Showing 84001 words to 87000 words out of 157517 words
a ranar su Yaya Haidar suka diro Nigeria, sosai hankalinsa ya tashi da jin zancen rashin lafiyar Alhaji Baba, hakan yasa aka fara gyaran part ɗinsa da ke gidan, in two days aka gama komai suka koma, Baby Nihal ma dai school aka Nema mata saboda ba su da tabbacin komawa nan kusa.
Sosai jikin Aunty Mabruka ya ƙara tashi, tuburan ta zama kamar mahaukaciya, ba ta iya cin komai saboda duk abun da aka kawo mata sai tace jini ne ba za ta ci ba, sosai Mamah ke jinyarta, a hakan tana tofa mata addu'o'i sosai da abun zai fi haka munana. Safiyar yau kuwa da matsanancin ciwon ciki ta tashi tun daga bakin part ɗin Hajjaty za ku fara jiyo sautin gunjin kukanta, a matuƙar birkice Mamah ta aika Meerah ta ƙira mata Aunty Salmah da sauri, jin irin ƙiran yasa gaban Aunty Salmah fara bugawa kamar me, da sauri tazo, yanayin da ta riski Aunty Mabruka shi ya ƙara ɗaga mata Hankali, da sauri ta fito da motarta, da ƙyar su biyun suka iya fita da Aunty Mabruka wacce ke cikin wani irin yanayi.
Wani private hospital suka wuce da ita direct, bayan sun kwashi delivery set ɗin da aka tanada. suna isa midwives ɗin da ke aiki suka yo kanta suka wuce da ita kan stretcher, Babu jimawa suka fito hannunsu riƙe da takardar amincewa (consent Form), bayan bayanin da aka yi wa su Mamah na cewar ana buƙatar mijinta yayi signing form ɗin nan saboda a samu a shiga da ita theatre a cire yaron in ba haka ba ita da ɗan dukkan su za su iya rasa ransu. Mamah ce tayi ƙarfin halin faɗin “Allah ya yi wa mijinta rasuwa kusan watanni goma sha ɗaya kenan.”
Midwife ɗin tace “To Babu wani namiji, Baba ko Yaya gare ta?”
Aunty Salmah ta bata amsa da “Bari a ƙira yayanta”.
Few minutes da kiran Yaya Haidar sai ga shi ya iso a matuƙar firgice kana yayi signing form ɗin daga nan ya nemi wuri ya zauna, da ƙyar Mamah ta lallaɓa shi ya koma office nasa saboda da cewa yayi babu yadda zai ce sai ya ga an fito da ƙanwarsa lafiya.
Tsawon wasu Awanni aka buɗe ƙofar theatre room ɗin, miƙewa tsaye Mamah da Aunty Salmah suka yi ganin ma'aikata ne yasa suka ƙarasa garesu da sauri, placenta suka ba su sannan Ɗaya daga cikinsu tace: “an cire mata Baby boy, lafiyar yarin ƙalau ita ma zuwa jimawa za a fito da ita.” sai a lokacin suka samu relief kan yadda suke ji hakan yasa suka zauna shiru babu mai magana cikinsu. Can bayan wani lokaci aka Turo mace a stretcher, bayansu suka bi har zuwa bakin ɗakin daza a ajiye ta don ba ta post op care.
Sai da midwives ɗin suka gama gyara ta tsaf tukun ɗayarsu ta fito ɗauke da Babyn a hannunta. Kai tsaye wurin su Mamah ta nufa tana murmushi “Congratulations, it's a baby Boy from Madam Mabruka, Za ku iya ganinsa sai ku bani na mayar da shi jikin mahaifiyarsa.” Mamah ce ta amshi yaron bakinta ɗauke da bismillah, sai da ta tofa masa addu'o'in tsari tukun tayi murmushi tana faɗin “Ubangiji ya raya ka, ya sa ka zama abun alfahari ga duniya, suna matuƙar kama da uban lokacin yana yaro.” ta idasa tare da miƙawa Aunty Salmah, itama dai ta karɓe sa addu'ar tayi masa kana ta miƙawa Midwife ɗin babyn.
“Ya ita uwar? Za mu iya ganinta kuwa?”
Murmushi Midwife ɗin tayi tace “Yanzu dai ba lallai ta gane ku ba, ku bari zuwa jimawa, za ku iya zuwa gida ku taho da kayayyakin da za a buƙata.”
Nan Mamah da Aunty Madina suka koma gida, Iya Hajiya Babba da Mommah suka sanarwa zancen haihuwar sannan suka ɗinke bakinsu da kar su sanar da kowa. Daga haka suka wuce asibitin tare da Mommah.
A reception suka zauna can Mamah ta miƙe tare da fita, Numbern Hajjaty ta bugawa ƙira, bugu ɗaya ta ɗaga tana sallama. Bayan sun gaisa Mamah tace “Congrats Hajjaty....Mabruka ta haihu amma aiki aka mata, an cire mata ɗa namiji.”
“Kai ma sha Allah, Ubangiji ya raya shi, ki shafa min kan yaron kafin mu dawo, muma cikin satin nan la'alla za mu dawo.”
“To Hajjaty, Allah ya dawo da ku lafiya”
“Amin amin” Mamah ta ƙara da “Ki gaida min Alhji Baba da jikin” daga nan kuma suka yi sallama.
Ba a daɗe ba Midwife ta buƙaci su Mamah su bayar da kayan Aunty Mabruka, sai da ta gama tsaftace su ita da yaron a karo na biyu tukun ta ce da su Mamah za su iya shiga, har rige-rigen shiga ake tsakaninsu. Bayan sun shiga suka tarar da Babyn jikin uwarsa, Mommah ce ta fara ɗago shi tana mai zuba idanuwanta a kansa har ba ta san lokacin da hawaye ya fara zuba daga idanuwanta, akan fuskar hawayen nata ya ɗisa sai a lokacin ta farga da hakan, da sauri ta goge na jikin yaron kana ta goge idanuwanta tana murmushi tace.
“Kamar dai Aliyu na lokacin yana yaro, babu bambanci sak mahaifinsa, Ubangiji ya raya ka, ya ba wa mahaifiyarka lafiya.”
“Amin” suka amsa mata. Zamam ɗin aka ɓula sannan aka ɗisa a bakin babyn, mulai ya haɗiye, Mommah da kanta ta tauna dabino kana ta saka masa a baki, daga nan su ma suka ƙara kallon yaron.
A lokacin Aunty Salmah ta fara ɗaukar Baby a photo, tana gamawa ta ɗaura a status nata da caption ɗin “It's a baby Boy from Mabruka....Allah ya raya Little Sadauki.” sannan ta tura a family group, kafin kace me sai ƙiranta ake a yi confirming. Kafin ka ce me Maza da mata sun fara cincirindon zuwa ganin babyn Yaya Sadauki, duk wanda ya zo ya ga babyn dole ya zuba ƙwalla saboda yanayin da yaron ke yi da ubansa tun yana jariri.
Zahrah da kuma sauran ƴan'uwanta sun fito daga lectures sun haɗu a masjid don yin sallar la'asar daga nan su wuce gida, Kamar wasa ta kunna data, messages ne suka shigo ganin almost 1000+ messages a group ɗin family yasa gabanta faɗuwa, Allah yasa ba mutuwa aka yi ba, ta faɗa can ƙasan ranta. Sliding tayi zuwa wurin status, da na Aunty Salmah ta fara cin karo. Kamar a mafarki taga picture ɗin yaron, ba ta gama shiga ruɗu ba sai da ta ga caption ɗin, hawaye ne ya fara zarya akan fuskarta.
Nainarh ce ta farga da hawayen kan fuska Zahrah, ƙarasowa wurinta tayi tana tambayar me yake damunta?
Zahrah kam ba ta san da cewa Nainarh na wajen ba don zuciyarta ta kula zuwa wata duniyar. Ganin hakan yasa Nainarh leƙo kanta ga screen ɗin da Zahrah ta danne tana kalla, idanuwa waje ta jujjuya Zahrah, sai a lokacin ta san da existence ɗin Nainarh. Tana goge hawayen nata tana cillawa Nainarh harara tace
“Madam ya dai?” ba tare da Nainarh ta maida hankali ga tambayar Zahrah ba tace “Babyn waye kike kallo.?”
“Guess whose baby is that”
“I don't know, ta faɗa fuska a yamutse.”
Cike da zumuɗi tace “Yaya Sadauki's son....daga nan can muka yi ko?”
Sun manta a masallaci suke suka rungume juna har da ɗan ƙaramin ihun su. Zakiyya ce ta cilla musu wani kallo tana faɗin “Remember You guys a in the mosque Kun wani zo kun tayar da hayaniya.” Nainarh ce ta juyo tana rufe bakinta, a hankali tace “Sorry Ustazah, wallahi mun manta ne saboda tsantsan farin ciki”
Matsowa kusa da su tayi tace “Farin cikin lafiya? Yaya Khalil aka aura miki?”
*React and share Lilah*
https://whatsapp.com/channel/0029VanUFkw5kg7G2ci16o2X
*🏡A BABBAN GIDA🏡*
*TAKUN ƘARSHE*
*©Diamond Bhatool*
*💎💍ELITE DIAMOND WRITERS💍💎*
_Where diamonds shine, words ignite_
_Wattpad: @diamond_bhatool_
_Arewabooks: @diamondbhatool3_
Please follow
*PAGE* 3️⃣9️⃣
﷽
Harararta tayi tana faɗin “Ba ki da lafiya, magana ake ta babyn Yaya Sadauki da Aunty Mabruka ta haifa yau, ku samu ku yi sallah mu wuce.”
“Don Allah dai?” ta tambaya fuskarta ɗauke da mamaki.
Harararta Zahrah tayi tana faɗin “Sai kuma ki yi ai, wallahi da zarar su Nasreen sun isar za mu wuce, ki yi sallarki” harara ta ɗan cillawa Zahrah kana ta shiga sallah.
Zahrah ce ta fice waje tana jiransu jikin motarta, Numbern Aunty Salmah tayi dialling, bayan ta ɗaga ta tambaye ta “wane asibiti ne kuke Aunty Salmah?”
Tana faɗa mata ta katse kiran Wanda yayi daidai da fitowar su Nasreen. Kowacce su motarta ta shige suka tayar sai asibiti. Ko da suka isa suka tabbatarea idanunsu cewa Babyn Yaya Sadaukin ne da gaske zo ka ga murnar da suka shiga, Zahrah tunda ta ɗauke shi ta hana kowa karɓan yaron in Banda kallonsa Babu abinda take yi, ji take kamar wa ita aka haifa wa yaron, gani take kamar an maye mata gurbin Yayanta ne da little. Pictures kuwa yaro ya sha su kamar me har sai da Mamah ta fara fadan ya isa tukun Zahrah ta dakata.
Tun kafin su tafi ta sauya profile nata na kowanne media handle nata zuwa picture ɗin baby Boy ɗin daga nan kuma status nata ya cika da pics na yaron don kuwa kusan sha biyar tayi posting lokaci guda, tabbas kuwa ba lallai a samu wanda yayi farin ciki da haihuwar nan sama da ita ba.
Ba su suka bar asibitin ba sai wuraren Maghrib. Suna komawa suka yi wanka kana suka wuce part ɗin Mommah wacce ta dawo tuntuni don haɗa abincin da za a kai. A nan suka yi sallah suka ci abinci sannan kowacce ta kama waya kamar abun gadara, ita dai Zahrah ta kama sofa ta make sai aikin editing picture ɗin babyn take yi tana haɗawa da pictures nata, tana zaune sai da ta haɗa kusan videos goma, ta tsaya ne sakamakon wayar Yaya Ishaq da ta shigo, gajeren murmushi ta saki tare da picking bakinta ɗauke da sallama.
Bayan ya amsa mata ta gaida shi cike da girmamawa.
Murya ƙasa-ƙasa tace “Sai yanzu ka tuna da Ni yau ko?”
“Ina na isa cutie am, wallahi ayyuka ne yau suka min yawa kinga ƙarshen wata ya yi.” a shagwaɓe kamar za ta yi kuka tace “Uhm shine to ko sau ɗaya ba za ka kira Ni ba?”
“I'm sorry my love, in kin ce kina son gani na ma yanzu zan ajiye aikin da nake na zo.”
“Uhm uhm shikenan Yaya, ba sai ka zo ba.”
“Yauwah thank you my baby doll, I love you.” a kunyace tace “Uhm nevermind Yaya na.”
“Ba za kice kema kina so na ba Cutie?”
A shagwaɓe tace “Uhm uhm Ni fa ba haka bane Yaya, ba ma wannan ba fushi nake da kai.”
“Fushi kuma My queen?”
“Uhm” ta ba shi amsa a gajarce.
A ɗan ruɗe yace “Subhanallah, hankali na ya tashi, me nayi Wa Queen haka?”
Cike da shagwaɓa tace “Uhm ba kai ne ba ka taya Ni murna ba yau An haifa min Baby ”
“Ma sha Allah My queen, ai ban sani ba, babyn waye hala?”
“Matar Yaya na da ya rasu ce ta haihu, ka ga babyn?”
“No...shine ba ki sanar da Ni ba?”
“To ai kaine ba ka kira Ni ba yau throughout”
“I'm sorry my Queen, yanzu dai gobe I'll be coming to see the baby, shikenan?”
Bakinta ta ɗan tura kamar tana gabansa tace “Uhm shikenan”
Ganin yau rigimarta mai sauƙi ce yasa ya tabbatarwa kansa irin don da take wa Babyn musamman da ya tuna yadda suke waya kullum, she always tends to be naughty, ba ta taɓa bari suyi hirar kirki, amma duk da haka he still loves her, so mai tsanani yake mata, gani take kamar in ba ita ba....
Babu laifi yau ta ɗan sake masa, bayan sun yi hanging call ɗin Zakiyya ta sa ta gaba da tsokana “Ana so ana kaiwa kasuwa” ita dai Zahrah ba ta kula ta ba sai ma mayar da hankalinta da tayi kan abun da take. Tana gamawa tayi posting ɗaya a tiktok....likes kam ta sha su, haka nan comments ma ba a magana kowa sai santin Babyn yake yi, cikin comments ɗin ne taga wata user ta yi comment da “Ɗan bugun zuciyata kenan, ka kusa ka bi ubanka yadda ya tafi tare da tsinanniyar uwarka.”
Mamaki fal ran Zahrah game da wannan comment, tabbas comment ɗin ya tsaya a ranta, kuma ta yi alƙawarin gano ko ma wane ne, idan kuwa furucin da aka yi ya zama gaskiya sai yadda ƙarfinta ya ƙare. (Kun ji fa future Barrister har an fara aiki tun yanzu.)
Washegari su Yaya Ishaq ma suka je har asibitin suka duba Baby, Yaya Khalil ma ya sanar da sauran friends ɗinsu and the promise to attend the naming ceremony, sun kuma yanke shawarar yaron ya zama under their custody.
A yau kam dai jikin Aunty Mabruka da sauƙi musamman da ta kalli babyn da ta haifa, haka za ta sa shi gaba da kallo ko shayar da shi take. Yanayin sauƙin da aka gani tattare da ita yasa aka yi discharging nasu. Bayan sun koma gida Mamah da Mommah suka kasa suka tsare Baby, Babu wani mahaluki da zai ɗauke shi ba tare da idanunsu na kansa ba gudun kada a cutar da shi musamman yanzu da suke hasashen cewa akwai Bara gurbin a cikin familyn. Zahrah kuwa da ta dawo daga school zata wuce can, bacci ne ko idan yaron yayi kuka ta miƙa wa uwarsa ke mata shamaki da shi.
Kwanan yaron huɗu a duniya su Alhaji Baba suka diro Nigeria. Kar ku so kuga yadda suka yi farin ciki sosai, addu'a da wannan yaro ya sha ta kamar me, soyayya kuwa ana nuna masa ta kowanne ɓangare, yaro kam ba dai farin jini ba, har zuwa wannan rana dai ba a yi wa yaron laƙani ba har sai da Alhaji Baba ya huta kana aka kai shi wurinsa. A nan ya masa addu'a sannan ya ɗaura da “Ubangiji ya Raya Aliyu Sadauki, yasa yayi koyi da ɗabi'un Sayyidina Ali, ya kuma yi halin marigayi Yaya Sadauki.” daga haka ya miƙawa Yaya Qasim shi yana faɗin “Ku sa wa ɗanku albarka, Khalil ga shi ko”
Lokacin da Yaya Khalil ya karɓi little Sadauki haka ta tsira masa idanuwa, har da ƴar ƙwallarsa tukun ya miƙawa mamarsa ɗan ta. Nan aka fara shirye-shiryen suna. Alhaji Baba me yayi fixing ranar juma'a a matsayin ranar da za a yi walimar, A wannan karan Alhaji Baba da kansa yasa aka sanar da kowa cewa bai ɗaukewa kowa halartar wannan walima da za a yi wa yaron ba, kowa ya tabbatar ya zo. Washegari kuwa Yaya Junaid ya diro Nigeria shi da iyalinsa.
*D day (Friday...)*
Ƙayatacciya kuma ƙasaitacciyar walima aka shirya, mahaifiyar yaro da yaro aka shirya su cikin shiga ta alfarma, kowa ka gani cikin familyn murna yake banda Mami wacce ke jin takaicin uwa da yaron, da yanzu wannan yaro ɗan Kausar ɗinta ne, abu mafi ban haushi yanzu wannan yaro da uwarsa su za su gaji dukiyar Uban. Wannan dalilin shi ya hana Mami zuwa walimar, ƴaƴanta kuma suka mata kunnen uwar Shegu suka je ban da Kausar da huɗubar uwar tayi tasiri akanta.
Amir dai duk irin rashin mutuncin da ta tsulawa Mommah yanzu sai Binta take tana don komawa jikinta saboda abun duniya, ta halarci taron ita da ƴaƴanta, duk taurin rai da baƙar zuciya irin ta Rumana ta halarci taron. A wurin taron sosai Aunty Mabruka ta samu kyaututtukan gaske daga wurin ahalinta. Tabbas wannan Little Sadauki da farin jininsa yazo duniya, abokan Yaya Khalil ma ba a bar su baya ba sun nuna bajintar su, yaya Ishaq da Mom ma dai sun kawo nasu gifts ɗin tunda suka san matsayin Babyn da mahaifinshi a familyn, sosai shagalin ya ƙayatar.
A wannan karan Prince Bello dai cewa yayi ba zai tafi ba sai ya zuba soyayyarsa zuciyar Zahrah, hakan yasa sai da ya nemo ta suka ɗan keɓe, a lokacin bai yi ƙasa a guiwa ba ya fallasa asirin zuciyarsa ga Zahrah tare da ajiye ƙoƙon bararsa gabanta, ba tayi rejecting nasa ba amma ta faɗa masa gaskiyar cewa akwai wanda yanzu haka suke tare kuma ba za ta iya cin amanarsa ba, amma haka Prince ya dake yace “Babu damuwa, ai mace allura ce cikin ruwa, mai rabo kan ɗauka, idn ya yi nasara kaina zan haƙura tunda haka Allah yayi, idan kuma Ni na yi nasara kansa same thing.”
Haka ya ɗan ja Zahrah da hira har ta ɗan sake da shi, daga ƙarshe ya amshi Numbern ta. Duk wannan tsayuwar da suka yi ashe Yaya Ishaq ya ƙira Numbern Zahrah sau ba adadi amma ba ta ga ba coz wayanta na silent. Yana cikin tafiya kawai ya hango ta tare da wani Guy, nan zuciyarsa ta zafafa ta yi ɗumi, Zahrah da wani?, da ƙyar dai ya rarrashi kansa ya wuce salin alin ya bar gidan.
Wani abu da ya kuma faruwa ashe lokacin da Zahrah ke tsaye da Prince Bello idanun Rumana da su Hibba na kansu, baƙin ciki ya taru ya yi wa Rumana katutu a zuciya musamman da take ganin komai na duniya daga zuwan wannan ballagazar yarinyar ya tsaya mata, abun haushi ma duk abun da ta ƙaunata ba zai so ta ba sai dai ya so shegiyar, ƙwafa ta ja tare da barin wurin a fusace ta koma part ɗinsu..
Bayan an gama taro lafiya kowa ya watse, su Aunty Mabruka ɗiyar Mamah ta wuce part ɗin Hajjaty wanda zuwa yanzu ya koma gidansu, bayan ta koma ta cire uban kayayyakin da ta saka kana ta shiga wanka, tana bayi kawai ta jiyo kukan Little Sadauki, ai babu shiri ko ɗauraye jikinta ba ta yi ba ta ɗauri towel ta fito. Me za ta gani, wata mata ce ko mutum oho fuska rufe ya ɗauke shi, yana shirin danne masa ƙofofin numfashi da hannunsa Aunty Mabruka ta cilla ihu tana faɗin “Jama'a ku taimako min za su kashe shi wallahi.”
Sai dai kafin wannan mutum ya