗin nasu kuma sun so gano wani abu cikin allon tsafinsu amma abun ya faskara, gabatowar alfijir yasa suka ɗaga tattaunar zuwa washegari.

*WASHEGARI*

Jama'a da suka halacci bikin daga nesa suka fara shirin komawa gidajensu, sassafe kuma Hajjaty ta sa Nasreen fitowa ta taya Laraba yin breakfast ɗin da za a kai wa amaren, bayan sun gama tayi wanka za ta miƙa Zahrah tace za ta je tunda itama ba ta san gidajen nasu ba, babu yadda Hajjaty ta iya haka ta bar ta ta fito duk da akwai igiyar auren Ya Sadauki a kanta wanda ba su san komai game da hakan ba.

Gidan Ya Khalil suka fara zuwa sai dai ga mamakinsu ko tashi basu yi ba, sun danna door bell ya fi sau shida amma shiru har suka fara tunanin ko babu kowa ne a gidan, suna shirin juyawa Ya Khalil ya buɗe entrance door ɗin, ganin Nasreen yasa ya haɗe girar sama da ƙasa tare da faɗin "Ke lafiya za ki wani zo gidan mutane sassafe?" Sanin halinsa yasa suka kunshe dariyar da ke cinsu, Zahrah tace "Yaya Hajjaty ce tace a kawo muku breakfast, fatan kun tashi lafiya." Kallon da ya aiko musu yana faɗin "Da ba lafiya ba kya ganni? Oya ku ajiye basket ɗin ku ɓace."

Dariyar da Zahrah ke dannewa ne ta kufce mata hakan yasa ta ajiye basket ɗin hannunta tare da juya baya tana sakin dariyar sai kuma suka fara takawa, daidai yadda Ya Khalil zai iya jiyota tace "a gaida mana amaryar Yaya" daga haka suka fara sauri tare da wucewa suka bar shi yana kallon su duka biyun cike da tausayawa musamman Zahrah da ba ta san an ɗaura aurenta da wani ba, sosai abun ya ba shi haushi, Allah ya taimaki Ishaq ɗin nan ya fito suna tare da ƙawayensa abun ya faru da babu shakka sai ya san ya taɓa kimar ƴar dangi. Ajiyar zuciya ya saki tare da murmusawa sannan ya ɗauki Basket ɗin zuwa cikin gidan, tare da rufe ƙofar.

Daga gidan Ya Khalil suka nufi gidan Ya Taj, shima dai hana su shiga yayi ya tare mashigar gidan, haka suka nufi gidan Ya Auwab suna mitar hala an yi abun siyasa suka hana su shiga, ƙarshe dai Zahrah tace "tsoro suke muga jiƙaƙƙe kuma ɗanyen aikin da suka aikata."
Kamar yadda suka yi tunani haka sauran gidajen suma dai ba a bar su sun shiga ba.

Ko da suka koma Zahrah bajewa tayi kan sofa don kuwa sosai ta gaji da ɗan kewayen da suka yi, hakan yasa Nasreen saka ta gaba da mita. A nan suka ƙarashe zamansu can Nasreen tace wa Zahrah tana son magana da ita, hakan yasa suka wuce ZAHRAH'S bedroom.

"Kin ce za mu yi magana, what's up?"
"Ke Dilla ki nutsu, akwai abunda nake so mu yi magana yau ɗin nan." Giving her full attention Zahrah tace "I'm all ears"
"Yauwah Sister, za ki iya tuna wasu moments da nake shiga damuwa a baya?"
"I guess yes! Akan soyayya ko?"
"E sister, kin san me? A yanzu zan iya sanar da ke komai..."

"Tun ranar da muka haɗu da Ya Ishaq ɗinki a shopping mall, kin tuna?" Kai Zahrah ta gyaɗa Nasreen ta ci gaba "Tun wannan ranar na fara sonsa sai dai na ɓoye hakan ne a tunani na zai furta min kalmar so kafin Ni, ashe abun da ban sani ba ya riga ya mace kan soyayyarki. Tunawa da irin gwagwarmayar rayuwa da kika sha yasa na fara ɓoye hakan na san tabbas kika gano cewa ina son sa za ki iya sacrificing nasa ma Ni, abunda ba zan so ba, na raba ki da shi bayan kema alamu sun nuna kina son sa."

"A haka dai duk ƙoƙarina na ganin na danne hakan amma abun ya faskara don ba ƙaramar ƙauna nake masa ba, ba na so cikinku wata ta fahimci hakan yasa duk lokacin da muke tare nake ƙoƙarin ganin na ɓoye baku fahimci komai ba, sai dai zuciya....shaiɗan ba za su bar Ni ba kullum cikin kissima mun abubuwa marasa kyau suke yi wanda dalilin haka yasa nake ja gefe daga wurinki."

"Zahrah, da zuciyata da ruhina nake ƙaunar Ya Ishaq, amma ƙaunar da nake masa ba irin wacce yake miki bane, hakan yasa kishi ke shirin kashe Ni ga shi kuma har an sa muku rana da shi, a wannan lokacin ne na tabbatar da cewa Ya Ishaq ya min rata, irin ratar da ba zan iya cinmasa ba, hakan yasa na fauwalar da al'amarin ga mahaliccina na koyi tsayuwar dare wacce tayi aiki sosai game da hakan, a ranar da na fara fuskantar akwai damuwa a tsakaninku na ji babu daɗi, na cigaba da kwantar miki da hankali saboda Ya Ishaq a tunani na miji ne da ba zan so ki rasa shi ba, na kuma ajiye hakan matsayin misunderstanding amma da naga abun ya yi yawa yasa na ƙara dagewa da sallar dare ina roƙar miki da Ni mafi alkhairi. Wallahi Zahrah rashin aurensa alheri ne gareki, kuma ina fatan ki yi farin ciki da angon da aka aura miki."

"Na ji Yaya Khalil yana sanar da Hajiya Babba irin cin fuskar da Ya Ishaq yayi wurin ɗaurin auren ku, hakan yasa na nemi soyayyar da nake masa na rasa saboda na san ya yi breaking heart ɗinki, Zahrah ki yi haƙuri, na so abunda kike so, amma ki gafarta mini..."
Hugging nata Zahrah tayi tare da faɗin "Worry not dear, wallahi ban taɓa jin son Ya Ishaq a raina ba sai dai kuma halaccin da ya yi min yasa ba zan ƙi shi ba, me yasa kika ɓoye min cewa kina son sa? Wallahi da na sani da tun lokacin ba zan bar zuciyar ƴar'uwata ta shiga garari ba, ki yi haƙuri Sister da ban iya gano abun da kike so na samar miki da shi ba, ki yi..."

"Ki daina ba Ni haƙuri sister" Nasreen ta dakatar da ita "Ni ya kamata na baki haƙuri, amma wallahi a yanzu ba na jin sonsa ko ɗiso a zuciyata tunda ya wulaƙanta jinina."

"Sai dai, kin fuskanci wani abu kuwa Zahrah?"
"Wani abu kamar ya Nasreen?"
"Ina ji ba haka kawai ya Ishaq ya bar ki ba, akwai wani abu da ke faruwa wanda ba mu sani ba."
Numfashi Zahrah ta sauƙe tana faɗin "Babu komai da Sister, Allah bai ƙadarta shi ɗin mijin aurena ba ne, ga shi mijina ya bayyana a lokacin da Ubangiji ya so?"
"Uhm" Nasreen ta faɗa tare da riko hannun Zahrah ta damƙe "Get something please, wallahi Jiya wani mafarki nayi, Allah kuwa duk yadda aka yi wani siddabarun aka yi, kuma kin san meye? Shekaranjiya wallahi na gan shi a estate ɗin nan sun shiga Mota da wata amma ban ga fuskar ta ba, Zahrah."

Kai kawai ta jinjina tana faɗin "ina jin ki"
Ƙasa-ƙasa da murya Nasreen tayi tare da faɗin "Wallahi Zahrah akwai abunda na gani a estate ɗin nan ya razanar da Ni, na rasa wa zan tunkara da batun amma na san ƙaryata Ni za a yi, ban sani ba ko wanda zan tunkara yana ciki ya hallaka Ni."
Dum! Gaban Zahrah ya buga,
"Sister wallahi akwai matsafa a gidan nan." Ta raɗa mata a kunne. "Ban San wa zan sanarwa ba amma batun da naji kuma na gani yasa nake son sanar da wani babba a ɓoye saboda a ɗau mataki kan su gama da mu gabaɗaya."

Jikin Zahrah sanyi yayi itama ta jawo kunnen Nasreen ta raɗa mata cewa "Nima na sha gani, lokacin da nake shirin sanar da Ya Sadauki sai Allah ya karɓi abunsa."
"To yanzu ya kenan?" Nasreen ta tambaya
"Kawai abunda za a yi, mu bari hankulan kowa ya dawo kansa sai mu sanar da Yaya Khalil, na san cewa zai fahimce mu."
Nasreen tace "A'a, kin san halinsa, ina laifin Ya Junaid? Ya fi shi sauƙin kai"
"Ke kin san shi fa rayuwar Turai za ta iya sawa yaƙi aminta da mu?"

"Zahrah! Zahrah!"
Ƙiran sunan Zahrah da Hajjaty ke yi yasa ta amsa da "Na'am"
"Ku zo ku yi breakfast ki sha maganin ki ko?"
"To Hajjaty ga mu nan zuwa" daga haka suka ajiye zancen da suke suka nufi dining area.

*11:32am*

Sallamar jigon wannan ahali, Alhaji Baba, Alhaji Babba, da sauran yan'uwansa suka doka sallama zuwa parlourn Hajjatyn. Bayanan gaisa kamar ko yaushe Alhaji Baba ya tambayi Zahrah......


*React and share fisabilillah*

Diamond 💎 Bhatool 🦋
*Follow my whatsapp channel fisabilillah:*

https://whatsapp.com/channel/0029VanUFkw5kg7G2ci16o2X











*🏡A BABBAN GIDA🏡*
*TAKUN ƘARSHE*
*©Diamond Bhatool*














_Wattpad: @diamond_bhatool_
_Arewabooks: @diamondbhatool3_
Please follow





*PAGE* 5⃣4️⃣





Mamah da kanta ta miƙe don kiran Zahrah, kafin ta dawo ne Hajjaty ke sanar da Alhaji Baba kwanciyar Zahrah a asibiti. Sosai ya ji tausayin Zahrah ya kuma yi mata ya jiki bayan sun zo ita da Mamah, haka sauran uncles nata ma. Bayan nan Alhaji Baba ya fara magana Tare Da ƙiran sunan Zahrah
"Kina ji na ko?"
Kanta ƙasa ta amsa da "Eh"
Wa'azi mai ratsa jiki Alhaji yayi a tunaninsa ba ta san ba Ya Ishaq ne mijinta ba kafin ya ɗaura da faɗin
"Allah bai yi yaron nan Ishaq shi ba ne mijiki ba, hakan kuma ba don Allah ba ya son ki ba ne sai dai ya kamata ki fahimci cewa kowanne bawa yana samun abunda Allah ya rubuta zai samu, ki rubuta wa zuciyar ki cewa can Dama Ubangiji bai ƙadarta aure tsakaninku ba, saboda haka Allah ya musanya miki da wanda ya fi shi. Zan so na sanar da ke da kuma iyayenki ko wanene mijin amma sai zuwa jibi bisa alfarmar da miji ya roƙa daga gare mu kenan."

"Ki ƙara haƙuri Zahrah, sannan kuma lefen da suka kawo ya kamata a mayar musu Hajiya domin fita daga Hakkinsu"
Hajjaty ta amsa da "Toh, in sha Allahu da Yamma za a mayar musu kamar yadda kace."

"Yauwah, Zahrah'u, ki ci gaba da addu'a kin ji, in sha Allahu alkhairi yana dab da zuwa gare ki, Allah ya miki albarka." Kanta ƙasa ta amsa da "Amin na gode Alhaji."
"Je ki abunki, shikenan." Daga haka Zahrah ta miƙe zuwa bedroom ɗinta.

Bayan fitar su Alhaji Baba, Hajjaty ta sa Laraba ɗaura lunch har da na amaren kamar yadda aka musu breakfast. Ƴan biki kuwa yawanci sun watse, Aunty Madina dai tana part ɗin Aunty Salmah da yake suna having good time da ita, da rana aka kai wa amaren abinci, haka dare ma.

*Yaya Ishaq*

Shigowar Mom ɗakin da yanayin da ta Riske shi yasa ta ƙara tabbatarwa kanta zargin da take kan sa, gudun kada hankulan ƴan biki ya kai kansu yasa ta ƙira Ayuba gateman ya fito da Ya Ishaq ɗin ta ƙofar ɗakinsa ta baya zuwa part ɗin Dad kamar wani gawa. Sosai hankulan Iyayen ya tashi ganin yanayinsa, Dad kam ya manta ma da furucin sa na ya sallama shi haka ya sa shi a mota zuwa asibiti tare da Mom. Sai da suka isa tukun Mom ta sanar da Mommy Salaha cewa ba sa gidan sun tafi kai ango asibiti ta kula da komai. Ganin shiru shiru har maghrib ba a kawo amarya ba kamar yadda a al'adance ake yi yasa Mommy Salaha kiran Mom ta sanar da ita, Mom kam amsa kawai ta ba ta da ta kula da hakan. Dama kun san akwai qaɗanda tsegumi ne ya kawo su musamman da suka ji cewa jikar Abatcha Ishaq ɗin zai aura, wasu kam ma ba a mutunci da su amma haka suka wanko ƙafafh don gulmar da ke cinsu suka zo. Ita dai Mommy Salaha amsa kawai ta basu da faɗin "Amarya an wuce da ita gidanta bisa al'adar gidansu, sai dare miji zai kawo ta gidansu da kansa." Sosai suka sha jinin jikinsu kafin kace me duk an watse.

Hakan ne yasa Mommy Salaha kiran Mom don jin ina suke, bayan sun gama tattare wa ta wuce asibitin. Yanayin da ta Riski Ya Ishaq yasa ta kalli Mom tace "Wannan abun nasa ai ya yi kama da irin na Nihla ɗiyar wajen Aminan KD, ko ba ki fahimci hakan ba?"
"Ƙwarai Kuwa Aunty, sai da kika faɗa, yanzu ya kenan?"
Numfashi Mommy Salaha ta sauƙe kana tace "The only solution shine mu wuce gidan Imam Nasir, don Jiya Fadhil ya ce min sun je gidansa hana gari, kafin lokaci ya ƙure kawai mu je."

Da wannan shawarar Mom suka wuce gidan Imam Nasir wanda babban malamin addini ne wanda ya shahara a Nigeria da kewaye, masani ne sosai game da lafiya ga kuma zunzurutun ilimin addini da yake da shi. A lokacin kuwa da suka isa sun ci Sa'a yana nan, da yake Dad ya san shi yasa ba su sha wahala ba yace da Dad ya mayar da su Mom gida shi sai ya dawo a yi komai gabansa. Daga haka kuma ya cika umarnin Imam Nasir ya mayar da su ba don sun so ba shi kuma ya dawo. A daren sosai aka yi artabu da shaiɗanun da aka tura zuwa jikin Ya Ishaq ɗin, sun kuma yi magana cewa tura su aka yi, ba su da ikon fita sai da izinin shugabansu, amma dai kafin nan za su sanar da Imam wani sirri game da zuwan nasu.

"Imam! Ka dakata ka ji, mu ba mu da laifi don haka ka daina hukunta mu, Magajiya ce ta sa mu wannan aiki, mun kuma riga mun kammala amma tace akwai ci gaba yasa ba mu tafi ba."
"Waye Magajiya? Kuma wane aiki ta sa ku?"
"Ah ah, ba sai ka ji ba saboda ina guje maka faɗawa tarkonta, aikin da ta saka mu shine gusar da hankalinsa daga auren

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login