Showing 87001 words to 90000 words out of 157517 words
shigo sai da ya tabbatar babu wani majiɓancin ta, dariyar ƙeta yayi tare da shirin ci gaba da abun da yayi niyya, babu zato babu tsammani yaji an buga masa ƙatoton ice a baya, ai babu shiri ya saki Little Sadauki, ba kowa bane ya ƙwala wannan ice sai Zahrah wacce shigowarta kenan taji kururuwar Aunty Mabruka, kafin Little ya ƙarasa ƙasa tuni ta cafke shi, da mugun hanzar Aunty Mabruka ta ƙaraso inda suke tana sharar ƙwalla don ta riga ta cire tsammani sai ga Allah ya aiko mai taimako.
Ganin hankalinsu ya ɗan bar kansu yasa mutumin ko matar ya saluɓe ya fice ita dai Zahrah sai faman jijjiga shi take, tsawon mintuna goma sha bakwai yana kukan ya ƙi yayi shiru saboda yadda ya tsorata shima. Bayan Aunty Mabruka ta ɗauraye jikinta ta sanya kaya ta karɓe shi don ta ba shi nono ya sha ko zai yi shiru amma ya ma ƙi kama nonon.
A matuƙar razane Mamah ta shigo part ɗin Hajjaty saboda yadda kukan Little Sadauki ke amsa ƙuwwa, tana isa ta tarar da shi hannun uwarsa ta tambaya ko lafiya? Aunty Mabruka ta buɗe baki za ta yi magana taji an raɗa mata magana cikin kunnenta sai dai da ta waiga babu kowa sai Mamah da ke jiran amsar ta, a ɗan kiɗime ta ƙara buɗe baki a karo na biyu za ta yi magana taji an kuma ce mata “Kul kika labrtawa wani abun da ya faru idan ba haka ba da ke da shi duk ba za ku rayu ba.”
“Lafiya kuwa Mabruka, ina tambayarki kin yi shiru?”
Cikin kame-kame tace “E Mamah lafiya fa, ina ga tsantsar gajiya ta sa yake wannan uban kukan, amma ina ga yanzu zai iya komawa.”
Ba tare da Mamah ta yadda ba ta ce “To shikenan, kawo shi nan na jijjiga shi ko zai yi baccin.” da haka Mamah ta wuce da Little sdauki zuwa bedroom ɗin Hajjaty ta kai wa Alhaji Baba shi, abun mamaki kuma yana karɓanshi yayi tsit kamar ba shi ba.
Bayan tafiyar Mamah still aka ƙara raɗawa Aunty Mabruka magana a kunne a matuƙar firgice ta miƙe za ta fice daga ɗakin kawai taji mutum ya mata katanga.
“Ina kike tunanin zuwa eye tsinanniyar?”
A matuƙar zabure ta ɗago jin Muryar da ba ta yi tsammanin ji ba, ta buɗe baki za ta yi magana kenan ta saɓule abinda ta rufe jikinta da fuskarta.
*React and share fisabilillah.*
https://whatsapp.com/channel/0029VanUFkw5kg7G2ci16o2X
*🏡A BABBAN GIDA🏡*
*TAKUN ƘARSHE*
*©Diamond Bhatool*
*💎💍ELITE DIAMOND WRITERS💍💎*
_Where diamonds shine, words ignite_
_Wattpad: @diamond_bhatool_
_Arewabooks: @diamondbhatool3_
Please follow
*PAGE* 4️⃣0️⃣
﷽
Tashin hankali wai ba a sa masa date, idan akwai abun da yafi tashin hankali a duniyar nan to Aunty Mabruka ta shige shi, ta buɗe baki za ta yi magana ta dakatar da ita.
“Kina mamaki ko? To ki daina, ki kuma kalle Ni da kyau Mabruka, don ina tabbatar miki tunda yaron nan ya tsira yanzu babu abun da zai hana Ni na hallaka ki da kai na, shi ma kuma ba wai na bar shi bane, zan dawo gareshi.”
Ba ta jira Aunty Mabruka ta ce komai ba ta kalli ƙofar ɗakin daga yadda take ta miƙa hannu ta tura ta, tsoro sosai ya kama Aunty Mabruka, ga shi ta gagara ko da ambaton sunan Ubangiji ne, fatan ta dai Allah ya kawo mata ɗauki. Dariya ta sheƙe da ita tana kallon Aunty Mabrukan lokaci guda siffarta ta sauya, haƙwarenta suka yi zaƙo-zaƙo haka faratunta kamar me saboda tsayi g su sun koma baƙaƙe ƙirin, gaba ɗaya dai siffarta babu kyan gani, sai a lokacin Aunty Mabruka ya fara ja baya tana jijjiga mata kai yayin da ita kuma take bin ta har ta isa bango.
Cike da rashin imani da tausayi ta ke biye da ita har ta kai jikin bango, wata irin dariyar shaƙiyyanci ta saki tana faɗin “Ina so kafin na sha jinin ki I mean kafin ki tafi wurin da mijinki ya tafi ki san Ni ɗin wace ce, saboda sanin hakan da za ki yi a yanzu ba shi da wani amfani.” Sai a wannan lokacin Aunty Mabruka tace “Kada ki kashe Ni, ina da burin inganta rayuwar ɗanmu, don Allah ki bar mu...”
“Ya isa haka Mabruka, kin riga kin makara, tun ranar da na haɗa makircin nan har maceccen mijinki ya shiga ɗakinki kafin ki yi aure naga buri na bai cika ba saboda ban samar da shaidar da za ta sa ku rarrabe ba, ban shiga damuwa ba sai da wancan tsinannen tsohon yace zai haɗa auren ku, duk iya yadda zan yi na tarwatsa hakan na gagara, ta ya kike tunanin zan bar ki ki rayu kuma? Na so dukiyar mijinki, kuma fansa na zo ɗauka cikin ahalin ku, ina tabbatar miki ɗaya bayan ɗaya sai na hallaka ku, kar ki manta da ga ke sai wannan tsohon banzan da ya tarwatsa min rayuwa...saura kuma ɗanki da ƙaddara ta sa ya zo duniyar, Ni nan zan shanye jininsa!!!” sai kuma ta sheƙe da wata mahaukaciyar dariya.
“Na roƙe ki da Allah ki bar rayuwarmu, ko ma me muka yi miki ba mu cancanci haka ba, kin san ba ki son mu me yasa kika shigo ahalinmu?”
“Fansa! Ɗaukar fansa ita ta shigo da Ni ahalinku kuma na yi alƙawarin sai na tarwatsa wannan Babban Gida da kuke ji da shi, sai na sa ya zama tamkar maƙabarta daga nan na tattare dukiyoyinku kana na maida wurin masarauta ta! Hhhh”
Tana gama dariyar ta tsaya cak sai kuma fuskarta ta koma baƙa tilik kamar gawayi, idanuwanta suka koma jajaye kamar gauta yayin da tsinin farcenta ya ƙara tsayi kamar na mashi. Duk irin roƙon da Aunty Mabruka take mata amma ina ba ta ji, burin ta kawai a wannan lokaci ta zuƙe jinin nan la'alla ta samu gamsuwa, faratanta na hannu ɗaya ta kafa a goshin Aunty Mabruka ɗayan hannun kuma ta zagaya da shi ta ƙeyarta tare da caka faratun, wani irin raɗaɗi da azaɓa ne suka ziyarci Aunty Mabruka sai dai babu damar yin kuka.
Wasu irin kalmomi take karantawa lokaci bayan lokaci kuma tana tanɗe baki “Awnn, so sweet, lallai jinin ku ba dai daɗi ba, tabbas zan shahara a Duniyar tsafi fiye da tunani na, ba zan ja aikin nan ba, zan gama shi da gaggawa na samu cikar buri,ba iya sarauniyar Devil's klans ba ta duniyar tsafi baki ɗaya.” tana faɗin haka ta hankaɗa Aunty Mabruka wacce ba ta iya magana, idanuwanta duk sun ƙafe, can dai ta fara sakin wani irin nishi, da ƙar ta furta sunan Allah daga haka kuma jikinta ya saki.
Ganin haka yasa ta kwashe da dariya tana ƙara duba jikinta, cikin wannan mummunan surar Tata ta buɗe bakinta wanda ke fitar da wani irin baƙin hayaƙi da ɗoyi tace “Na ƙosa na kaiwa tsohon farmaki amma sai na gama da ƙananan don kuwa da alamun nasa sai ya fi daɗin zuƙa.” tana gama faɗin haka ta lashe baki kana ta lulluɓe jikinta da wannan farin ƙyallen, lokaci guda kuma ta ɓace ɓat kamar ba a halicci Mutum a wurin ba.
Hajiya Babba ce ta shigo part ɗin Hajjaty hannunta riƙe da food flask ɗin da ta gama dafawa Aunty Mabruka pepper soup 🍲 sauri take ta kai mata tunda babu kowa yau a part ɗinta Banda baƙi, tana shiga gabanta ya ɗan buga, ƙarasawa tayi sai da ta shiga bedroom ɗin Hajjaty don tunaninta ma Aunty Mabruka ɗin na can, bayan ta tarar ba ta can sai ta nufi bedroom ɗin Mamah don ta kai mata ta koma.
Labule ta buɗe tare da sallama a bakinta, baki uku tana sallamar amma ba a amsawa ga bulb ɗin ɗakin a kashe alamar ba kowa, hakan yasa ta koma bedroom ɗin Hajjaty ta tambayi Mamah, Mamah tace “Muje naga, wataƙila ma tana ciki baccin asarar ya ɗauke ta kin san yanzu gabaɗaya ba ta haske.”
Mamah na gaba Hajiya Babba na biye da ita baya har suka isa.
Mamah ce ta shige Hajiya Babba kuma ta tsaya waje har sai da taga an kunna haske ta shiga. Innalillahi wa'inna ilaihi raji'una! Abun da Mamah ta gani ne ya ɗan tsoratarta amma sai zuciyarta ta kwantar mata da hankali da faɗin “Mabruka uwar bacci” a zahiri kuma tace “Kin ganta nan kwance Hajiya Babba, dama dai yanzu kam Mabruka sai a hankali” ƙarasawa tayi gare ta tana taɓa ta tare da ambatar sunanta. “Mabruka! Mabruka!” shirin da ta ji yasa ta ɗan tsorata.
“Hajiya Babba ɗan taya Ni mu mayar da ita kan bed” Sanin dama yanzu tana irin wannan baccin yasa Hajiya Babba taimakawa Mamah don su ɗaga ta, abun ka da masu hankali sun san mutuwa ai, ko'ina na jikin Aunty Mabrukan ya riga ya sake ga kuma yadda fuskarta tayi fayau alamar dai babu lafiya. Cikin ƙarfin Hali Mamah tace “Anya kuwa lafiya, sai nake ga kamar babu isasshen jini a jikinta, kamar ma faɗuwa tayi fa ba kwanciya tayi ba.”
Nazartar Aunty Mabrukan Hajiya Babba tayi gabanta na tsananta faɗuwa, a dai iya fahimtar ta babu rai a jikin nan, haka yasa kai tsaye tace “Ni fa hasashe na sai nake ga kamar babu rai a jikinta”
Kallonta Mamah tayi tace “Habadai Hajiya Babba, kamar ba ki san baccin nata ba, bari na ƙira Zahrah ta zo mu miƙa ta asibiti don Mazan nan ba lallai mu samu kansu ba.”
Fita Mamah tayi daga ɗakin ta ɗauko wayar ta a parlour sannan ta dawo bayan ta ƙira Zahrah ta faɗa mata cewa ta zo ta miƙa su asibiti. Komawa ɗakin tayi sai dai me za ta gani? Hajiya Babban ma a yashe ta gan ta, nan gabanta ya faɗi, da sauri ta ƙarasa garesu, ai kuwa sai yanzu ta lura da Aunty Mabrukan da kyau, sam ko mahaukaci ne ya ganta ya san babu rai a jikinta.
“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'una ” Mamah ta fara furtawa sannan ta ƙara ɗaga wayarta, ta ma rasa wa za ta ƙira, lokaci guda ta fita hayyacinta, ba tare da ta sani ba hannunta ya dannawa Numbern Daddy ƙira, maganarsa da taji yasa ta ɗan dawo hankalinta, ko ta kan sallamar da Daddy yake ba ta bi ba tace “Yaya Babu lafiya....part ɗin Hajjaty ” ta faɗa a rarrabe, daga haka ta cilla wayarta gefe tana nanata innalillahi wa'inna ilaihi raji'una.
Zuwan Zahrah yasa ta miƙe tsaye, ɗauke da kallon mamaki Zahrah ke bin Mamah, can dai tayi ƙarfin halin faɗin “Lafiya Mamah?” Mamah ba ta iya ba ta amsa ba sai pointing Mommah da Aunty Mabruka da tayi, idanuwa waje Zahrah tace “What?, me ya same su?” daga haka ta ƙarasa kan Hajiya Babba tana mai riƙe hannunta, ajiyar zuciya ta sauƙe tana faɗin “Alhamdulillah, taya Ni mu ɗaga su Mamah, suna buƙatar kulawar asibiti.
Shigowar Daddy ne tayi sanadiyyar miƙewarsu tsaye gabaɗaynsu. Da sauri Mamah ta ƙarasa gabansa tana nuna masa Hajiya Babba da Aunty Mabruka, don zuwa yanzu magana dai ta fi ƙarfin ta. Da sauri ya ƙarasa zuwa gaban Aunty Mabruka, kallo ɗaya yayi mata ya tabbatar babu rai a gangar jikinta, cikin ransa ya fara furta Innalillahi wa'inna ilaihi raji'una kana yace da Mamah ta ƙoƙarta su fita da Hajiya Babba zuwa mota, shigowar Aunty Na'eemah zuwa wurin Aunty Mabruka yasa Daddy ya dube ta yace “Please help them take her in to the car outside.”
A kiɗime ita ma tayi kansu, da ƙyar suka iya ɗaga Hajiya Babba har zuwa mota. Lokacin da suka saka ta Daddy ya duba su duka biyun, ganin Zahrah ta ɗan fi nuna alamun hankali yasa ya tambaye ta “Can You drive?” Kai ta gyaɗa, hakan yasa yace “Ki wuce da ita asibiti, i'm on my way, ok?” daga haka ya koma a ɗan kiɗime, Numbern Mommah yayi dialling yace mata ta sake shi part ɗin Hajjaty.
Ba a jima ba sai ga ta kuwa, bai mata wani bayani ba yace “Mu je asibiti, ba zan iya driving ba” cike da fargaba ta amsa masa da to, daga haka ta ja shi zuwa asibin da Zahrah ta wuce da Hajiya Babba. Sai da suka isa tukun hankalinsa ya ɗan kwanta da aka sanar da shi ba mutuwa tayi ba. Nan ya baro Mommah a can yace in sun tashi komawa su taho da motar Zahrah.
Yana komawa can ya ƙara komawa,har lokacin kuma babu wanda ya shiga bedroom ɗin Mamah, Hajjaty da ta Ganshi cikin tashin hankali tace “Lafiya Umaru?” “Lafiya Hajjaty, zauna mana”
Zama tayi tana binsa da kallon mamaki tace “Ba lafiya ba Umaru.”
“Hajjaty kina gidan nan, ai yarinyar nan ce, Mabruka nazo dubawa, na ƙira Layinta ba ya tafiya.”
“Ai sai ka ce min na raka ka, bari na dubo ta, hala tana can tana baccin nta na asara tunda yaron yana wajen Alhaji.”
Itama dai abun da ta gani ta ɗaga mata hankali, amma kuma sai zuciyarta tayi wani ƙarfi a lokacin, fitowa tayi waje, ganinsa tsaye bakin ƙofar yasa ta dube shi tace. “Umaru ita ma ta rasu wallahi, Innalillahi wa'inna ilaihi raji'una, shigo ka gani wallahi babu rai a jikinta”
Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da bin bayan Hajjaty, dama ita ɗaya ce tunaninsa tunda ta yi tawakkali yasa ya ɗan yi mata nasiha, hawaye kawai take sharewa, nan yace ta koma can ɗakinta, zai ƙira ya sanar da kowa.
Kamar yadda ya faɗa haka kuwa ya ƙira ƴan uwansa ya fara da su, yana sanar musu ya ƙira wani ma'aikacin gidan TV yace don Allah ayi passing sanarwar jana'iza a estate ɗinsu. Daga nan kuma ya shiga group na family nan ma ya sanar.
Tabbas dukkan mai rai mamaci ne amma kuma abun ya so ya fara aure kan kowa, yaushe aka tashi daga wasan sunan? Abun da ko good one hour ba a yi ba amma yanzu a ce musu wai ta rasu?, ko dan Al'amarin Allah ya kere hakan, nan gabaɗaya family ya ɗauki batun mutuwar, kowa sai addu'a yake mata, shaida kam mai kyau ta samu, ba ta da abokin faɗa a rayuwarta coz irin mutanen nan ne da ba su shiga abun da bai shafe su ba, ba ta da rowa hatta ma'aikatan gidan sun san da haka, idan kaya ne haka za ta ɗinka kawai ta bi duk masu hidima da gidan ta raba musu tun lokacin da ta fara aiki. Allah Sarki, Allah yayi miki rahama Aunty Mabruka.
*React and share fisabilillah*
https://whatsapp.com/channel/0029VanUFkw5kg7G2ci16o2X
*🏡A BABBAN GIDA🏡*
*TAKUN ƘARSHE*
*©Diamond Bhatool*
*💎💍ELITE DIAMOND WRITERS💍💎*
_Where diamonds shine, words ignite_
_Wattpad: @diamond_bhatool_
_Arewabooks: @diamondbhatool3_
Please follow
*PAGE* 4️⃣1️⃣
﷽
*ZAHRAH*
Daga Mamah har Mommah babu wanda yace uffan, kowa dai da abun da yake saƙawa a zuciyarsa. Ganin Mamah ba za ta faɗa mata abun da ke faruwa ba yasa ta tambaye ta. A lokacin da ta sanar da ita abun da ke faruwa sai da ta kusa faɗuwa ita ma sai innalillahi wa'inna ilaihi raji'una take maimaitawa, babu shakka wannan mutuwa ta duka ta fiye ma da ta Late Yaya Sadauki, duka-duka yaushe ma Maghrib tayi aka watse daga taro amma yanzu ace Allah ya yi wa Aunty Mabruka rasuwa, “Gaskiya akwai lauje cikin naɗi, akwai abinda ke faruwa da ba mu da masaniya a kansa A BABBAN GIDA, amma mene ne?”
Zahrah dai cikin motarta ta koma tana alhinin irin wannan mutuwa da ake musu cikin ƙanƙanin lokaci, nan kuma ga jikin Alhaji Baba da shima yaƙi daɗi. Wani abu da ta tuna yasa ta dafe ƙirjinta, “matar ko mutumin da yayi attempting hallaka Little Sadauki!” ta faɗa a ranta. “Akwai wanda ke da alaƙa da mutuwar nan cikin gidan nan, lokaci yayi da zan fara aiki na, ƙarfin guiwar da na rasa a baya zan dawo da ita, Allah yayi maka rahama Yaya na, matar Yaya ke ma Allah yayi miki rahama, na rantse da Sarkin da ke bisa numfashi ko ma waye ke da hannu a wannan ta'asdanci da ake mana in har na gano shi ba zan sarara masa ba, su ma waɗannan matsafan da sannu zan gano su waye.”
Hannunta ta haɗe wuri guda tana ɗaga kanta sama tace “Ya Ubangiji ka bani nasara akan maƙiya da kuma magauta waɗanda ke bibiyar wannan ajalinsa sharri, Ubangiji na ka bani ƙwarin guiwar da zan tunkari kowanne mai nufin mu da sharri, ya Rabbi jini na da kuma rayuwata fansa ce a yanzu ga ahali na, Ubangiji ka ba Ni ikon gano wannan ɓoyayyen al'amarin da ke kewaye da BABBAN GIDA” hawayen fuskarta ta goge da handkerchief ɗin da yayi mata kyautarsa tun yana da rai kana ta sheƙi ƙamshinsa da har yanzu bai gushe daga jiki ba.
Idanuwanta ta lumshe tare da fitowa waje tunawa da tayi ba fa yi sallah ba, masallacin da ke cikin mosque ɗin ta nufa, daga nan tayi sallah tukun ta dawo wurin su Mamah waɗanda suka yi jugum. Allah da ya taimaka ma around 10pm aka sallame su, zuciyar Hajiya Babba a raunane suka koma gida,hawaye kuwa yayi ƙaura a idanuwanta, kuka ma ya ƙi zuwa sai dai na zuci wanda yafi ciwo.
Daren ranar ma dai wannan ahali da dama ba su rintsa ba, yayin da wasu kuma suke can suna murnar samun nasara da suka fara. Little Sadauki kuma a wurin Mamah ya kwana wacce ita da Hajiya Babba duk kwana tare da gasar, Washegari da misalin ƙarfe goma na safe aka kai Aunty Mabruka gidanta na gaskiya, Ubangiji